Ticker

6/recent/ticker-posts

Sarautun Gargajiya Na Bayi Da Ayyukansu A Fadar Katagum (2)

 Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriyawww.amsoshi.com

NA

MUHAMMAD ABUBAKAR ZABI

BABI NA ‘DAYA


BITAR AYYUKAN  DA SUKA GABATA DA HUJJAR CI GABA DA BINCIKE


GABATARWA


A duk inda aka samu al’umma suna zaune a wuri d’aya, suna gudanar da rayuwarsu bai-d’aya za a same su bisa wani tsari na musamman, wanda aka d’ora bisa wata k’a’ida da aka amince da cewa mutum guda ya zama shugabansu domin ya jagorance su. Irin wannan shugabancin yakan bambanta daga wuri zuwa wuri, saboda bambanci al’adun al’ummar da tsarin rayuwa ta yau da kullum da kuma fasalin muhallinsu.

Dalilin da ya haifar da wannan bincike shi ne, za a dubi wani ‘bangare ne na tsarin shugabanci a k’asar Hausa musamman ma irin muk’aman da bayi kan rik’e a fada. Binciken zai waiwayi irin gudummawar da suke bayarwa ta wajen raya k’asa. Aikin ya ke’banta ne a ‘bangaren masarautar Katagum. A masarautar ma za a dubi tsarin sarautar Bayi ne, na masarautar.

Katagum k’asa ce da ta yi suna a fagen yak’e-yak’e, domin an sami gwarazan sarakuna da suka yi fice k’warai da gaske. Katagum tana d’aya daga cikin k’asashe masu mak’wabtaka da k’asar Hausa tun kafin zuwan masu jahadi.

Manyan sarakunan Katagum sukan rarraba muk’amai ga al’umma ko mutane da suka dace su jagoranci jama’a, ba tare da nuna son zuciya ba. Masarautar tana kulawa da hak’ok’in kowane rukuni na al’ummarta. Daga cikin ire –iren al’ummar da suka sami gatan kula da hak’k’in nasu har da bayin da masarautar ta mallaka.

A mafi yawancin daulolin k’asar Hausa sun fi mai da hankali kan muk’aman da suka shafi ‘ya’yan gidan sarauta. Misali ana samun irin sarautun Waziri da Galadima da Ciroma da sauran muk’aman da suka shafi zuriyar masarauta. Wato ba a faye duba sarautun da bayi kan rike ba. Misalin irin sarautun da Bayi kan rik’e a k’asar Hausa akwai ‘shantali’ da ‘figini’ da ‘zagi’ da wasu muk’amai da ake kula da lafiyar sarki ko masarauta.

Ganin yadda masarautar Katagum ke ba da muhimmanci kan sarautun Bayi, shi ya sa aikin ke son gudanar da bincike kan ire-iren sarautun Bayi a fadar Katagum, tare da nuna irin ayyukan da suke gudanarwa a fadar. Wannan aikin an kasa shi zuwa babi-babi har guda hud’u, kamar yadda za a ga bayanin yadda aikin ya gudana a nan gaba kad’an.

Babi na d’aya yana d’auke da shimfid’a sannan  an gudanar da bitar ayyukan da suka gabaci wannan aikin da nufin samun madafar ci gaba da wannan binciken. Samun hujjar yin aiki ya ba da damar nuna hanyoyin da za aka bi don samun nasarar kammaluwar aikin. Kafin ci gaba da binciken an fad’i iyakar farfajiyar aikin, sai kuma aka nuna muhimmancin binciken. Daga k’arshe aka nad’e babi domin nuna matsayar aikin.

A babi na biyu aikin ya nuna inda aka dosa, bayan shimfid’a, sai aka bayyana asalin mutanen Katagum da kafuwar masarautar. Bayan an nuna yadda masarauta ta kafu, sai aikin ya fito da fasali ko tsarin masu za’ben sarki a fadar. An kawo jerin sarakunan da suka mulki masarauta a k’ark’ashen wannan babin. Nuna yanayi muk’aman masarautar ya taimaka wajen fahimtar ire-iren sarautun Bayi na masarautar sai kuma aka nad’e babin da tak’aita abin da ya gudana a cikin babin.

