https://www.amsoshi.com/game-da-mu/

Na

Shu’aibu Murtala Abdullahi

 

KUNDIN BINCIKEN NEMAN DIGIRI NA FARKO SHASHEN NAZARIN HARSUNAN NIJERIAYA JAMI’AR USMANU DANFODIYO SAKKWATO

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

 

BABI NA BIYU


Kud’i Da Muhimmancinsa Da Matsalolinsa


2.0 Shimfid’a


A wannan babi za a dubi abin da ya shafi kud’i da wasu muhimman abubuwa da yake tattare da su. Wanda tilas ne a kud’i da wad’annan abubuwa, wad’anda suka had’a da muhimmancin kud’in kansa da matsalolin da yake tattare da su ko yake haifarwa da kuma nau’o’in kud’in sannan da dabarun neman kud’in.

Kud’i ya shafi wad’annan abubuwa da aka zayyana domin dole ne sai an sami kud’i da wad’annan abubuwa, domin kud’i yana da muhimmancin gaske a cikin rayuwar al’umma ko a duniya ma gaba d’aya wanda saboda muhimmancinsa ya sa babu wata al’umma ta duniya da ba ta amfani da shi. haka kuma akwai irin matsalolin da yake haifarwa, a kowane ‘bangare na rayuwa a k’asa ne ko a gari ko a gida ko tsakanin al’umma. Sannan kowane kud’i akwai irin nau’insa tun daga k’aramin kud’i har zuwa babba, kuma kowace k’asa haka take da irin nau’in kud’inta daban da na wata k’asar.

Akwai dabaru da ake bi wajen neman kud’i daban-daban, da kuma hanyoyi da  ake bi domin a nemi kud’i, ta hanyar  sana’o’I manya da k’anana wad’anda ake yi domin a sami kud’i.

https://www.amsoshi.com/2018/01/24/bambanci-da-kamanci-tsakanin-karin-harshen-sakkwatanci-da-katsinanci-3/

2.1 Kud’i


Magana a kan abin da ya shafi kud’i ba k’aramin abu ba ne wanda za a yi shi a wani tak’aitaccen lokaci. Saboda wani ‘bangare ne mai fad’in gaske wanda ya mamaye kowane lungu da sak’o na duniya da kuma rayuwar al’umma gaba d’aya. Saboda haka ya sa babu wata ma’ana guda d’aya da za a ce an bai wa kud’i, sai dai kowane da yadda yake kallon sa da kuma yadda zai iya fad’in ma’anarsa. Wannan nazari zai yi k’ok’ari wajen bayar da abin da kud’i yake nufi.

Kud’i wani abu ne da ake yinsa da takarda ko k’arfe ko kuma leda domin amfani da shi wajen harkokn rayuwa ta yau da kullum, a kasuwanni ne ko makarantu da wasu ‘bangarori na gwmnatin k’asa ko jiha gaba d’aya. Wannan yana nuna mana cewa kud’i abu ne da ya shafi rayuwar al’umma gaba d’aya, domin dole ne sai an yi amfani da shi a rayuwa ta yau da kullum. Haka kuma, wannan yana nuna mana cewa kud’i abu ne mai girman gaske wanda a wannan zamani ko rayuwar da ake ciki a yanzu ba za a iya tafiyar da ita ba dole ne sai an yi amfani da kud’i, domin dole sai da shi za a yi amfani wajen saye da sayarwa da sauran abubuwa na rayuwa.

