Ticker

6/recent/ticker-posts

Sarautun Gargajiya Na Bayi Da Ayyukansu A Fadar Katagum (3)

 Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriyawww.amsoshi.com

NA

MUHAMMAD ABUBAKAR ZABI

BABI NA BIYU


TARIHIN DA KAFUWAR MASARAUTAR KATAGUM

  • SHIMFIDA


A wannan babi aikin zai kawo tarihin asalin mutanen Katagum tare da bayyana yadda masarautar ta kafu. Za a bayyana masu za’ben sarki, daga baya a jero sunayen wad’anda suka gudanar da mulki a masarautar tun daga inda tarihi ya nuna zuwa yau. Bayan sanin wad’anda suka mulki garin na Katagum sai a waiwayi sauran muk’aman da masarautar take da su, tare da fito da tsarin muk’aman da aikinsu a fadar. Za a nad’e babin daga k’arshe.

2.1     ASALIN MUTANEN KATANGUM DA KAFUWAR MASARAUTAR KATAGUM.


Kusan kowace al’umma ta duniya tana da tarihin kafuwarta a doron k’asa. Al’adun wannan k’abilar suke bambanta da sauran al’ummu da suke mak’wabtaka da ita.

Ta hanyar al’adunsu ake samun tarihi wasu mashahuran shugabanni ko jarumansu da suka yi fice a duniya. Fice nasu ya dogara kan irin fagen da suka kware, wasu a fagen mulki, wasu a fagen yak’e, ya yi fice a zamaninsa.

Masana sun tabbatar da hanyoyi guda uku da ake iya k’ididdige tarihi domin a sami sahihancinsa. Hanyoyin ga su kamar haka:

Hayar ta farko ita ce ta la’akari da ajiyayyen tarihi na gargajiya wanda ake aiwatarwa a ka (kai). Wato wanda aka fi sani da kunne-ya girmi kaka.

Hanya ta biyu kuwa ita ce ta lura da wasu alamu na zahiri wato ta kula da alamu na al’ada. Hanya ta uku ita ce, ta rubutattun abubuwa ko dai wad’anda na bayansu suka rubuta suka bari ta yin amafani da hanya ta d’aya da ta biyu da ta uku. Tarihin kafuwar masarautar Katagum, da asalin sarautar da kuma tarihin asalin malam Zaki, an same shi ne ta wad’annan hanyoyi uku da aka ambata.

Tarihi ya nuna cewa akwai wasu muhimman rubuce-rubuce da littafai da k’asidu da ire-iren rahotannin da ma’aikatun gwamnatin ingila ta tattara ta hannun turawa masu yawan neman labarai ko a ce masu binciken k’asa da k’asa suka rubuta. Wanda ya shafi k’asar Katagum; misali rahoton shekara ta 1822. Da kuma irin rahotannin da ake gudanarwa duk shekara a lardin Bauchi, inda aka sami rahoton shekarar 1961.

An sami wasu tarin takardun tarihi da turawan Ingila irin su Dr. Low suka rubuta dangane da k’asar Katagum. Wani Bature mai suna Captain Clapperton da ya shigo k’asar Katagum kan hanyarsa ta zuwa Libya zamanin mulkin Sarkin Katagum Muhammad D’ankauwa a shekara ta 1824, ya gudanar da bincike kan k’asar Katagum kuma ya rubuta k’asida kan masarautar da al’ummar

Kowace al’umma tana da mafarinta don haka tarihin Katagum ba zai cika ba, sai an waiwayi tarihin garuruwan Shira da Tashena tare da al’ummarsu. Wani abin kuma sai an had’a da tarihin Sarkin farko na Katagum wato Malam Ibrahim Zaki. A nan za mu fara kawo tarihin garin Shira kafin Tashena da kuma tarihi Malam Ibrahim Zaki su biyo bayan.