Babi na uku, bayan an yi shimfid’a sai aka kawo bayani game da ire-iren muk’aman sarautun bayi a fadar Katagum. Sannan sai aka bayyana irin ayyukan da masu irin wannan sarautun suke aiwatarwa a fadar. Haka kuma an bayyana irin mahimmancin ayyukan da masu irin wannan sarautar suke gudanarwa a fadar ta Katagum.

Daga k’arshe kuma  binciken ya shiga cikin babi na hud’u, inda ya fara da shimfid’a, sannan sai aka kawo tak’aitaccen jawabin da aikin ya k’unsa, wanda daga nan aka nad’e babin da sakamakon bincike da aikin ya gano. Daga nan sai aikin ya bayar da shawarwari ga masu nazari. Sai manazarta ta biyo baya.

 

 


  • SHIMFI’DA
A k’ark’ashin wannan babin, binciken ya yi tsokaci ne kan abin da ya shafi muhimman abubuwa da aka gudanar a aikin, kamar haka: Bitar ayyukan da suka gabata shi aka fara kawowa, sannan hujjar ci gaba da bincike da farfajiyar bincike. An  dubi hanyoyi gudanar da bincike, sannan aka kawo muhimmancin binciken. Ga yadda aikin ya kasance d’aya- bayan- d’aya.

1.1     BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA


Abin da ya wajaba ga kowane irin bincike makamancin wannan kafin a gudanar da shi, shi ne a dubi nazarce-nazarce da aka yi a fagen bincike don gane ayyukan da aka yi a fagen nazari saboda gudun maimaita abin da aka rigaya aka aiwatar. Abin so shi ne, ko dai a d’ora a kai ko a kalli wani ‘bangaren da ba a ta’bo shi ba. Ko kuma a kafa hujja da rashin samuwar ingataccen nazari a kan abin da aka gudanar da nazarin a kai. Don a samar da hujjar ci gaba da wanna binciken. Wannan nazari shi ma ba zai kauce wa irin wannan tsarin ba. Don haka a nan binciken ya mai da hankali ne ga duban ayyukan da suka gabaci wannan aikin wad’anda suke da dangantaka da shi. Daga cikin ayyukan da binciken ya nazarta, akwai wad’anda suka shafi sarautun gargajiya tsantsa da kuma wad’anda suka shafi masarauta ko kuma k’asar Katagum ko kuma k’asar Hausa baki d’aya.

Gowers (1903) ya bayyana Katagum a matsayin lardi daga cikin lardunan arewa, a cikin rubutunsa da ya yi wanda ya bayyana matsayin kowane lardi na arewacin Nijeriya. wannan rubutu bai gamsar da wannan bincike ba, Saboda aikin ya ke’banta ne kan matsayi da aikin larduna ba masarauta ba. Don haka wannan binciken ya ke’bantar da nazarinsa a kan sarautun bayi a masarautar Katagum. Shi kuwa wanna manazarcin bai ta’bo wajen da wannan yake son ta’bo wa ba. Saboda haka ne, wannan matsayin ya ba binciken damar ci gaba da wanzuwa.

Fremantle  (1903) wannan shi ne,  Razdan na farko, kuma ya yi rubuce-rubuce masu yawa a kan k’asar Katagum, ya bayyana cewa: “k’asar Katagum da Had’eja da Jama’are sun bi Turawa ne cikin ruwan sanyi a shekarar (1903) bayan Kano ta mik’a wuya ba tare da tashin hankali ko gardama ba. Wannan ba shi ne damuwar wannan bincike ba, don haka ganin wanna ya ba mu damar ci gaba da bincike.

Alk’ali, (1979) ya rubuta kundin digirinsa na farko mai taken “A Hausa community in crisis, Katagum in nineteenth century” a Jami’ar Maiduguri a cikin kundin nasa ya bi diddigin tarihin kafuwar Katagum da irin bajintarta da kuma rawar da sarakunanta suka taka. Alk’ali ya bi tarihin Katagum ne da bajintar da sarakunanta suka nuna, shi kuma wannan binciken ya yi Magana ne a kan ire-iren sarautun bayi na masarautar Katagum. Ganin cewa aikin ya sami bambancin da wannan, shi ya sa aka sami damar ci gaba da gudanuwa wannan binciken.

