Ticker

6/recent/ticker-posts

Kudi A Idan Mawakan Hausa Na Baka Da Rubutattu, Wakar Kudi Ta Alhaji Audu Wazirin Danduna Da Ta Alhaji Mamman Shata Da Kuma Gambo Hawaja (4)

Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriyawww.amsoshi.com
NA
Shu’aibu Murtala Abdullahi

BABI NA UKU

JIGO DA TURKEN WAK’OK’IN KUD’I

3.0 Shimfid’a


        Wannan nazari zai yi k’ok’ari wajen kawo ma’anoni da masana suka bayar dangane da wak’a da kuma manazarta su ma yadda suka kalli wak’a da yadda su kansu marubuta da mawak’an baka suka bayar da ma’anar wak’a. Wannan nazari zai yi k’ok’ari wajen kawo ma’anar jigo daga bakin masana da kuma ma’anar turke a wak’ar baka tare da fito da babban jigon wak’a da kuma fito da manyan turakun wak’ok’in, tare da kawo inda aka yi wa’azi ko gargad’i daga baitoci ko d’iyoyin wak’ok’in.

3.1 Ma’anar Wak’a


Masana da manazarta da kuma su kansu masu rera wak’ok’i sun tofa albarkacin bakinsu wajen bayyana abin da ake nufi da wak’a.

3.1.1 Ma’anar Wak’a Daga Manazarta


Manazarta da masana adabin Hausa sun tofa albarkacin bakinsu wajen bayyana ma’anar wak’a. Misali: D’angambo (2007: 6) cewa ya yi: “Wak’a wani sak’o ne da aka gina shi kan tsararriyar k’a’ida ta baiti da d’ango da rerawa, da kari (bahari) amsa amo (k’afiya) da sauran k’a’idojin da suka shafi daidaita kalmomi, za’bensu da amfani da su  cikin sigogin da ba lalle ne haka suke a maganar baka ba.

Yahya, (1994) a nasa ra’ayi ya bayyana ma’anar wak’a da cewa: “Wak’a tsararriyar maganar hikima ce da ta k’unshi sak’o cikin za’ba’b’bun kalmomi da aka auna domin manganar ta reru ba fad’uwa kurum ba.”

Gusau, (2003) cewa ya yi: “Wak’ar baka wani zance ne shiryayye cikin hikima da azanci da yake zuwa ga’ba-ga’ba bisa k’a’idojin tsari da daidaitawa a rere cikin sautin murya da amsa-amo kari da kid’a da amshi.”

  • Wak’a magana ce aunanniya wadda ake rerawa tattare da wannna ma’ana a dunk’ule, tana nuna cewa, ita wak’a da fatar baki ake yin ta, kamar magana, amam ta bambanta da magana, saboda ita tana da ma’auni, kuma rerata ake yi cikin murya mai dad’i.

  • Wak’a wani sak’o ne da aka gina a kan tsararriyar k’a’ida da ta shafi baiti da layuka da kari da kuma amsa-amo, ta hanyar za’bar kalmomi da jeranta su a bisa ma’auni.

  • Wak’a ta k’unshi k’ololuwar hikima da tunanin d’an Adam ta hanyar yin amfani da k’wayoyin muryoyi aunannu da kuma kalmomi za’ba’b’bu tare da jeranta su cikin tsari fitacce kumka k’ayyadadde (Yar’aduwa, 2010: 75).


Su ma mawak’a (na baka da marubuta) ba a bar su a baya ba wajen tofa albarkacin bakinsu dangane da fahimtar da suka yi wa wak’a. Alal misali, Alk’ali Bello Gid’ad’awa, wanda yake marubucin wak’ok’i ne kuma shugaban k’ungiyar manazarta da marubuta wak’ok’in Hausa ta k’asa ne ya bayyana ra’ayinsa kamar haka: “Wak’a dai managa ce tsararriya wadda ake shiryawa a bisa wasu muryoyi na musamman, wadda kuma ta bambanta da maganar yau da kullum. Ba kowa da kowa yake iya yin wak’a ba sai wanda Allah ya yi wa baiwar iya yin ta.”