 

 

2.1.1  TARIHIN K’ASAR SHIRA


K’asar Shira tana da fad’in gaske domin ta fara tun daga Buzuwa ta nufi zuwa k’asar kare-kare wato yankinsu Dambam da Potiskum ta kewaya zuwa iyakar kogin kari ta nufi Gwaram. Duk k’asar Shira ce, saboda da fad’in k’asar ya sa mutane ke yi mata kirari da badali d’ibar fari.

Wannan suna ya samu asali ne daga Shiraka wanda suka fitar da ga’bar k’arshe ya koma shira, wanda aka ce shira da Tashena da Auyu duk an samu sunayen ne daga sunayen masarautun marghi ne guda uku wanda suka fara zama a duten shira.

An samu jeren sunayen wad’anda suka yi sarautar shira tun asali a shekarar (1883), amma ruwa ya wanke rubutun. Haka kuma an ce marghi sun yi mulki fiye da shekara d’ari tara 900, kafin Fulani su tun’buke su a shekara ta 940.A.D. kusan shekara d’ari takwas kafin zuwan Shehu Usmanu Danfodi akwai harshe shiranci wanda yanzu ya ‘bata.


  • TARIHIN K’ASAR TASHENA




K’asar Tashena tana da muhimmanci sosai a tarihin kafuwar masarautar Katagum. Bayan da Malam Ibrahim Zaki ya ci Tashena da yak’i sai ya zauna a garin ya ci gaba da mulki har tsawon shekaru da d’an dama kafin ya taso ya dawo garin Katagum a shekara ta 1810. haka kuma malam Ibrahim Zaki shi da mataimakansa ne suka jaddada musulunci a k’asar Katagum.

Tarihi ya nuna kwararrafa sun ta’ba mulkin garin Tashena. Haka kuma abu ne da yake bayyane k’asar Tashena ba ta kai girman k’asar Auyo ba, balle garin Tashena daga Tashe aka samu Karin ga’bar na ya koma Tashena. Wad’ansu da suka kiyaye sunayen sarakunan Tashena sun fad’a cewa an yi har guda saba’in (70) kafin masu jahadi Malam Ibrahim Zaki su isa garin Tsahena a wajen shekara ta 1807.


  • TAK’AITACCEN TARIHIN MALAM IBRAHIM ZAKI.




An haifi Ibrahim Zaki a ranar 14-14-1165 hijirar Annabi Muhammadu sallahu alaihi wasalam wanda ya zo dai dai da Haifuwar Annabi Isah (A.S) cikakken sunansa Ibrahim tare da lak’abin “Zakiyulkalbi” sunan mahaifinsa Malam Lawal d’an Abdullahi d’an Muhammadu Sambo, d’an Hamdata d’an Abdulkadir, wadaya sunan Mahaifiyar sa kuma Fatima Nasabarsa ta isa har zuwa ga sayyadina Usmanu (A.S) amma ta wajen mahaifiyarsa.

Sanadiyar fitowar kakan-kakansa shi ne neman ilimi, wanda ya fara zuwa Adamawa, wajen sarki Adamu, wanda sarki ya ba shi yarsa Zubahawa wanda ta haifa masa d’a Muhammadu Sambo, daga nan ya kara zuwa k’asar Bagarmi inda Muhammadu Sambo ya auri yar Goni Bukar Albarnawi. A nan Hamdata ya rasu. Shi Muhammadu Sambo ya yi zamansa a Bagarmi ya haifi Abdullahi, shi kuma Abdullahi ya haifi Malam Lawan.

Malam Lawan ya yi karatu a k’asar Bagarma, sai kuma ya koma k’asar Borno. Daga k’asar Borno ya iso garin Nafad’a, sarkin Nafad’a ya ba shi ‘yarsa (ko kuma aka ce ‘yar d’an uwansa). Ta Haifa masa d’a aka sa masa suna Muhammadu Bunni. Malam Lawan ya zauna a Nafad’a tsawon shekara tara (9). Daga nan sai ya d’auki d’ansa Muhammadu Bunni sai garin yayu. Bayan shekara uku da aka san shi, Malami ne ya samu kar’buwa sosai a yayu, wanda Sarkin yayu ya ba shi ‘yarsa Fatima, wanda ta haifi masa ‘ya’ya shidda had’e da malam Ibrahim Zaki.

