Ticker

6/recent/ticker-posts

Sautukan Hausa A Bakin Jukunawa (1)

 Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriyawww.amsoshi.com

NA

SANUSI GAMBO BELLO

SADAUKARWA


Na sadaukar da wannan aikin ga iyayena da Malamaina da kuma dukkan ‘yan’uwa da abokan arziki domin irin gudunmawar da suka bayar don kammalar wannan aikin, Allah ya saka musu da mafificin alhairinsa, ya kuma albarkaci rayuwarsu, sannan ya nufe su da cikawa da imani.

TABBATARWA

Mun tabbatar da cewa wannan aikin ya cika sharud’d’an da Jami’a ta shimfid’a, wanda ake bukatar d’alibin da ya kai shekarar karatu ta karshe, da ya rubuta kundin bincike domin ba da gudunmawa ga masu buk’atar nazari a Sashen da ya gudanar da karatu.

…………………………….                                                  ……………………….

Sa hannun mai dubawa                                                          Kwanan wata

Mal. Sama’ila Umar

……………………….                                                       ………………………

Sa hannun Shugaban Sashe                                                  kwanan wata

Prof. Salisu Ahmad Yakasai

………………………..                                                    ………………………..

Sa hannun mai dubawa na waje                                        Kwanan wata

(Ed’ternal Ed’aminer).

 

 

GODIYA


Dukkan godiya ta tabbata ga Allah mad’aukakin Sarki, mai kowa mai komai, wanda ya k’addaremu da kasancewa a bisa wannan doron k’asa. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabin Rahama, Annabi Muhammadu (S.A.W) da Sahabbansa da duk wad’anda suka bi su da kyautatawa har zuwa ranar k’arshe.

Ina mik’a godiyata mafificiya ga mahaifana da suka kula da tarbiyata tun daga haihuwata har ya zuwa matakin rayuwar da na tsinci kaina a halin yanzu, da fatar Allah ya gafarta masu dukkannin zunubansu, wad’anda suka aikata a baya da wanda za su aikata har ya zuwa k’arshen rayuwarsu, da fatar Allah ya sa su cika da imani. Wannan d’angon ba zai cika ba, har sai na mik’a godiyata ta musamman ga malamina Mal. Sama’ila Umar, wanda ya d’auki d’awainiyar duba wannan aikin, tare da ba da shawarwarin da suka taimaka mini wajen d’ora ni kan hanya don ganin aikin ya inganta tare da kar’buwa tun daga farkonsa har ya zuwa kammaluwarsa ba tare da ya gajiya da ni ba. Allah ya saka masa da mafificin alhairinsa ya albarkaci zuriyarsa.

 

 

Ina mik’a godiya ta musamman ga shugaban Sashen Nazarin Harsunan

Nijeriya Farfesa Salisu Ahmad Yakasai, tare da dukkannin malamaina na sashe

gaba d’aya da ma’aikatan sashe, da fatar Allah ya saka masu da mafificin alherinsa. Kuma ina fatar Allah ya k’ara masu hakurin kula da ‘yan’uwana d’alibai da juriyar ba su shawarwari kamar yadda suka tarbiyantar da ni.

Ina gode wa hukumar Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo da ta ba ni damar zuwa

yin karatu, tare da kula da inganta tarbiyata don ganin na zama mutum nagari. Allah ya saka masu da aljanna Firdausi. Daga k’arshe ina mik’a godiya ga dukkan ‘yan’uwa da abokanen arzik’i, na gida da na makaranta wad’anda suka ba ni gudummawa ta fuskar addu’a da taimako na shawarwari ko na wani mahimmin abu na gudanar da rayuwa. Ina rok’on Allah ya saka masu da mafificin alherinsa, kuma ya albarkaci rayuwarsu da ta zuriyarsu baki d’aya.

 

 

 

                                       K’UMSHIYA


TAKEN BINCIKE………………………………………………………………….i

SADAUKARWA…………………………………………………………………..ii

TABBATARWA…………………………………………………………………..iii

GODIYA…………………………………………………………………………..i’b

K’UMSHIYA………………………………………………………….……………’bi

 

BABI NA ‘DAYA: BITAR AYYUKA DA DALILIN BINCIKE.


 

GABATARWA…………………………………………………………………….1

1.0 Shimfid’a………………………………………………………………………4

1.1 Bitar Ayyukan da suka gabata…………………………………….……………4

1.2 Dalilin Bincike…………………………………………………….…………10

1.3 Manufar Bincike………………………………………………………………11

1.4 Hanyoyin Gudanar da Bincike……………………………………..…………12

1.5 Muhimmancin Bincike ………………………………………………………13

1.6 Farfajiyar Bincike……………………………………………………………13

1.7 Nad’ewa………………………………………………………………………14

 

 BABI NA BIYU: Dangantakar Hausawa da Jukunawa ta Fuskar Harshensu.


2.0 Shimfid’a………………………………………………………………………15

2.1 Dangantakar harshen Hausa da na Jukun…………………………..…………15

2.2 Sautukan Hausa…………………………………………………….…………18

2.2.1Sautukan Bak’ak’e......………………………………………………………19

2.2.3Sautukan Wasulla…………………………………………………………....21

2.2.4 Gajerun Wasula……………………………………………………………22

2.2.5 Dogayen Wasula…………………………………………………………….22

2.2.6 Taswirar Wasula……………………………………………………………23

2.2.7 Tagwan Wasula……………………………………………………………24

2.2.8 Taswirar Tagwan Wasula…………………………………………………...24

2.3 Sautukan Jukun……………………………………………………..…………25

2.3.1 Sautukan Bak’ak’e……………………………………………………………25

2.3.2 Wasulan Jukun…………………………………………………………….28

2.3.3 Wasula ‘Yan baki...........……………………………………………………28

2.3.4 Wasula ‘Yanhanci…………………………………………………………29

2.4 Nad’ewa……………………………………………………………..…………31

     BABHI NA UKU: Tsarin Sautin Hausa a Bakin Jukun.