Jibril, (1985) ya bayyana cewa an samu sarautun gargajiya ne, a masarautar Katagum tun farkon mulkin Malam Zaki. Muk’aman su ne kamar haka: ‘Galadima’ da ‘Makama’ da ‘Sarkin yak’i’. Wannan aiki na Jibril ya bar wani gi’bi domin bai ta’bo ‘bangaren sarautun bayi ba. Wanna ya ba da damar ci gaba da wannan binciken.

Muhammad, (1987) ya rubuta kundin digirinsa na farko mai taken ‘tasirin sarautar Hausawa bisa kabilu Urawa da kamukawa a k’asar kwangwama ta jihar Neja’. Ya nuna irin tasirin da muk’aman sarautun Hausawa suka yi a kan kabilu biyu. Wato aikin na Muhammad ya yi magana ne kan sarautun Hausawa da wasu k’abilu na k’asar Neja. A inda wannan aikin kuma yake magana a kan muk’aman sarautun k’asar Katagum, a k’asar Katagum d’in ma an yi tsokaci ne kan sarautun bayi kawai. Don haka wannan binciken ya sami dalilin da ya dogara da shi wajen yiwuwar cigabansa.

Bature Z.M. (1992). Ta rubuta kundin digirinsa na farko mai taken ‘Nad’in sarautu a birnin sakkwato’. Yadda ta nuna hanyoyin da ake bi wajen nad’in  sarauta a k’asar Sakkwato. Don haka a wannan binciken ya bar wani babban gi’bi, domin bai ta’ba bangaren sarautar bayi ba. An yi magana ne a kan yadda ake nad’in sarauta a k’asar sakkwato, don haka an samu damar aiwatar da wannan.

Zungeru I.M (1993) marubucin ya gudanar da bincikensa ne, kan sarautun gargajiya da gudumuwar da suka bayar a k’asar Hausa” ya kawo tushen sarauta a k’asar Hausa da kuma irin gudanarwar da sarakunan ke bayarwa dangane da ci gaban k’asa. A wanna ya kawo irin gudumawar da sarakuna ke bayarwa, wannan aikin kuma zai duba tsarin sarautun bayi ne a k’asar Katagum don haka aikin bai zo guda ba, wannan ne ya ba mu dammar ci gaba da gudanar da wannan aiki.

Wadata U. (1998) a cikin rubutunsa mai suna tarihin Katagum yadda ya bi tarihin k’asar Katagum daga farko har zuwa yau.

Gulbi (2000) ya yi nasa bincike ne a kan sarautun gargajiya a k’asar Gummi jiya da  yau. Binciken ya fito da yadda sarautun suke a da can da kuma yanzu tare da yin la’akari da irin sauye-sauyen da aka samu ta fuskar canjin zamani.

Sale A. (2004) ya ba da tak’aitaccen tarihin masarautar Katagum da kuma irin ci gaban da aka samu tun daga zamani malam Lawal har zuwa kan sarki na goma shad’aya. Wannan ma aikin ya sha bamban da juna domin yana Magana ne a kan masarautar, shi kuma wannan kan tsarin sarautun bayi ne.

Isah S.F (2005) ya rubuta kundinsa mai taken tasirin zamananci a kan masarautun k’asar Zamfara yadda ya nuna irin tasirin da zamani ya yi a kan masarautun k’asar Zamfara. Wannan aikin ya ke’banta ne a kan tasirin zamananci a k’asar Zamfara, wannna kuma yana Magana ne a kan masarautar Katagum, don haka farfajiyar binciken ma ta bambanta. Wannan shi zai ba mu dammar aiwatar da wannan  aikin namu.

Abdulhadi M. (2005) ya gudanar da bincikensa mai taken fadanci a masarautar Tsafe, yadda marubucin ya nuna yadda fadanci yake a masarautar Tsafe

Aminu A. (2007) ya rubuta kundin kamala karatunsa mai taken tarihi da al’adun masarautar Gwandu.