Haka kuma malam Ibrahim Zaki ya yi karatu a wajen malam kiyari a birnin Ngazagarmu kamar yadda Dr.Low ya fad’a a cikin littafinsa, haka kuma tarihi ya nuna a wajen shehu Usmanu Danfodiyo ya yi karatun sahihil bukari.

Ta ‘bangare yak’e-yak’e da ya yi kuma suna da yawa, ya fara kaddamar da jahadinsa a garin shellun, daga baya ya kai hari udubo, yakinsa na karshe shi ne yakinsa da Ngazargamu. Wasu ya samu nasara wasu kuma bai samu nasara ba. Daga cikin garuruwan da ya yi yaki da sun sun had’a da Udubo, Gadiya, Uzum, Faguji Gad’au, Garko Dawasa. A hankali sai da k’asar Katagum ta zama k’ark’ashin malam Ibrahim zaki ganin haka sai malam Ibrahim zaki ya himmatu wajen shirin mulkin Katagum shi kuma malam Ibrahim zaki ya gudanar da mulkinsa ne tare da shawarar mutanensa.

Bayan an tabbatar da komi a cikin Katagum, musulunci ya yi k’arfi sai malam ya maida hankalinsa ga harkokin mulki, an tattauna a kan wurin da yafi dacewa da ya zama cibiyar mulki sai shawar ta tsaya a kan tsakiyar k’asar wato Gad’iya. To amma ita kuma Gad’iya tana da matsalar ruwa. Haka dai aka ci gaba da rokon Allah kan ya ba da za’bi. Daga bisani sai shawara ta tsaya a kan a dai nemi wajen ruwa daga k’arshe aka za’bi Tashena.

A nan Tashena ne, ma, aka ce shehu ya bawa malam Ibrahim zaki da ya je ya yak’i Barno kuma ya ci nasara har ma ya zama sarkin Borno na d’an wasu watanni, shi ne ma dalilin da yasa ake masa lak’abi da sarkin Borno.

Binciken Dr. Low da ya gudanar, ya nuna cewa ana  ne malam zaki ya nemi shehu ya yi masa izini zama, amma bai yarda ba. Rashin barinsa ya zauna a k’asashen da ya ci da yak’i, inji Dr. Low zatonsa dalilin da ya sa shehu bai yarda malam Ibrahim zaki ya zauna a Borno ba gudum kada malam zaki ya kafa daula tsakanin sakkwato da Borno, ma’ana dai kada malam zaki ya fita a k’asar Usumaniya shi ne, dalilin da yasa shehu bai amince da buk’atar malam Ibrahim Zaki ba.

 


  • MASU ZA’BEN SARKI A FADAR KATAGUM





  1. Waziri shi ne kamar matsayin mataimakin sarki a wasu masarautun k’asar Hausa a al’ada idan aka kai Magana gaban sarki ko sako a rubuce,idan an ji sak’on sarki zai tambayi waziri domin ya ji nasa ra’ayi tare da neman shawar da mashawartan sarki, haka kuma waziri yana d’aya daga cikin masu za’bin sarki, inda wanda yake kai ya rasu.

  2. Galadima- A zamanin da, Galadima yana kula da abubuwan da suka shafi bayi ne, amma a yanzu shi ke gudanar da sha’anin da ya shafi al’amurran da suka shafi gari, bayan haka kuma Galadima yana daga cikin masu za’ben sabon sarkin a fadar Katagum.

