Ticker

6/recent/ticker-posts

Sarautun Gargajiya Na Bayi Da Ayyukansu A Fadar Katagum (4)

Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriyawww.amsoshi.com

NA

MUHAMMAD ABUBAKAR ZABI

BABI NA UKU

IRE-IRE SARAUTU NA BAYI A FADAR KATAGUM


3.0 SHIMFID’A


A wanna babi na uku aikin ya yi k’ok’ari kawo irin sarauatun bayi da ake da su  a fadar Katagum, da kuma irin ayyukan da suke yi da kuma irin tasiri da suke da shi a fadar ta Katagum. Bisa ga abin da wanna aikin ya nuna, duka-duka ana da ire-iren sarautu na bayi a fadar Katagum guda goma sha biyu (12) Ga su kamar haka:-

3.1    IRE-IREN SARAUTUN BAYI DA AYYUKANSU A FADAR KATAGUM



  1. Wambai:- Wannan sarauta ta wambai a yanzu wanda yake rik’e da ita Alhaji Dokta Aminu Sale, shi kuma ya kar’ba a wajen wansa Alhaji Yalwaji Mansa, shi kuma ya gaje ta daga hannun mahaifinsu, wato Wambai Salisu.


Amfanin wannan sarauata a fadar Katagum shi ne wakiltar sarki a wurin da bai samu damar zuwa ba. Bayan haka kuma shi ne, wanda ya san dukkan sirrin sarki. Tsabar muhimmancin wannan sarauata ta wambai akwai wani Baturen ingila da ya zo Katagum a shekara ta 1824, sai da ya fara ganin wambai kafin su gana da sarki.

  1. Makama:- Wannan sarauta ta makaman Katagum Alhaji Ali Hussaini shi yake rik’e da ita. Makama shi ne babban bawan sarki domin duk cikin wad’anda suke rike da sarautar bayi a fadar Katagum babu kamar sa a wajen sarki.


Amfanin mai rik’e da wannan sarautar ta makama shi ne, wanda yake rik’e da makamai a zamanin da ake yak’i sannan kuma shi yake rike da gari in sarki baya nan da sauran garuruwan Hakimai. Alal misali idan Hakimin wani gari ya mutu ko ya yi wani laifi shi ake turawa domin ya wakilci sarki a wannan garin kafin a za’bi wani. Haka kuma shi ne, mai kamawa sarki masauki in ya yi tafiya ta rangadi, kuma shi ne idan an ba wa mutum sarauata yake kawo shi ya zaunar da shi a gaban saraki kafin liman ya nad’a masa rawanin sarautar da aka aba shi. Haka zalika makama yana daga ciki mutum biyar masu za’ben sabon sarki.

  1. Sarkin Yak’i:- Wannan sarauata ta sarkin yak’in Katagum wanda yake rik’e da ita Malam Abubakar Muhammad wanda shi kuma daga hannun Alhaji Dokta Aminu Sale ya kar’ba. Babban aikin wanna sarauta a fada shi ne kan gaba a fagen fama wato shi ne ja gaban dakarun rundunar mayak’a.

  2. Sarkin Dogarai: Aikin mai rik’e da wanna sarauta shi, ne shugaban tsaro a fada wato, duk abin da ya shafi tsaro a fada, to shi yake kula da shi. Ba yadda wani abu zai shiga fada kaya ko mutum ba tare da sanin sarkin dogarai ba.

  3. Barade: Babban aikin mai rik’e da wannan sarauta a fada shi ne lokacin da za a tafi yak’i sukansa sulke wato rigar yank’i da janjami da d’amaru kala-kala domin fita yak’i. Haka kuma lokacin hawan Sallah idan sarki ya yi hawa su Barde ne kan gaba wato masu shiga gaban sarki da d’amaru kamar za a aje yak’i. Duk wannan ana yi ne domin kare lafiyar sarki.

  4. Dandalma: Amfanin wannan sarauta shi ne duk yadda muhallin fada yake to shi ne mai kula da shi bayan haka kuma duk wani taro da za a yi, in dai na fada ne, to shi ne mai gabatar da taron a ‘yan majalisar sarki. Haka kuma idan an yi aure a fada, idan dukkan biyun jinin sarauta ne, to Dandalma sai an biya shi kud’in filinsa da aka yi amfani da shi, haka kuma idan hidima a fada ce dole a sanar da shi.

