Ticker

6/recent/ticker-posts

Hausar Masu Ƙwallon Ƙafa A Cikin Garin Kano (3)

KUNDIN DIGIRI NA FARKO WANDA AKA GABATAR A SASHEN NAZARIN HARSUNAN NIJERIYA, JAMI’AR USMANU ‘DANODIYO, SAKKWATO

USMAN ADAM ROGO

Ƙwallon Ƙafa

BABI NA BIYU

BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA

2.0    Shimfiɗa


Wannan bincike zai duba wasu ayyuka da suka gabata masu alaƙa ta ƙut-da-ƙut da wannan bincike, domin yin hakan zai taimaka wajen samar wa wannan bincike alƙibla sosai da sosai. A wajen wannan bincike, an duba littattafai da kundayen bincike a matakai daban-daban da maƙalu da kuma intanet wajen zantar da bitar. Za a nuna abin da binciken nasu ya gano a taƙaice, tare da nuna inda wannan bincike ya sha bamban da nasu. Wannan bitar za ta kasance kamar haka:

2.1    Ma`anar Ƙwallon Ƙafa


Ƙwallon ƙafa wasa ce da ake yi tsakanin ɓangarori guda biyu, a wani fili murabba`i mai tsarin na musamman bisa ƙa`ida. Ƙungiyoyin za su riƙa ƙoƙarin jefa ƙwallo, wacce ake bugawa da ƙafa, zuwa cikin ragar abokiyar hamayya domin samun nasara. Wasan yana da ƙa`idoji wajen gudanar da shi. Bari a waiwayi abin da masana suka ce kan wasan ƙwallon ƙafa:



Sil
verman (2008)

Football is a family of team sports that inɓolɓe, to ɓarying degrees, kicking a ball with the foot to score a goal.


 

             Fassara

Ƙwallon na nufin wasa da ake gudanarwa tsakanin ƙungiyoyi guda biyu da ake bugawa da ƙafa domin a zura ƙwallo a cikin ragar gola.


Lincoln (1998)

 

Football is a game played by two teams of ele
ven players (11) on a rectangular field (100) one by hundred.


             Fassara

Wasan ƙwallon ƙafa nufin wasa da ake gudanarwa tsakanin ƙungiyoyi guda biyu wanda kowannensu ke da `yan wasa goma sha ɗaya a cikin fili mai tsayin yadi ɗari ɗaya.

Merriam Webster (2004)


Football is any several games played between two teams of a usually rectangular field haɓing goal posts or goals at each end and whose object is to get the ball oɓer a goal line, into a goal, or between goal posts, by running, passing or kicking.”

             Fassara

Wasan ƙwallon ƙafa na nufin wasa da ake tsakanin ƙungiyoyi guda biyu a cikin babban fili na wasa mai ɗauke da gololi biyu da ake son zura ƙwallo a cikin ragar gola, ta hanyar gudu da bugawa da kuma miƙawa.

 

Collins, (2012)



Football is a game played by two teams of eleɓen players using a round ball. Players kick the ball to each other and try to score goals by kicking the ball into a large net.

            Fassara

Wasan ƙwallon ƙafa na nufin wasa da ake gudanarwa a cikin fili da ke da `yan wasa guda sha ɗaya, waɗanda za su riƙa bubbugawa tare da miƙa wa junansu ƙwallo don su yi ƙoƙarin zura ƙwallo a cikin ragar gola.



 

Bayan ganin ra’ayoyin ayyukan da suka gabata kan ma’anar ƙwallo ƙafa a taƙaice, ƙwallon ƙafa wasa ce da ake yi tsakanin ɓangarori guda biyu, a wani filin ƙwallo bisa wasu ƙa’idoji da aka shata, duk wanda ya saɓa za a hukunta shi. Kowane ɓangare zai riƙa ƙoƙarin jefa ƙwallo, wacce ake bugawa da ƙafa, zuwa cikin ragar abokiyar hamayya domin samun nasara a ƙarshen wasar.

2.2    Ƙwallon Ƙafa a Cikin Garin Kano


A wannan ɓangaren za a yi taƙaitaccen tsokaci ne  kan yadda ƙwallon ƙafa ta kasance a cikin garin Kano. Tsokacin zai kasance ta hanyar kawo ra’ayoyin masana daga wallafaffun litattafai da kuma tattaunawar da aka yi da ma’abota wasan ƙwallon ƙafa.

Fagge (2002:134-135), Tarihi ya nuna cewa an fara buga ƙwallon ƙafa a wani gari da ake ƙira Deɓry da ya ke cikin ƙasar Ingila a shekara ta (217) masihiyya, wato shekaru aru-aru da suka shuɗe. Bayan haka an haƙiƙance cewa mutum na farko a duniya da ya fara gwada buga ƙwallon-ƙafa shi ne mai suna Adam, wanda ya buga wata abarba ta yi gari a bakin wani lambu a wannan gari na Deɓry. “Wasan ƙwallon ƙafa da aka fara yi a zamanance, shi ne a ƙasar Biritaniya a ƙarni na 19. A Biritaniyar ne aka fara tsarawa wasan ƙa`idoji a shekarar 1930.”

Wasan ya ci gaba da yaɗuwa a hankali a hankali inda a yanzu za a iya cewa ya karaɗe kusan duk yankin ƙasar Hausa, kuma ya samu karɓuwa musamman a wurin wasu matasa masu sha`awar wasan har ma da masu buga shi, haka kuma ana ta buɗe gidajen kallon wasan ƙwallon ƙafa a wurare daban-daban da ke cikin garin Kano.

