Ticker

6/recent/ticker-posts

Sautukan Hausa A Bakin Jukunawa (3)

 Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriyawww.amsoshi.com

NA

SANUSI GAMBO BELLO

BABI NA BIYU:


DANGANTAKAR HAUSAWA DA JUKUNAWA TA FUSKAR HARSHENSU


2.0     SHIMFID’A


A wannan babin mun dubi irin dangantakar da ke tsakanin harshen Hausa da na Jukun, sannan muka kawo sautukan Hausa da kuma na Jukun tare da bayanin su da kuma irin bambance-bambancen da ke tsakanin su.

2.1      DANGANTAKAR HARSHEN HAUSA DA NA JUKUN


Duk lokacin da aka yi magana a kan dangantaka to kuwa ana nufin tsarin zaman mutane ta hanyoyi daban-daban, kamar ta fuskar addini da tsarin ilimi da al’adu da kuma zamantakewa tsakanin wad’annan al’umma. Haka nan zamantakewar kowace k’abila ba zai cika ba, sai an fito da rayuwar wad’annan al’ummar. Misali, rayuwar al’ummar Hausawa za ta k’unshi tsarin da suke gudanar da al’adu da na harshensu da kuma addini cikin yanayin tsarin zamantakewarsu ta yau da kullum.

Idan an yi magana dangane da dangantaka da ya shafi harsuna, masana kan fara duba al’amarin daga tsarin zamantakewar wad’annan harsunan a yayin zuriyar harshe, ta yadda ake duba cewar shin wad’annan harsuna suna zuriyar harsuna d’aya

ne, ko kuma mabambanta ne. Harshen Hausa da harshen Jukun, harsuna  ne da suka fito daga zuriyar harsuna mabambanta.

Newman (1973) ya bayyana cewa “A yankin hamadar Afirka, masu magana da harshen Hausa sun fi kowane harshe yawa, kuma harshen ya fito ne daga zuriyar harsunan yankin tafkin Chadi (Chadic family), wanda  yake daga cikin wani ‘bangare na rukunin kason zuriyar harsuna mafi girma (Afro-Asiatic Phylum). Harshen Hausa yana d’auke da wani rukuni nasa na musamman daga ‘bangaren yammacin tafkin Chadi”.

Harshen Jukun kuwa a nasa ‘bangaren, ya fito ne daga zuriyar harsuna da suke yankin tsaunukan duwatsu (wide Plateau), d’aya daga ‘bangarorin zuriyar harsunan da suka samo asali daga duwatsun ‘Nuba’ wanda yake kudancin gundumar ‘Kordofan’ na Sudan (Benue-Congo, Kordofanian).[1]

Duk da yake wad’annan harsunan biyu  wato Hausa da Jukun ba su da wata alak’a a tsarin zamantakewa ta zuriyar harsuna, amma akwai dangantaka ta zamantakewar muhalli a tsakanin su wanda zai yi wuya a iya k’ididdige tsawon lokacin da aka faro mu’amalar. A bisa ga tarihi Hausawa da Jukunawa sun sami cud’anya tun zamanin Jahiliyya.

A jaridar ‘Sunday Trust’ ta goma ga Disamba, dubu biyu da shida (10th Dec. 2006) a wani bayani wanda ‘Ujorha’ ya ruwaito mai taken “Tracking the Kwararrafa….(1) The story of four Yakasai’s”, mai rahoton ya bayyana cewa ‘Yakasai’ kalmar Jukun ce wadda take nufin ‘mu je mu dawo’, ko kuma ‘za mu je mu dawo’ wadda har yanzu ana amfani da ita, kuma wannan kalmar tana fitowa ne daga bakunan mayak’an Jukunawa yayin da suka ci ko suka far wa al’umma da yak’i. Wad’annan mayak’a na Jukunawa sun yak’i Kano, sannan an sami kwatankwacin irin wannan al’amarin a garin Zariya, da wasu sassa na k’asar nan (Nijeriya). Wannan  ne ma ya sanya har yanzu akwai unguwa a garin Zariya mai suna tudun Jukun.

