Ticker

6/recent/ticker-posts

Hausar Masu Kwallon Kafa A Cikin Garin Kano (2)

KUNDIN BINCIKEN KAMMALA KARATUN DIGIRI NA FARKO (B.A. HAUSA) A SASHEN KOYAR DA HARSUNAN NIJERIYA, JAMI’AR USMANU DANFODIYO, SAKKWATO

NA

USMAN ADAM ROGO

BABI NA DAYA

Gabatarwa


Kasancewar Harshen Hausa harshe ne mai bunk’asa k’warai da gaske, kuma mai tafiya da zamani, kuma mai kar’bar bak’in abubuwa, ya sanya ana ta samun yawaitar sababbin ma`anoni a cikin Harshen. Masu kallon wasan k’wallon-k’afa a cikin  garin Kano suna amfani da wasu kalmomi da jimloli da  suka ke’banta gare su, sai dai wasu daga cikinsu sanannu ne ga mutane amma ma`anar wasu takan sha bamban da yadda sauran mutane suka san ta, kuma suke amfani da ita a harkokin yau da kullum. A wannan bincike mai taken: “HAUSAR MASU KWALLON K’AFA A CIKIN GARIN KANO”, za a yi k’ok’arin tabbatar da wanzuwar karin harshen masu kallon k’wallon-k’afa a cikin garin Kano. Haka zalika za a tattaro wasu daga cikin kalmomin da masu kallon k’wallon-k’afa ke amfani da su a wajen zantukansu a yayin kallon k’wallon da kuma lokacin hirarsu da ta shafi kwallo. Yawaitar kalmomi da jimlolin da ake samu a Hausa ya k’ara ba da k’warin guiwa da zama hujjar ci gaba da wannan bincike.

Wannan bincike ya k’unshi babi guda biyar. Babi na d’aya yana d’auke da manufar bincike, da farfajiyar bincike, da muhimmancin bincike, da kuma nad’ewa. Babi na biyu yana d’auke da bitar ayyukan da suka gabata, musamman masu alak’a da aikin ko batutuwan  da ya k’unsa. Babi na uku yana d’auke da tsarin gudanar da bincike. Babi na hud’u kuma yana magana ne a kan gundarin aiki, wato Hausar masu k’wallon k’afa a cikin garin Kano. Haka kuma, za a yi amfani da jadawali wanda zai k’unshi sassa uku wad’anda suka had’a da: Sashin kalma ko jimlar masu k’wallon k’afa, da sassan ma’ana ta asali da kuma sabuwar ma’ana. Babi na biyar kuma zai yi magana ne a kan tak’aitawa da kammalawa.

1.1 Manufar Bincike


Manufar wannan bincike ita ce, k’ok’arin fito ko gano hanyoyin samuwar Hausar masu kallon k’wallon k’afa a cikin garin Kano, ta hanyar tattaro ire-iren wad’annan kalmomi da jimlolin da suka ke’banta ga masu kallon k’wallon k’afa, wad’anda ke amfani da su  kafin a fara kallon wasa da lokacin kallon k’wallo da kuma bayan an kammala kallon wata wasar, inda ake samun  magoya bayan kulob-kulob suna amfani da salon fad’ad’a ma’anar kalmomi da k’irk’ira sabbin kalmomi ko jimloli da kuma sarrafa kalmomin aro, don biyan buk’atunsu na sadarwa. A tak’aice, wannan bincike na da manufar amsa tambayoyin bincike kamar yadda ya dace, don samun nasarar kammaluwarsa.

1.2    Farfajiyar Bincike (Scope and Limitation)


A wannan bincike an tak’aita shi ne a kan Hausar masu kallon k’wallon k’afa a cikin garin Kano (metropolis). Binciken ba zai ta’bo sauran k’ananan hukumomin garin Kano ba da kuma sauran garuruwa ko jahohin da ba Kano ba. Wato binciken ya shafi  masu kallon wasan k’wallon k’afa a gidajen kallon wasa, da kuma masu kallon wasan a filayen wasan k’wallo a unguwanni ko k’ananan hukumomin da aka za’ba. Ga jerin wasu k’ananan hukumomi da  ke cikin garin Kano, wad’anda za a gudanar da bincike a kansu. A kowace k’aramar hukuma an ziyarci wasu za’ba’b’bun gidajen kallon k’wallo na kud’i da kuma wasu filayen buga k’wallo daban-daban, domin k’ara tattaro bayanai.

 1. Nassarawa

 2. Kano Municipal
 3. Dala
 4. Fage
 5. Tarauni
 6. Kumbotso

1.3    Muhimmancin Bincike (Importance)


Wannan bincike yana da muhimmanci kasancewar sa kundin kammala Digiri na D’aya. Sannan kuma idan aka duba gudanar da irin wannan aiki zai sa a harshen Hausa da masu bincike su amfana da wad’annan abubuwa, da za su bayyana a cikin gundarin aiki da kuma sakamakon bincike kamar haka:

 1. Binciken zai tabbatar da wanzuwar karin harshen masu kallon wasan k’wallon k’afa a cikin garin Kano.

 2. Binciken zai tabbatar da hanyoyin samuwar Hausar masu kallon k’afa a cikin garin Kano. Za a yi bayanin su a babi na hud’u.

 3. Binciken zai fito da dangantakar da ke tsakanin sababbin ma`anoni, da kuma ma’anoni na asali, tare da bayyana yadda sauyawar ma`anar take kasancewa.

 4. Binciken yana da muhimmanci sosai saboda zai taimaka wajen taskace kalmomi da jimlolin Hausar masu k’wallon k’afa a cikin garin Kano, domin amfanin gobe. A tak’aice, bincike kafa ce ta adana harshe.

1.4    Tambayoyin Bincike (Research K’uestions)


        Tambayoyin bincike suna taimakawa ainun wajen tsara aiki, da kuma gina shi kamar yadda ya dace, musamman idan aka yi nasarar  amsa tambayoyin bincike. Amsar wasu daga cikin tambayoyin ita ce za ta rik’a bayyana a cikin babunan wannan aiki, tare da cikakken sharhi da kuma misalai a wuraren da suka dace don kafa hujja da k’arin haske. Ga tambayoyin:

 1. Me ake nufi da k’wallon k’afa?

 2. Mece ce Hausar masu k’wallon k’afa?
 3. A wad’anne wurare ake yin Hausar masu k’wallon k’afa?
 4. Ta wace hanya Hausar k’wallon k’afa ta bambanta da sauran wasanni?
 5. K’irk’iro Hausar k’wallon k’afa ake yi ko ita ke samar da kanta?
 6. Wad’anne abubuwa ke haifar da Hausar masu k’wallon k’afa?

1.5    Nad’ewa


Wannan babi na d’aya shi ne gabatarwar wannan bincike baki d’aya. A wannan babi an yi bayanin manufar bincike da muhimmancin bincike da farfajiyar bincike da tambayoyin bincike da dai sauransu. Wannan babi shi ke bayar da haske ga mai karatu domin ya fahimci inda aikin ya dosa.
www.amsoshi.com

Post a Comment

0 Comments