Shi kuma Alk’ali Haliru Wurno a wak’e ne ya bayyana nasa ra’ayi kan ma’anar wak’a yana mai cewa:

Wak’a d’umi ne hira ko labari,

Zargi yabo zagi da kiznin sharri,

Koko kwad’ai ga mutum ya ba ka ka amsa.

 

Labar d’umi na wanda kay yi ga tsari,

Wani dunk’ulalle kay yi jeri-jeri,

A cikin nashad’i ko ganin ka k’osa.

 

Wak’e bayani na kad’anna da tari,

Wani bi ka sa gishiri ka yo mishi k’ari,

Had’ari na wak’e mai fad’in damassa.

 

Wak’a da wak’e Hausa sun d’auke su,

Sunansu wak’a ko’ina an san su,

Ka bid’o bayani babu sai dai kansa.

 

Wak’a fasaha ne da yac cud’e ka,

Kuma ba karatuna ba in an ba ka,

Ilimi dubu sai ka bid’o wani nasa.

 

A cikin d’umi wak’e kamar rana ne,

Kuko ya zam hadarin ruwan bazara ne,

Shi taho da sanyinai na ma’aunin nesa.

(Alkali Haliru Wurno ma’anar wak’a)

Su ma mawak’an baka ba a bar su a baya ba ga yin nuni zuwa ga abin da suke ganin shi ne wak’a. Ibrahim Narambad’a ya yi nuni da abubuwan da yake ganin tilas ne kowace wak’a ta k’unsa kafin a ce ta amsa sunanta na wak’a. Ya yi wannan nuni ne  yayin da yake son ya bayyana cewa shi fa ba kanwar lasa ba ne a ‘bangaren wak’a. Ga abin da ya ce:

Ai ba a gama ni da yaro,

Na san yaro ai yi muk’amina ba,

Kak ku gama ni da yaro,

Kun san yaro bai yi zalak’ata ba,

Kak ku gama ni da yaro,

Kun san yaro bai yi fusahata ba,

Kak ku gama ni da yaro,

K’aryab banza yaro bai kai inda,

Narambad’a mai tabarukun sarki.

(wak’ar sarkin Gobir na Isa Ahmadu Bawa)

A wannan d’an wak’a Narambad’a yana nuni ne da cewa akwai zancen k’warewa a fagen tsara wak’a. K’warewar kuma ta had’a da ta harshe. Nazambad’a ya ambaci zalak’a da fasaha kalmo da suka tattara gwaninta da azanci da tsari da rerawa da salo da kuma sak’o wato jigo.

Si kuwa Alhaji Musa D’ank’wairo shi ma ya yi nuni da abin da yake gani ita ce wak’a. A wak’arsa da ya yi wa ‘Yandoton Tsafe Aliya yana cewa:

Dum makad’an da at Tcahe na shahe,

Hab bak’i ha ‘yan gida su duka,

Babu mai shirya wak’a kamat tawa,

Dum makad’an da at Tcahe nai jam’i,

Hab bak’i ha ‘yan gidan su duka,

Babu mai k’ulla wak’a kamat tawa,

Ga makad’i ya k’ulla wak’a tai,

Sai a amsa mashi ba a k’ara mai,

In nak k’ulla wak’a a k’ara man,

Mu hud’u du azanci gare mu,

Shin a’a mutum guda za ya yarde mu.

(Shirya kayan fada)

Wannan d’an wak’a yana nuni da cewa wak’a dai magana ce da ake tsarawa (shirya) tare da zuba magana cikin rauji mai gard’i saboda aunawa (k’ulla) da kuma bin hanyoyi ko dabarun harshe, wato salo (azanci) wadannan su za su sa magnar ta reru (amsa).

3.2 Jigo


Wannan shi ne muhimmin abu na biyu da ake yin la’akari da shi wajen nazarin wak’a. Bayan an k’are duba tsarin wak’a sai kuma a duba jigonta.