2.2 Nau’o’in Kud’i


        A wannan ‘bangare kuma nazarin zai yi k’ok’ari wajen kawo irin nau’o’in kud’ad’en da ake  amfani da su a wannan k’asa, nazarin zai yi k’ok’arin kawo nau’o’in kud’ad’e na baya da kuma na yanzu. Kud’ad’en da aka yi amfani da su a lokacin Tuwaran mulkin mallaka da kuma bayan samun mulkin kai sun had’a da:

2.2.1 Lokacin Mulkin Mallaka 1. D’ari (rabin kwabo)

 2. Kwabo

 3. Taro (kwabo uku)

 4. Sisi (kwabo shida)

 5. Sulai (kwabo goma sha biyu)

 6. Dala (kwabo ashirin da biyar)

 7. Fan d’aya (kwabo hamsin)


2.2.2 Bayan Samun Mulkin Kai Lokacin Yakubu Gowan (1973) 1. D’ari

 2. Kwabo

 3. Sisi (Kobo biyar)

 4. Sulai (kwabo goma,)

 5. Dala (Kwabo ashirin)

 6. Naira d’aya (kwabo d’ari ko sulai goma)

 7. Naira biyar (kwabo biyar ko sulai hamsin)

 8. Naira goma (kwabo dubu ko sulai d’ari)


2.2.3 Lokacin Obasanjo Da Shehu Musa ‘Yar’aduwa (1977) 1. Naira ashirin


2.2.4 Lokacin Mulin Babangida A Shekarar (1991) 1. Naira hamsin


Sai a lokacin mulin farar hula shekarar (1999) lokacin mulkin obasanjo aka yi naira d’ari (#100). A dai mulkin nasa a shekarar (2000) aka yi d’ari biyu (#200). A cikin mulkin sana a shekarar ta (2001) aka yi naira d’ari biyar (#500). Ita kuma naira dubu (#1000) sai a Oktoban shekara ta dubu biyu da biyar (2005) sannan ta fito.

A shekarar ta dubu biyu da bakwai 2007 aka fito da sababbin kud’i na k’arfe naira d’aya da kuma silai biyar wato k’wandala da ficika. Haka kuma nazarin zai kawo nau’in kud’ad’en wasu k’asashe da suka had’a da yan daga k’asar Japan da dola daga Amerika da riyar daga Saudi Arebiya da Yuro daga Turai da sefa daga k’asar Faransa.

2.3 Muhimmancin Kud’i


Kud’i abu ne mai muhimmanci a cikin rayuwar al’umma wanda saboda muhimmancinsa ne ya sa rayuwa ba ta tafiya ba tare da shi ba. wannan nazari zai yi k’ok’arin kawo muhimmancin kud’i daga cikin wak’ok’in baka da kuma rubutacciya wad’anda za a yi nazari.

2.3.1 Wak’ar Kud’i ta Gambo Hawaja


Gambo Hawaja mawak’in NEPU ne, a cikin wak’ar da ya rubuta ta kud’i ya bayyana muhimmancin kud’i a cikin wad’ansau baitoci daga cikin wak’arsa ta kud’i. Misali: a baiti na arba’in yake cewa ya sani lafiya da rai sun fi komai, to su ma a kan ba da su don a sami kud’i.

40) Gama lafiya dai da rai sun fi komai,

Akan ba da su don a samo kud’i.

Haka kuma a baiti na hamsin da hud’u nan ma yake cewa mara lafiya ma yana kwance yana nishi amma da an girgiza kud’i ko ya ji motsin kud’i sai ya d’ago kai ya dubi kud’i.

54) Maras lafiya na ta nishi a d’aki,

Da ka girgiza sai ya dubo kud’i.

A baiti na hamsin da biyar ya ce idan banda rai to kud’i ya fi komai, kuma sai da kud’i ne ake zama lafiya domin idan babu su akwai matsala. Misali:

56) Idan ban da rayi kud’i ya fi komai,

Abokin zaman lafiya rai kud’i.

Sannan a baiti na hamsin da shida ya ce, saboda muhimmancin kud’i duk abincin da ka sani a duniya idan kana son shi to za a kawo maka shi duk da kud’i. Misali:

56) Abincin da duk ka sani yau a duniya,

Kana son shi ka gan shi in kai kud’i.

Haka kuma wani muhimmancin na kud’i da ya k’ara ya ce, idan mutum ya yi kud’i masu k’asa sai su so shi, har ya je shawara a fada saboda yana da kud’i ya bayyana haka ne a baiti na saba’in da uku:

73) Idan kai kud’i mai k’asa sai Iso ka,

Ka je shawara fada domin kud’i.

