Ticker

6/recent/ticker-posts

Wakar Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko Mai Suna: Mai Ban Tsoro Magatakarda Wamakko Ta Alhaji Musa Danba’u Gidan Buwai

Sauraro Da Rubutawa

Hirabri Shehu Sakkwato

08143533314

Amshi: K’ara shirawa,

Aliyu za’ba’b’ben gwamna,

Mai ban tsoro magatakarda Wamakko,

Sarkin Yamman Sakkwato bai san wargi ba.
 

Jagora: Na gaya wa mutane d’auke dafi sai giwa,

Yara:    Maza tahi kauce zomo ba ka iyawa wa kai nan?

 

Amshi: K’ara shirawa,

Aliyu za’ba’b’ben gwamna,

Mai ban tsoro magatakarda Wamakko,

Sarkin Yamman Sakkwato bai san wargi ba.

 

Jagora: Ali d’an Lamid’o Ali uban Lamid’o,

Baba jikan Umar Sakkwato yau ta zama taka,

Yara:    Wahidun Allah mai ida nuhi kai yab baiwa.

 

Amshi: K’ara shirawa,

Aliyu za’ba’b’ben gwamna,

Mai ban tsoro magatakarda Wamakko,

Sarkin Yamman Sakkwato bai san wargi ba.

 

Jagora: Na sani Allah shi ka ba da mulki ya ba ka,

Don kak ka bi shawara katan keke,

Mai son a k’i wa kowa komai,

Yara:   D’an Barade Alu kai ta wa mutane adalci.

 

 

Amshi: K’ara shirawa,

Aliyu za’ba’b’ben gwamna,

Mai ban tsoro magatakarda Wamakko,

Sarkin Yamman Sakkwato bai san wargi ba.

 

Jagora: Mun sani Allah shi ka ba da mulki ya ba ka,

Don kak ka bi shawara buhun kowa,

Mai son a k’i wa kowa komai,

Yara:    D’an Barade Alu kai ta wa mutane adalci.

 

Jagora: Don Allah d’an Barade Alu,

Yara:    Kai ta wa mutane adalci.

 

Amshi: K’ara shirawa,

Aliyu za’ba’b’ben gwamna,

Mai ban tsoro magatakarda Wamakko,

Sarkin Yamman Sakkwato bai san wargi ba.

 

Jagora: Mugun madambaci kake Ali,

Baba da kat tattako ka bugi bakin dogo,

Yat tahi ba ban kwana,

Yara:   Bar maganar guntu shi hag ga cikinai ya rude.

 

Jagora: In ka ji k’i gudu ‘Danba’u,

Sa gudu ne ab bai zo ba,

Ranaz za’benka d’an Barade na Wamakko,

Wad’ansu maza hay Yamai suna ‘boyo,

Yara:    Kahin a yi za’be sun tcere.

 

Amshi: K’ara shirawa,

Aliyu za’ba’b’ben gwamna,

Mai ban tsoro magatakarda Wamakko,

Sarkin Yamman Sakkwato bai san wargi ba.

 

Jagora: Wad’ansu maza sun yi rantsuwa kama sun k’ara,

Sun ce maka d’an Barade ba ka zama gwamna,

Allah ya yarda yau Alu ka zama gwamna,

Bamaguje kai kuma ya za ka yi zance kokonka,

Yara:   Du hatcin Sakkwato kaf ba su cire mai kahwara.

 

Amshi: K’ara shirawa,

Aliyu za’ba’b’ben gwamna,

Mai ban tsoro magatakarda Wamakko,

Sarkin Yamman Sakkwato bai san wargi ba.

 

Jagora: Tauraron gabas mijin Arziki gaishe ka na Murja,

D’an Garba farin wata Ali,

Yara:    Ka iske mutanen birni har da mutanen k’auyuka.

 

Amshi: K’ara shirawa,

Aliyu za’ba’b’ben gwamna,

Mai ban tsoro magatakarda Wamakko,

Sarkin Yamman Sakkwato bai san wargi ba.

 

Jagora: Wane Sakkwato sun d’au kai mutumin kirki,

Dab baya ya yi lalata yat tabka abin kunya,

Yara:    Dan nan daraja tai tah hwad’i. ×3

 

Jagora: Mun gane shi mutunci madara ne,

Da ya zube a k’asa,

Yara:    Ban san wani mai kwasa tai ba ×2

 

Amshi: K’ara shirawa,

Aliyu za’ba’b’ben gwamna,

Mai ban tsoro magatakardan Wamakko,

Sarkin Yamman Sakkwato bai san wargi ba.

 

Jagora: Ji wane d’an hwad’in rai,

Wai bai bid’ar sanata,

Shugaban k’asa yaka so,

Bana ya yi bakan-bak’antantam,bai yi firesidan ba,

Kuma nan ga jaha tai ya hwad’i,

Ba zama Sakkwato,

Yara:   Sai dai ya tsaya kwatano,

Ko kuma ya wuce birnin Ghana.

 

Jagora: Wane ba zama Sakkwato,

Yara:    Sai dai ya tsaya kwatano,

Ko kuma ya wuce birnin Ghana.

 

Jagora: Yanzu ba zama binni,

Yara:    Sai da ya tsaya kwatano,

Ko kuma ya wuce birnin Ghana.

 

Amshi: K’ara shirawa,

Aliyu za’ba’b’ben gwamna,

Mai ban tsoro magatakardan Wamakko,

Sarkin Yamman Sakkwato bai san wargi ba.

 

Jagora: Mai jama’as siyasa,

Bana ya hwad’i ina magana?

Dan sakandare ya kasai ya shiga sabati,

Yara:    Bana ko magana tai ya noce.