Idan aka yi la’akari da bayanin da Ujorha ya gabatar za a ga cewa,  Jukunawa da Hausawa sun sami cud’anya tun kafin Jukunawa su sami matsuguni na din-din-din  a garin Wukari Jihar Taraba a yau. Don haka dole ne a sami wata nasaba ta musamman tsakanin harshen Hausa da na Jukun. Don haka za mu koma mu dubi k’awayoyin sautukansu a kaso na 2.2 da 2.3.

2.2        SAUTUKAN HAUSA


Idan ana maganar sautuka, ana nufin sautin ‘bak’i’ (consonant) da kuma ‘wasali’ (‘bowel) a harshe.

Masana kimiyyar harshe sun raba k’wayoyin sautuka gida biyu don gudanar da nazari a kansu. Akwai sautukan ‘bak’i’ (consonant) da sautukan ‘wasali’ (‘bowel). Masana irin Skinner (1977) da Bagari (1980) da Sani (1999/2010) da kuma Yelwa (2008) duk sun tabbatar da wannan fasali na sautukan harshe. Ga yadda tsarin yake a Hausa.

2.2.1  SAUTUKAN BAK’AK’E


A daidaitacciyar Hausa, harshen Hausa yana da sautukan bak’ak’e guda talatin da hud’u (34). Ga yadda suke a rubutun yau da kullum da rubutun k’wak’k’wafi da misalan yadda suke zuwa a cikin kalmomi tare da bayanin su dangane da mafurtai. (Wurin furuci da yanayin furuci da kuma matsayin mak’wallato) kamar haka:
























































































































































































































































 Rubutun yau da kullumMisali a kalmomiRubutun sautiBayanin mafurtai
1./b/Baya‘Dbd’bale’be – tsayau – mai ziza
2./’b/Ta’barya‘D’bd’bale’be – had’iyau – mai ziza
3./m/mangwaro‘Dmd’bale’be – d’an hanci – mai ziza
4./f/Kumfa‘Dɸd’bale’be – zuzau – maras ziza
5./t/Tudu‘Dtd’bahank’e – tsayau – maras ziza
6./d/Daree‘Ddd’bahank’e – tsayau – mai ziza
7./l/Huulaa‘Dld’bahank’e – d’an jirge – ma ziza
8./h/Hayaak’ii‘Dhd’hamza – zuzau – maras ziza
9./d’/D’aakii‘Dd’d’nad’e harshe – had’iyau – mai ziza
10./r/Bara‘Drd’bahank’e – ra-gare – mai ziza
11./r/Ruwaa‘Dɽd’nad’e harshe – ra-kad’e – mai ziza
12./n/Noonoo‘Dnd’bahank’e – d’an hanci – mai ziza
13./n/Can‘Dᵑd’bagand’e – d’an hanci – mai ziza
14./n/Hanya‘Dᶮd’bahand’e – d’an hanci – mai ziza
15./s/Saabulu‘Dsd’bahank’e – zuzau – maras ziza
16./ts/Tsintsiya‘Ds’d’bahank’e – tunkud’au – maras ziza
17./c/ciyaawaa‘Dʧd’d’an bayan hank’a – d’an atishawa – maras ziza
18./j/Jaakii‘Dʤd’d’an bayan hank’a – d’an atishawa – mai ziza
19./z/Zaanee‘Dzd’bahank’e – zuzau – mai ziza
20./fy/Fyaad’ee‘Dɸjd’gand’antacciyar bale’be – zuzau – maras ziza
21./sh/Shaanuu‘Dʃd’d’an bayan hank’a – zuzau – maras ziza
22./y/Yaboo‘Djd’bagand’e – kusantau –wasali mai ziza
23./k/Karee‘Dkd’bahand’e – tsayau – maras ziza
24./ky/Kyau‘Dkjd’gand’antaccen bahand’e – tunkud’au – maras ziza
25./kw/Kwarii‘Dkwd’le’bantaccen bahand’e – tsayau – maras ziza
26./k’/K’ayaa‘Dk’d’bahand’e – tunkud’au – maras ziza
27./k’w/K’waaroo‘Dk’wd’le’bantaccen bahand’e – tunkud’au – maras ziza
28./k’y/K’yalle‘Dk’jd’gand’antaccen bahand’e – tunkud’au – maras ziza
29./g/Raagaa‘Dgd’bahand’e – tsayau – mai ziza
30./gy/Gyaaraa‘Dgjd’gand’antaccen bahand’e – tsayau – mai ziza
31./gw/Gwanii‘Dgwd’le’bantaccen bahand’e – tsayau – mai ziza
32./w/Wuk’aa‘Dwd’le’be-hand’e – kusantau – wasali mai ziza
33./?/ba’a‘D?d’hamza – tsayau
34./‘y/‘ya’ya‘D?jd’gand’antacciyar hamza – tsayau