3.2.1 Ma’anar Jigo


Masana sun tofa albarkacin bakinsu dangane da ma’anar jigo. Misali ‘Yar’aduwa (2010:149) ya ce: “Jigo kalma ce da masana adabin Hausa suka amince su rik’a yin amfani da ita wajen ambaton sak’on da zube ko wasan kwaikwayo ko wak’e suke d’auke da shi. to da yake wak’a tana iya d’aukar sak’onni da yawa, masu nazarin rubutattun wak’ok’in Hausa sun amince da cewa, wak’a tanan da babban gundarin jigo da kuma k’aramin/k’ananan jigogi.

D’angambo (2007: 14) ya bayyana ma’anar jigo da cewa: “Jigo shi ne sak’o, manufa, ko abin da wak’a ta k’unsa wato abin da take magna a kai.” Yahya (1997) ya bayyana ma’anar jigo da cewa: “Jigo na nufin sak’o ko manufa ko bayani ko ruhin da wak’a ta kunsa wanda kuma shi ne abin da wak’a ke son isarwa ga mai sauran ko karatu ko nazarinta.”

3.2.2 Ma’anar Turke


Turke a k’a’idar masu nazarin wak’ar baka na nufin sak’on da wak’a take d’auke da shi. idan an ce sak’o ana magana ne kan manufar da ta ratsa wak’a tun daga farkonta har zuwa k’arshenta, ba tare da karkacewa daga cikikin abin da ake zance a kansa ba.

Ma’anar Turke daga bakin masanai: Gusau, (1993: 28) ya bayyana ma’anar turke da cewwa: “Turke shi ne abin da wak’a take magana a kansa wanda ya ratsa ta tun daga farkonta har zuwa k’arshenta.”

3.3 Jigon Gargad’i da Wa’azi A Wak’ar Kud’i Ta Gambo Hawaja


Babban jigon wannan wak’a shi ne neman kud’i akwai k’ananan jigogi da ya yi amfani da su, wajen yin gargad’i da kuma wa’azi a kan neman kud’i. Misali: a baitocin da ya yi gargad’i a cikinsu misali:

3.3.1 Gargad’i


10 Mu koma jawabin kud’i tara dangi,

Akwai gargad’i masu neman kud’i.

Wannan shi ne baiti na farko a wak’ar inda yake cewa jawabi zai yi tare da gargad’i ga masu neman kud’i.

A baiti na (7) ya ce:

7) Ku zo gargad’i zan yi duk mai fahimta,

Idan dai ya gane ya nemo kud’i.

A wannan baiti kuma kira yake yi cewa gargad’i ne zai yi sannan wanda ya fahimta to ya je ya nemi kud’i.

A baiti na (98):

98) A neme shi amma idan anka samu,

A bar yin butulci manema kud’i.

A wannan baitin ma gargad’i yake yi cewa a nemi kud’i amma idan aka same su to kada a yi butulki.

212) A wannan bitin kuma ya ce:

212) Ina gargad’i kun k’i ji to ku zauna,

A ranar biki a yi zambar kud’i.

A wannan baitin gargad’i yake yi cewa idan mutane ba su ji gargad’in da ya yi ba suka zauna ba za su nemi kud’i ba to suna gani za a dinga watsi da kud’i suna kallo saboda ba su da shi.

3.3.2 Wa’azi


20 Ina ‘yan uwana ku zo ga jawabi

Mun ayin wa’azi ga neman kud’i.

A wanan baitin kuma kira yake yi tar da wa’azi da kuma jawabi ya kira ‘yan’uwa ya ce ga jawabi zai yi tare da wa’azi a kan neman kud’i.

A baiti na (99)

99) idan anka samu a bar ratse hanya,

Mu nemo gafara tun da sauran kud’i.

A wannan baiti wa’azi yake yi cewa idan an nemi kud’in an samu to a bar ratse hanya wato kana bin hanya wadda ka saba ba amma saboda ka yi kud’i kuma sai ka daina bi dan kada mutane su ganka ya k’ara ya ce a nemi gafara wurin Allah tun da sauran kud’in ba su k’are a.

A baiti na (22)

22) Fatauci, giya, caca neman kilaki,

A bar yin su in dai ana son kud’i.

A wannan baiti wa’azi ne inda ya gutsoro wani ‘bangare na ayar Al’k’ur’ani mai girma na  wasu abubuwa da Allah ya haramta wato (innamal khamru wal maisiru) a sura ta biyar aya ta tamanin da tara.

