Ticker

6/recent/ticker-posts

Kwatanci Na Kamanci Da Bambanci Tsakanin Jimlar Tambaya Da Jimlar Korewa Ta Hausa Da Ta Fulatanci (1)

 Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriyawww.amsoshi.com

NA

DAYI RILWANU

TABBATARWA


Mun tabbatar da cewa wannan aiki ya cika sharud’d’an da jami’a ta shimfid’a wanda ake buk’atar duk d’alibin da ya kai shekarar karatu ta k’arshe, da ya rubuta kundin bincike domin ba da gudummuwa ga masu buk’atar nazari a Sashen da ya gudanar da karatu.

____________________                                       __________________

Sa Hannun Mai Dubawa                                                 Kwanan wata

Mal. Sama’ila Umar

 

 

 

____________________                                       _________________

Sa Hannun Shugaban Sashe                                            Kwanan wata

Prof. Atiku Ahmad Dunfawa

 

 

 

 

___________________                                                  _____________

Sa Hannun Mai Dubawa Na Waje                                    Kwanan wata

______

SADAUKARWA


Na sadaukar da wannan aiki nawa ga iyayena da kuma ‘Yan’uwana. Da fatar Allah Ubangiji Sarki Ya saka musu da mafificin alherinSa Ya albarkaci rayuwarsu Ya kuma nufe su da cikawa da imani amin.

 

 

GODIYA


Dukkan godiya da yabo sun tabbata ga Allah mak’agin halitta, kuma fiyayyen masani wanda ya sanar da d’an Adam abin da bai sani ba, ya kuma umurce shi da neman ilimi da yad’a shi. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzon Allah Annabi Muhammadu (S.A.W.) fiyayyen halittu wanda ya kwad’aitar da a nemi ilimi komai nisan wurin za a same shi.

Ina mik’a godiyata mai d’imbin yawa ga malamina kuma uba a gare ni, wanda ya jure da yanayin rayuwata, yake ba ni shawarwari kuma yake d’aukar nauyin duba wannan aiki nawa. Wannan malami shi ne malam Sama’ila Umar Allah ya saka masa da mafificin AlherinSa ya kuma gafartawa mahaifansa ya sa aljanna ta zama makomarsu shi da zuriyarsa baki d’aya amin.

Godiya ta musamman ga dukkan malaman Sashen Harsunan Nijeriya da na Sashen Turanci dukkansu na Jami’ar Usmanu ‘DANFODIYO Sakkwato. Ina mik’a godiyata ga malam Nazir Abbas da Dr. Umar Bunza, haka kuma, ina mik’a godiyata ga iyayena, da kuma ‘yan uwana da abokan arzik’i na gida da kuma wad’anda muke tare da su a makaranta baki d’aya. Har ila yau, ina mik’a godiyata ga duk wanda ya ba da taimako ta kowane fanni domin ganin cewa na sami nasarar ci gaba a tsarin rayuwata, don ganin rayuwata ta inganta. Haka kuma wannan aikin ba zai kammala ba sai na mik’a godiyata ga abokaina Tukur Umar, Abdullahi Usman da Is’haka Aliyu da Abubakar Mainasara da Adamu Lemu da Lawal Ahmad Maru da dai sauran abokan karatu gaba d’aya, na gode Allah ya saka da mafificin alherinSa gare su da iyalanSu baki d’aya.

Ba zan yi tuya in manta da albasa ba, tilas ne in mik’a godiyata ga malamina, wato malam Yusuf Ka’oje da ke Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sakkwato (C.O.E.) wanda ke Sashen Koyar da Harshen Fulfulde. Ya taimaka min matuk’a wajen ganin wannan bincike ya kammala, ba abin da zan ce sai godiya mai tarin yawa a gare shi Allah ya saka mishi da alherinSa amin.

Godiya ta girmamawa zuwa ga yayyena da k’annena wad’anda su ne matsayin jagorannina ta kowace hanyar rayuwata, ina mik’a godiya da kuma gaisuwar ban girma zuwa ga Nasare Dayi da Fatima Dayi da Faruku Dayi da Abubakar Dayi da fatar Allah ya taimake su da hanyoyin alherinSa fiye da taimakon da suka yi min. Haka kuma ina mik’a gaisuwata zuwa ga k’annena Hadiza Dayi da Halima Dayi da kuma masoyiyata Hassana D. Muhammad Zagga da fatar Allah ya taimake su da alherin Sa fiye da tamakon da suka yi mini.  Allah (S.A.W.) Ya taimaki duk wanda ya ba ni gudummuwa wajen ci gaban rayuwata da tarbiyyata, Ya kuma saka masu da gidan aljanna Amin.