Jadawalin sautukan Bak’ak’e na Daidaitacciyar Hausa (Hausa consonant chart)

 

 

 

 








































































































































































 Bale’begand’antaccen balel’beBahank’enad’e harshed’an bayan hank’abagand’eBahand’ele’be-hand’ale’bantaccen bahand’egand’antaccen bahand’ehamzagand’antacciyar hamza
Tsayaub t d   k g kw gwkj gj??j
Had’iyau‘b  d’        
tunkud’au  s’   K’ k’wk’j  
d’an hancim n       
Zuzauɸɸjs z ʃ     h 
d’an atishawa    ʧ ʤ       
d’an jirge  l         
ra-gare  r         
ra-kad’e   ɽ        
kusantau/

kinin wasali
     j w    

 

2.2.2       SAUTUKAN  WASULA


Abin dubawa a nan shi ne lokacin  furucin wasali iska ba ta samun matsalar fitowa daga mafurtai, tana fita ne kai tsaye.

A daidaitacciyar Hausa ana samun wasula iri biyu. Ana samun gajerun wasula da kuma dogaye kamar yadda za a nuna a cikin jadawali, tare da misalai daga kalmomi

GAJERUN WASULA

‘Did’   ciyaawaa

‘Ded’  mace

‘Dod’  saabo

‘Dad’  gashii

‘Dud’  uwa

DOGAYEN WASULA

‘Diid’  jiikaa

‘Deed’  geemu

‘Dood’  k’oofaa

‘Daad’  baashii

‘Duud’  buutaa

 

 

TASWIRAR WASULAN HAUSA

gaba                tsaka-tsaki                     k’urya

ii                                              uu                        sama

i                                                   u

ee                                       oo                         tsakiya                              e                                             o

a                                        k’asa

aa

Daga wasula da  aka nuna yanayin su da misalan su, biyar na farko gajeru ne, wasu masana na kiran su tilo. Biyar na rukuni na biyu dogaye ne kuma duka suna iya zuwa a cikin kalma d’aya tare da gajeru.

Bayan wad’annan wasula akwai kuma tagwai, wannan na nufin inda wasula biyu daban-daban suka had’u, wato inda ake furta wasulan biyu daban-daban lokaci guda. Akwai tagwan wasula iri uku kamar haka, tare da misalai daga kalmomi.

