Ticker

6/recent/ticker-posts

Wakar Tanimu Dangaliman Kyadawa Ta Alhaji Musa Danba’u Gidan Buwai

Sauraro Da Rubutawa

Hirabri Shehu Sakkwato

08143533314

Amshi: Dogo kana da shirin yak’i,

Tanimun na Alhaji Yakuba.
 

Jagora: K’ara hank’uri kar ka ji komai,

Hank’urinka shi nak kai ka haka,

Hak ka yi ciyaman k’asar Gada,

Kak kada biri sarkin k’walama,

Ci k’urgunguma a ci buzuzu,

Nac ce biri a yi a hankali,

Yara:   Wata ran cikinka yana baci.

 

Amshi: Dogo kana da shirin yak’i,

Tanimun na Alhaji Yakuba.

 

Jagora: Kai dai rik’a k’warai don kada ka sake,

In don mazan yau sun katce,

Yara:   Suna son ta’ba ka suna shakka.

 

Amshi: Dogo kana da shirin yak’i,

Tanimun na Alhaji Yakuba.

 

Jagora: Kai dai rik’a k’warai dan kada ka sake,

In don mazan yau mata ne,

Yara:   Suna son ta’ba ka suna shakka.

 

Jagora: Dogo,

Yara:   Suna son ta’ba ka suna shakka.

 

Jagora: Wa su nan.

Amshi: Dogo kana da shirin yak’i,

Tanimun na Alhaji Yakuba.

 

Jagora: Ranar za’ben Gada ‘Danba’u,

Ban gani ba labari naj ji,

Wad’ansu maza sun ji azaba,

Wani ya bar hula da agogo,

Wani kau ya mance gilashi nai,

Wasu kau sun d’auko k’ahwahunsu,

Yara:    Can sun ka mance kubuttansu.

 

Amshi: Dogo kana da shirin yak’i,

Tanimun na Alhaji Yakuba.

 

Jagora: Dogo kana da shirin yak’i,

Tanimun na Alhaji Yakubu.

 

Amshi: Dogo kana da shirin yak’i,

Tanimun na Alhaji Yakuba.

 

Jagora: Kowa da abin da yake sauna,

Kowa da abin da yake tsoro,

Kusa kyanwa yaka jin tsoro,

In ga kura a cikin gari,

Yara: Aura ba za ya hitowa ba,

 

Jagora: A ina ga kura a cikin gari,

Yara:   Aura ba za a ya hitowa ba.

 

Amshi: Dogo kana da shirin yak’i,

Tanimun na Alhaji Yakuba.

Jagora: K’ara hank’uri kar ka ji komai,

Hank’urinka shi nak kai ka haka,

Hak ka yi ciyaman k’asar Gada,

Kak kada biri sarkin k’walama,

Ci k’urgunguma a ci buzuzu,

Nac ce biri a yi a hankali,

Yara: Wata ran cikinka yana ‘baci.

 

Amshi: Dogo kana da shirin yak’i,

Tanimun na Alhaji Yakuba.

 

Jagora: Ni munahukin Gada na san shi,

Don bak’in jininai ya yi yawa,

D’azu ya wuce mu muna hira,

Sai nij ji yara suna ihu,

Yada nij ji ana kard’a-kard’a,

Nac ce gudun ga na aura ne.

Yara:   Shi bai yawo a cikin Gada,

Kuma bai shiri da mak’wabtansa.

 

Amshi: Dogo kana da shirin yak’i,

Tanimun na Alhaji Yakuba.

 

Jagora: Na gode Muhammam Musa,

Yara:    Dun yadda yai muna ya kyauta.

 

Jagora: A gaishika Muhamman Musa,

Yara:    Du yadda yai muna ya kyauta

 

Jagora: A Isuhu Musa na gode ma,

Yara:    Da yanda yai muna ya kyauta.

Jagora:  A sarkin mota ciyama ya yi d’a,

Yara:     Du yadda yai muna ya kyauta.

 

Jagora:  A ina Halilu sarkin mota,

Yara:     Du yadda yai muna ya kyauta.

 

Jagora:  A janar sakatare na gode ma,

Yara:     Du yadda yai muna ya kyauta.