 

 

 

GAB ATARWA


Babu shakka masana da manazarta sun yi bayanai masu muhimmanci da gamsarwa a kan harshen Hausa. Hausa harshe ne wanda duk d’an asalin harshen yake tunk’aho da shi. Harshen Hausa yana d’aya daga cikin harsunan da ake samu a nahiyar Afirika ta Yamma. A nazari irin na masana ilimin kimiyar harshe, harshen Hausa yan a cikin wani gundari babban rukuni na sauran harsunan duniya. Wannan aiki ya gudanar da bincike ne a kan yadda ake samun kamanci ko bambanci tsakanin jimloli biyu na Hausa da na Fulatanci (Fulfulde) wato jimlar korewa da ta tambaya, domin fayyace irin dangantakar da ake samu tsakaninsu.

An karkasa aikin zuwa babi-babi inda aka fitar da babuka hud’u don samun nasarar kammaluwar aikin. Babi na farko yana d’auke ne da Shimfid’a da kuma Waiwayen ayyukan da aka gabatar da suka shafi nahawun harshen Hausa da na Fulatanci (Fulfulde). Bayan an waiwayi ayyukan masana sai aka sami dalilin gudanar da binciken da kuma manufar da bincike yake d’auke da shi. An bayyana farfajiyar da za a gudanar da binciken, da hanyoyin gudanar binciken da kuma muhimmancin da binciken yake da shi. Daga k’arshe kuma sai aka nad’e babin da tak’aita abin da ya k’unsa.

A babi na biyu kuma an fito da ma’anar jimlar Hausa da ta Fulatanci (Fulfulde)) da ire-iren jimla, kamar jimlar tambaya, jimlar korewa, jimlar umurni da kuma sassauk’ar jimla. Daga k’arshe kuma an nad’e babin da bayanin kammalawa.

A babi na uku kuma an nuna kamanci na jimlar tambaya ta Hausa da ta Fulatanci (Fulfulde) da kuma Bambanci na jimlar tambaya ta Hausa da ta Fulatanci (Fulfulde). Haka kuma, an fito da kamanci da  Bambanci na jimlar korewa ta Hausa da ta Fulatanci (Fulfulde). A k’arshe an nad’e babin ta hanyar tak’aita jawabin kammalawa.

Babi na hud’u kuwa babi ne da yake k’unshe da tak’aitawar aikin gaba d’ayansa, tare da jawabin kammalawa. Manazarta ta biyo baya domin inganta aiki gaba d’aya.

 

 

ABUBUWAN DA KE CIKI


 

Tabbatarwa                                                                              ii

Sadaukarwa                                                                             iii

Godiya                                                                                               i’b

Gabatarwa                                                                                ‘bii

Abubuwan da ke ciki                                                                id’

 

BABI NA D’AYA: BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA


1.0     Shimfid’a                                                                                 1

1.1     Bitar Ayyukan Da Suka Gabata                                                 1

1.1.1  Bitar Kundaye                                                                          2

1.1.2  Bitar Muk’alu                                                                          4

1.1.3  Bitar Littattafai                                                                         6

1.2     Dalilin Bincike                                                                         8

1.3     Manufar Bincike                                                                      8

1.4     Farfajiyar Bincike                                                                     9

1.5     Hanyoyin Gudanar Bincike                                                       10

1.6     Muhimmancin Bincike                                                             11

1.7     Nad’ewa                                                                                  11

 

BABI NA BIYU: MA’ANAR JIMLAR HAUSA DA RABE-RABEN TA


2.0     Shmfid’a                                                                                  12

2.1     Ma’anar Jimla                                                                          12

2.2     Ire-Iren Jimlolin Hausa                                                             13

2.3     Jimlar Tambaya                                                                        15

2.4     Jimlar Korewa                                                                          17

2.5     Sassauk’ar Jimla                                                                       21

2.6     Jimlar Umurni                                                                          22

2.7     Nad’ewa                                                                                  24

 

BABI NA UKU: KAMANCI DA BAMBANCI NA JIMLAR TAMBAYA DA TA KOREWA TA HAUSA DA TA FULATANCI (FULFULDE)


3.0     Shimfid’a                                                                                 25

3.1     Kamanci na Jimlar Tambaya Ta Hausa Da Ta Fulatanci

(Fulfulde)                                                                                 25

3.2     Bambanci na Jimlar Tambaya Ta Hausa Da Ta Fulatanci

(Fulfulde)                                                                                 28

3.3     Kamanci Na Jimlar Korewa Ta Hausa Da Ta Fulatanci

(Fulfulde)                                                                                 30

3.4     Bambanci Na Jimlar Korewa Ta Hausa Da Ta Fulatanci

(Fulfulde)                                                                                 32

3.5     Nad’ewa                                                                                   34

 

 

BABI NA HUD’U: TAK’AITAWA DA KAMMALAWA


4.0     Tak’aitawa                                                                               35

4.1     Kammalawa                                                                             36

4.2     Shawarwari                                                                              38

Manazarta                                                                                40

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

Post a Comment

0 Comments