Ticker

6/recent/ticker-posts

Kwatanci Na Kamanci Da Bambanci Tsakanin Jimlar Tambaya Da Jimlar Korewa Ta Hausa Da Ta Fulatanci (3)

Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriyawww.amsoshi.com

NA

DAYI RILWANU

BABI NA DAYA

BITAR AYYUKA DA MANUFAR BINCIKE


1.0     SHIMFID’A


        A babi na d’aya an yi amfani da shimfid’a a matsayin mabud’in aikin, kuma an yi waiwaye a kan ayyukan masana da suka gabaci wannan bincike tare da bayyana dalilin da ya sa ake gudanar da wannan binciken. An bayyana Manufar wannan bincike da muhimmancinsa  . Daga k’arshe an nad’e babin da bayanin abubuwan da aka bincika a cikin nazarin.

1.1     BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA


An gudanar da bitar ayyukan ne ta la’akari da hanyoyi da masana suka gudanar da su. Akwai hanyoyin guda uku da ya kamata a yi amfani da su wajen aikawatar da bitar ayyukan. Da farko an dubi kundaye da aka gabatar a fagen ilimin ginin jimla, sannan kuma, an dubi muk’alu da aka gabatar a wuraren taron k’ara wa juna sani, sai kuma, littattafai da aka wallafa wad’anda aka tattauna a kan ginin jimlar Hausa ga yadda suka biyo baya kamar haka:

 

 

1.1.1  BITAR KUNDAYE


D’akingari, (1989). Ya rubuta kundin digirinsa na farko a Sashen Harsunan Nijeriya na Jami’ar Usmanu ‘DANFODIYO Sakkwato, D’akingari ya kawo dangantakar da ke tsakanin al’ummar Fulani (Ful’be) da Hausawa da kuma mahauta (rundawa) ta fuskar al’adu da zamantakewa da siyasa da tattalin arzikinsu. Haka kuma, ya yi k’ok’arin fito da muhimman wurare da harshen Fulatanci (Fulfulde) ya yi aro daga harshen Hausa, wad’anda suka had’a da ginin jimla da tsarin sauti da kuma sunaye.

Wannan aikin na D’akingari (1986) ya bambanta da wannan nazari ta fuskar zubi da tsarin ayyukan, shi ya dubi al’adu da zamantakewa da aro da tattalin arziki da yanayin ginin jimla da tsarin sauti da kuma, sunaye. Wannan aikin kuma, ya mai da hankali ne kan kamanci da bambanci na jimloli biyu na harshen Hausa da na harshen Fulatanci, wato jimlar korewa da ta tambaya.

D’akingari, (2014). Ya rubuta kundin digirinsa na farko a Sashen Harsunan Nijeriya na Jami’ar Usmanu ‘DANFODIYO Sakkwato. Wannan marubucin ya dubi azuzuwan kalmomin harsunan biyu da harshen Hausa da na harshen Fulatanci (Fulfulde) da kuma tsarin ginin sassauk’ar jimla. Wannan aiki na D’akingari yana da alak’a da wannan aiki ta fuskar nazari saboda shi wannan aikin zai mayar da hankali ne kan kamanci ko bambanci na jimloli biyu na harshen Hausa da na harshen Fulatanci (Fulfulde) wato jimlar tambaya da ta korewa.

Imam, (2011). Ya rubuta kundin digirinsa na farko a Sashen Harsunan Nijeriya da ke Jami’ar Usmanu D’anfodiy Sakkwato. A cikin kundin nasa ya yi magana a kan wasu daga cikin azuzuwan kalmomin harshen Hausa da na harshen Fulatanci da kuma, dangantakarsu a jimlar Hausa da ta Fulatanci (Fulfulde). Amma wannan aiki yana magana ne kan kamanci da bambanci na jimloli biyu na harshen Hausa da na Fulatanci (Fulfulde). Ke nan aikin Imam yana da bambanci da wannan aiki, duk da cewa suna da alak’a da juna ta fuskar harsunan da aka gudanar da nazari.