TAGWAN WASULA

‘Daid’      aikii da mai

‘Daud’      k’auyeee da taurii

‘Duid’       guiwaa da kui’bii

 

TASWIRAR TAGWAN WASULAN HAUSA

 

i                                              u

 

ai                                            au

 

a                               a

 

 

 

2.3   SAUTUKAN  JUKUN


Kowane harshe na duniya yana da ire-iren k’wayoyin sautukan da ya mallaka, harshen Jukun ma yana da k’wayoyin sautuka iri biyu kamar wasu harsunan duniya. Misali, harshen Ingilishi da na Hausa. kuma hanya iri d’aya ake bi wajen nazarin k’wayoyin sautukan Hausa da na Jukun. Wato ana ware sautin bak’i a nazarce su, a kuma ware na wasali don fito da bayanin su a fili. Ga yadda suke:

2.3.1  SAUTUKAN BAK’AK’E


Shimuzu (1971), da wani binciken da Jami’ar Ibadan ta gabatar a (1972) da kuma aikin Ladan (2008) duk sun bayyana cewa harshen Jukun na da sautukan bak’ak’e guda arba’in da takwas (48). Sai dai ayyukan Shimuzu (1971) da binciken da Jami’ar Ibadan ta gabatar (1972) suka gabatar, ba su yi bayanin sautukan dangane da mafurta, da yanayin furuci da kuma matsayin mak’wallato ba, sai aikin Ladan (2008) ya fitar da wad’annan bayanan. Ga yadda suke a rubutun yau da kullum da rubutun k’wak’k’wafi da misalan yadda suke zuwa a cikin kalmomi tare da bayanin su dangane da mafurtai, kamar haka:









































































































































































































































































































