Ticker

6/recent/ticker-posts

Sarautun Gargajiya Na Bayi Da Ayyukansu A Fadar Katagum (5)

Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriyawww.amsoshi.com

NA

MUHAMMAD ABUBAKAR ZABI

BABI NA HUD’U

TAKAITAWA DA SAKAMAKON  BINCIKE


4.0SHIMFID’A


Hausawa kan ce komai ya yi farko zai yi k’arshe. Wannan  batu haka  yake ko shakka, domin kuwa wannan bincike da aka gabatar kan sarautun gargajiya na Bayi da ayyukasu  a fadar Sarkin Katagum ya kawo k’arshe. Saboda a wannan  babin aka tak’aita dukkan bincike da aka gudanar, tun daga babi na d’aya zuwa na uku tare da bayyana sakamakon da binciken ya gano.

An kawo jerin manazartar da aka duba a lokacin  aiwatar da binciken. Sannan an jeru wasu wad’anda aka yi hira da su  a lokacin  gudanar da wannan bincike.

4.1 TAK’AITAWA


Godiya  ta tabbata ga Allah subhanahu wata’ala mai kowa mai komai wanda ya nufe ni da kammala wannan aiki nawa lafiya. A cikin wannan aiki a babi na d’aya  an gabatar da aikin gaba d’ayansa, kafin a yi shimfid’a. Daga nan  sai aka dubi wasu ayyukan da suka gabaci wannan aikin da aka gudanar  da ayyukansu. A nan ne aikin ya sami hujjar gudanarwa. An nuna farfajiyar aikin, tare da hanyoyin da aka bi don samun nasarar kammaluwar aikin. Sai  aka nuna muhimmancin aikin aka nad’e, babin da tak’aitaccen bayanin kamala shi.

A babi biyu an fara da shimfid’a aka duba asalin mutanen Katagum da kafuwar masarautar da masu za’ben Sarki duk a fadar Katagum. Daga nan kuma aka kawo sauran sarautun da suke k’asar Katagum, sai kuma tsarin muk’aman sarautu a fadar Katagum, sannan aka nad’e babin da  tak’aita shi.

A babi na uku baya ga shimfid’a, sai aka yi bayanin muk’aman sarautun gargajiya na bayi a fadar Katagum da bayyana ayyukan da masu  rik’e da sarautun a fadar Katagum. Da kuma irin tasirin ayyukan sarautun a fadar Katagum. Sannan aka nad’e babin da tak’aitawa. A babi na hud’u wanda shi ne, na k’arshe, babin yana d’auke da tak’aita dukkan aikin, sannan sakamakon aikin daga nan kuma sai manazarta.

4.2    SAKAMAKON  BINCIKE


Bayan kamala duba ayyukan  da suka gabaci wannan aikin. An tabbatar da cewa ba a ta’ba samun aiki da aka gudanar kan sarautun bayi  na masarautar Katagum ba. Aikin ya yi k’ok’arin fito da muk’aman bayin a fili tare da nuna yadda suke ba da gudummuwarsu wajen kula da fadar Katagum.

An gano cewa yanzu sarautar bayi ana amfani da su a fadar Katagum, duk da kasancewar yanzu ba lokacin bauta ba ne. Amma saboda muhimmancinsu har yanzu a kan yi amfani da su. A yanzu sarautun bayi a fadar ya shafi kusan dukkanin ‘bangarorin masarautar idan aka yi la’akari ta fuskar tsarin mulki, wato yadda ake gudanar da sha’anin mulkin a fadar. Haka kuma abin yake a ‘bangaren tsaron lafiyar Sarki.

Zamananci yana da tasiri ta wajen yadda a yanzu, aka sami canji a fagen sarautun bayi  a fadar Katagum. Ainihin yadda a yanzu aka yarda wanda bai gaji sarautar ba, ya shiga cikin tsarinta. A farkon zamani irin wannan al’amari ba a san shi ba, domin  kuma  kome lalacewar sarauta sai mutum ya   gaje ta  kafin a bashi ita.

Daga k’arshe za a ga tsarin sarautun bayi ya canja a yanzu, domin yana tafiya  ne da zamani don kusan ayuykan da suke gudanarwa a da, yanzu ba haka abin yake ba. Haka kuma al’adun ne na farkon zamani an yi watsi da su, an kawo sabbin al’adu  ana kuma amfani da su cikin tsarin sarautar, wannan kuwa  a yanzu shi ya kai ga mantawa da al’adu na asali na wad’annan sarautun farko suke yin amfani da su  a wajen gudanar  da mulkinsu. Duka-duka kusan ko’ina a yanzu a ‘bangarori da suka  shafi   wannan sarautar zamananci ya yi tasiri a kanta.

 

4.3 SHAWARWARI


Wannan bincike mai taken ‘Sarautun Gargajiya na Bayi da Ayyukansu a Fadar Katagum’,  ya tak’aita ne kawai ga sarautun bayi da ake samu a fadar Katagum. Kuma  ga wad’anda suke sha’awar fad’ad’a bincike kan wannan batun.  To wannan binciken yana iya zama tushe ko harsashi na dora sabon ginin wani binciken, domin gudanar da bincike a kan sarautun bayi a fadar Katagum, ko ma a k’asar Hausa  baki d’aya.

Kuma  duk  wanda zai aiwatar da bincike ya kamata ya gina shi a kan abu mai amfani ga al’umma.

 

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

Post a Comment

0 Comments