Ticker

6/recent/ticker-posts

Hausar Masu Kwallon Kafa A Cikin Garin Kano (6)

KUNDIN BINCIKEN KAMMALA KARATUN DIGIRI NA FARKO (B.A. HAUSA) A SASHEN KOYAR DA HARSUNAN NIJERIYA, JAMI’AR USMANU ‘DANFODIYO, SAKKWATO

NA

USMAN ADAM ROGO

BABI NA BIYAR

JAWABIN KAMMALAWA


5.0 Shimfid’a


          Wannan babi shi ne na k’arshe wanda zai yi tak’aitaccen sharhi kan waiwaye ko tak’aitawa da sakamakon bincike da kuma shawarwari.

5.1    Waiwaye


A wannan sashe za a waiwayi abin da babukan bincike suka k’unsa, a tak’aice. Babi na d’aya ya k’unshi gabatarwa ta gaba d’aya. Sai babi na biyu inda aka yi bitar ayyukan da suka gabata masu alak’a da taken bincike. Babi na uku ya k’unshi hanyoyin gudanar da bincike. Babi na hud’u ya kawo kalmomi da jimloli wad’anda su ne Hausar rukunin masu k’wallon k’afar, ta hanyar  fito da n sabuwar ma`ana da kuma ma`ana ta asali, domin sawwak’a fahimta. A k’arshi akwai jawabin kammalawa a babi na biyar.

https://www.amsoshi.com/2018/01/04/fassarar-wasu-kalmomin-kiwon-lafiya-nazari-kan-asibitin-koyarwa-ta-jamiar-usmanu-danfodiyo-usmanu-danfodiyo-university-teaching-hospital-uduth-da-asibitin-kwararru-ta-sakkwato-2-2/

5.2 Sakamakon Bincike


Bayan kammala bincike an yi nasarar gano wasu muhimman abubuwa kamar haka:

  1. Hausar masu k’wallon k’afa ta samu ne ta hanyoyin fad’ad’a ma`anar kalmomin asali da na aro da k’irk’ira daga kalmomin asali, ko ta had’a kalmomin asali da na aro, ko ta samar da kalmomi wad’anda babu su a Hausa da kuma sarrafa kalmomin aro, ta hanyar Hausantar da su.

  2. Kirari- A cikin wannan Hausar masu k’wallon k’afa an samu yin amfani da wasu za’ba’b’bun kalmomi da jimloli, don zuga ko kambamawa wani kulob ko ‘yan wasa.

  3. Lak’abi- Wannan kuma kalma ce da ake d’auka a lak’aba wa wani d’an wasan k’wallo.

  4. Masu kallon k’wallo ba su cika mayar da hankali ga kallon wasannin gida Nijeriya ba, sai dai wasannin k’asashen Turai.

  5. Maza matasa `yan shekaru k’asa da sha takwas zuwa sama su ke kallon k’wallo a gidajen nuna wasanni na kud’i. Kuma ana samun k’abilu mabambanta wad’anda ke zaune a cikin garin Kano.

  6. Ana amfani da Hausar k’wallon k’afa a lokacin kallon wasanni da masu majalisu ko mahad’ar samari ta hira inda ake sharhi kan yadda wasa ta k’are. Sai dai wasu lokuta ana samun gardama mai tsanani.

  7. Gidajen kallon k’wallo na kud’i sana`a ce ta zamani wadda Hausawa suka runguma hannu bibbiyu, domin samun abin masarufi.

  8. An lura da bambancin karin harshe a Hausar masu k’wallon k’afa inda karin harshen Kananci ya yi tasiri sosai a wannan karin harshen Hausa na rukuni, musamman kasancewar Kano muhallin bincike.

  9. Hausar masu k’wallon k’afa ta k’ara fad’ad’a Hausa a bunk’asa ta, tare da haifar da sauye-sauye daban-daban a cikin rumbun kalmominta


5.3 Shawarwari


Yana da matuk’ar muhimmanci a rik’a gudanar da irin wannan bincike, saboda yana k’ara fito da bunk’asar harshen Hausa. Ko ba komai, mai nazari zai fa`idantu da wannan bincike ta hanyoyi da dama. Da farko aikin ya shafi kimiyyar walwalar harshe. Kai mai nazari akwai hanyoyi dama da za ka fad’ad’a bincike a kwatankwacin irin wannan aiki. Ka iya yin bincike a kan wasu masu kallon k’wallon a wani gari domin ka gano irin tsarin karin harshen nasu. Za a iya kwatanta misali na Kano da Sakkwato. Ana iya duba yanayin tsarin sautinsu, ko yanayin k’irar kalmarsu da sauransu.

Ina bayar da shawara ga hukuma ta d’auki matakin inganta harkokin wasan k’wallon k’afa a cikin garin Kano da ma sauran garuruwan Nijeriya. Yana da kyau a rik’a kula da `yan wasa daidai gwargwado. A rik’a sayen ingantattun kayan wasa. A kuma rik’a horar da `yan wasa sosai. Wannan ba ko shakka zai taimaka wajen k’arfafa sha`awar masu buga wasan su kansu, da kuma masu kallon wasan. An fad’i wannan ne kasancewar binciken ya gano cewa mafi yawan masu kallon wasan k’wallon k’afa ba su da sha`awar kallon wasannin da ake bugawa a tsakanin k’ungiyoyin da suke a nan gida Nijeriya.

5.4 Nad’ewa


A wannan babi an yi bayani ne a kan waiwaye ko tak’aitawa da sakamakon bincike da kuma shawarwari kamar yadda aka gani a sama.

www.amsoshi.com

Post a Comment

1 Comments

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.