Tsakanin Dan Adam Da Kudi Ta Alhaji Audu Wazirin Danduna

    Sauraro Da Rubutawa

    Shu’aibu Murtala Abdullahi

    Mu duba tsakanin d’an Adam mu gani,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.
     

    Had dai mu lura tsakanin d’an Adam mu gani,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Bari in lek’a tsakanin d’an Adam in gano,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Abdul tsaknin d’an Adam in gani,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    An dubi tsakanin d’an Adam in gano,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ai mu lek’a tsakanin d’an Adam da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Yanzu ba wata harka sai kana da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Saboda ba ka sawa sai kana da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Kuma ba ka hanawa sai kana da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Zamani ya zo sai kana da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ba ka komai sai kana da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ba ai maka komai sai kana da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Kuma ka kan gaza komi in kana da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Kana iya komai don saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Kuma kakan gaza komai don saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Akan shiga kunya ma saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Akan fita kunya ma saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ba ka sawa sai kana da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Kuma ba ka hanawa sai kana da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Allah ya Allah hi ba mu kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Allah don Allah ka ba mu kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Tsakanin d’an Adam d’an Adam,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Yanzu du wata harka sai kana da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Hakanga ba ka da girma sai kana da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ana janye huld’a saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Kuma akan sabon harka saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ana d’ebo rigima saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ana warre rigima saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ana wasu hud’d’od’i saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ana wasu harka don saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ana janye harka saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Yanzu ba ka komi sai kana da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Kai ko girma ma sai kana da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Kuma akan yi rashin girma saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Kai mu duba tsaknin d’an Adam mu gani,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ana zare ido saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ka ga mutum yana limshe ido saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Yanzu duk wata hud’d’a sai saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Mu duba tsakanin d’an Adam mu gani,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ummh! Kud’ii!

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Aaag! Kud’ii!

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    D’an Adam d’an Adam,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Kai d’an Adam D’an Adam,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ku tausa kalangunku saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Yaraaa kui anshi saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ni ma ga shi ina wak’a saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ana sake tahiya saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ka ga mutum yana d’ebo sauri saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ana k’aura da gudu saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Akan ruga da kud’i saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Mutum yana ruga da gudu saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ana tafiya sannu saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Yanzu duwata had’d’a sai saboa kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Kai muduba tsakanin d’an Adam d’an Adam,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Mutum yak an saki matatai saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Tsakanin d’an Adam da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Kuma ana sabon aure saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ana k’aramar murya saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Kanshentama ana wasan ‘bugu saboa kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ka ga mutum yana wasan ‘buya saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ana maganar surri saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ana d’ebo rigima saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ana kai naushi saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Mutum yakan saki matarsa saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ana sabon aure saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Yanzu dubi wata hud’d’a sai kana da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Kai komai ma sai kana da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Yanzu ba ka mutane sai kana da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Jama’a suna damunka idan kana da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Jama’a suna damunka idan kana da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Kuma ba ka ganin kowa saboa kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Yanzu komai za ka yi sai kana da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ya Allah ka ba mu kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Mutum ya mik’e k’ahwahu in yana da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ya zauna yay hutu saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ana yajin aiki saboa kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Akan koma aiki saboa kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ana d’aukam magana saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

     

    Ana k’in magana saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    ana k’in magana saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Kai mu duba tsakanin d’an Adam mu gani,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Yanzu dubi wata hud’d’a sai kana da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Dan ba ka iya komai sai kana da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Kai duba tsakanin d’an Adam d’an Adam,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Kud’ii!

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Abh! Kud’ii!

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Duk wata harka sai kana da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ba ka iya komai sai kana da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Yanzu komi za kai sai kana da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Zamani ya canzaa sai kana da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    K’aramin yaro saboa kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Kaga anai masa ban girma saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ka ga ana korar k’ato saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ana son mummuna saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ka ga ana k’in kyakkyawa saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Kai akan so mummuna saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ka ga ana k’in kyakkyawa saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ana aurar gurgu saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ana k’in mai k’afa saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Yanzu duw wata hud’d’a sai kana da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    K’allau kake saboda kana da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Yanzu komi za ai sai saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Kai maduba tsakanin d’an Adam mu gani,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Yanzu duw wata harka sai kana da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Gama ba ai maka komai sai kana da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ba ka iya komi sai kana da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Mu duba tsaknin d’an Adam d’an Adam,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ooh! Kud’ii!

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ooy! Kud’ii!

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Tsakanin d’an Adam da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Mu duba tsaknain d’an Adam da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ko gidanka ba ka da girma sai kana da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Gama ba kai musu tsawa sai kana da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ba su jin maganarka sai kana da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Sai Alhaji ya zo sai kana da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Alhaji ko ba ya nan don saboda klud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Kai mu duba tsakanin d’an Adam d’an Adam,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Yanzu dud wasu hud’d’od’i sai saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Jama’a ya Allah ba mu kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Jama’a ya Allah ya ba mu kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ana iya komai sai saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ana iya ‘batawa saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ana iya shiryawa saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Kai ma mutum ya daddaki matarsa saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Kai mu duba tsakanin d’an Adam mu gani,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Kai mu duba tsakanin d’an Adam mu gani,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Yanzu duw wata hud’d’a sai kana da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Kakan zama babba wa saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ana babban yay saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ana k’in yanyenma saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Yanzu komai za ai sai kana da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ba ai maka komai sai kana da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ana turka-turka saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    ka ga mutum ya janye wando d’an saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ana ma kai naushi saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Mu duba tsakanin d’an Adam mu gani,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Mutum yana kallon banza saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Mutum yana d’iban fara’a saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ka ga mutum ya kaure ma huska saboa kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ana sakin fuska saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Mu duba tsakanin d’an Adam mu gani,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Mu duba tsakanin d’an Adam mu gani,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Yau kud’i mai sa fad’a uba,

    Kud’i mai sa fad’a da uwa,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Yara tsakanin d’an Adam d’an Adam,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Mu duba tsakanin d’an Adam mu gani,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Yara ku ruttumi gangarku saboa kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Tsakanin tsanin d’an Adam da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ku duka kalangun nan saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ku kuma kui anshi saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Dan ni ga ni ina wak’ar saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Kai mu duba tsakanin d’an Adam d’an Adam,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Yanzu duw wata hud’d’a sai saboda kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ba ai maka komai sai kana da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Mu duba tsakanin d’an Adam mu gani,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Tsakanin d’an Adam,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Yanzu du hud’d’od’i sai kana da kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

    Ya Allah ka ba mu kud’i,

    Tsakanin d’an Adam da kud’i.

     

     

     

     

     

     

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.