KUNDIN BINCIKEN KAMMALA KARATUN DIGIRI NA FARKO (B.A. HAUSA) A SASHEN KOYAR DA HARSUNAN NIJERIYA, JAMI’AR USMANU ‘DANFODIYO, SAKKWATO
NA
USMAN ADAM ROGO
BABI NA UKU
TSARIN GUDANAR DA BINCIKE
3.0 Shimfid’a
Akwai buk’atar kowane bincike ya kasance an yi bayanin tsarin da aka bi wajen gudanar da shi, domin kyautata shi da amfanin masu nazari. Wannan babi zai yi bayani ne a kan yadda wannan bincike ya kasance, wato tsarin da aka bi domin gudanar da shi, da kuma hanyoyin tattara bayanai da aka yi amfani da su wajen gudanar da wannan bincike.
3.1 Hanyoyin Gudanar da Bincike
A duk lokacin da za a gudanar da wani aiki, yana da kyau a samu tsarin da za a bi wajen tafiyar da aikin, domin samun alk’ibla da sauk’in gudanarwa. Kasancewar wannan aiki, bincike ne da zai kalli Hausar masu kallon wasan k’wallon k’afa a cikin garin Kano. Wannan dalili ne ya sanya aka za’bi hanyoyin gudanar da bincike na gani da ido, inda za a je a ziyarci wasu za’ba’b’bun wuraren kallon k’wallo na kud’i da filayen buga k’wallo na cikin garin Kano, domin samun damar tattatro ingantattun bayanai daga wuraren, da kuma amfani da hanyar nazartar kayan karatu a d’akunan karatu daban-daban. Ga hanyoyin:
3.1.1 Hira
Wannan bincike zai kalli Hausar masu kallon k’wallon k’afa a cikin garin Kano. Wannan ke nuna cewa bincike ne a k’ark’ashin ilimin walwalar harshe kuma a karin harshen rukuni. Yanayin bincike irin wannan ya nuna akwai buk’atar a zauna da masu kallon k’wallon k’afa, domin samun bayani daga tushe. Saboda haka, za a yi amfani da hanyar hira wajen tattaro bayanai da za su taimaka a cimma manufar fito da wannan nau`in Hausar masu k’wallon k’afa kamar yadda take.
Wannan bincike ya za’bi mutum uku daga kowace unguwa daga wad’annan unguwanni sha biyar da za a ambata a gaba, domin gunar da hira da su. An yi wannan za’ben ta fuskar wanda yake da masaniya a kan wasan na k’wallon k’afa, kuma ya aminta da ya bayar da lokacinsa wajen wannan tattaunawar. Baya ga wad’annan mutane uku-uku, hakazalika an yi hira da wasu fitattun masu sha`awar wasan k’wallon k’afa, wad’anda suka dad’e suna bin kadin wasan a garin Kano.
Wasu daga cikin hirarrakin da aka gudanar, an samu sukunin nad’ar maganar a rikoda da wayar hannu; wasu kuma daga ciki ba a samu damar nad’ar zantukansu ba, amma kuma an rubuta bayanan da aka samu a takarda domin amfani.
Bayanan da aka samu a wannan hira, sun nuna cewa lallai akwai wanzuwar karin harshen masu kallon wasan na k’wallon k’afa a garin Kano. An fahimci haka ne daga wasu daga cikin tambayoyin da aka yi da wad’anda aka yi hira da su. Misali, (1) Ko kana da masaniya cewa masu kallon k’wallon-k’afa a garin Kano suna amfani da wasu kalmomi na musamman wad’anda ma`anarsu ta sha bamban da yadda ma`anar sauran mutane ke amfani da su a harkokin yau da kullum. (ii) Me ya sa masu k’wallon k’afa ba sa da sha`awar kallon wasan k’wallon gida Najeriya? A tak’aice, kashi dari (100%) na wad’anda aka yi hira da su sun nuna suna da masaniya a kan kalmomin, sai dai ba su cika mayar da hankali a kan wasannin k’wallo da ake bugawa na cikin gida ba.
3.1.2 Lura ta Kai-Tsaye
Kasancewar lura ta kai-tsaye tana bayar da damar ganin hak’ik’anin yadda ake aiwatar da abu ko gudanar da shi. An za’bi wannan hanya ce, bayan waccan ta farkon, domin tattaro ingantattun bayanai a kan abin da ake bincike. An yi amfani da gidaje goma sha biyar. Wad’annan gidaje, gidaje ne na kallon wasan k’wallon k’afa a cikin garin Kano. Kowane d’aya daga cikin wad’annan gidaje ya fito ne daga unguwanni sha biyar da za a ambata a gaba.
Mai binciken shi ne da kansa ya rik’a shiga wad’annan gidaje yana kallon wasan tare da masu kallon wasan k’wallon k’afar. An rik’a shiga lokaci bayan lokaci, musamman lokacin da ake gudanar da wasa a tsakanin fitattun k’ungiyoyin wasan k’wallon k’afa. An yi haka ne saboda shigar ta bayar da dama a tattaro jawabai daga wurinsu, musamman abin da ake nema na kalmomi da jimloli. Da samun a fahimci sababbin ma`anoni da suke baiwa kalmomin da sauran jawaban da ake buk’ata. Don haka, wannan hanya ta lura ta kai tsaye ta bayar da dama an tattaro jawabai masu yawan gaske, kama daga kalmomin da ma`anarsu da Hausance sunayen `yanwasa da masu kallon kan yi, ta yi la`akari da jerin sautin bak’ak’en sunayen asali na `yan wasa da sauransu.