Yunusa, (1986). A rubutunsa na kundin digiri na farko a Sashen Harsunan Nijeriya da ke Jami’ar Usmanu ‘DANFODIYO Sakkwato. Wannan marubucin ya yi bayani ne kan harshen Hausa da, harshen Fulatanci (Fulfulde). Sannan ya kawo bayani kan yadda are-aren kalmomi suka yi tasiri a tsakaninsu. Daga k’arshe kuma sai ya kawo bayani kan yadda harshen Hausa da na Fulatanci suka yi tasiri a kan junansu. Wato Hausa a kan Fulatanci (Fulfulde) da kuma, Fulatanci (Fulfulde) a kan Hausa. Shi Yunusa ya dubi aro ne cikin harshen Hausa da na Fulatanci (Fulfulde). Inda wannan bincike zai dubi kamanci dabambanci na jimloli biyu na harsunan Hausa da na Fulatanci (Fulfulde) wannan binciken ya yi la’akari da duk ayyukan da aka gabatar babu aikin da ya yi daidai da wannan aiki ta fuskar zubi da tsari, don haka wannan aiki ya samu gurbin gudanarwa.

1.1.2  BITAR MUK’ALU


Muk’alu su ne takardun dam asana da manazarta suka gabatar a wuraren k’arawa juna ilimi, don haka wannan nazarin ya yi k’ok’arin bin diddigin su don tantance su ko a sami wad’anda suka yi daidai da wannan nazarin. Ga yadda tsarin bitar ya gudana.

Haruna, (2004). A takardar da ya gabatar don nuna yadda Hausawa kan fuskanci wasu matsaloli a lokacin koyon harshen Inglisihi. Wannan takarda ta bayyana muhimmancin koyon harshen Ingilishi a matsayin harshe na biyu, sannan ya kawo bambance-bambance da ke tsakanin Ingilishi da Hausa ta yadda ya bayyana cewa akwai wasu sautukan da Ingilishi ke da su wad’anda Hausa ba ta da su kamar P, K’, ‘B, D’. Sannan ya kawo tsarin ga’ba ta Ingilishi yadda ta bambanta da ta Hausa inda aka sami ga’ba ta Ingilishi da ta ke amfani da cincirindon k’wayoyin sautuka ita kuma ga’bar Hausa ba ta da cincirindon sautukan.

Daga k’arshe kuma sai ya kawo kalmomin da Hausawa ke fuskantar cikas yayin furta su ta hanyar musanyar su da kwatancin sautukan da suke da su a Hausa. Idan aka kalli wannan aiki za a ga cewa bai shafi aikin da aka gudanar ba a wannan nazari, saboda shi yana magana ne a kan harshen Ingilishi da na Hausa. Haka kuma, ya yi bayanin Hausawa masu koyon harshen Ingilishi da matsalolin da suke fuskanta wajen koyo. Inda wannan aiki ya ke mai da hankali a kan Hausa da Fulatanci (Fulfulde) wato jimloli biyu na Hausa da Fulatanci (Fulfulde) wato jimlar tambaya da ta korewa da tsarin gininsu.

Muhammad, (2013). A takardar da ya gabatar a taron k’ara wa juna sani, marubucin ya yi bayanin irin matsalolin da Hausawa ‘yan asalin harshen Hausa ke cin karo da su wajen koyon harshen Fulatanci (Fulfulde) a matsayin harshe na biyu. Ya fito da matsalolin ta hanyar nuna wasu sautukan da Hausawa ba su da su a harshen Hausa, sannan ya nuna yadda Hausawa su ke maye gurbin sautukan Fulatanci da na Hausa a yayin furucinsu. Idan za a dubi wannan aiki na Muhammad za a ga cewa shi ya yi aiki ne a kan matsalolin da Hausawa ke cin karo da su a yayin koyon harshen Fulatanci (Fulfulde), a matsayin harshe na biyu. Wannan aikin ya dogara ne kan kamanci da bambanci na jimloli biyu na harshen Hausa da na harshen Fulatanci.