  5. Hard’o: Babban aikin hard’o a fada shi ne, kar’bar kud’in haraji da jangali. Amma wannan sarauata a yanzu kusan ta daina amafani ko kuma ba ta da k’arfi sosai a fada saboda canjawar zamani. Haka kuma yana daga cikin yan goma mazauna gefen sarki, wato goma dama, goma hagun.


 

  1. Garkuwa: Aikin shi kare sarki a fagen fama da kuma duk wani kayan sarki yana hannunsa, haka kuma duk ranar Sallah yakan yi d’amaru da sulke wato rigar yak’i ta k’arfe da hamilu da janjami a k’ugu ake d’aura wa domin kare kai daga sara ya kuma rik’e garkuwa a hannu.

  2. Lifidi: Aikin mai rik’e da wanna sarauta a fadar Katagum shi ne, wakiltar makama in har baya nan. Kuma shi ne, wanda yake rik’e da ‘yan lifida, wato yana gaban sarki a kowace fita da zai yi domin kariya wato dai yana cikin dakaru masu kare lafiyar sarki.

  3. Sarkin Zagi: Babban aikin sarkin zagi a fadar Katagum shi ne, mai shiga gaban sarki in zai fita rangadi ko hawan Sallah da dai duk wani muhimmin taro, su ne gaban sarki, wato daga su sai sarki kuma wani jefen a k’asa suke tafiya ba a kan dawakai ba domin kare lafiyar sarki. Sukan yi shigar manyan kaya da bakin rawani da yafa luru ko gwado na sak’i da dora alkyabba su kuma rataya takwabi da d’ora malafa kan rawaninsu. Haka kuma shi sarkin zagi shi mai rik’a da ragamar dokin sarkin kuma shi ne shugaban zagage.

  4. Shamaki: Aikin wanna sarauta shi ne kula da dawakan sarki da kuma yan barga wato (muri) ana yi masa kirari da cewa “korau kayin baya”

  5. Shantali: Aikin mai rik’e da wannan sarauta a fadar Katagum shi ne, wanda dukkan d’awainiyar fada a hannunsa take, wato dawainiyar sarki da iyalansa.


3.2    TASIRIN MASU SARAUTAR BAYI A FADAR KATAGUM


Hak’ik’a dukkan abin da ba  shi da tasiri a wuri wani a wurin wani kuma abu ne mai matuk’ar muhimmanci gaske a wurin tasirin masu rik’e da sarautun bayi a fadar Katagum abu ne wanda ba zai misaltu ba, ballle ma har ya k’irgu, sai dai a d’an kwatanta a tak’aice, ga kad’an daga cikin tasirinsu. Masu sarautar bayi su ne masu kula da huld’od’in fada cikin da wajenta. Haka abun yake ta fuskar tsaro a fada ciki da wajenta duk wad’anna su suke da alhakin kula da su.

Haka kuma sune masu taimakawa wajen gudanar da harkokin mulki kuma sune masu kula da lafiyar sarki. Haka kuma su kan taiamaka wjen aiwatar da wasu abubuwa maimakon shi zai yi da kansa

Haka zalika sune masu wakiltar sarki in baya nan, sune kuma masu taimakawa wajen ci gaban fada. Sune wad’anda ke kare matan sarki da ‘ya’yansa wajen ganin ba abin da ya ta’ba musu lafiya. Haka kuma su wannan, su wanda sarki yake da ikon su yi duk abin da yake so ba tare da jakada tsakani ba. Haka kuma sune ke fitowa fada kullum kafin fitowar sarki. Su ne idan sarki zai zauna suke tashi da sauri su baza manya rigunansu, Saboda zaman sarki a karaga ko tashinsa.

 

 

3.3     NAD’EWA


A wannan babi mun ga irin ayyukan sarautun bayi a fadar Katagum da kuma yawansu. Yadda aikin ya nuna mana masu rik’e da wanna sarauta su goma sha biyu ne. haka kuma mun ga irin tasirin da wad’annan sarautu suke da shi a fadar, lallai mun tabbatar in babu wad’annan kusan al’amuran fada ba za su gudana kamar yadda ake buk’ata ba.

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

Post a Comment

0 Comments