Ticker

6/recent/ticker-posts

Kudi A Idan Mawakan Hausa Na Baka Da Rubutattu, Wakar Kudi Ta Alhaji Audu Wazirin Danduna Da Ta Alhaji Mamman Shata Da Kuma Gambo Hawaja (2)

 Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriyawww.amsoshi.com
NA
Shu’aibu Murtala Abdullahi

BABI NA D’AYA

GABATARWA


Gabatarwa


Kusan kowane nazari ba a fahimtar inda ya sa gaba sai an gabatar da k’udurin da binciken yake d’auke da shi. A nan burin wannan binciken shi ne, a gabatar da abin da ya k’unsa don sanin abin da za a gudanar. A babin farko nazarin ya yi shimfid’a a farkonsa, sannan ya gudanar da bitar ayyukan magabata, bisa sakamakon da aka samu a bitar sai ya bayyana hujjar da ta ba da damar aiwatar da wannan nazarin. Manufar bincike ita ta biyo bayan hujjar ci gaba da bincike, daga nan sai aka kawo ire-iren hanyoyin da binciken ya bi don ganin an sami nasarar kammala nazarin. A cikin babin na farko an bayyana mahimmancin bincikea da aka gudanar, daga nan sai aka nad’e babin da jawabin kammalawa.

A cikn babin na biyu kuwa, nazarin ya kawo ma’anar kud’i da nau’o’in kud’i da mahimmancin kud’i a rayuwar al’umma ta zahiri. Sannan aka kawo ire-iren matsalolin kud’i da dabarun neman kud’i, sai aka nad’e babin. Babi na uku kuwa mai take “Jigo Da Turken Wak’ok’in Kud’i”, an kawo ma’anar wak’a bayan shimfid’a, sai ma’anar jigo. An kawo turke da jigon gargad’i da wa’azi, daga nan sai shima aka nad’e babin. Babi na hud’u babi ne da yake d’auke da ginshik’in nazarin wak’a, wato salo, don haka aka yi wa babin suna “Salon Wak’ok’in Kud’i”, a inda aka kawo ma’anar salo da salon sa’bi zarce da na aron kalmomi da salon kambamawa. An bayyana salon dabarun jan hankali daga nan sai aka nad’e babin da tak’aitaccen abin da nazarin ya binciko game da kud’i cikin salailan wak’ok’in kud’i. Babi na biyar wanda shi ne babin na k’arshe, an gabatar da shimfid’a a farkonsa sai shawarawari, bayan shawarwari sai aka bayyana manufar wak’ok’in kud’i. Daga k’arshe sai nazarin ya jero manazartar da aka yi amfani da su a lokacin da ake bincike don gudanar da aikin. An kawo ratayen wak’ok’in kud’i da nazarin ya yi amfani da su don k’arawa nazarin armashi.

1.0 shimfid’a


        Wannan babi yana tattare da k’udurin yin shimfid’a kan abin da kundin ya k’unsa musamman kan wasu mahimman ‘bangarorin da ya kamat kowane kundi a bayyana su kafin a sami damar ci gaba da binciken da ake son gudanarwa. Da farko bayan shimfid’a babin ya k’unshi bayani kan abubuwa guda biyar wato, an yi bayani kan rubuce-rubuce da suka shafi ayyukan da aka gabatar kan mawak’a baka da rubutattun wak’ok’in Hausa, a matsayin bitar ayyukan da suka gabata. Daga nan sai aka bayyana hujjar da aka samu wadda ta samar da ci gaba da binciken. Bayan nan sai aka bayyana manufar gudanar da binciken da kuma hanyoyin da aka bi domin gudanar da bincike, sannan a k’arshe aka nuna muhimmancin binciken.

https://www.amsoshi.com/2018/01/25/bambanci-da-kamanci-tsakanin-karin-harshen-sakkwatanci-da-katsinanci-5/

1.1 Bitar Ayyukan da Suka Gabata


Masana da manazarta da dama sun gudanar da ayyuka masu dimbin yawa kan wak’ok’in baka da rubutattu na Hausa. Kuma manzarta da dama sun gudanar da bitar su, kusan duk wani nazari da ake buk’atar aiwatarwa sai an gudanar da bitar wad’ancan ayyuka da suka gabata. Sanin haka shi ya sa wanna nazarin yake son tak’aita bitar ayyukan da suka gabace shi kan ke’ba’b’bun mawak’an da ya tanada don gudanar da nazarin wasu daga cikin wak’ok’insu da suka shafi babban al’amari kan rayuwar d’an Adam, wato wak’ok’in kud’i. Mawak’an su ne; Alhaji Audu Wazirin Danduna da Gambo Hawaja da Alhaji Mamman Shata Katsina. Daga cikin ayyukan da aka ci karo da su akwai:

Yahaya A. (2012), taken nazarin shi ne, “Nazari a kan wak’ar kud’i ta Audu Wazirin D’anduna”, mai wannan nazari ya dubi zubi da tsarin wak’ar ne kawai, ba tare da ya yi tsokaci a kan kud’i ba. Wannan aikin an yi a Jami’ar Usmanu D’anfodiyo Sakkwato. Ganin cewa ya tak’aita bayanin wak’ar kan zubi da tsarin d’iyan wak’ar da laluben tsarin amshinta, shi ya ba wannan nazarin damar sake bibiyar ta don fito da mahimmancin kud’i da aka gina wak’ar a kansa. Wannan aiki na Yahaya (2012) yana da alak’a da wannan nazarin, sai dai alak’ar ba za ta hana shi gudanuwa ba. Wannan shi ne aikin da nazarin ya iya cin karo da shi wanda aka yi kan wak’ar kud’i ta Audu Wazirin D’anduna.

Shi kuma Gambo Hawaja nazarin ya yi iya k’ok’arinsa amma bai samu wani aiki da aka yi dangane da wak’ok’insa ta kud’i ba. Amma nazarin ya sami tak’aitaccen tarihinsa. Nazarin ya sami wannan tarihin nasa ne a wata lacca da aka gabatar a shekarar karatu ta 2016 a ajin shekara k’arshe ta masu karatun digirin farko a Jami’ar Usmanu D’anfodiyo Sakkwato. Inda aka ba da tarihin haihuwarsa kamar haka; an haifi Gambo  Hawaja a k’aramar hukumar Takai ta garin Sumaila da ke jahar Kano a shekarar 1914, kuma ya yi wak’e-wak’e da dama, amma yafi fice kan wak’ok’in siyasa. Gambo Hawaja mawak’in  jam’iyyar N.E.P.U kuma ya yi mata wak’ok’i da dama a jumhuriyar farko. A jumhuriyya ta biyu ya yi wa jam’iyyar P.R.P. wak’ok’i da dama. Haka kuma ya yi wak’ok’in sha’awa irin su wak’ar Lebura da makamantan su.

Shi kuma Alhaji (Dr.) Mamman Shata Katsina, an sami wasu ayyuka da aka yi a kansa da yawa. Wasu daga cikin ayyukan akwai kundin digiri na farko da aka gabatar a jami’ar Usmanu D’anfodiyo Sakkwato, mai taken “Gudummuwar Wak’ok’in Alhaji (Dr) Mamman Shata Katsina A Fagen Bunk’asa Sana’o’in Gargajiya”, wanda Abubakar D’ayyabu Safana ya gabatar a shekarar karatu ta (2007). Wannan aikin an gudanar da shi ne kan wak’ok’in Mamman Shata Katsina da suka shafi sana’o’in gargajiya na k’asar Hausa. Manazarci ya dubi irin gudummawar da wak’ok’in suka bayar wajen buk’asa sana’o’in tare da taimawa tattalin arzik’in k’asar Hausa da ma Nijeriya gaba d’aya.

Haka kuma, Alhaji Mamman Shata kasancewansa mashahurin mawak’i akwai kundin digiri na farko a Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato mai taken “Nazarin Wak’ok’in Alhaji (Dr) Mamman Shata Katsina Na Mata”, wanda wata d’aliba mai suna Rahila Attahiru ta gabatar a shekarar karatu ta (2012). Daga cikin wak’ok’in matan da aka nazarta akwai wak’ar Kyauta da Hajiya Goshin D’angude da Hajiya Maijidda. Idan aka lura dukkan kundayen ba su ta’bo wak’ar kud’i ba da Alhaji (Dr.) Mamman Shata Katsina ya yi ba, don haka wannan nazarin zai iya ci gaba da wanzuwa. Domin wannan nazarin zai tak’aita ne a kan wak’ok’in kud’i da wad’annan mawak’an suka yi wato Audu wazirin D’anduna da Gambo Hawaja da kuma Alhaji Mamman Shata.

1.2 Hujjar Cigaba da Bincike


Mai karatu idan ya lura a cikin bitar ayyukan da suka gabata babu wasu ayyuka masu yawa da aka yi, dangane da mawak’an da aka gudanar da nazarin su a cikin aikin. Wato su Audu Wazirin D’anduna da Gambo Hawaja da Alhaji Mamman Shata. A cikin su an fi samun ayyukan da aka gudana kan Alhaji (Dr.) Mamman Shata Katsina. Ko shi ma ba a ci karo da aikin da aka gudanar a kan wak’ar kud’i ba. Duk da yake mawak’a biyu daga cikin mawak’an baka ne, wato Alhaji Mamman Shata da Audu Wazirin D’anduna. Shi kuwa Gambo Hawaja shi kad’ai ne marubucin wak’a, wato shi sha’iri ne ba mawak’in baka ba ne. Wad’annan mawak’an sun yi tarayya wajen yi wa abu d’aya wak’a wato kud’i. Haka kuma ganin irin yadda masana suka nuna muhimmancin wak’a ga adabin Hausa, nazarin ke ganin wannan hujja ce ta aiwatar da nazari dangane da yadda hak’ik’a da muhimmancin a ‘bangaren adabi.