Abin la’akari a nan shi ne duk binciken da aka gabatar wajen bitar ayyukan da suka gabaci wannan aiki ba a samu wani aiki da ya yi daidai da wannan aiki ba, ta fuskar take ko manufa. Saboda haka, wannan aiki ya samu mafaka a fagen nazari.

1.1.3  BITAR LITTATTAFAI


Ayyukan masana da aka fara yin bitar a kansu akwai irin su: Arnotte (1976) wannan marubucin ya yi bayani ne a kan ilimin nahawu (Grammar) wanda ya shafi ilimin ginin jimla (syntad’) da ilimin tsarin sauti (phonology) da sauran abubuwan da suka shafi fannin nahawu. Amma wannan aiki na shi ya gudanar da shi ne a kan kwatance tsakanin harshen Fulatanci da na harshen Ingilishi. Wannan marubuci ya yi bayanin ginin jimla (syntad’) ne a babi na biyu. Amma wannan bincike yana magana ne a kan kwatanci na kamanci da bambancin jimloli biyu na harshen Hausa da na harshen Fulatanci (Fulfulde) wato jimlar tambaya da ta korewa da kuma, fito da inda suka yi kama ko bambanci da juna.

Daudu, (2009), wannan marubuci ya rubuta littafi a cikin harshen Fulatanci inda ya yi bayani kan yadda ake ginin jimla a harshen Fulatanci kawai. Idan aka yi la’akari da wannan aiki na marubucin za a ga cewa yana da alak’a da wannan aikin. To amma sai dai shi yana magana ne a kan harshen Fulatanci kawai, inda wannan aiki yake k’ok’arin kwatanta jimloli biyu na harshen Hausa da na Fulatanci. Wato jimlar tambaya ta Hausa da ta Fulatanci, da kuma, jimlar korewa ta Hausa da ta Fulatanci (Fulfulde).

M.C. Intosh, (1984). Wannan marubuciyar ta yi aiki ne a kan nahawu cikin harshen Ingilishi. A cikin littafinta ta yi bayanai masu d’imbin yawa wad’anda suka danganci ilimin ginin jimla (syntad’) da ilimin tsarin sauti (phonology) da sauran abubuwan da suka danganci nahawu (Grammar). Marubuciyar ta yi bayani a kan ginin jimlar Fulatanci a harshen Ingilishi ta  ba da misalai yadda tsarin ginin jimlar Fulatanci (Fulfulde) ta ke zuwa a harshen Fulatanci. To amma sai dai ita ta rubuta littafin ne a kan kwatanci tsakanin harshen Inglishi da na harshen Fulatanci. Inda wannan binciken zai maida hankali kan kamanci da bambanci na jimlolin biyu   na harsunan. Wad’annan su ne littafan da binciken ya sami damar gudanar da bita a kansu. Amma kafin kammala aiki in an sami wasu za a gudanar da bitar tasu.

1.2     DALILIN BINCIKE


Dalilin gudanar da wannan bincike shi ne cika k’a’idojin da jami’a ta shimfid’a kan duk wani d’alibi da ya zo shekarar k’arshe ta karatu don ya ba da ta shi gudummuwa a fagen da ya ke nazari. Na biyu, domin bunk’asa da kuma ciyar da harshen Hausa da na Fulatanci (Fulfulde) gaba, ta fuskar nazari, don haka wannan aiki zai taimaka sosai wajen bunk’asa wad’annan harsunan biyu ta fuskar nazarin ginin jimlarsu. Wato harshen Hausa da hashen Fulatanci (Fulfulde). Wani dalili kuma shi ne, zai taimakawa d’alibai masu sha’awar bincike ta hanyar ilimin kwatanci don samun haske.