  3. Makama- Babban aikin makama shi ne, wanda yake rike da makamai a zamanin da ake yaki, sannan shi ne yake rik’e gari in sarki baya nan da sauran garuruwan hakimai. Alal misali idan Hakimi ya mutu ko ya yi laifi kafin a kowa sabon sarki shi ake turawa. Haka kuma yana d’aya daga cikin masu za’ben sabon sarki a fadar Katagum.

  4. Liman- zai kasance shugaban al’umma musulmi shi ne shugaba a harkokin addini kamar sallah da kuma sauran harkokin rayuwa, misali su aure, da zaman jama’a da kula da tarbiyar. Haka kuma liman a fadar Katagum yana d’aya daga cikin masu za’ben sabon sarki, saboda muhimmancinsa a cikin al’umma.

  5. Madaki- shi ne mai kula da dawakin fada shi ma kamar dogari yake, amma ya fi sauran muhimmanci.


    • WAD’ANDA SUKA YI MULKI A FADAR KATAGUM






Masarauta Katagum ta yi zamani mai tsawo, inda har ta sami jeren sarakuna da dama da suka mulke ta. Wad’annan sarakuna sun taka muhimmiyar rawa wajen ganin masarautar ta yi fice ta fuskoki da dama. Al misali,ta fuskar jaramtaka masarautar ta yi yake-yake da suka sa ta cikin jerin k’asashen da suka yi suna a fagen yak’i.

A k’alla masarautar katagum tana da jerin sarakuna fitattu har goma sha d’aya. An fara lissafa jerin sakunan ne tun daga kan sarkinta da aka fi sani da Malam Zaki. A k’ark’ashin wannan ka son ga yadda jerin sarakunan suke bi-da-bi don fito da su fili.


  • SARKIN KATAGUM IBRAHIM ZAKI (SARKI NA FARKO)




Malam Ibrahim Zaki da ya ga cewa duk k’asar Katagum jahadi ya je kuma musulunci ya samu kar’buwa, sai ya maida hankalinsa wajen ganin shari’a ta samu gindin zama a zukatan mutanen Katagum. Abin da ya fara yi shi ne, d’auke cibiyar mulki daga Tashena ya mayar da ita garin Katagum a shekara  1810.

Na biyu kuma, abin da malam Ibrahim Zaki ya yi shi ne, sai ya rarraba muk’amai a masarautar Katagum. Malam zaki ya nad’a D’ankauwa d’an malam Bunni a matsayin sarkin shira, ya nad’a babban d’ansa Abdulrahman a matsayin sarkin Azare, sai ya nad’a d’ansa Isma’ila a matsayin yariman cinade (Hakimin Cinada) har ila yau ya nad’a d’ansa Yusuf a matsayin Sarkin Udubo.

Malam Ibrahim Zaki kafin rasuwarsa ya kafa masarautu 103, aikinsu da sanin Amirul muminin ya kuma rasu a shekara ta 1814. kafin rasuwarsa malam Ibrahim zaki Allah ya wadata shi da ‘ya’ya guda goma sha shida, guda goma sha biyar maza guda d’aya ‘ya mace, sha d’aya sun yi sarauta guda hud’u kuma Allah bai yi ba.


  • SARKIN KATAGUM SULAIMAN LIMAN ADANDAYA (SARKI NA BIYU)




Bayan rasuwar Malam Zaki wanda ya fi kowa cancanta ya gaje shi, don karatunsa da dad’ewa a gwagwarmayar jihadi shi ne k’anensa, kuma shak’ik’insa Sulaiman Adandaya d’an Malam Lawal. Sai dai a lokacinsa an d’an samu sa’bani tsakaninsa da mutane Tashena, wanda har ta kai lokacin da ya tafi sakkwato domin mubaya’a suka kar’bi mulkin. Bayan dawowarsa bai wuce shekara biyu a kan mulki ya yi murabus.

A binciken da aka gudanar kafin ya rasu ya haifi ‘ya’ya kamar haka; Allah ya ba shi ‘ya’ya guda hud’u d’aya mace, uku maza a cikin ukun guda ne ya yi sarauta.

