Ticker

6/recent/ticker-posts

Sautukan Hausa A Bakin Jukunawa (2)

Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriyawww.amsoshi.com

NA

SANUSI GAMBO BELLO

BABI NA DAYA: BITAR AYYUKA DA DALILIN BINCIKE


1.0     SHIMFID’A


Wannan babi zai yi waiwaye ne don duba ayyukan da aka gabatar da suka danganci wannan aikin domin duba al’amurar da aka cimma. Sa’annan ya bayyana dalilan da suka haifar da yin wannan binciken da kuma muhimmancinsa ga al’umma baki d’aya. Haka kuma zai bayyana mana farfajiyar binciken domin sanin iyakar inda binciken zai tsaya da kuma hanyoyin da za a bi wurin gudanar da wannan bincike.
  • BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA


Kamar yadda Hausawa kan cewa “waiwaye adon tafiya”,  don  haka a lokacin gudanar da wannan nazari an ci karo da wasu nazarce-nazarcen da wad’ansu suka gabatar da suke da dangantaka da batun da ake gudanar da bincike a kansa, domin tantance alak’a, bambanci da kuma zangon da aka cimma.

Wad’annan kuwa sun had’a da littattafai da kundaye da k’asidu da jaridu wad’anda suka danganci wannan nazarin. Haka kuma a lokacin da ake gudanar da wannan bincike an ci karo da nazarce-nazarce da aka gudanar a kan tasirin harshen farko (harshen uwa) yayin furta kalmomin Hausa.

Da wannan ne George,  (1985) a wani binciken da ya gudanar don k’ok’arin ya fayyace gaskiyar al’amarin, ya bayyana ma’anar harshe da cewa, “d’an’Adam  da sautukan da yake furtawa na da k’arfi musamman ma in ya had’u da wani d’an’Adam”.

Shi kuma Kumary, (2005) a nasa binciken ya yi k’ok’ari ne na bayyana irin dalilin da ke haddasa irin wannan sauyi a harshe inda yake cewa “Bak’on al’amari zai yi wuyar nashewa a cikin tsarin wani harshen da ya yi aro saboda abubuwa da dama da suka had’a da, bambancin asalin harshe da al’adun masu harshe da makamantansu”. Sannan ya k’ara da cewa, wasu al’amura dole za su kasance a yayin da ake k’ok’arin nak’altar wani sabon hanyar sadarwa saboda tasirin da harshen uwa ke da shi ta yadda zai janyo sauye-sauye a tsarin sauti, da tsarin ginin kalma da kuma sauk’ak’a kalmomi ta yadda za su dace da fad’in masu wannan harshen. Dangane da irin ra’ayoyin da suka gabata dangane da harshe ne ya ba mu haske don bin diddigin ayyukan da aka gudanar kan tasirin wani harshe a kan d’an’uwansa, kamar haka:

Sani, (2004) a takardar da ya gabatar mai taken “Tone Placement and Stress replacement in English and Arabic Loan Words in Hausa” a wannan aikin marubucin ya bayyana yadda harshen Hausa yake amfani tsarin karin harshe da yake amfani da shi don maye tsarin k’arfafawa da harshen Turancin Ingilishi da kuma harshen Larabci suke amfani da shi a kalmomin da ya aro.

‘Dakingari (1989) ya rubuta kundin digirinsa na farko, Jami’ar Usmanu Danfodiyo mai taken “The  influence of Hausa on Fulfulde Language a case study of  ‘Dakingari District”. Bayan ya yi bayanin garin ‘Dakingari da al’ummar cikin sa, sannan ya kawo dangantakar da ke tsakanin al’ummar Ful’be da Hausawa da kuma Rundawa ta fannin tsarin al’adu da siyasa da kuma tattalin arziki. Da wannan ne ya yi k’ok’arin gutsuro muhimman wuraren da Fillanci ya yi aro daga harshen Hausa, da suka had’a da, ginin jimla da tsarin sauti da kuma sunaye.

Auna (1992) ya rubuta kundin digirinsa na farko, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo mai taken “Influence of Hausa  Language on the Kambari Language”. A inda ya yi k’ok’arin bayyana asalin Kambarawa da muhallinsu da rabe-rabensu da karin harshensu da kuma Hausawan da ke zaune  a yankin Kambari, a inda ya bayyana wasu hanyoyi hud’u da Kambari suka bi don sarrafa d’inbin kalmomin Hausa zuwa harshensu na Kambari ta hanyar amfani da d’afi.

