Ticker

6/recent/ticker-posts

Hausar Masu Kwallon Kafa A Cikin Garin Kano (5)

KUNDIN BINCIKEN KAMMALA KARATUN DIGIRI NA FARKO (B.A. HAUSA) A SASHEN KOYAR DA HARSUNAN NIJERIYA, JAMI’AR USMANU ‘DANFODIYO, SAKKWATO

NA

USMAN ADAM ROGO

BABI NA HUDU

YANAYIN HAUSAR MASU K’WALLON K’AFA A CIKIN GARIN KANO

4.0    Shimfid’a


Wannan babi ya k’unshi gundarin aikin. Babin ya kawo jerin kalmomi da jimloli da masu k’wallon k’afa ke amfani da su a wajen kallon wasan da kuma lokacin hirarsu da ta shafi wasan. An kuma kawo bayanin hanyoyin da masu kallon k’wallon ke amfani da su wajen samar da sababbin kalmomi a harshen. Musamman hanyoyin fad’ad’a ma`ana da k’irk’ira da kuma sarrafa kalmomin aro.

4.1    Hanyoyin Samuwar Hausar Masu K’wallon K’afa


Bature (2004: 132), ya bayyana hanyoyin da Hausawa suke bi wajen k’irk’irar sababbin ma`anoni ko kalmomi a harshen Hausa wad’anda suka had’a da: Fad’ad’a ma`ana daga kalmomi asali da na aro; k’irk’irar kalmomi wad’anda za su iya zama daga cikin kalmomin Hausa na asali, ko k’irk’irar kalmar da sam babu ita a harshe. Sannan kuma akwai sarrafa kalmomin aro. A wannan bincike, za a yi amfani da wad’annan hanyoyi da aka ambata a sama, domin ganin ko ana samun amfani da wad’annan hanyoyin a Hausar masu kallon k’wallon k’afa a cikin garin Kano.

4.2    Yanayin Hausar Masu K’wallon K’afa a Cikin Garin Kano


Hausar masu k’wallon k’afa a cikin garin Kano, Hausa ce da ake samu tsakanin matasa a filayen buga k’wallon-k’afa, wato wuri ne da ake kira filin wasa, inda ake buga k’wallo a matsayin motsa jiki. Yayin gudanar da wannan wasa ake samun yawan amfani da salon magana wanda ya ji’binci yanayin wasar k’wallon k’afa. Misali rik’a ambatar sunayen da suka shafi k’wallo, da fili, da `yan wasa da sauran yanaye-yanayen yadda aka gudanar da wasar. Haka kuma, lokacin kallon k’wallo ake samun ma`abota kallo na jefa kalmomi ko jimloli, wad’anda ke dacewa da yanayin yadda `yan wasa ke taka leda a cikin talabijin, ko sharhi irin na d’an kallo ko bayan fage.

4.2.1 Fad’ad’a Ma`ana Daga Kalmomi


A yayin da wani bak’on abu ya shigo wanda ba a san shi ba, Hausawa kan lura da yanayinsa, da aikinsa da sauransu, sai su sa masa suna ta yin amfani da kalmar da ta dace da shi (Bature 2004). Masu kallon k’wallon k’afa su ma ba abar su a baya ba, domin su ma sukan d’auki kalmomi domin su rik’a kiran sababbin abubuwa da su.