2.3.2 Wak’ar Kud’i ta Shata


Alhaji Mamman Shata mawak’in baka ne kuma makad’in jama’a, shi a cikin wak’ar ta kud’i a kashe su ta hanya mai kyau, shi ma ya kawo muhimmancin da kud’i yake da shi, misali:

A d’iya na biyu ya nuna cewa saboda muhimmancin da kud’i yake da shi ba a samun shi haka nan sai an sha wuya. Misali:

2) Ka tuna yanda ka sami kud’inka,

Ka sha wuya ka sami kud’inka,

To je ka kashe su ta hanay mai kyau.

A d’a na takwai kuma ya k’ara bayyana muhimmancin kud’i cewa kud’i abin nema ne kuma sai an dage an sa k’arfi sannan za a same su misali:

8) Tsaya dukiya abin nema ce,

Su kud’i abin nema ne.

A d’a na goma sha hud’u ya k’ara bayyana cewa su fa kud’i sai an sha wuya ake samunsu. Misali:

14) Na sha wuya na sami abina,

Na tara has sun taru,

Kud’i a kashe su ta hanya mai kyau.

Haka kuma ya nuna cewa in dai kana so ka zama mai wadata ka cika buri ka zama mai kirki to ka kashe kud’i ta hanay mai kyau. Ya bayyana haka ne a d’a na sha biyar. Misali:

15) In dai na so in cika kirki,

In cika buri,

In ta wadata,

To in kashe su ta hanya mai kyau.

A d’iya na sha bakwai ya nuna cewa kud’i saboda muhimmancinsa yana sa ka sami yardar Allah da annabi da kuma sauran mutane inda dai mutum ya kashe su ta hanya mai kyau.

17) Idan ya kashe su ta hanya mai kyau,

Farko Allah na gode masa,

Kana Annabi na gode mai,

Mu ma mutane na gode mai.

 

 

 

2.3.3 Wak’ar Audu Wazirin D’anduna ta Kud’i


Audu wazirin D’anduna mawak’in baka ne kuma makad’in jama’a, shi ma a cikin wak’arsa ta tsakanin d’an Adam da kud’i ya bayyana muhimmancin kud’i a d’iyoyi daban-daban na wak’ar. Misali:

A wannan d’iya yake cewa a yanzu ba wata harka da za ka iya yi dole sai kana da kud’i. Misali:

6) Yanzu ba wata harka sai kana da kud’i,

Tsakanin d’an Adam da kud’i.

Ya k’ara da cewa, yanzu kana iya komai idan kana da kud’i, ya nuna cewa ke nan idan kana da kud’i komai kana iya yi. Misali:

13) Kana iya komai dan saboda kud’i

Tsakanin d’an Adam da kud’i.

Sannan ya k’ara bayyana muhimmancin kud’i cewa ana fita kunya idan ana da su, misali, za ka iya wa yanka aure to sai ka yi komai ba wanda zai ce ya taimaka maka ko a gida ma kana iya fitar da su wata kunya idan kana da kud’i. Misali:

16) Akon fita kunya ma saboda kud’i,

Tsakanin d’an Adam da kud’i.

Haka kuma, yana nuna cewa idan da kud’i to ana iya warware rigima tsakanin mutane. Misali:

25) Ana ware rigima saboda kud’i,

Tsakanin d’an Adam da kud’i.

Ya bayyana muhimmancin kud’i cewa idan mutum yana da su to har sabon aure ma yana iya yi misali:

 

47) Kuma ana sabon aure saboda kud’i,

Tsakanin d’an Adam da kud’i.

A wannan ‘bangaren na muhimmancin kud’i nazarin ya yi k’ok’arin kawo muhimmancin da kud’i yake da shi daga baitoci da d’iyoyin wak’ok’in da aka yi nazari wato wak’ar Gambo Hawaja ta kud’i da wak’ar Alhaji Mamman Shata ta kud’i a kashe su ta hanya  mai kyau, da kuma wak’ar kud’i ta Audu Wazirin D’anduna watp tsakanin d’an Adam da kud’i.