A wanan ayar Allah ya haramta wasu abubuwa guda biyu da mawak’in ya ce a bar yin su wato shan giya da kuma caca, wanda aka haramta aikata su a cikin wannan aya mai girma. Aya ta 89 sura ta biyar (Suratul Ma’ida).

A baiti na (26)

26) A bar son lauta amale ya kasa,

Gama babu kyawo manema kud’i.

A wannan baitin ma wa’azi cewa idan za a d’aura wa rak’umi kaya to kada a d’aura masu yawa wad’anda ba zai iya d’auka ba ya ce jin hakan babu kyau.

Wad’annan su ne wasu daga baitocin da mawak’in ya yi gargad’i da wa’azi a kan yadda ya kamata a nemi kud’i da kuma yadda ya dace a kashe su idan aka kawo inda aka kawo wasu daga cikin baitocin da suke magana a kan harkan.

3.4 Turken Wak’ar Kud’i Ta Audu Wazirin D’anduma Da Alhaji Mamman Shata


Turke a wak’ar baka shi ne sak’o ko manufa da ta ratsa wak’a tun daga farkonta har zuwa k’arshenta. Babban turken wak’ar Alhaji Audu Wazirin D’anduna wato wak’ar “Tsakanin D’an Adam da Kud’i” shi ne garad’i misali:

A d’a na shida (6)

6) Jagora: Yanzu ba wata harka sai kana da kud’i,

‘Yan Amshi: Tsakanin d’an Adam da kud’i.

A wannan d’a yana yi wa mutane garad’i cewa yanzu idan ba ka da kud’i to ba wata harka da za a sa ka a ciki.

A d’a na bakwai (7)

7) Jagora: Saboda ba ka sawa sai kana da kud’i,

‘Yan Amshi: Tsakanin d’an Adam da kud’i.

Ya ce kuma idan ba ka da kud’i ba ka isa ka hana abu ba saboda kawai baka da kud’i.

A d’a na goma (10)

10) Jagora: Ba ka komi sai kana da kud’i,

‘Yan Amshi: Tsakanin d’an Adam da kud’i.

A wannan d’an ma gargad’i ne yake yi cewa idan ba ka da kud’i to ba za ka iya komai ba sai dai ka yi kallo.

A d’a na talatin (30)

30) Jagora: Kai ko girmama sai kana da kud’i,

‘Yan Amshi: Tsakanin d’an Adam da kud’i.

A wannan baitin ma gargad’i ne yake yi cewa idan ba ka da kud’i ba wanda yake ganin girmamaka.

A d’a na talin da d’aya (31)

310 Jagora: Kuma akan yi rashin girma saboda kud’i,

‘Yan Amshi: Tsakanin d’an Adam da kud’i.

A wannan d’a kuma ya ce idan mutum ba shi da kud’i to ba shi da wani girma a idon mutane saboda kawai rashin kud’i.

Haka kuma akwai inda yake k’ara yi wa mutane gargad’i cewa kud’i yana sa fad’a da iyaye misali:

Jagora: Kud’i mai sa fad’a uba kud’i mai sa fad’a da uwa,

‘Yan Amshi: Tsakanin d’an Adam da kud’i.

3.4.1Wak’ar Kud’i A Kashe Su Ta Hanya Mai Kyau Ta Alhaji Mamman Shata


 

https://www.amsoshi.com/2018/01/27/kudi-idan-mawakan-hausa-na-baka-da-rubutattu-wakar-kudi-ta-alhaji-audu-wazirin-danduna-da-ta-alhaji-mamman-shata-da-kuma-gambo-hawaja-3/

3.4.1.1Gargad’i


A d’a na d’aya (1)

Jagora: Amma ba bisa shashanci ba,

Kana ba bisa sakarci ba,

Kud’i a kashe su ta hanya mai kyau.

Y/Amshi: Kud’i a kashe su ta hanya mai kyau.

A wannan d’a gargad’i ne yake yi cewa idan za a kashe kud’i kada a kashe su ta hanyar sakarci da shashanci abu mafi kyau a kashe su ta hanya  mai kyau.