 

Jagora: A sakataren Gada ban rena ba,

Yara:   Du yadda yai muna ya kyauta.

 

Jagora: Sai godiya nikai gu DPM,

Haji Garba Bashar ka kyauta man,

Yara:    Du yadda yai muna ya kyauta.

 

Amshi: Dogo kana da shirin yak’i,

Tanimun na Alhaji Yakuba.

 

Jagora: ‘Yan yara mu je Gada in kwana,

Haji Bak’o Alhaji ya gode,

Yara:     Du yadda yai muna ya kyauta.

 

Yaro:   Kai Alhaji Musa ‘Danba’u,

Ko cikin maza ka tuna mata,

Ga ‘yabbagadai sarkin yak’i,

Yara:  Du yadda tai muna ta kyauta,

 

Yaro: A ga ‘yanbagadai sarkin yak’i,

Du yadda tai muna ta kyauta.

 

Jagora: A na gode Taladan garin gada,

Yara:    Du yadda tai muna ta kyauta.

 

Jagora: A na gode Taladan a can gada,

Yara:    Du yadda tai muna ta kyauta.

 

Jagora: In Hajiya Kulu Rungumi na gode,

Yara:   Du yadda tai muna ta kyauta.

 

Amshi: Dogo kana da shirin yak’i,

Tanimun na Alhaji Yakuba.

 

Jagora: In Haji Buda na Wauro na gode,

Yara:   Du yadda yai muna ya kyauta

 

Jagora: A Haruna Kabera Muzakkari,

Yara:    Du yadda yai muna ya kyauta

 

Jagora: A in tunu da baban ‘Danba’u,

Haji Ila Gada sannu da hwama,

Yara     Du yadda yai muna ya kyauta

 

Jagora: A in tunu da baban ‘Danba’u,

Haji Ila Gada sannu da yak’i,

Yara:   Du yadda yai muna ya kyauta

 

Yaro: A kid’an ga kid’an yak’i nai ma,

D’au garkuwa da takobinka,

Ko wa gaya maka bai kai ba,

Kai ma ka ce masa ba shi ba,

Kowa gaya maka ya shirya,

Kai ma ka ce masa ka shirya,

Don duniya haka ta saba,

A lokacin wani ya kwanta,

Yara:  A lokacin wani zai tashi.

 

Jagora: A du lokacin wani ya kwanta,

Yara:   A du lokacin wani zai tashi.

 

Jagora: Dogo kana da shirin yak’i,

Yara:   Tanimu na Alhaji Yakubu.

 

Jagora: A Haji Garba na Alhaji Yakubu,

Yara:    Du yadda yai muna ya kyauta

 

Jagora: A mu gaida Murtala birnin Wauro,

Yara:    Du yadda yai muna ya kyauta

 

Jagora: A hwanarablil Duwa na gode mai,

Yara:    Du yadda yai muna ya kyauta

 

Jaogra: A Dogo kana da shirin yak’i,

Tanimun na Alhaji Yakubu,

 

Yara: A Dogo kana da shirin yak’i,

Tanimun na Alhaji Yakubu.

https://www.amsoshi.com/2018/01/16/wakar-aliyu-magatakarda-wamakko-mai-suna-gwamnanmu-mun-yi-mun-kare-ta-alhaji-musa-danbau-gidan-buwai/

Jagora: Nai rok’o ‘Danba’u wajenka Tanimun na k’ara,

Dauda k’iri nike kallo ka ba shi wuri nai ya dace,

Na so a hidda d’an gwadda mai ja,

Yara:    Mun gane bai muna alheri.

 

Amshi: Dogo kana da shirin yak’i,

Tanimun na Alhaji Yakuba.

 

Jagora: A in kun yi mitin kuma kun k’are,

Don Allah kira Dauda k’iri,

Ka san aiki nai dattijo,

A ba shi babban aikinai,

Tunda wurinai ya saba,

A hid da wanga hwarin doki,

Yara:  Don na ga bai muna alheri.

 

Jagora: A kai a hid da wanga hwarin doki,

Yara:   Mun gane bai muna alheri.

 

Post a Comment

0 Comments