2.4 Matsalolin Kud’i


Tabbas kud’i yana haifar da matsaloli masu yawa a cikin rayuwar al’umma wannan dalili ya sa nazarin zai yi k’ok’arin fito da wasu matsaloli na kud’i daga cikin wad’annan wak’ok’i da ake nazari a kansu. Misali:

Gambo Hawaja a cikin wak’arsa ta kud’i ya kawo matsalolin kud’i a baitoci daban-daban na wak’ar misali. A wannan baiti ya nuna yadda yaye suke zubar da girmansu a gaban mijin yansu suna rok’on sa ya mayar da ‘yar gidansa, saboda yana da kud’i maimakon ya je biko a iyayenta ne suke zuwa su yi bikonsa kawai saboda yana da kud’i. Misali:

154) Iyayen d’iya sai su zo gun ka biko,

Su sasanta zancenku domin kud’i.

 

155) Suna ba ka baki su komad da ‘yarsu,

Ka san ba abin so a yau sai kud’i.

Haka a wannan baiti ya k’ara bayyana mana matsalar kud’i, cewa sai ka yi wa ‘yarka miji ta ce ba ta son shi kawai dan ba shi da kud’i misali:

138) Ka bai wa d’iyarka miji, sai ta k’ishi,

Ta ce tak’i tad’inka in ba kud’i.

A nan kuma sai ya k’ara kawo wata babbar matsala da kud’i ke haifarwa, cewa mutum yak’i yin salla da fitar da zakka da zuwa cikin Hajji da tauhidi saboda kud’i ko dan yana son kud’i. Misali:

117) Mutum ya k’i salla da zakka da Hajji,

Da tauhidi amma yana son kud’i.

Haka kuma, a wani baitin sai ya k’ara kawo matsalar kud’i, cewa kud’i fa yana iya yanek zumunta, har ta kai ga ana kashe juna, duk dan kud’i ko a wajen neman kud’i. Misali:

92) Kud’i shi yakan sa zumunta ta watse,

Ana kashe juna a neman kud’i.

Sai a wak’ar Alhaji Mamman Shata ta kud’i a kashe su ta hanya mai kyau, misali:

Akwai wani d’an wak’a da yake cewa idan mutum ya yi gumi ya sami kud’insa kuma ya sha wuya, amma da ya zo wajen kashewa sai ya kashe su ta hanyar da ba ta dace ba to ka ga kud’in ba su amfane shi ba sai ya kira shi da wawa. Misali:

10) Ga wani ya yi gumi ya samu,

Ya sha wuya ya samu,

Ya zo a wurin ‘baddawa,

Ya ‘badda a cikin sakarci,

Wannan ya zama wawa kenan,

Bai ji ba zancen Mamman Shata.

Sannan a wanann d’iyan ma ya k’ara kawo matsakar kud’i ya ce idan mutum yasha wuya ya samu kud’insa ya tara suka taru, ya je yai shashanci kuma ya kashe su tafarkin banza ba ta hanyar mai kyau ba to wannan ya zama shashasha. Misali:

14) Na sha wuya na sami abi na

Na tara has sun taru,

In na je han nai shashanci,

Na kashe su tafarkin banza,

To ba d’a na rikid’e shashasha.

Haka shi ma Alhaji Audu wazirin D’anduna a cikin wak’arsa ta tsakanin D’an Adam da kud’i shi ma ya bayyana matsalolin kud’i daga cikin wasu d’iyoyin wak’ar misali, a wannan d’iya yana cewa idan mutum yana da kud’i wani sai ya yi ta dukan matarsa saboda kawai yana da kud’i yana ganin in sun rabu yana da kud’i zai auro wata misali:

Sai mutum ya daddake matarsa saboda kud’i,

Tsakanin d’an Adam da kud’i.