A hirar da na yi da wani matashi mai suna Safiyanu Ɗan-kulob, ya tabbatar min da cewa, su suna buga wasan ƙwallo kusan shekaru talatin da bakwai (37) da ta wuce a garin Kano. Matashin ya nuna cewa kafin su kuma akwai waɗansu da suka riga su a wajen wasan ƙwallo, kamar irin su Muhmud Fele, da Habu Delpiero, da dai sauransu, ya nuna cewa fara wasan ƙwallo a garin Kano yana da nasaba da buɗe makarantar boko a 1905 a cewar  (Yahaya, 2002:92). Malamai Turawa irin su Danny, da su Gabriel da sauransu, su ne suka fara buga wasan ƙwallon ƙafa a makarantar Kano, wato Rumfa College.


A hirar da na yi da malam Audu mai Doya a ranar (19-05-2017) da misalin ƙarfe (4pm) na yamma, da Malam Idris Isa (20-05-2017) sun tabbatar min da cewa kafin shekara ta 1980, ba a samu wani gidan kallon wasan ƙwallon ƙafa ba, wanda ake biya ana shiga domin kallo a garin Kano. Ya nuna cewa tarihin ginuwar gidajen kallo a garin Kano ba zai cika ba in ba a ambaci gudummawar da tashar watsa shirye-shirye ta FREEDOM ta bayar ba. An nuna cewa wannan shi ne gidajen rediyo na farko na gida, da ya fara watsa shirye-shirye na ƙwallon Turawa a garin Kano a wajen 1983.


Gidan farko da ake ganin shi ne na farko a garin Kano, shi ne na “Yahsar ɓiewing Center.” Duk da cewa akwai masu ra`ayin cewa gidan farko na kallon wasan, shi ne “Yahaya Sinima” da kr Farm Center. Wannan kuma ake ganin ya zo bayan waɗancan, shi ne “Lahai”. Waɗannan gidaje kusan su ne tushe na wanzuwar gidajen kallon wasan ƙwallon ƙafa a garin Kano. Bincike ya tabbatar da cewa a halin yanzu akwai gidajen kallon wasan wajen guda  270 a cikin garin Kano. Abin da yake sananne shi ne cewa an daɗe ana kallon ƙwallo a filayen ƙwallo da ke cikin garin Kano kamar dai yadda wancan matashi Safiyanu Ɗan Kulob ya faɗa. Kallon wasan ƙwallon ƙafa a gidajen kallo shi ne ya zo daga baya.

2.3    Hausar Masu Ƙwallon Ƙafa


A wannan ɓangaren za a duba ma’anar  Hausar masu ƙwallon ƙafa  daga bakin masana kamar haka:


Yahaya, (2012:26) ya ce, Hausar masu ƙwallon ƙafa Hausa ce da ake samu tsakanin yara ko matasa a yayin buga ƙwallon ƙafa ko a wurin kallonta. Wato wuri ne da ake zama a kalla sannan kowa ya faɗi albarkacin bakinsa game da wasan da ake gudanarwa ga ƙungiyoyin hamayya. Ma’ana ‘yan adawa a tsakanin ƙungiyoyin nan guda biyu.


Umar da Shehu (2016:135) “Hausar masu ƙwallon-ƙafa Hausa ce da ake samu a tsakanin matasa a filayen buga ƙwallon ƙafa, wato wuri ne da ake kira filin wasa, inda ake buga ƙwallo a matsayin motsa jiki. Wannan karin harshe yana samuwa ne kafin a fara kallon wasa, inda kowane mai goyon baya zai tofa albarkacin bakinsa a kan yadda wasar za ta kasance. Sai dai, idan an fara kallon wasar, lokaci ne da ake samun tsananin adawa, nuna goyon baya, da riƙa jefa kalaman tsokana ko na wasa kai, musamman idan ana kan nasara. Sai babban lokacin gardandami bayan an gama kallon wasar, wanda ke haifar da hirar ƙwallo a duk inda aka ga gungun matasa. Irin wannan lokaci ne magoya bayan ƙungiyoyi da suka fafata ke bayyana ra`ayoyinsu a kan rashin adalcin da aka yi wa wani ɓangare, ko nuna jin daɗi ko rashin jin daɗin yadda ƙwallon ta kaya. Ita ma wannan Hausar masu ƙwallon ƙafar kamar takwararta da ake yi  filin buga ƙwallo, ana samun ma`abota kallon wasar ƙwallon ƙafa na amfani da ita a cikin maganganunsu na yau da kullum, musamman idan sun haɗu da junansu.

A ra`ayin mai rubutu ko bincike, Hausar masu ƙwallon-ƙafa Hausa ce da ake yi tsakanin magoya bayan kowace ƙungiya da masu kallonta ke so. Sannan kuma kalmominta na iya kasancewa masu harshen damo, domin wasu ma`anoninta kan bambanta da yadda aka san su a harshen Hausa.

Naɗewa

Wannan babi na biyu ya yi bayani ne a kan bitar ayyukan da aka gabatar masu alaƙa da wannan bincike. Don haka, a wannan babi an yi bayanin ma`anar ƙwallon ƙafa da Hausar masu ƙwallon ƙafa, musamman kamar yadda ayyukan da suka gabata suka zo da su.

Post a Comment

0 Comments