A wani aikin na  Yunusa (1986), kundin digirinsa na farko, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, mai taken “Tasirin Hausa da Fulatanci a kan Juna”. Wannan marubucin ya yi bayani ne kan harshen Hausa da kuma Fulatanci, sannan ya kawo bayani kan yadda are-aren kalmomi ya yi tasiri a tsakaninsu. Daga k’arshe kuma sai ya kawo bayani a kan yadda kowane harshe ya yi tasiri a kan wani, wato Hausa a kan Fulatanci da kuma Fulatanci a kan Hausa.

Sai kuma Yunusa da Rabi’u (2007) kundin digirinsu na farko, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo mai taken “Mother tongue interference, a Phonological Le’bel: A Study of Igala speaker of English Language”. Wannan kundin ya fara ne da ba da tarihin al’ummar Igala da kuma muhallinsu, sannan ya bayyana dalilan da ke haifar da gur’batacciyar yanayi a ‘bangaren tsarin sauti, ta yadda suka zayyano sautukan Ingilishi da kuma na Igala da irin bambance-bambancen da aka samu.

Daga k’arshe kuma suka k’ark’are da bayyana dalilan aukuwar hakan (tasirin).

Baba, (2005) a aikinsa mai taken “Hausa Spoken as a Second Language in Jos/Bukur Background”. Marubucin ya nuna Hausa a matsayin harshe na biyu a wurin al’ummar Jos/Bukur yadda take fuskantar wasu matsaloli da suka had’a da: rashin hamzantawa da hamzanta wasu bak’ak’e. Rashin bambantawa tsakanin ra-kad’e ‘Drd’ da ra-gare ‘Drd’, musanya sautin /c/ da /sh/ da d’ayanta tagwan wasula. Rashin bambantawa tsakanin jinsi da sauya tsarin ginin kalma da kuma ginin jimloli da makamantansu.

A aikin Tukur, da Birnin-gwari, (2005) mai taken “The Use of Hausa Led’eme  yaya (how) and sai (until) among Kataf cluster Language, a Socio-linguistic Perspecti’be”. Wannan takarda ta zayyano cincirindon harsunan Katafawa da suka had’a da, Atijab (Katab) da Baju (Kaje) da Auworok (Kagoro) da sauransu. Sannan ya bayyana yadda suka sarrafa d’imbin kalmomin Hausa zuwa harshensu.

Shi ko Haruna, 2004. A nasa binciken a takardar da ya gabatar mai taken “Wad’ansu Manyan matsaloli da Hausawa kan fuskanta wajen Koyon Turanci a matsayin harshe na biyu”. Wannan takardar ta bayyana muhimmancin koyon Turanci a matsayin harshe na biyu, sannan ya kawo bambance-bambancen sigar da ke tsakanin Turancin Ingilishi da Hausa ta yadda ya bayyana cewa, akwai wasu sautuka da Turancin Ingilishi ke da su wad’anda Hausa ba ta da su kamar ‘D , . ‘b, k’d’ da sauransu. Sannan ya kawo tsarin ga’ba ta Turanci yadda ta Turanci ta bambanta da ta Hausa, ta yadda ta Turanci ke amfani da cincirindon kalmomi ita kuma Hausa ba haka ba ne. Daga k’arshe kuma sai ya kawo kalmomin da Hausawa ke fuskantar cikas yayin furta su ta hanyar musanya su da kwatankwacin sautukan da suke da su a Hausa.

A wani aikin kuma na Baba, da Munkaila, (2011) sun gabatar da wata takarda mai taken “Morphosyntactic ‘Bariation in Jos/Bukur Hausa”. a cikin wannan takardar sun fara da waiwaye ne dangane da aikin Baba, (2005) ta yadda suka nuna cewa Hausar al’ummar Jos da Bukur ta sha bamban da daitacciyar Hausa a tsarin sauti, ta yadda yakan sami rashin hamzantawa da d’ayanta tagwan wasali kamar “ai” da “au” a mayar da su “ee” da “oo”. Yanke wani sashe na kalma  da dai makamantansu. Daga k’arshe kuma sun kawo bambancin da ke aukuwa dangane da tsarin giredin Hausa ta yadda wad’annan al’ummu ba su bambancewa tsakanin giredi kamar yadda yake.

Abin dubawa a nan shi ne duk ayyukan da aka gudanar wajen bitar ayyukan da suka gabaci wannan aikin ba a sami wani aikin da ya yi daidai ko kamanci da aikin namu ba,  ko da ta fuskar take. Don haka za a fito a fili na cancantar gudanar da wannan aikin a kaso na gaba don samun damar gudanar da wannan binciken.

1.2    DALILIN BINCIKE


Komai na rayuwa bai rasa dalilin wanzuwarsa ta hanyar wani dalili. Sanin haka shi ya sa nake ganin ya fi dacewa da in kawo dalilin da ya sa nake son gudanar da wannan binciken.