1.2     HUJJAR CI GABA DA BINCIKE


Ta la’akari da nazarin da binciken ya yi a wurin bitar ayyukan da suka gabata za a fahimci cewa babu inda aka gudanar da wani gamsashen bayani dangane da sarautar bayi, musamman a k’asar Katagum. Wannan kuma ba karamin nak’asa ba ne, idan ana maganar samar da bayani a kan muhimman sarautun gargajiya na Hausawa.

Idan aka dubi aikin Alk’ali (1979) kasancewar aikinsa a kan tarihin daular ne gaba ki d’aya, bai yi wani ke’ba’b’ben sharhi mai gamsarwa ba a kan sarautar da ya  shafi sarautar bayi ba a masarautar Katagum.

Haka A. Musa (1985) ko kad’an ba ta  ambaci sarautar bayi ba a ciki aikinta ba.

Shi ma Zangeru (1993) a cikin bincikensa ko kad’an bai wadatar ba, domin bai kawo bayani game da sarautun bayi a masarautar Katagum.

Inda wad’annan masana suka yi suya suka manta da albasa bai wuce rashin kawo tsarin sarautun bayi a masarautar ba. Bisa ga wad’annan hujjujin na ga ya zama wajibi in gudanar da zurfaffen bincike a kan wannan matsayi mai  dad’ad’d’en tarihi a wannan  masarauta ta katagum wato sarautar bayi a k’asar Katagum.

1.3     FARFAJIYAR BINCIKE


Wannan bincike za a gudanar da shi ne a kan batun ire-iren sarautun gargajiya na bayi a fadar Katagum da ayyukansu da suke gudanarwa don ci gaban masarauta.

1.4     HANYOYIN GUDANAR DA BINCIKE


A nan za a yi bayani ne a kan hanyoyin da za a bi wajen gudanar da bincike don samun ingantaccen tsarin aiki.

  1. za a yi hira da muhimman mutane na cikin masarautar Katagum.

  2. Karance-karance na littafan tarihi da kwalayen digiri

  3. Ziyartar d’akunan karatu na manyan makarantu.

  4. Duba mujallu da k’asidu da muk’alu da aka buga.


1.5     MUHMMANCIN BINCIKE


Bincike kowane iri ne yana da muhimmanci da yake zai iya ilimantarwa a kan wani abu da  ba a sani ba, ko ya fito da muhimmancin wani abu don mutane su yi koyi su amfana ko kuma ya fito da illar wani abu don mutane su guje shi. Saboda haka shi ma wannan bincike yana da nasa muhimmanci.

Wannan nazarin ya shafi sarautun bayi a masarautar Katagum. Saboda haka zai zama a matsayin cike gurbi ne a kan abin da aka bari. Wannan nazari zai taimakawa d’alibai samu wani abu a kan sarautun da bayi suke rik’ewa a k’asar Hausa da yake ba ko’ina ake samunsu ba.

Haka kuma irin wannan  nazari zai wayar da kan mutane da yawa da suke da jahilcin irin rawar da bayi ke takawa a tsarin sarautun gargajiya na Bahaushe, ganin cewa ba a ko’ina ake samunsu ba. Ba abin mamaki ba ne a sami ire-iren wad’annan  sarautu a wurare da dama, amma rashin adana su a rubuce ya sa ba a san da su ba. Wannan kundin zai taimakawa sauran d’alibai  su ma, su mayar da hankali wurin bincike a kan irin wad’annan nazarce-nazarce da suka k’aranta.

1.6 NADEWA


Bayan shimfid’a ga bak’o in ya tafi sai a nad’e. Don haka a nan za a nad’e wannan babin da tak’aitaccen bayanin abin da babin ya k’umsa. Abin lura a nan shi ne, duk  ayyukan da aka gudanar  wajen bitar aikin da suka gabaci wannan aikin ba a sami wani aiki da ya yi dai dai ko kamanci da aikin namu ba, ko da ta fuskar

take. Don haka za a fito da bayani a fili  na cancantar gudanar da wannan aikin da ake son nan gaba, don samun damar gudanar da wannan bincike. K’udirin wannan aiki shi ne samar da k’wak’k’waran aiki wanda zai yi matuk’ar tasiri ga rayuwar Hausawa da ma wad’and’a ba Hausawa ba. Domin fito da wannan sarauta ta bayi a fili.

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

Post a Comment

0 Comments