1.3     MANUFAR BINCIKE


Manufar wannan bincike shi ne ganin cewa Fulani (Ful’be) al’umma ce da suke da nasu harshe, sannan kuma, suna gudanar da ma’amalarsu da Hausawa ta fuskar zamantakewa da auratayya da cinikayya a tsakaninsu da juna. Shi ne wannan aikin ya ga ya dace ya nazarci jimlolinsu don ya fito da kamanci da bambanci tsakanin jimloli biyu na Hausa da na Fulatanci ta yadda al’ummar Fulani za su k’ara fahimtar harshen Hausa suma Hausawa su k’ara fahimtar jumlar Hausa da ta Fulatanci (Fulfulde).

1.4     FARFAJIYAR BINCIKE


Wannan bincike zai tak’aita ne a kan nazarin jumlar tambaya da ta korewa na harshen Hausa da na Fulatanci (Fulfulde) inda za a dubi kamanci da bambanci na jimlolin biyu, saboda da haka wannan aiki ya tsaya ne kan nazarin harshen Hausa da harshen Fulatanci (Fulfulde).

Bisa ga tsarin nazari kusan kowane bagire aka d’auka da nufin gudanar da bincike, abu mafi muhimmanci shi ne a ke’ba masa farfajiyar da za a gudanar da shi. Wannan nazarin an ke’ba masa farfajiya ne a fannin ilmin ginin jumla na harshen Hausa da na harshen Fulatanci. A cikin wannan fanni na ginin jumla an za’bi ‘bangaren ilimin kwatanci don gudana da nazarin ilimin wasu daga cikin nau’o’in jimlolin harsunan biyu. Wato jumlar tambaya da ta korewa a harshen Hausa da Fulatanci. Yin hakan na nufin zak’ulo wuraren da suke da kama da kuma inda suke da bambanci da juna.

1.5     HANYOYIN GUDANAR DA BINCIKE


Hausawa na cewa, “Hannu d’aya ba ya d’aukar jinka.” Lallai haka abin yake domin wannan bincike zai ziyarci d’akunan karatu da kuma, zurfafa bincike a kan ayyukan da suka shafi tsarin jimlolin harshen Hausa da harshen Fulatanci (Fulfulde). Sannan an had’a da karance-karancen littattafai da muk’alu da kuma shiga yanar gizo domin samun wasu bayanai masu k’ara wa aikin haske.

A lokacin da ake gudanar da wannan bincike an samu damar shiga d’akin karatu da ke wannan sashe, haka kuma, na samu shiga babban d’akin karatu na wannan Jami’a. Wato (Abdullahi Fodiyo Library Compled’) domin neman bayanai dangane da abin da ya shafi aikin da kuma neman shawarwari daga cikin wasu malamai na wannan sashen, duk domin samun k’arin bayani a kan aikin. Haka kuma na samu ziyartar malamai masana kan ginin jimla ta Fulatanci (Fulfulde). Wuraren da na ziyarta sun had’a da: malaman sashen koyar da harshen Fulatanci da ke kwalejin ilimi ta Shehu Shagari da ken an Sakkwato (SSCOE) Sokoto.

1.6     MUHIMMANCIN BINCIKE


Wannan bincike yana da matuk’ar muhimmanci domin zai taimaka wurin fito da kamanci da bambancin da ake samu na jimlar tambaya da ta korewa tsakanin harsunan biyu. Haka kuma, aikin zai taimaka wa masu nazari wurin sanin abubuwan da ke aukuwa dangane da tsarin ginin jimlar Hausa da Fulatanci.

1.7     NAD’EWA


Wannan babi, babi ne da ke d’auke da shimfid’a a farkonsa, sai kuma, bayani dangane da abin da ya shafi bitar ayyukan da suka gabata, da kuma, dalilin bincike tare da manufar bincike har wayau na yi bayani kan farfajiyar bincike da kuma hanyoyin gudanar da bincike da muhimmancin, daga k’arshe aka rufe babin da jawabin kammalawa wato nad’ewa a tak’aice.

 

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

Post a Comment

1 Comments

  1. Slm, don Allah ina so a bani ma'anar kwatanci da kuma Gudajin ma'ana.

    ReplyDelete

Post your comment or ask a question.