 Kalma ko JimlaMa’anar AsaliSabuwar Ma’ana
1.KatangaKatanga ko garuJerawar ‘yan wasa domin kariya ko tsaron gida.
2.AmaiDawo da abin da aka ciSakin k’wallo bayan mai tsaron gida a wannan k’wallo ya kama (gola)
3.K’waayaaNau’in hatsi ko k’wayar maganaSunan wani d’an wasa (Rio Ferdinand) yayin da yake wasa a k’ungiyar Manchester United
4.RumbuD’akin aje hatsiRaga
5.SarkiiShugaba mai mulkiSunan d’an wasa Ronaldinho
6.HariiKai farmakiA jawo k’wallo zuwa gidan abokan hamayya
7.TattarawaHarhad’a abu waje d’ayaJawo ‘yan wasa waje d’aya, domin a wuce da k’wallo
8.TsarkiiWanke al’aura bayan an gama kasha ko fitsariK’wallon da ake zurawa ta tsakanin k’afafuwa
9.AskiiD’ebe gashi ko rage gashiD’an wasa ya buga ta bi ta saman kan abokan wasan a d’an gajeren zango.
10.‘BaraawooMutuum mai satar kayan jama’aD’an wasa ya da ya yi kwantan gida aka kuma bugo masa k’wallo
11.WankaaTsabtace jiki da ruwaWucewar k’wallo ta kafad’un mai tsaron gida
12.MadaraaaNono sabon tatsaSunan kulob d’in Real Madrid
13.TabarmaaAbin zama ko kwanciyaD’auke k’wallo daga abokin wasa daga kwance
14.BangooKatanga‘Yan baya ko masu tsaro wad’anda ba a iya wuce su
15.JirgiJirgin sama ko k’asa ko na ruwaA buga k’wallo ta shiga ta saman turken raga
16.KanikawaMasu gyare-gyaren abubuwaSunan kulob d’in Chelsea
17.DatsaawaaRaba abu gida biyuYanka ko dabarun rik’e k’wallo ba tare da abokin karawa ya kar’ba ba.
18.TauriiK’arfi ko tsauriD’an baya da ba a iya wucewa ta wurinsa
19.GashiGasa wani abu kamar nama ko masaraWuya ke nan ko wahalar da abokan karawa
20.KunuuAbin sha da ake sarrafa shi daga dakakken gero da tsamiya ko kanwaK’ungiyar da ake cin nasa a kanta
21.GubaAbu mai dafi wanda in an ci zai iya kasha mutumK’ungiyar k’wallon k’afa ta Arsenal
22.CireTuge abu ko tum’buke shiA fitar da k’wallo daga yadi na 18
23.RigaaAba ce da ake sakawa a jiki mai hannaye da wuya domin suturta jikiDaidai da aski
24.ZagayawaGewayawaD’an wasa ya buga k’wallo ta daman wani d’an wasa sai ya gewaya ta hagu ya d’auki k’wallonsa
25.SingeeJifa da mashiBuga k’wallo da tsinin yatsu
26.AciiciMai yawan cin abinciD’an wasa mai sa’ar cin k’wallo
27.TaunewaaSarrafa abu da hak’ora don a had’iyeRashin nasara
28.MurfiAbin da ake rufe wani abu da shiK’wallon da ake bugawa da k’arfi tana saman iska
29.DafewaaD’owa hannu kan kafad’a ko kan wani abu don a dogaraRashin samun nasara
30.HariiKai yak’i ko yi wa mutuum farmakiA jawo k’wallo zuwa gidan abokan hamayya
31.GyarewaKyautatawaSamun nasara
32.TaushewaaA haye abuRashin samun nasara
33.JifaaWurga wani abuAiki da ‘yan k’wallo ke yi a wurga
34.MacijiDabba ce mai jan ciki wurin tafiyaSalon yanka mai kama da tafiyar maciji
35.MurjiZare biyu da aka had’aA bugi k’wallo da gefen babban d’an yatsa
36.CefaneSayen kayan miya na abinciSayen sababbin ‘yan wasa
37.RufeA rufe k’ofa ko kwano ko dai wani abuLokacin da wani d’an wasa ya yi shot ko  ya buga k’wallo da k’arfi don neman zura k’wallo cikin raga
38.GyadoWata dabbar dawaRonaldinho

4.2.2 K’irk’ira Daga Kalmomi


K’irk’ira na nufin k’ago sabon abu ta hanyar harhad’a kalmomin harshe na asali ko ta yin sarrafa kalmomin aro ko had’a kalmomin asali da na aro ko kuma samar da wata ma`ana da babu ita kwata-kwata a Hausa. A wannan sashe za a dubi yadda aka k’irk’iro wasu kalmomi daban daga bakin masu kallon k’wallon k’afa a cikin garin Kano. Ga misalan:

 Kalma ko JimlaMa`anar AsaliSabuwar Ma’ana
1.Dogon ragaInuwar ragaRonaldo na Brazil
2.Na ShakiraKirarin Gerrard Pik’ueSunan da ake yi wa Gerrad Pik’ue na Barcelona
3.Yi sama da shiA d’auki abu ko a cira shi.Mai tsaron gida ya hana wucewa
4.Ya buga masa suYin leg-o’berWasa da k’afafu ko yin wala-wala da su bayan d’an wasa na rik’e da tsakiyar k’afafunsa
5.Golan duniyaKirarin Iker CasilasIker Casilas golan k’ungiyar Real Madrid
6.Sajiyo k’wayaKirarin Sergio RamosWato “Sergio Ramos” d’an kulob d’in Real Madrid ta k’asar Spain
7.Alhajin Allah ko D’andauduLak’abin da ake yi wa wanda ya je Haji ko mai kwaikwayon mata“Mesut Ozil” na Arsenal ta k’asar Ingila
8.‘Barawon atakaSatar fage a wasan k’walloA bar d’an wasa shi kad’ai cikin gidan da ba nasu ba
9.Mai masallaciLak’abiWato Muhammad Kanoute d’an kulob d’in Se’billa ta k’asar Spain
10.K’arfi banzaaK’arfi wanda bai da amfaniSunan wani d’an wasa. Anderson
11.Yanka doleLak’abiSunan wani d’an wasa, Aaron Lennon
12.‘Yan biyu sha biyarTagwaye biyar guda ukuSunan k’ungiyar  Arsenal
13.Goron sallahKyautar da ake ba yara ranar sallaWasan k’wallon nasara da aka buga ranar salla
14.Kofi haramHaramtaccen kofiSunan k’ungiyar Arsenal saboda a lokacin sun dad’e masu ci wani kofi ba
15.Tada balbeluuA kori balbeluA buga k’wallo saman turken raga
16.A-ci-kullumLak’abiD’an wasa mai sana’ar ci k’wallo ko da yaushe
17.AsibitiWurin duba marasa lafiyaNau’in k’eta wacce ake fitar da mutum daga filin wasa
18.‘Yan damben gidaMasu wasar dambe a gidaSunan k’ungiyar k’wallo ta Arsenal da ke Ingila

4.2.3 Sarrafa Kalmomin Aro


Idan masu kallon wasan suka sami wani sabon abu ya shigo, wanda ba sa da shi a harshen Hausa, sukan d’auki kalmar aro sai a sarrafa ta, ta yadda za ta dace da sabon abin. Ana yin haka ne domin a sama wa bak’in abubuwa ko wani bak’on yanayi suna a harshen Hausa. Ga misali:

 Kalma ko JimlaMa`anar AsaliSabuwar  Ma`ana
1.      InjiniyaaMasani a fannin na`uroriSunan wani d’an wasa Deco saboda rarraba k’wallo ga `yan’uwansa.
2.      BenciiAbin zama na katakoJiran da d’an wasa ke yi a zaune.
3.      AlmakashiAbin yanka  yadi ko fata da sauransuNau`in k’eta ce ta amfani da k’afa biyu a sare
4.      RezaAska ce mai kaifi   biyuD’an wasan da ya iya yanka.
5.      MalamMasani ko mai koyarwa.Sunan wani d’an wasa Zinedine Zidane
6.      Kwastoma kulubMutum mai sayan kaya a wajenka ko wajen waniD’an wasa da duk suka had’u da wani kulob sai ya ci su k’wallo
7.      SugaaAbin sha fari mai zak’i da aka yi daga rakeK’ungiyar k’wallo da a ke yawan samun nasara
8.      Mainos  (Minus)TauyewaD’an wasa ya ja k’wallo da gudu kuma sai ya
9.      FashaaKalmar Turanci PartialitySon-kai
10.  Shaid’anIbilisSunan wani d’an wasa Da’bid Beckham
11.  LedaaAbar zuba kayaK’wallo
12.  Siri`aaSunan gasar da ake yi a k’asar ItaliyaYin wasan k’wallo tare da k’eta
13.  FirimiyaaSunan gasar da ake yi a BiritaniyaWasan k’wallo da za`a rik’a buga Biritaniya
14.  KataakooItce ne da ake gogewa don a yi tebur ko kujera ko gadoSunan wani d’an wasa Patrice E’bra
15.  HaddasanaaMai farar wani abu.Sunan wani d’an wasa Da’bid Beckham
16.  MonitaaShugaban aji a makaranta.D’an wasa Ste’ben Gerrard
17.  AljaniiHalittar ‘boye ko isaD’an wasa Lionel Messi
18.  TamaninGoma gida takwasD’an wasa Cristiano Ronaldo

 

4.3    Nadewa


An yi nazarin Hausar masu kallon k’wallon k’afa a cikin garin Kano. An tattaro kalmomi da jumloli na masu kallon k’wallon k’afar daga gidajen kallon k’wallo goma sha biyar da filayen wasa na k’wallon k’afa guda biyar a cikin garin Kano. An tattaro kalmomin kuma an bayyana ma`anoninsu. An yi kuma bayanin hanyoyin da aka bi wajen samar da kalmomin kama daga fad’ad’a ma`ana da k’irk’ira da sarrafa kalmomin aro. Haka kuma, masu kallon sukan Hausance wasu sunaye na `yan wasan ta hanyar sa masu sunayen Hausawa da suka yi kama da nasu na asali.
www.amsoshi.com

Post a Comment

0 Comments