Babban dalilin shi ne, ganin yadda aka gudanar da bincike kan wasu k’ananan k’abilu takwarorin Jukun ta fannono daban-daban. Kuma tun daga al’adunsu da adabinsu zuwa uwa uba harshensu. Ire-iren wad’annan ayyuka kamar irin aikin tasirin Hausa kan Dakarkarin Zuru da tasirin Hausa kan Rungawan Yawuri da makamantansu, shi ya sa nake ganin yana da kyau da in nazarci irin tasirin da Hausa ta yi kan Jukunta fuskar furuci don ba da gudummuwa ga masu sha’awar gudanar da bincike na kwatanci tsakanin harsuna biyu.

Dalili na biyu shi ne a lokacin da ake gudanar bitar ayyukan da suka gabata ba a ci karo da wani aiki da ya yi kama da wannan binciken ba ko da ta fuskar take ko tsarin aikin. Wato aikin da aka gudanar kan Jukunawa ba. Wannan shi ya ba ni  damar  gudanar da wannan aikin.

1.3   MANUFAR BINCIKE


A hak’ik’anin gaskiya duk wani abu da d’an’Adam ya fuskanta ba zai rasa wani manufa ba. Saboda haka wannan binciken ma yana da manufar yin sa. Ganin cewa Jukunawa al’ummu ne da suke da nasu harsunan, sannan kuma suna gudanar da ma’amala da Hausawa, sai aikin ya ga ya dace da ya fito da matsalolin furucin sautukan Hausa da k’abilun Jukunawa ke yi a yayin furucin wasu kalmomi. Tare da nuna yadda suke sarrafa su a yanayin zamantakewarsu cikin kalma.

Aikin zai fito da fasalin guraben da sauyi ya shafa dangane da lura da mafurtai na sautuka da suka shafi matsayin mak’wallato da yanayin furuci da wurin furuci. Aikin zai nuna yadda ake shafe wasu guraben furuci cikin kalma da kuma sauya wasu da makusanta da su.

1.4     HANYOYIN GUDANAR DA BINCIKE


Masu hikimar magana kan ce “K’arfe d’aya baya amo”, wannan binciken zai dogara ne a kan wasu muhimman hanyoyin da ake ganin za su taimaka wajen gudanar da wannan binciken. Misalin wannan hanyoyin sun had’a da: zurfafa bincike a kan ayyukan da suka gabata. Sannan kuma za a gudanar da karance-karancen litattafan da suka shafi furuci da tsarin sauti. Aikin kuma zai ziyarci wasu daga cikin manyan Jukunawa da nufin tantance abin da ake son fitowa da shi a matsayin gudumawa.

 

1.5     MUHIMMANCIN BINCIKE


Wannan bincike yana da matuk’ar muhimmanci domin zai taimaka wurin gano dangantaka da kuma bambancin da ke tsakanin sautukan harsunan Hausa da Jukun. Kuma zai taimaka wurin bayyana wuraren da matsaloli ke aukuwa yayin da Jukunawa ke furta sautukan Hausa. Aikin zai taimaka wa masu nazari wurin sanin abubuwan da ke aukuwa dangane da tsarin sautin Hausa a bakin Jukunawa. Wannan aiki zai bai wa wasu k’abilu damar k’ok’arin gudanar da binciken da suka shafi furuci a harshensu da na mak’wabtansu.

1.6    FARFAJIYAR BINCIKE


Wannan bincike ya shafi k’ok’ari ne na gano tasirin da ke akwai yayin da Jukunawa ke furta sautukan Hausa. sai dai binciken zai tsaya ne kan Jukunawa da ke garin Wukari (Jukun wapa) kuma zai tsaya ne a farfajiyar cikin  garin Wukari, ba zai lek’a wasu wurare ba, duk da yake akwai Jukunawa a can. An yi haka ne saboda Wukari ne cibiyar Jukunawa inda suke gudanar da sha’aninsu na siyasa da al’adu da sha’anin addini da sarautunsu.

1.7     NAD’EWA


A tak’aice wannan babi ya bayyana irin matakan da aikin zai bi tare da irin muhimmancinsa ga al’umma, ta yadda aka fara bayyana bitar wasu daga ayyukan da suka gabata domin sanin makamar aikin. Wannan babin ya zayyano dalilan gudanar da binciken sannan kuma ya nuna mana irin manufar da bincike ke son cimma. Daga nan kuma sai babin ya bayyana mana irin hanyoyin da binciken zai bi domin kammaluwa cikin sauk’i. Haka nan ya nuna irin muhimmanci da binciken ke d’auke da shi, sannan kuma farfajiyar binciken ya biyo domin nuna mana inda binciken zai tsaya. Daga k’arshe kuma sai aka kawo nad’ewa don rufe babin.

 

 

 

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

Post a Comment

1 Comments

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.