Ticker

6/recent/ticker-posts

Sautukan Hausa A Bakin Jukunawa (1)

Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriyawww.amsoshi.com

NA

SANUSI GAMBO BELLO

BABI BA BIYAR

TAKAITAWA DA KAMMALAWA

5.0 SHIMFID’A


Wannan babin shi ne babi na k’arshe a wannan aikin don haka aka yi k’ok’arin tarkato tak’aitaccen bayanan da aka gudanar a cikin babukan da aikin ya gudana gaba-d’aya. A kaso na 5.1 an kawo tak’aitaccen bayanin aikin, sai kuma jawabin kammalawa a 5.2. manazarta ta biyo bayansu don nuna k’arewar aikin. An kawo ratayen wasu muhimmin ayyuka da aka gudanar kan kalmomin da ake samun matsalolin furucinsu a bakin Jukun don k’awata aikin, da kuma tak’aitawa mai sha’awar nazarin aikin.

5.1 TAK’AITAWA


Wannan binciken ya yi k’ok’ari na fito da irin matsalolin da ke aukuwa tsakanin harsuna biyu, wato harshen Jukun da na Hausa, yayin da mai amfani da harshen Jukun yake k’ok’arin furta sautukan harshen Hausa, da suke amfani da shi wajen mu’amalar yau da kullum, da kuma irin tasirin da ake samu daga harshen-Uwa, ta yadda aikin ya dubi al’amarin ga Jukunawa yayin da suke k’ok’arin mu’amala da sautukan harshen Hausa. Babi na d’aya wanda shi ne ginshik’in aikin, mai taken bitar ayyuka da dalilan bincike, wanda ya fara da shimfid’a don nuna yadda babin ya gudana, sannan ya yi waiwaye don duban irin ayyukan da aka gabatar da suka shafi wanann aikin don duba al’amarin da aka cimma. Haka nan babin ya dubi dalilan da suka haifar da aiwatar da wannan binciken don masu nazari su fahimta, tare da zayyano irin hanyoyin da za a bi don samun aikin ya kammala cikin sauk’i. Sa’annan babin ya bayyana irin muhimmancin da binciken ke d’auke da shi ga al’umma da kuma bayyana farfajiyar inda binciken zai tak’aita. Sannan daga k’arshe aka nad’e babin. Shi kuwa babi na biyu, mai taken dangantakar Hausawa da Jukunawa ta fuskar harshensu, bayan shimfid’a babin ya yi bayanin irin dangantakar da ke tsakanin harshen Hausa da harshen Jukun, sannan ya zayyano sautukan Hausa da na Jukun tare da bayanai da kuma misalai, sannan ya fayyace irin bambance-bambancen da ake samu tsakanin sautukan harshen biyu. Daga k’arshe aka nad’e babin don bayyana abin da aka tattauna a tak’aice.

Babi na uku wanda aka yi masa take da tsarin sautin Hausa a bakin Jukun, ta yadda ya fara da shimfid’a, sannan ya yi bayanin tsarin sautin Hausa da na Jukunawa da kuma irin tasirin da ake samu daga harshen Jukun a muhallin furucin sautukan Hausa. sa’annan babin ya yi tsokaci kan irin bambancin da ke aukuwa a wajen furucin sautukan Hausa a harshen Jukun, don mai nazari ya gane yadda al’amarin yake da kuma irin sauye-sauyen da ake samu. Babi na hud’u kuwa, mai taken gurbin sautukan Hausa a bakin Jukun, ta yadda ya fara da shimfid’a don nuna yadda babin ya  fuskanta. Sannan babin ya kawo musanyar da ake samu da ya shafi bak’i da kuma wanda ya shafi wasali ta yadda aka yi bayani tare da misalan kalmomi cikin daidaitacciyar Hausa da kuma yadda Jukunawa ke yin furucinsu. Haka kuma babin ya k’ara da kawo inda ake samun shafewar wata ga’ba ta kalma, sannan ya kawo inda ake samun tsarma bak’i a tsakiyar kalma. Babin ya yi bayani tare da kawo kalmomin da ake samun shafewar harafi a farkon kalma da wad’anda ake samu a tsakiyar kalma da kuma a k’arshen kalma, sa’annan ya kawo shafewar da ta shafi wasali a cikin kalma, sai kuma babin ya yi bayanin  d’ayanta tagwan wasula tare da ba da misalan dukkanin wad’annan sauye-sauyen cikin kalmomi ta yadda aka kwatanta su cikin daidaitacciyar Hausa da kuma yadda Jukunawa ke furta su don mai nazari ya fahimta.

5.2 KAMMALAWA


Dangane da binciken da aka gudanar daga farko zuwa yanzu, ya tabbatar da cewar akwai gagarumin tasiri da ake samu na harshen-Uwa yayin da Jukunawa ke k’ok’arin mu’amala da sautukan Hausa. Irin wannan tasirin ya shafi sautuka masu hamza (k’ugiya) ta yadda suke musanya gurbinsu da wad’anda ba su da hamza. Misali “d’aaki-daaki, k’ayaa-k’aya, tsooroo-sooro”, sannan kuma ya tabatar da aukuwar musanya sautukan da babu su a harshen Jukun da wad’anda suke da su, irin sautin /r/ a kalmar ‘‘barna’ da /r/ barna da kuma sautin /Ø/ da /f/ a Kalmar “øitsaarii > fitsaarii” ko kuma /ø/ da /p/ a kalmar “fushi > pusi”. Haka nan suna musanya gurbin wani wasali da wani, kamar /a/ da /i/ a kalmar “rakee > rikee” da /a/ da /o/ a kalmar “zarto > zorto” ko kuma /a/ da /e/ a Kalmar ”daga > dage”, haka kuma  /o/ da /u/ a kalmar  “kwaano > kwaanu”. Binciken ya tabbatar da shafe wata ga’ba ta kalma kamar haka “makaranta > manta, lokaci > loci” da kuma shafe wani harafi a kalma irin wannan ya shafi sautin bak’i da kuma dogon wasali zuwa gajere, ga misalai kamar haka: “mahaifi > ma’aifi, hawainiya > awainiya, saa’aa-sa’aa, faataarii > fataarii”, sannan ya tabbatar da aukuwar tsarma bak’i a tsakiyar kalma, ga misalai kamar haka: “Audu > Awudu, hak’uri > hank’uri.” Haka kuma binciken ya tabbatar da aukuwar d’ayanta tagwan wasali kamar haka: “Sauroo > sooroo, sai > see, daidai > dede”. Dukkanin wad’annan al’amurar binciken ya tambatar da aukuwar su yayin da Jukunawa ke k’ok’arin furucin sautukan Hausa. Daga k’arshe binciken ya gano cewar wasalin da ke biye da bak’i da kuma muhallan furucin sautuka kan taimaka wurin haifar da wad’annan sauye-sauyen na sautuka.

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

Post a Comment

0 Comments