Sannan ya k’ara kawo wata babbar matsala da kud’i yake haifarwa wato kud’i sai ya sa mutum ya yi fad’a da ‘ya’yansa. Misali:

Kud’i mai sa fad’a da uba kud’i mai sa fad’a da uwa,

Tsakanin d’an Adam da kud’i.

Haka kuma ya k’ara da cewa idan mutum yana da kud’i za ka ga yana yi wa mutane kallon banza, to wannan ma wata matsala ce da kuji ke haifarwa. Misali:

Mutum yana kallon banza saboda kud’i,

Tsakanin d’an Adam da kud’i.

Ya k’ara kawo wata matsala da kud’i ke haifarwa cewa, a gidanka ma idan ba ka da kud’i to ba a ganin girmanka. Misali:

Ko a gidanka ba ka da girma sai kana da kud’i,

Tsakanin d’an Adam da kud’i.

Wata matsalar da kud’i ke haifarwa ita ce auri-saki, mutum ya auri wannan ya saki ya auri wannan ya saki saboda kawai yana da kud’i, misali:

Mutum yakan saki matatai saboda kud’i,

Tsakanin d’an Adam da kud’i.

A wannan ‘bangare nazarin ya yi k’ok’arin fito da wasu d’iyoyi da baitoci da suke d’auke da wata matsala da kud’i ke haifarwa, inda aka kawo su daga cikin wak’ok’in da ake nazari.

 

2.5 Dabarun Neman Kud’i


Kud’i wani abu ne mai muhimmanci wanda shi ma ba a samun sa haka kawai, dole ne akwai wasu dabaru da ake bi wajen neman sa. Wad’annan dabarun sun had’a da sana’o’i manya da k’anana.

Manyan  sana’o’i sun had’a da masan’antu kamar kamfanonin da ake sak’e-sak’e da kamfanonin jaridu da kamfanonin magunguna da na man shafawa da bankuna da kamfunan had’a robobi da na kayan sawa da sauran al’amuran yau da kullum.

Daga cikin k’ananan sana’o’i da ake yi sun had’a da d’inkin takalmi da wanki da sai da tireda da faci da keke ko babur ko mota da sai da kalanzir da d’inki kaya da sak’a da jima da sana’o’in fawa da k’ira da wanzanci da kanikanci da sauran k’ananan sana’o’i da ake yi domin neman kud’i.

Daga cikin dabarun neman kud’i akwai aikin gwamnati da ake yi a ‘bangarori daban-daban duk wanan shi ma yana daga cikin dabarun neman kud’i. Wad’annan sana’o’i da aka lissafa duk dabaru ne na neman kud’i, kuma ana yin su ne domin  a nema ko samun kud’i.

2.6 Nad’ewa


Bayan gabatarwa da aka yi daga farkon nazari ya kawo wasu muhimmancin abubuwa da aka yi magana a kansu wad’anda suka shafi kud’i. An yi magana a kan muhimmancin kud’i a rayuwar al’umma gaba d’aya inda aka kawo d’iyoyi da baitoci daban-daban daga wak’ok’in da aka yi nazari. Haka kuma nazarin ya yi k’ok’ari wajen kawo nau’o’in kud’i da aka yi amfani da su a wannan k’asa tun daga lokacin mulikin malla har zuwa samun mulkin kai, da kuma wasu nau’o’in kud’i na k’asashen waje.

Wannan nazari ya yi k’ok’ari wajen bayyana matsalolin da kud’i yake  haifarwa a cikin al’umma inda aka kawo baitoci da d’iyoyi daga wak’ok’in da ae nazari da kuma inda wak’ok’in suke magana a kan abin da ya shafi matsala ta kud’i.

An yi magana dangane da kud’i nazarin ya yi k’ok’ari wajen ba da fahimtarsa dangane da abin da ake kira kud’i. Wannan nazari ya yi magana a kan dabarun neman kud’i inda aka kawo hanyoyi na neman kud’i, kamar sana’o’i manya da k’anana.

 

 

 

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/