2.3.3 SARKIN KATAGUM MUHAMMAD DANKAUWA (SARKI NA UKU)


Bayan sarkin Katagum sulaiman Adandaya ya yi murabus wanda ya ga je shi muhammadu Dankauwa d’an malam Bunni a shekara ta 1816. kuma daga kansa ne aka fara samun duk wanda ya mulki shira shi ake kyautata zaton zai mulki fadar Katagum.

Sarkin Katagum Dankuwa ya rasu a shekara 1846, kafin rasuwarsa Allah ya azurta shi da ‘ya’ya bakwai duk maza, d’aya daga cikinsu ne kawai bai yi mulki ba.


  • SARKIN KATAGUM ABDULRAHMAN (SARKI NA HUD’U)




Abdulrahman shi ne babba a cikin ‘ya’yan Malam Ibrahim Zaki, ya kuma rike sarautar Azare a shekara ta 1807-1814, sannan ya zama sarkin shira a shekara 1816-1846 ya kuma yi shekara biyu a gadon mulkin Katagum kafin rasuwarsa Allah ya ba shi ‘ya’ya tara hud’u mata biyu maza hud’u daga cikin mazan sun yi sarauta.


  • SARKIN KATAGUM ABDULK’ADIR NA I (SARKI NA BIYAR)




Abdulk’adir I d’a ne ga Dankauwa, kuma shi ne sarkin Katagum a bayan rasuwar Abdulrahman. Daga kan Abdulk’adir I sarautar Katagum ta dawo gidan Dankauwa har zuwa yau. Abdulk’adir I ya yi sarauta daga shekara ta 1851-1868.

Kafin rasuwarsa  a 1868 ya hafi ‘ya’ya guda hud’u duk maza ne, kuma sun yi sarauta dukkansu.


  • SARKIN KATAGUM MUHAMMADU HAJJI




Muhammadu Hajji ya gaji wansa Abdulk’adir I. daga hawansa ya fuskanci bore iri-iri daga k’abilun kare-kare, kuma a lokacin ne Katagum suka yi yak’i da Ningi an yi yak’in ne a shekara ta 1883.

Haka kuma Muhammadu Hajji shi ya jagoranci yak’in da sarkin musulmi ya tura su Gobir da marad’i, yak’in da aka fi sani da yak’in madarumfa, Muhammadu Hajji ya rasu a ashekara ta 1896.


  • SARKIN KATAGUM ABDULK’ADIR NA II (SARKI NA BAK’WAI)




Abdulk’adir ya gaji mahaifinsa Muhammadu Hajji ya zama sarkin Katagum bayan  rasuwar mahaifinsa ya fuskanci hare-hare daga Ningi a lokacinsa ne kuma aka yi yak’in Gamawa a (1900), Haka kuma a lokacinsa ne Baturen Ingila mai suna Captain Swords column ya zo Katagum a shekara ta 1902.

Haka kuma sarki Abdulk’adir ya rasu a watan mayu na 1905.

 

2.3.8 SARKIN KATAGUM MUHAMMADU (SARKI NA TAKWAS)


Muhammadu ya zama sarki bayan rasuwar mahaifinsa Abdulk’adir II. Ya kuma hau sarautar Katagum a shekara ta 1909, Haka kuma rasuwarsa ta haifar da rigima a Katagum har ta kai aka sace tuta.

2.3.9 SARKIN KATAGUM ABDULK’ADIR III (SARKI NA TARA)


Abdulk’adir III ya zama sarkin Katagum bayan rasuwar mahaifinsa Muhammadu a lokacin da mahaifinsa Muhammadu ya rasu, da farko masu za’ben sarki sun za’bi k’aninsa sarkin Gad’au Matta a matsayin sarkin Katagum. Bayan nan ne, wasu daga cikin masu za’ben sarkin suka sanarwa Turawa cewa shi sarkin da ya  rasu yana da babban d’a. A lokacin Abdulk’adir na III yana matsayin Hakimin Azare. Turawa da wasu masu za’ben sarki suka ce lallai sai dai a nad’a Abdulk’adir III. Hakan kuwa aka yi, Katagum ta kasu kashi biyu, wasu na goyon bayan matta, da kuma ‘bangaren Abdulk’adir. Daga cikin masu goyon bayan Matta suka sace tuta aka boye a yashin kogi, wasu kuma sun ce a bayan gari aka ‘boye ta.

