https://www.amsoshi.com/game-da-mu/

          NA


SHEHU MUHAMMAD TAFIDAKUNDIN BINCIKE NA KAMMALA DIGIRIN FARKO (B.A Hausa) A SASHEN KOYAR DA HARSUNAN NIJERIYA NA JAMI’AR USMANU ‘DANFODIYO SAKKWATO.


https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

 

                                      Sadaukarwa                                                        


Ina mai sadaukar da wannan aikin ga Mahaifana da d’aukacin ‘yan’uwa da suka taimaka wajen ganin na kammala wannan karatun nawa. Allah ya saka da alheri, da fatar Allah ya sa mu zama sahun gaba wajen aikin alheri.

 

 

 

Tabbatarwa


Wannan kundi ya cika dukkan k’a’idojin da aka shimfid’a. Domin kammala Digirin Farko na (B.A HAUSA). A Sashin Nazarin Harsunan Nijeriya Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo Sokoto.

 

-------------------------------                                                 ------------------------

Sa hannun mai duba aiki                                                 Kwanan wata

Mal. Sama’ila Umar

 

-------------------------------                                                 --------------------------

Sa hannun Shugaban Sashi                                              Kwanan wata

Prof. S.A Yakasai

 

------------------------------                                                  -------------------------

Sa hannun mai Dubawa na waje                                      Kwanan wata

 

 

                                                Godiya


Dukkanin godiya da yabo sun tabbata ga Allah Mad’aukakin Sarki mai kowa mai komai. Tsira da amincin Allah ya k’ara tabbata ga Manzon tsira Annabi Muhammadu (S.A.W). Ina mai k’ara bayyana cikakkiyar godiyata ga Allah, da ya ba ni ikon kammala wannan binciken cikin nasara. Allah ya sa wannan aikin ya zama mai amfani ga duk wanda ya karanta shi.

Ina mik’a godiya ta musamman ga Shugabanni da d’aukacin Malaman da ke wannan sashe na Nazarin  Harsunan Nijeriya. Jinjina da yabo na musamman ga malamina da ya duba wannan aikin, Malam Sama’ila Umar. Babu shakka ya yi namijin k’ok’ari da nuna jajircewarsa wajen ganin kammaluwar wannan aiki.

Har ila yau ina mai mik’a kyakkyawar godiyata da jinjina wadda ba zan iya bayyana iyakarta ba ga babana kuma jagoran ci gaban rayuwata, wanda ya d’auki d’nauyi lura da ni a lokacin da nake gudanar da karatuna har ya zuwa kammaluwarsa, wato Farfesa A.H. Amfani, da fatar Allah ya saka masa da gidan Aljanna mad’aukakiya kuma ya yafe masa zunubansa. Ba zan mance da malamina da ke taimaka mini da shawarwari dangane da harkar karatuna ba wato Malam Naziru Ibrahim Abbas.

Wannan shafin ba zai kammalu ba har sai na mik’a godiyata ga uwa ma ba da mama, wato Hussaina Halliru Amfani (Tagwai), na gode Allah ya saka mata da mafificin alherinsa duniya da lahira. Daga k’arshe ina godewa duk d’aukacin ‘yan’uwana na gida da d’alibai ‘yan’uwana, da duk wad’anda ya ba ni gudummawa ko taimako wajen ganin na kammala wannan karatun nawa da fatar Allah ya yi sakayya da gidan Aljanna.

 

 

                                                            K’unshiya


Taken Bincike…………………………………………………………………i

Sadaukarwa………………………………………………………………...…ii

Tabbatarwa…………………………………………………………...............iii

Godiya……………………………………………………………………......iv

K’unshiya…………………………………………………………………...…vi

                              BABI NA ‘DAYA


                             Bitar Ayyuka Da Dalilin Bincike


Gabatarwa…………………………………………………………………...1

1.0 Shimfid’a…………………………………………………………………..1

1.1 Bitar Ayyukan Da Suka Gabata…………………………………………..1

1.2 Dalilin Bincike …………………………………………………………...5

1.3 Farfajiyar Bincike…………………………………………………………5

1.4 Muhimmancin Bincike……………………………………………………6

1.5 Hanyoyin Gudanar Da Bincike…………………………………………...6

1.6 Nad’ewa……………………………………………………………………7

 

 

                                    Babi Na Biyu


Ma’anar Tubulan Bincike Da Gabatar Da Tushen Bincike

2.0 Shimfid’a………………………………………………………………......8

2.1Ma’anar Zama…………………………………………………………......8

2.2 Ma’anar Gandu…………………………………………………………..10

2.3 Zamantakewar Bahaushe Da Iyalansa…………………………………...12

2.4 Zamantakewar Gargajiya………………………………………………..14

2.5 Zamantakewar Zamani…………………………………………………..15

2.6 Nad’ewa…………………………………………………………………..25

 

                                      Babi Na Uku


                              Zaman Gandu A Garin Zazzau


3.0 Shimfid’a ………………………………………………………………...26

3.1 Zamantakewar Iyali A Garin Zazzau……………………………………26

3.2 Jagoranci Da Ayyukan Ci Gaba Ga Iyali………………………………..28

3.3 Zumunci Da Matsayinsa A Zaman Gandu………………………………30

3.4 Kimar Matan ‘Yan’uwa …………………………………………………34

3.5 Nad’ewa…………………………………………………………………..36

                               

 

                                 Babi Na Hud’u


                               Tak’aitawa Da Kammalawa


4.0 Shimfid’a…………………………………………………………………37

4.1 Tak’aitawa………………………………………………………………..37

4.2 Jawabin Kammalawa ……………………………………………………40

4.3 Shawarwari………………………………………………………………40

Manazarta……………………………………………………………………41

 

Gabatarwa


Zaman gandu wani irin ingantaccen zamantakewa ne na iyali da al’ummar Hausawa ke aiwatar da shi. Ganin mahimmancin wannan zamantakewar ne aikin ya duk’ufa don zak’ulo yadda tsarinsa yake, tare da bayyana yadda ire-iren gudummawar rayuwa da suke k’unshe a cikinsa. Aikin ya k’uduri shiga cikin birnin Zazzau ne da nufin fito da fasalin zaman gandu ne don ba da gudummawa wajen adana mahimman al’adun Hausawa na gargajiya musamman wad’anda suka shafi al’ummar Zazzau.

Domin sauk’ak’a fahimtar wannan aikin ne ya sa aka kasa shi zuwa babuka hud’u kamar haka: Babi na farko ya k’unshi bitar ayyukan da suka gabata da dalilin bincike da farfajiyar bincike da muhimmancin bincike da hanyoyin da aka bi wajen gudanar da bincike. A babi na biyu kuwa aka bayyana ma’anar zama da ma’anar gandu wad’anda sune ginshik’an tubalan nazarin. An bayyana yanayin zamantakewar Bahaushe da iyalansa. Sannan aka nuna zamantakewar gagajiya da Hausawa ke yi a zamanin da ba su had’u da wata al’umma ba. Dagan a sai aka yi bayanin yanayin zamantakewar Bahaushe na zamani. A babi na uku ne aka kawo zamantakewar iyali a garin Zazzau, tare da nuna yadda ake jagoranci da kuma irin  ayyukan ci gaba na iyali, sannan aka bayyana yanayin zumunci da matsayinsa a zaman gandu. A cikin babin ne aka fito da mahangar binciken kan yadda al’ummar Zazzagawa ke kallon matan dangi tare da kimar su a tsarin zaman gandu. Yayin da babi na hud’u ya k’unshi, tak’aitawa da kammalawa tare da shawarwari.

 

 

 

 

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/