3.1.3 Nazarin Rubuce-Rubuce
Wannan ita ce hanya ta uku da aka yi amfani da ita domin tattaro jawabai a wannan bincike da aka gudanar. An yi nazarin rubuce-rubuce ne daga wallafaffun littattafai da kundaye da kuma mak’alu irin su:
Ire-iren karin Harshen Hausa na Rukuni na Fagge (2004), da Hausar `Yan tashe na Abdu A (2008), da Led’ico Semantic Ed’tention, in Present day Kano na Abdullahi Fagge da sauransu (ba shekara), da Dialectal Influence in the Choice of ‘Boiceless Labials in Kano Hausa na Fagge (2006), da Semantic Cur’be disruption in Karin magana na Cal’bin Y.G, (2007), Zaurance a matsayin kwari na Ashiru, (2016), da Political Language as the Source of Led’ical Ed’pantion na Sammani (2005), da Issues in Hausa Dialectology na Zariya da sauransu (2008), da Nazari a kan Hausar Gidan Rediyo na Kaduna ta Munir Mamman (2012)., da The De’belopment of Neologism: The Role of Urban Spaces ta Adamu M.Y da sauransu (2013).
An gudanar da wannan bincike daga d’akunan karatu manya da k’anana, daga cikin d’akunan karatu da aka ziyarta a k’ok’arin gudanar da wannan aiki sun had’a da:
- Babban d’akin karatu na jami`ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto.
- Babban d’akin karatu na jami`ar Bayero da ke Kano.
- Babban d’akin karatu na jami`ar Ahmadu bello da ke Zariya.
- Babban d’akin karatu da ke garin Kano.
- D’akin karatu da ke Sashen Koyar da Harsunan Najeriya da ke jami`ar Usmanu Danfodiyo Sokoto.
- D’akin karatu na Kwalejin Tarayya da ke Kano.
https://www.amsoshi.com/2017/09/27/ke%c6%83a%c6%83%c6%83-kalmomin-intanet-da-amfannsu-ga-bunkasa-tattalin-arzikin-kasa/
3.2 Yadda aka Tattaro Bayanai
Mai bincike ne da kansa ya tafi takanas ta kano, domin samo wad’annan bayanai saboda haka ba a yi amfani da d’an sak’o ba wajen tattaro bayanan da aka yi amfani da su wajen aiwatar da wannan bincike. An tattaro bayanai ta hanyar gudanar da hirarraki, wad’anda daga cikinsu an d’auki hirar a wayar hannu, wasu kuma daga ciki an gudanar da hirar ce ta hanyar rubuta manyan bayanan da ake buk’ata. An gudanar da lura ta kai tsaye a gidajen kallon wasan k’wallon k’afa da ke cikin garin Kano. An kuma yi nazarin rubuce-rubuce, musamman wallafaffu.
3.2.1 Wuraren da Bincike ya Shafa
An za’bi gidajen guda goma sha biyar wad’anda ake kallon k’wallo guda biyar. An yi haka ne domin a rik’a samun sukunin zama da su masu kallon k’wallon domin a fahimci kalmomin da ma`anoninsu daga wurinsu. An za’bi wad’annan gidaje ne daga unguwanni goma sha biyar (15), wad’anda suka had’a da:
- Tukuntawa
- Yakasai
- Sabuwar Gwandu
- Tudun Malik
- Sallari
- Madile
- Tsamiyar boka
- Dawanau
- Darmanawa
- Rijiyar lemo
- Hausawa sbon titi
- Mandawari
- `Yan kaba
- Gwammaja
- D’orayi.
3.2.2 Adadin Bayanai da aka Tattaro
A wasu daga cikin wad’annan gidaje ne da kuma filayen aka tattaro bayanan da suka taimaka wajen gina wannan aiki. Don haka, an tattaro kalmomi da dama kusan hamsin (50), tare da jumloli kusan ashirin da shida (26). Kamar yadda nazari zai zo a babi na hud’u.
3.3 Yadda aka Sarrafa Bayanai
Wannan ‘bangare zai nuna yadda aka sarrafa bayanan da wannan bincike ya yi nasarar tattarowa. Za a yi amfani da jadawali wanda aka kasa gida uku, kamar haka: Kashi na farko ya k’unshi kalmomi da jumloli masu matsayin Hausar masu k’wallon k’afa a cikin garin Kano. Kashi na biyu shi ne na sabuwar ma`anar wannan karin harshe na rukuni. A k’arshe, akwai kashi na uku mai d’auke da ma`ana ta asali wadda sauran mutane su ke da masaniya a kanta sa’banin sabuwar ma`ana.
3.3.1 Kalma ko Jimla a Matsayin Hausar Masu K’wallon-K’afa
Wannan sashe ya k’unshi gundarin kalmomi da jimloli wad’anda aka samo daga gidajen kallon k’wallon k’afa, ko majalisun samari daban-daban da ke cikin garin Kano. A tak’aice, kawo wad’annan kalmomi da jimloli tare da sabuwar ma`anarsu ita ce gudunmawar wannan aiki a fagen nazari.
3.3.2 Ma`an ta Asali
Wannan ma`ana ce wadda kowa zai iya fahimta a cikin harshe. Don haka za a kawo wannan ma`ana ta asali a cikin babi na hud’u.
3.3.3 Sabuwar Ma`ana
A wannan ‘bangare za a yi bayani ne a kan sababbin ma`anoni, wad’anda suka ke’banta ga rukunin jama`a masu kallon k’wallon k’afa a cikin garin Kano. Wad’anda ma`anonin sun sa’ba wa ma`anonin da aka sani na asali. Don ganin yadda sabuwar ma’ana take a Hausar masu k’wallon k’afa sai a dubi babi na hud’u.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.