A lokacin Abdulk’adir ne Turawa suka yak’i Hard’awa da zadawa a k’ark’ashin Katagum suka maida misau saboda wasu dalilai.

A lokacin sa ne aka fara bud’e makarantar zamani ta farko a garin Azare, wato Central firamare a shekara ta 1940, shi da Baturen Ingila mai suna captain Makenze. Abin da ya sake faruwa a lokcinsa na tarihi shi ne dawo da hedikwatar masarautar Katagum cikin garin Azare daga tsohon garin Katagum a shekara ta 1911. saboda wasu dalilai.

2.3.10 SARKIN KATAGUM UMARU FAROUK (SARKI NA GOMA)


Umaru farouk shi ne, sarki Katagum na goma ya zama sarki a bayan murabus d’in mahaifinsa Abdulk’adir III. A lokacin mulkin Umaru aka kafa Nati’be Authority (NA). haka kuma Katagum ta samu ci gaba mai yawan gaske da ya had’a da ruwan fanfo a garin Azare. Uamaru farouk ya yi shekara talatin da uku (33) yana gadon sarautar Katagum wato daga shekara ta 1947-1980.

2.3.11        SARKIN KATAGUM MUHAMMADU KABIR UMAR


Muhammadu Kabir umar  ya gaji ubansa a shekara ta 1980, kuma a zamanin Alhaji Dr Kabir Umar an samu canje-canje na zamani masu d’inbin yawa ta ‘bangarori da dama. Allah cikin ikonsa har yanzu shi ke rik’e da sarautar Katagum.

SARAKUNAN KATAGUM

2.4    SAURAN SARAUTUN DA KE K’ASAR KATAGUM (HAKIMAN SARKIN KATAGUM)


Katagum k’asa ce mai fad’in  gaske, dan haka sarki ya wak’ilta wak’ilansa a sassa daban daban na k’asarsa. Wanda ita ma Katagum kamar sauran masarautun k’asar Hausa ne tana da tsarin shugabanci kamar haka.

Hakimi

Dagaci

Mai anguwa

Abin nufi a nan shi ne, Hakimi shi ne gaba da dagaci, dagaci kuma shi ne gaba da mai unguwa.

K’asar Katagum tana da Hakimai a k’alla goma sha biyu (12) ga su kamar haka

  1. Sarkin Shira Hakimin  Shira

  2. Sarkin Azare Hakimin Azare

  3. Galadiman Katagum Hakimin Katagum (zaki)

  4. Sarkin dawakin Katagum Hakimin Madara

  5. Sarkin Sakuwa Hakimin Sakuwa

  6. Yariman Cinade Hakimin Cinade

  7. Sarkin Gad’au Hakimin Gad’au

  8. Sarkin Disina Hakimin Disina

  9. Sarkin Udubo Hakimin Udubo

  10. Tafidan Katagum Hakimin Itas

  11. Sarkin Gamawa Hakimin Gamawa

  12. Sarkin Giade Hakimin Giade


Dukka wad’annan suna matsayin wakilan sarkin Katagum ne a yankunan na su.

 

 

2.5    TSARIN MUK’AMAI A FADAR KATAGUM


Wannan wani ‘bangare ne na gudanar da harkar mulki a fada, wato mataimaka wajen gudanarwa. Ga su kamar kaha:

  1. Sarki: Shi ne shugaban wato shi ne a gaban kowa shi ne mulki ke hannunsa da iko a k’asar da yake shugabanta baki d’ayanta. (Alhassan it. Eta, 1985:76).



