Ticker

6/recent/ticker-posts

Wakar Alhaji Musa Lumu Ta Alhaji Musa Danba’u Gidan Buwai

Sauraro Da Rubutawa

Hirabri Shehu Sakkwato

08143533314

Amshi: Gwaron giwa kullun yana halin yabo,

Alhaji Lumu Musa ciyaman zarumi.

Jagora: Mu tafi Gwadabawa,

Musa ciyaman ya kiran,

Yara:   Ina a gida na don ban zuwa sai an kiran.

Amshi: Gwaron giwa kullun yana halin yabo,

Alhaji Lumu Musa ciyaman zarumi.

Jagora: K’asar Gwadabawa,

Mu mun yi babban arziki,

Don mun ije kunkuru mai idanu kakkahe,

Yara:   Kai bari d’an tulluk’i ba a yin komai da kai.

Amshi: Gwaron giwa kullun yana halin yabo,

Alhaji Lumu Musa ciyaman zarumi.

Jagora: Wane an kashe shi sai ya tcira min tcegumi,

Mai babban gaba mig gami na ni da kai,

Yara:     Ka isko ni gida ka ce za ka tungatci da ni.

Amshi: Gwaron giwa kullun yana halin yabo,

Alhaji Lumu Musa ciyaman zarumi.

Jagora: Mutan Gwadabawa akwai tambaya ni da ku,

Mutan Gwadabawa akwai tambayata ni da ku,

Don Allah rak’umi na garin ko ba ya nan,

Sai suka ce rak’umi ai yana nan zumbuge,

Yara:   Bai iya tahiya cinai sun kare sai rarrahe.

Amshi: Gwaron giwa kullun yana halin yabo,

Alhaji Lumu Musa ciyaman zarumi.

Jagora: Bak’a akuya wance ke ad da k’allalen k’aho,

Ban layya da ke kuma ba mu yin suna da ke.

Yara:    Mu ba mu sayen labari masu yin tsahi su sai.

Jagora: Umaru sarkin maguri babban bak’o kake,

Yara:    Maza ba su kamakka ko su ishe wa ba su ja.

Amshi: Gwaron giwa kullun yana halin yabo,

Alhaji Lumu Musa ciyaman zarumi.

Jagora: Ina Alhaji Audu D’anhwaransi ya taimaka man,

Yara:    Ban rena mai ba hairan yakai ya taimaka.

Jagora: Ina D’an Nakaduna Audu babban bak’o kake,

Yara:   Ban rena mai ba hairan yakai ya taimaka.

Jagora: A sarkin rwahii abin da ka yi mani ka biya ni,

Yara:    Ban rena mai ba hairan yakai ya taimaka.

Amshi: Gwaron giwa kullun yana halin yabo,

Alhaji Lumu Musa ciyaman zarumi.

Jagora: Baba sarkin rwahi ubanmu na gode ma k’warai,

Ban rena mai ba hairan yakai ya taimaka.

Jagora: Mai tasa Haji Umaru Ghana da godiya,

Yara:   Ban rena maiba haira  yakai ya taimaka.

Jagora: A na gode ma ciyaman Haji Sani a ka

Ubangidana ‘ya taimaka man,

Yara:   Ban rena mai ba hairan yakai ya taimaka.

Jagora: Alhaji Sani a ka nidai kai k’ok’ari,

Yara:    Ban rena mai ba hairan yakai ya taimaka.

Jagora: Ana gode Zubairu S. Magori yai taimako,

Yara: Ban Ban rena mai ba hairan yakai ya taimaka.

Jagora: Mu je magina in ga maigidana,

Mamman uban gidana ya san da ni,

Yara:   Ban rena mai ba hairan yakai ya taimaka.

Jagora: A Mamman D’anbarno za ni magina in gai da shi,

Yara:   Ban rena mai ba hairan yakai ya taimaka.

Yaro: Haji ‘Danba’u akwai tambaya ta ni da kai,

Yaran Musa akwai tambayata ni da ku,

Marok’an Musa akwai tambayara ta ni da ku,

Shin don Allah ina mai hwad’in sai ya bugan?

Wani d’an kutu’bi bak’i mai idanun raguna,

To na zage ka.

Yara:  Komai kakai man sai ka yi.

Jagora: Wane yau na zage ka,

Yara:    Komai kakai man sai ka yi.

Amshi: Gwaron giwa kullun yana halin yabo,

Alhaji Lumu Musa ciyaman zarumi.

Jagora: Mu je Gwadabawa Musa ciyaman ya kiran,

Yara:    Ina a gida na don ban zuwa sai an kiran.

Amshi: Gwaron giwa kullun yana halin yabo,

Alhaji Lumu Musa ciyaman zarumi.

Jagora: A d’an Amadu baba jikan Alu namijin tsaye,

Yara:    Rik’a a sakamma duk masu ja sun barkace.

Jagora: Ina Bello Magaji na yaba maka kai k’ok’ari,

Yara:    Ban rena mai ba hairan yakai ya taimaka.

Jagora: Ciyaman na Tangaza ina Musa Ausa

Koyaushe ba kud’i yakai,

Yara:   Ban rena mai ba hairan yakai ya taimaka.

Jagora: Ina Haji Aminu Garkuwa ka kyauta k’warai,

Yara:    Ban rena mai ba hairan yakai ya taimaka.

https://www.amsoshi.com/2018/01/16/wakar-alhaji-aliyu-magatakarda-wammako-ta-alhaji-musa-danbau-gidan-buwai/

Amshi: Gwaron giwa kullun yana halin yabo,

Alhaji Lumu Musa ciyaman zarumi.

Jagora: Inda sai godiya nikai ma injin nik’a,

Ban rena mai ba hairan yakai ya taimaka.

Jagora: A Bashiru Gigane uban gidan ‘Danba’u kake,

Yara:    Ban rena mai ba hairan yakai ya taimaka.

Jagora: A na gode Mairi Turd’a tanai man k’ok’ari,

Yara:   Ban rena mar ba hairan takai ta taimaka.

Jagora: A na gode Bara’atu ‘Yar Audu da godiya,

Yara:   Ban rena mar ba hairan takai ta taimaka.

Amshi: Gwaron giwa kullun yana halin yabo,

Alhaji Lumu Musa ciyaman zarumi.

https://www.amsoshi.com/2018/01/16/wakar-jamiyyar-pdp-ta-alhaji-musa-danbau-gidan-buwai/

Jagora: Akwai magana yara sai na fad’i na jaddada,

Kai ‘Danba’u halan ka yi gwajen A’isha?

A’isha tawa ni na yabamat tabiya,

Yara:    Ban rena mar ba hairan takai ta taimaka.

Jagora: Sanusi Wali Sanusi ka taimaka k’warai,

Yara:   Ban rena mai ba hairan tak’aita tamaka.

Jagora: A A d’an Amadu baba jikan Alu namijin tsaye,

Yara:    Rik’a a sakamma duk masu ja sun barkace. ×3

Jagora: A gyare-gyare Mu’azu,

Yara:    Allah dad’a mai arziki,

Jagora: A bara har jaki ya ban yai tuma sai ni sakai.

Amshi: Gwaron giwa kullun yana halin yabo,

Alhaji Lumu Musa ciyaman zarumi.

Post a Comment

0 Comments