Rubutun yau da kullumMisalan

Kalmomi
Bayanin mafurtaiRubutun

k’wak’k’wafi
/b/bi/ zoobale’be  tsayau  mai ziza‘Dbd’
/bw/bwan/ sakiLe’bentaccen bale’be  tsayau  mai ziza‘Dbwd’
/by/byena/ gadooGand’antaccen bale’be tsayau  mai ziza‘Dbjd’
/f/fitse/ dareeLe’be-hank’a  zuzau  maras ziza‘Dfd’
/fy/afyo/ agwagwaGand’antaccen le’ba-hank’a  zuzau  maras ziza‘Dfjd’
/’b/a’bo/ hannuLe’ba-hank’a  zuzau  mai ziza‘D’bd’
/’by/a’byu/ ‘baraawooGand’antaccen le’ba-hank’a  zuzau  mai ziza‘D’bjd’
/p/pajukun/ jama’aBale’be  tsayau  maras ziza‘Dpd’
/py/Apyu/wutaGand’antaccen bale’be tsayau mai ziza‘Dpjd’
/pw/Pwadzu/fita wajeLe’bantaccen bale’be tsayau maras ziza‘Dpwd’
/m/Ama/mahalicciBale’be d’anhanci mai ziza‘Dmd’
/mb/Mbya / dubaKusantau – d’anhanci, bale’be tsayau mai ziza‘Dmbd’
/mbw/Mbwa/ macijiKusantau d’anhanci le’bantaccen bale’be tsayau mai ziza‘Dmbwd’
/my/Myan/maakooGand’antaccen bale’be d’anhanci mai ziza‘Dmjd’
/d/Denden/kurwaaBahank’e tsayau mai ziza‘Ddd’
/dw/Dwadzwe/tsugunaLe’bantaccen bahank’e tsayau mai ziza‘Ddwd’
/t/Taba/huulaaBahank’e tsayau mai ziza‘Dtd’
/nd/Ndekuto/a kanKusantau-d’anhanci bahank’e tsayau mai ziza‘Dndd’
/l/La/dank’ooBahank’e d’an-jirge mai ziza‘Dld’
/r/Rito/lafiyaBahank’e ra-gare mai ziza‘Drd’
/n/Nuge/alk’awariBahank’e d’an-hanci  mai ziza‘Dnd’
/n/Wando/ mata su ne gidaGand’antaccen bale’be, tsayau mai ziza‘Dnd’
/n/‘Byonkhen/ gidan zumu ba kasuwa ba ne.Le’bantaccen bale’be tsayau mai ziza‘Dnd’
/s/Sansan/ kyauBahank’e tsayau, maras ziza‘Dnd’
/sw/Aswe/ zaboLe’bantaccen bahank’e, zuzau mzras ziza‘Dswd’
/z/Azin/ tsoroBahank’e tsayau, mai ziza‘Dzd’
/zy/Azyin/ jibiGand’antaccen bahank’e, zozau mai ziza‘Dzjd’
/ts/Tsuken/ rufeBahank’e tunkud’au maras ziza‘Dšd’
/tsw/Atswi/iri na nomaLebantaccen bahank’e, tukud’au maras ziza‘Dšwd’
/sh/Shesho/ gùùduD’anbayan hank’a zuzau maras ziza‘Dsd’
/c/Cidon/ UbangijiD’anbayan hank’a, d’an’atishawa maras ziza‘Dtsd’
/j/Jape/ ruwaD’anbayab hank’a zozau maras ziza‘Dd3d’
/y/Ya/ tàfííBagand’e kusantau wasali mai ziza‘Djd’
/ny/Nyutu/ ranaBahand’e tsayau maras ziza‘Dnjd’
/k/Aku/ sarkiGand’a - hand’a tsayau maras ziza‘Dkd’
       /kh/Akhifo/tsandoLe’ba-hank’a tsayau marar ziza‘Dkhd’
/kp/Khasunya/matsaLe’ba-hank’a tsayau marar ziza‘Dkpd’
/ky/Nyakyon/ k’ofaGand’antaccen bahank’e, tsayau maras ziza‘Dkjd’
/kw/Kwakyi/ babbaLebantaccen bahand’e tsayau maras ziza‘Dkwd’
/g/Gongon/ dogoBanhand’e tsayau mai ziza‘Dgd’
/gb/Gbejo/ rawaaLebe-hand’a tsayau mai ziza‘Dgbd’
/gy/Agye/zoomooGand’antaccen bahand’e tsayau mai ziza‘Dgjd’
/ng/Angha/ kalar kiifiiKusantau d’anhanci, bahande tsayau mai ziza‘Dngd’
/w/Awi/ naamaaLe’ba – hand’a kusantau, wasali mai ziza‘Dwd’
/nw/Nwuda/jììkaKusantau d’anhanci le’ba hand’a kusantau mai ziza‘Dnwd’
/h/Hobe/ fatanyaHamza zuzau maras ziza‘Dhd’
/hy/Hyu/kurmiGand’antaccen hamza zuzau maras ziza‘Dhjd’
/hw/Ahwen/ talauciLe’bantaccen hamza zuzau maras ziza‘Dhwd’

 

2.3.2        WASULAN JUKUN


Shimuzu (1971)  da Welmers (1973) da kuma  Ladan(2008) duk sun tabbatar da cewa harshen Jukun yana da gajerun wasula guda biyar sannan kuma duka biyar d’in suna da kwatankwacin su ‘yan hanci. Ga yadda suke tare da misalai daga kalmomi.

2.3.2.1 WASULA ‘YAN BAKI

‘Di d’ bi / zoo

‘D e d’ aje / kiifii

‘D a d’ apa / mutum namiji

‘D o d’ azo / ido

‘D u d’ acu / ruwan sama

 

2.3.2.2    WASULA ‘YAN HANCI


‘D i d’ afin / k’adangare

‘De d’ akwen / wuk’aa

‘Da d’ nana / barci

‘D o d’ ano-myi / kada

g’D u d’ wunu / namiji

Kamar yadda harshen Hausa ke da tagwan wasula, haka ma harshen Jukun yana  da tagwan wasula guda biyu. Ga yadda suke tare da misalai daga kalmomi.