 

Amshi: K’ara shirawa,

Aliyu za’ba’b’ben gwamna,

Mai ban tsoro magatakardan Wamakko,

Sarkin Yamman Sakkwato bai san wargi ba.

 

Jagora: Na difiti gwamna Muntari d’an Shehu,

Zaki na Alu A.A. na baba D’anda birnin Mana,

Kar ka ji tsoro,

Yara: Sa arna su shira kai ka shirya.

 

Jagora: Na baba D’anda birnin Mana ban da sakewa,

Yara:    Sa arna su shira kai ka shirya.

 

Amshi: K’ara shirawa,

Aliyu za’ba’b’ben gwamna,

Mai ban tsoro magatakardan Wamakko,

Sarkin Yamman Sakkwato bai san wargi ba.

 

Jagora: Gaisheka shugaba na matasa binni,

Har k’auye gaishe ka Itali,

Yara:    Mai kwana da shiri ranar yak’i.

 

Amshi: K’ara shirawa,

Aliyu za’ba’b’ben gwamna,

Mai ban tsoro magatakardan Wamakko,

Sarkin Yamman Sakkwato bai san wargi ba.

Jagora: Ahmed Aliyu ya ban mota saboda jin dad’i,

Yara:    Domin darajar sabon gwamna.

 

Amshi: K’ara shirawa,

Aliyu za’ba’b’ben gwamna,

Mai ban tsoro magatakardan Wamakko,

Sarkin Yamman Sakkwato bai san wargi ba.

 

Jagora:D’an da gabas ga Sakkwato gaishe Haji Gwanda Gobir,

Yara:   Bai maganar banza in yai magana ta bat tashi.

 

Amshi: K’ara shirawa,

Aliyu za’ba’b’ben gwamna,

Mai ban tsoro magatakardan Wamakko,

Sarkin Yamman Sakkwato bai san wargi ba.

 

Jagora: Ambasada a gaishe ka,

Gai da Haji Ladan Shuni,

D’an masanin Sakkwato,

Yara:   Mai hora marasa imani.

 

Amshi: K’ara shirawa,

Aliyu za’ba’b’ben gwamna,

Mai ban tsoro magatakardan Wamakko,

Sarkin Yamman Sakkwato bai san wargi ba.

 

Jagora: Muntari baba maigona,

D’an Bello uwa yak’i,

Ku an ka sani bunni,

Ku an ka sani k’auyukka,

Yara:   Tun ana yak’i an san da mutanen Yarlar’be.

 

Jagora: Yanzu ko ana yak’i,

Yara:   An san da mutanen Yarla’be.

 

Amshi: K’ara shirawa,

Aliyu za’ba’b’ben gwamna,

Mai ban tsoro magatakardan Wamakko,

Sarkin Yamman Sakkwato bai san wargi ba.

 

Jagora: Sai godiya ciyaman fati Arzika na gode,

Yara:    Du yanda ya kai man ya kyauta.

 

Jaogra: A gaida tsalha Sidi Alhaji ya gode,

Yara:    Du yanda ya kai man ya kyauta.

 

Jagora: Sai godiya ni kai Ila Gada Alahaji ya gode,

Yara:    Du yanda ya kan man ya kyauta.

Jagora: Gaishe ka Mai’akwai Yabo,

Yara:    Du yanda ya kai man ya kyauta.

 

Jagora: D’angaskiya ina Ibrahim,

Yara:    Du yanda ya kai man ya kyauta.

 

Jagora: Sai godiya nikai Loto ni Alhaji na gode,

Yara:    Du yanda ya kai man ya kyauta.

 

Jagora: Sai godiya Yahaya Haji D’an Buhari na gode,

Yara:    Du yanda ya kai man ya kyauta.

 

Jagora: Muntari mafiya na gode,

Yara:    Du yanda ya kai man ya kyauta,

 

Yaro: Dakata ‘Danba’u akwai magana ni wajena,

Duw wanda yai alk’awali k’ila in ya mance,

Sai a tuna mai ubandawaki Shi’itu shi zai ba ni gida

‘Danba’u duka ni da mutane na,

Jagora/Yara: Ban koma zuwa kwana Loja.

 

Yara: Dakata ‘Danba’u wanda yai alk’awali,

Sai a tuna mai wata k’ila takan yu ya manta,

Ubandawaki shi zai ba ni gida Sakwkato,

Kaf nida mutane na,

Jagora/Yara: Ban koma zuwa kwana Loja.

 

Jagora: Kaf ni da mutanena,

Yara:   Ban koma zuwa kwana Loja.

 

Amshi: K’ara shirawa,

Aliyu za’ba’b’ben gwamna,

Mai ban tsoro magatakardan Wamakko,

Sarkin Yamman Sakkwato bai san wargi ba.

 

Jagora: Ina Bala Musa,

Yara:    Du yanda yakai man ya kyauta.

 

Jagora: Sai godiya Bala Musa,

Du yanda ya kai man ya kyauta.

Amshi: K’ara shirawa,

Aliyu za’ba’b’ben gwamna,

Mai ban tsoro magatakardan Wamakko,

Sarkin Yamman Sakkwato bai san wargi ba.

 

Yaro: Dama hank’urin kwaram sai goga,

Wuyau ta sai k’arfe,

Jure fari sai tofa,

Baba ruwa da kada ba a zuwa wanka,

Sai dai a tsaya kallo,

Yara: Wani ya shiga zai wanka,

Da ya shiga bai kai waje ba.

 

Jagora: Ba a zuwa wanka sai dai a tsaya kallo,

Yara:   Wani ya shiga bai kai waje ba.

 

 

 

 

 

Post a Comment

0 Comments