3.0 Shimfid’a ……………………………………………………………………...33

3.1 Tsarin Sautin Hausa a Bakin Jukun………………………………...…………33

3.2 Tasirin harshen Jukun a muhallin furucin sautukan Hausa………...…………37

3.2.1 Tawsiri marar Haifar da Sauyin ma’ana……………………………………38

3.2.2 Tasiri mai Haifar da Sauyin Ma’ana………………………………………...38

3.3 Bambancin da ake samu a wajen furta sautukan Hausa a harshen Jukun….…42

3.4 Nad’ewa……………………………………………………………………..…47

     BABI NA HU’DU: Gurbin sautukan Hausa a Bakin Jukun.


4.0 Shimfid’a………………………………………………………………………48

4.1 Musanyar Bak’i………………………………………………………………..49

4.1.1 Rashin Hamzatawa………………………………………………………….50

4.1.2 Hamzatawa…………………………………………………………………57

4.2 Musayar wasali ……………………………………………………………….57

4.3 Shafe wata ga’ba ta kalma……………………………………………………..60

4.4 Tsarma Bak’i a tsakiyar kalma……………………………………………...…61

4.5 Shafe wani harafi a kalma…………………………………………………….61

4.5.1 Shafe Bak’i a Kalma………..………………………………………………62

4.5.2 Shafe Bak’i a Farko Kalma…………………………………………………62

4.5.3 Shafe Bak’i a Tsakiyar Kalma……………………………………………….62

4.5.4 Shafe Bak’i a K’arshen Kalma………………………………………………63

4.5.5 Shafe Wasali a cikin Kalma…………………………………………………64

4.6 ‘Dayanta tagwan wasali ……………………………………………………….64

4.7 Nad’ewa………………………………………………………………………..67

     BABI NA BIYAR: Tak’aitawa da Nad’ewa


5.0 Shimfid’a ……………………………………………………………………...68

5.1 Tak’aitawa……………………………………………………………………..68

5.2 Kammalawa…………………………………………………………………...71

Manazarta ……………………………………………………………………..73

 

 

GABATARWA


Masana da dama sun dad’e suna k’ok’arin bayyana ra’ayoyinsu dangane da furucin sautukan harsuna daban-daban. Da haka ne ma masana irin su:

Hashim, (2005) ya bayyana ilimin furuci da cewa “ fage ne na nazari wanda yake bayani a kan yadda ake furucin sautin magana da harshen d’an’adam yake iya furtawa ko bak’i ko wasali”.

Haka nan Sani (2010) ya bayyana shi da cewa “ kimiyya ce ta bayyana sautukan magana na harsunan duniya”.

Shi kuma Yalwa ( 2008 ) ya bayyana shi da cewa “Wani reshe ne na ilimin harsuna (linguistics) wanda ake duban yadda sautuka na kowane harshe suke da yadda ake samar ko aiwatar da su ta hanyar furta su tun daga fitowar iska daga huhu har ya zuwa le’b’ba.” Sannan ya k’ara da cewa, a lura ilimin furuci na gama gari ne, watau ma’ana ana nazarin sautuka ne daban-daban na harsuna da dama ba wai kawai na harshe guda ba kamar a ilimin tsarin sauti (phonology).

Da wannan ne aka raba wannan aikin zuwa babi-babi har biyar don a tantance irin abubuwan da ke faruwa kan sautukan Hausa a bakin Jukunawa.

A wannan binciken babi na farko zai dubi wasu ayyukan da suka gabata da bayyana dalilan yin bincike sai kuma a nuna manufar binciken da hanyoyin gudanar da binciken sannan a fito da muhimmancin binciken fili, ta yadda aikin zai bayyana farfajiyar binciken. Za a ambace su tare da nad’e babin a k’arshe.

A babi na biyu aikin zai dubi irin dangantakar da ke tsakanin harshen Hausa da na Jukun sai kuma a fito da bayani kan sautukan Hausa da na Jukun. Za a nuna irin bambancin da ke samuwa tsakanin harshen Hausa da na Jukunawa ta fuskar sautuka. Sai a nad’e babin daga k’arshe.

A babi na uku aikin zai dubi yadda tsarin sautin Hausa yake a bakin Jukun, sai a bayyana yadda harshen Jukun ya yi tasiri ta wurin muhallin furucin  sautukan Hausa. nad’ewa za ta zama murfin babin.

Babi na hud’u yana k’unshe da shimfid’a a farkonsa sai kuma a kawo  irin musanyar da ya shafi bak’i da kuma musanyar da ya shafi wasali tare da nuna yadda ake shafe wata ga’ba ta kalma a yayin furuci. Babin zai kawo yadda ake tsarma bak’i a tsakiyar kalma tare da  nuna yadda ake shafe wani harafi a kalma, sannan a kawo fasalin da yake aukuwa wajen d’ayanta tagwan wasali. Dukkan wad’annan abubuwa suna faruwa a yayin da Jukun ke amfani  da harshen Hausa. Nad’ewa ita za ta zo daga k’arshe.

A babi  na biyar wanda shi ne babi na k’arshe. Yana k’unshe da tak’aita aikin tare da jawabin kammalawa. Manazarta da rataye su za su kasance murfin babin.

 

 

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

 

Post a Comment

0 Comments