‘D au d’ au / kai (you)

‘D ai d’ attai / mahaifinmu ( our father)

Daga sautukan bak’ak’e da aka zayyano a kaso na 2.2 da na 2.3 an ga cewa Hausa tana da bak’ak’e  talatin da hud’u (34), harshen Jukun kuma na da arba’in da takwas (48). Saboda haka, wannan binciken ya bayyanar da cewa, harsunan biyu wato Hausa da Jukun sun yi tarayya a akasarin sautukan da harsuna duniya suka yi  tarayya a kansu. International Phonetics Alphabet (I PA). Sai dai akwai sautukan da harshen Hausa ke da su harshen Jukun ba shi da su. Ga yadda suke tare da misalan yadda suke zuwa cikin kalma.

‘D k’ d’ misali k’aya ko k’umshi

‘D ‘b d’ misali ‘barawoo ko ‘baawo

‘D d’ d’ misali d’ari ko Mad’i

‘Dr d’ misali ruwaa

‘DØd’ misali farii ko marfi

A  wannan sauti na /f/ harsunan sun yi tarayya a inda ake rubuta su a rubutun yau da kulum, sai dai sun bambanta dangane da mafurta. Haka nan le’bantattu da kuma gand’antattun sautukan Hausa akwai su a harshen Jukun, amma ban da sautuka kamar su:

Gand’antaccen hamza tsayau ‘D?jd’699699999  misali; ‘ya’ya da gand’antaccen bahand’e tunkud’au ‘Dk’jd’ misali; k’yaamaa da gand’antaccen bale’be zuzau maras ziza ‘DOjd’ misali; fyaad’ee, da le’bantaccen bahand’e tunkud’au maras ziza ‘Dk’wd’ misali; k’waaroo, sa’annan hamza tsayau ‘D ? d’ misali; A’i. Daga jerin sautuka talatin da hud’u da harshen Hausa ke da su, harshen Jukun na da ashirin da biyu da suke amfani da su, kamar haka: / b, m, d,t , r, n, n, n, s, s’, z, S, ts, d3, k, g, kj, gj, kw, w, j, h / .  Idan aka dubi al’amarin a ‘bangaren harshen  Jukun kuma, za a ga cewa yana da sautuka da dama wanda harshen Hausa ba ta da  su kamar su: / bj, bw, f,fj, ‘b, ‘bj, p, pj, pw, mb, mbw, mj, dw, nd, nj, mg, mw, zj, kh, kp, gb, bj, hw /.

Idan aka dubi al’amarin a ‘bangaren wasula kuma, za a ga cewa harshen Jukun na da wasula  iri biyu; wanda ake furtawa a baki ( oral) da kuma ‘yan hanci(nasal). Harshen Hausa kuwa duk wasulan sa a baki ake furta su (oral). Da wannan za a ga cewa harshen Hausa kwata-kwata bat a da wasula ‘yan hanci kamar yadda harshen Jukun ke da su.

2.4         NAD’EWA


A  wannan babi, bayan an yi shimfid’a don nuna yadda babin zai nufa, sannan aka nuna irin dangantakar da ke tsakanin Hausawa da Jukunawa ta fuskar harshensu don bayyana irin dangantakar da ke tsakanin su. Babin ya bayyana tare da zayyano tsarin sautukan da Hausa take da su. Wato tana da sautukan bak’i talatin da hud’u, tare wasula biyar tilo, biyar dogaye da kuma masu aure ko tagwai guda uku. Harshen Jukun yana da bak’ak’e guda arba’in da takwas da wasula biyar ‘yan baki da kuma wasu biyar ‘yan hanci, sannan biyu tagwai. Aikin ya fito da wuraren da Hausa da Jukun suka yi tarayya a bak’ak’e da wasula. Amma sun sha bamban a wasu wurare, ta yadda nad’ewa ta kasance marufin babin don bayyana abin da aka tattauna a tak’aice.

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

[1]A dubi kundin digiri na uku (ph.D Thesis) na Fakuade, G. 1995 . Jami’ar Ilorin.

Post a Comment

0 Comments