Ticker

6/recent/ticker-posts

Wakar Kudi Ta Mamman Shata

Sauraro Da Rubutawa

Shu’aibu Murtala Abdullahi

Jagora: Kud’i a kashe su ta hanya mai kyau,

‘Y/Amshi: Kud’i a kashe su ta hanya mai kyau.

Jagora: Kud’i a kashe su ta hanya mai kyau,

‘Y/Amshi: Kud’i a kashe su ta hanya mai kyau.

Jagora: Amma ba bisa shashanci ba,

Kana ba bisa sakarci ba,

Kud’i a kashe su ta hanya mai kyau.

‘Y/Amshi: Kud’i a kashe su ta hanya mai kyau.

Jagora: Ka tuna yanda ka sami kud’inka,

Ka sha wuya ka sami kud’inka,

To je ka kashe su ta hanya mai kyau.

‘Y/Amshi: Kud’i a kashe su ta hanya mai kyau.

Jagora: Tun da sai kai gumi ka sami abinka,

Ashe ko kashe shi ta hanya mai kyau.

‘Y/Amshi: Kud’i a kashe su ta hanya mai kyau.

Jagora: A kashe su ta hanya mai kyau.

‘Y/Amshi: Kud’i a kashe su ta hanya mai kyau.

Jagora: Maln duk cinikin da kake yi,

Du wuyar shi dud dad’in shi,

In ka sami kud’in ka ka tara,

In dai kai niyyar ‘bad da su,

Je ka kashe su ta hanya mai kyau.

‘Y/Amshi: Kud’i a kashe su ta hanya mai kyau.

Jagora: Ko ni Alhaji sarkin wak’a,

In nai wak’a kyakkyawa,

Na sami kud’i mai k’wari,

Na tara has sun kauri,

Ba ashararu,

Ba sakarci,

Sai in kashe su ta hanya mai kyau,

‘Y/Amshi: Kud’i a kashe su ta hanya mai kyau.

Jagora: Bare mai saye yana sai dawa,

Yai gumi ya sami abi nai,

Ya sha wuya ya sami abi nai,

To ya kashe su ta hanya mai kyau,

‘Y/Amshi: Kud’i a kashe su ta hanya mai kyau.

Jagora: Ya san abin da dud zai zo mai,

Ya san abin da zai koma can,

To a kashe su ta hanay mai kyau.

‘Y/Amshi: Kud’i a kashe su ta hanya mai kyau.

Jagora: Tsaya dukiya abin nema ce,

Su kud’i abin nema ne,

Ciccije nemi abinka,

Baza k’arfi nemi kud’inka,

In kuma ka tashi kashewa,

To ka kashe su ta hanya mai kyau.

‘Y/Amshi: Kud’i a kashe su ta hanya mai kyau.

Jagora: Wanda ka yi wa sai ya ji dad’i,

Kai da ka yi kai ma ka ji dad’i,

In ka kashe su ta hanya mai kyau,

‘Y/Amshi: Kud’i a kashe su ta hanya mai kyau.

Jagora: Kud’i mu kashe su ta hanya mai kyau,

‘Y/Amshi: Kud’i a kashe su ta hanya mai kyau.

Jagora: An daina albuzzaranci,

Ba shashanci,

Ba sakarci,

In ka nemi kud’i ka tara,

In kai niyya za ka kashe su,

To ka kashe su ta hanay mai kyau.

‘Y/Amshi: Kud’i a kashe su ta hanya mai kyau.

Jagora: Ga wani ya yi gumi ya samu,

Ya sha wuya ya samu,

Ya zo a wurin ‘baddawa,

Ya ‘bad da a cikin sakarci,

Wannan ya zama wawa ke nan,

Bai bi ba zancen Mamman Shata,

‘Y/Amshi: Kud’i a kashe su ta hanya mai kyau.

Jagora: Mutuk’ar da ka sha wuya kas samu,

In za ka ‘batar,

Kai imani,

Yi tunani can a k’wak’walwa,

Zo ka kashe su ta hanya mai kyau,

‘Y/Amshi: Kud’i a kashe su ta hanya mai kyau.

Jagora: Muddin dukiya ta samu,

Muddin dukiya ta samu,

Ka zan na,

Kuma ka huta tsaf,

Ka yi tunani can daga zucci,

Ka yi tunani nan a k’wak’walwa,

In dai kai niyyar ‘bad da su,

Je ka kashe su ta hanay mai kyau.

‘Y/Amshi: Kud’i a kashe su ta hanya mai kyau.

Jagora: Kud’i amma su ‘yan nema ne,

In kai niyya za ka kashe su,

Tafi ka kashe su ta hanay mai kyau.

‘Y/Amshi: Kud’i a kashe su ta hanya mai kyau.

Jagora: Na sha wuya na sami abina,

Na tara har sun taru,

In na je han nai shashanci,

Na kashe su tafarkin banza,

To dad’a na rikid’i shashasha,

‘Y/Amshi: Kud’i a kashe su ta hanya mai kyau.

Jagora: In dai na so in cika kirki,

In cika buri,

In ta wadata,

To in kashe su ta hanya mai kyau,

‘Y/Amshi: Kud’i a kashe su ta hanya mai kyau.

Jagora: In zan alheri in sami fa,

In zan sayo,

In je in sanifa,

In zan sayar,

In rink’a tunani,

In san riba,

Fitar da uwa,

Kud’i a k’arshe su tafarki mai kyau,

‘Y/Amshi: Kud’i a kashe su ta hanya mai kyau.

Jagora: ko mutumin daji da na birni,

Yan nemi dukiyassa ya tara,

Yai ta tunani can daga zucci,

In dai ya d’akko zai ‘bad da,

To ya kashe su ta hanya mai kyau.

‘Y/Amshi: Kud’i a kashe su ta hanya mai kyau.

Jagora: Idan ya kashe su ta hanay mai kyau,

Farko Allah na gode masa,

Kama Annabi na gode mai,

Mu mutane muna gode mai,

‘Y/Amshi: Kud’i a kashe su ta hanya mai kyau.

Jagora: Tun da mun san bai shiga shashanci ba,

‘Y/Amshi: Kud’i a kashe su ta hanya mai kyau.

Post a Comment

0 Comments