A d’a na biyu (2):-

Jagora: Ka tina yanda ka samu kud’inka,

Ka sha wuya ka sami kud’inka,

To je ka kashe su ta hanya mai kyau,

Y/Amshi: Kud’i a kashe su ta hanya mai kyau.

A wannan d’a ma gargad’in mutane yake cewa, su tuna yadda suka sami kud’in to su je su kashe su ta hanya mai kyau.

A d’a na biyar (5)

Jagora: Malam duk cinikin da kake yi,

Duk wuyar shi dud dad’in shi,

In ka sami kud’in ka tara,

In dai kai niyyar ‘badda su,

Je ka kashe su ta hanya mai kyau,

Y/Amshi: Kud’i a kashe su ta hanya mai kyau.

A wannan d’a gargad’i ne yake yi cewa duk cinikin da mutum zai yi duk wuyar shi duk dad’in shi in ka samu kud’i ka tara kuma idan ka yi niyyar ‘batar da su to ka je ka kashe su ta hanya mai kyau.

A d’a na shida (6)

Jagora: Ko ni Alhaji sarkin wak’a,

In nai wak’a kyakkyawa,

Na sami kud’i mai kauri,

Ba ashararu,

Ba sakarci,

Sai in kashe su ta hanya mai kyau

A wannan d’an wak’a yana gargad’in mutane cewa ko shi Alhaji sarkin wak’a in yai wak’a kyakkyawa kuma ya sami kud’i masu kauri ya tara has sun kauri, ba asharu ba sakarci to sai ya kashe su ta hanya mai kyau.

A d’a na tara (9)

Jagora: Tsaya dukiya abin nema ce,

Su kud’i abin nema ne,

Tittieje nemi abinka,

Baza k’arfi nemi kud’inka,

In kuma ka tashi kashewa,

To ka kashe su ta hanya mai kyau.

A wannan d’a gargad’i ne yake yi cewa su kud’i abin nema ne ka daddage ka nemi kud’i kuma ka baza k’arfi ka nemi kud’i, amma in za ka akshe su to ka kashe su ta hanya mai kyau.

A d’a na sha biyu (12)

Jagora: An dena almubazzaranci,

Ba shashanci ba sakarci,

In ka nemi kud’i ka tara,

In kai niyya za ka kashe su,

To ka kashe su ta hanya mai kyau.

A wannan d’an ya ce idan an daina almubazzaranci ba shashanci ba sakarci, idan ka nemi kud’i ka tara, in kai niyyar za ka ‘batar to ka kashe su ta hanya mai kyau.

A d’a na sha uku (13)

Jagora: Ga wani ya yi gumi ya samu,

Ya sha wuya ya samu,

Ya zo wurin ‘baddawa,

Ya ‘badda a cikin sakarci,

Wannan ya zama wawa ke nan,

Be ji ba zancen Mamman Shata.

 

Ya ce idan mutum yai gumi ya tara ya sha wuya ya samu ya zo a wurin ‘baddawa ya ‘badda a cikin sakarci ya ce to wannan ya zama wawa kenan bai ji ba gargad’in da Mamman Shata ya yi ba.

Wad’annan su ne d’iyoyi daga wak’ar Audu wazirin D’anduna ta tsakanin d’an Adam da kud’i da kuma wak’ar kud’i ta Alhaji Mamman Shata wato kud’i a kashe su ta hanya mai kyau, wad’anda suke gargad’i da kuma irin abubuwan da kud’i ke sawa.

3.5 Nad’ewa


Daga k’arshen wannan babi wanda ya yi magana a kan jigo da turke, an kawo ma’anar wak’a daga bakin masana da ma’anar jigo da kuma ma’anar turke duk daga bakin masana inda aka bayyana jigogin da suke gargad’i da wa’azi a wak’ar kud’i ta Gambo Hawaja daga cikin baitocinta da kuma jigon gargad’i daga d’iyoyin wak’ar kud’i a kashe su ta hanya mai kyau ta Mamman Shata da kuma wak’ar tsakanin d’an Adam da kud’i ta Audu Wazirin D’anduna.

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

 

Post a Comment

0 Comments