Wad’annan mawak’a sun fito da abubuwa muhimmai a cikin wad’annan wak’ok’i nasu shi ya sa nazarin yake ganin irin wad’annan muhimman abubuwa da wak’ok’in suka k’unsa ita ma hujja ce da za a bincike a kan wad’annan wak’ok’i.

1.3 Manufar Gudanar da Bincike


Manufar gudanar da wannan bincike ita ce, fito da hikimomi da fasahar da Allah ya yi wa wad’annan mawak’an, wato Gambo Hawaja da Audu Wazirin D’anduna da Alhaji (Dr.) Mamman Shata Katsina, domin d’alibai da masu sha’awar nazarin wak’ok’insu su amfana. Wannan bincike ya zama wata gudunmawa ce wadda nazarin ya bayar a sashen koyar da harshen Najeriya na Jami’ar Usmanu D’anfodiyo Sakkwato tare da samun cike wani gi’bi na samun shaidar kammala karatun digiri na farko.

Kasancewar wad’annan mawak’a wato Gambo Hawaja da Audu wazirin D’anduna kuma Mamman Shata, sharaharrun mawak’an Hausa lokaci ya yi da za a yi nazarin wak’ok’insu musamman ma Gambo Hawaja da Audu Wazirin D’anduna, a kuma k’ara cigaba da na Alhaji Mamman Shata, domin masu nazari su amfana da hikimomi da salailan da ke cikin wak’ok’insu.

https://www.amsoshi.com/2018/01/24/bambanci-da-kamanci-tsakanin-karin-harshen-sakkwatanci-da-katsinanci-4/

1.4  Hanyoyin Bincike


Kasancewar kowane nazari yana da buk’atar shiri don gudanar da shi, akwai hanyoyi da dama da aka bi, domin samun bayanai a kan k’udurin wannan binciken. Da farko shi ne ziyartar d’akunan karatu (library) domin nemo wasu littattafai da aka riga aka rubuta a wannan ‘bangare na adabi da kuma amfani da wasu kundayen digirin da suka gabata don cimma nasarar bincikensu.

Bayan wannan akwai kuma, tambayoyin da binciken ya shirya don yi wa masana domin samun gudummawa na ganin an kammala wannan bincike cikin nasara, tare da neman shawarwarinsu a kan yaya ya dace a fuskanci aikin. Sai kuma an amfani da yanar gizo (intanet) domin tattaro wasu bayanai masu muhimmanci da za su k’ara taimakawa wajen ganin nazarin ya sami inganci da samun nasara.

1.5 Muhimmancin Bincike


Babu shakka, wannan nazari yana da matuk’ar muhimmanci a ‘bangaren abin da ya shafi adabin baka da kuma rubutaccden adabi musamman a fannin nazarin wad’annan wak’ok’i. Ta wannan nazari za a iya bayyana irin gudummuwar da makad’a da marubuta suka bayar wa wajen ha’baka da ciyar da adabin Hausa gaba ta hanyar amfani da abubuwa da dama.

Haka kuma ta wannan nazari za a iya fahimtar dalilai ko kuma abin da ke sa makad’i ko marubuci yin wak’a. Yana daga cikin muhimmancin wannan nazari sanin irin tasirin da wad’annan wak’ok’in suke da shi ga al’ummar Hausawa.

1.6 Nad’ewa


A cikin wannan babin an tattauna kan bitar ayyukan da magabata suka aiwatar, inda aka tak’aita bitar kan nazarce-nazarcen da aka gudanar kan mawak’an da binciken yake son gudanar da aiki a kansu, wato Alh. Audu Wazirin D’anduna da Alh. (Dr.) Mamman Shata Katsina da Gambo Hawaja. Inda aka sami gundi d’aya da aka gudanar da nazarin wak’ar Audu Wazirin D’anduna da Kundaye biyu da aka gudanar da bincike kan wak’ok’in Dr. Mamman Shata Katsina, inda aka sami tak’aitaccen tarihin Gambo Hawaja ba tare da nazarin wak’arsa ba. Bayan bitar ayyukan sai aka sami hujjar ci gaba da binceken da ake burin yi. Daga nan sai aka bayyana manufar da aka dogara da ita don gudanar da nazarin. An kawo ire-iren hanyoyin da nazarin ya yi amfani da su don ganin an sami nasarar kammala bincken. Inda aka bayyana hanyoyi manya guda uku da nazarin ya yi amfani da su don ganin an kammala aikin cikin nasara. Nazarin ya yi k’ok’arin bayyana irin mahimmancin da binciken yake da shi ga masu sha’awar nazarin wak’a.

 

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

 

Post a Comment

0 Comments