  • Waziri: Shi ne, kamar matsayin mataimakin sarki a wasu masu sarautun k’asar Hausa, domin a al’ada idan aka kai Magana gaban sarki ko sako a rubuce idan an ji sak’on sarki zai tambayi waziri domin ya ji nasa ra’ayi tare da neman shawar daga mashawartan sarki.



  1. Galadima: A zamanin da Galadima yana kula da abubuwa da suka shafi bayi ne, amma a yanzu shi ke gudanar da sha’anin da shafi al’amuran da suka shafi gari

  2. Magajin Gari: Yana daga cikin manya masu bawa sarki shawara dangane da dukkan abin da ya shafi aikace-aikacen gona na masarauta a wancan lokacin, amma a yanzu yana gadar sarki ne idan baya nan.

  3. Turaki: Wannan sarauta ta kasu kashi biyu kamar haka:

    • Turakin cikin gida

    • Turakin waje




Turakin cikin gida: shi ne mai kula da dawakin sarauta na cikin gidan sarki kuma shi ke ba da doki ga duk wanda sarki ya ce a ba doki.

Turakin waje: shi ne mai kula da dawaki musamman a wajen yak’i, misali idan dokin wani ya kasa a wajen yak’i, to zai dubi yiwar sama masa wani dokin a wancan zamanin.

Wasu kuma suna ganin mai rika da sarautar turaki yana iya zama jagoran mayak’an sama, wato mayak’an da ke bisa dawakai, kuma yana iya kar’bar dokin wani a wajen yaki idan ya ga wancan d’in bai cancanta da wannan dokin ba. (Jega S.M 1994:5)

  1. Sarkin Gida: Mutum ne wanda ke zama can kusa da barayar sarki, kuma yana iya shiga ko’ina a cikin gidan sarki amma wannan yana faruwa ne a lokutan da suka gabata da kuma yanzu a warare

  2. Shamaki: Shi ne ake fara gani kafin sarki ya fito daga cikin gidansa. Kuma shi yake yi wa mutane iso zuwa ga sarki don neman biyan buk’atar rayuwa.

  3. Shimfid’a: Shi ne wanda yake da hak’k’in kula da barayar sarki da duk wani abu da ya shafi shimfid’un sarauta da tufafi abinci shi ma yana wannan hidimar ne a lokatan da, da suka gabata.

  4. Sallama: Shi ne, mai raba kyatuttukan sarki da kuma isar da gaisuwar talakawa zuwa ga sarki, shi sallama har yanzu yana gudanar da hidima ga sarki


10 Barga: Shi ne, mutumin da ke kula da abincin dawakin sarki da kilisarsa da kuma lafiyarsa. Shi ma har yanzu yana gudanar da wanna hidimar ga sarki

 

  1. Sardauna: Shi ne, magatakaradan sarki, wato shi ke karanta da kuma rubuta sak’on sarki.

  2. Shantali: Shi ne, mai kula da takalmin sarki kuma shi ke d’ebowa sarki ruwa idan zai yi wata buk’ata.

  3. Wali: Sarauta ce da ake bayarwa ga wanda ya fito daga gidan malamai ko limamai, saboda haka yawanci mai ilimi na addini ake bawa wanna matsayi. Wannan bayani an samu shi ne daga (Bunun Tsafe 2004).


2.6     NAD’EWA

Wannan shi ya kawo mu k’ashen babi na biyu. A nan mun ga muhimman abubuwa game da k’asar Katagaum da kuma sarakunan Katagum, da irin rawar da suka taka a wajen ha’baka daular Usumaniyya da kuma fito da masarautar Katagum a fili k’arara. To wannan hanyar mun ga irin ci gaban da aka samu daga sarkin farko har zuwa na goma sha d’aya. (Dangane da kafuwar masarautar bisa tsarin masulunci).

 

 

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

Post a Comment

0 Comments