NA
ABUBAKAR ZAHARADEEN MAINIYO
07031168630
BABI NA UKU: TAKAITACCEN TARIHIN ASIBITIN KOYARWA TA JAMI’AR USMANU ‘DANFODIYO DA ASIBITIN K’WARARRU TA SAKKWATO
3.0 Shimfid’a
A babi na biyu an kawo bayanai a kan tak’aitaccen tarihin fassara da ma’anar fassara da nau’o’in fassara da kuma muhimmancin aikin fassara.Wannan babi na uku zai tattauna a kan tak’aitaccen tarihin Asibitin Koyarwa ta Jami’ar Usmanu ‘DANFODIYO, Sakkwato(Usmanu Danfodiyo University Teaching Hospital UDUTH) da kuma tarihin Asibitin K’wararru Ta Sakkwato (Specialist Hospital Sokoto ) wadda aka fi sani da Asibitin Daji.
3.1 Tk’aitaccen Tarihin Asibitin Koyarwa ta Jami’ar Usmanu ‘DANFODIYO Sakkwato (Usmanu Danfodiyo University Teaching Hospital, UDUTH)
Wannan asibiti hukumar ci gaban asibitoci ta k’asa tare da ma’aikatar lafiya ta k’asa ce suka kafa ta a shekarar (1972) bayan shekara goma sha bakwai da kafata, a shekarar (1989) ne shugaban k’asa Ibrahim Badamasi Babangida ya k’addamar da ita a mazaunin ta dake kan titin Garba Nadama dake Gawon Nama, Sakkwato.
Asibiti tana da manyan sassa da suka had’a da Sashen mulki (Admin) da Sashen kula da majinyata (Patient Department) da Sashen likitoci (Medical Department) da Sashen Tiyata (Surgical Department) da Sashen magani (Pharmaceutical Department) da Sashen Kud’i (Finance Department) da Sashen kula da masu rashin lafiyar Kunne da Hanci da Mak’oshi (ENT Department) da Sashen kula da had’ari na gaggawa (Accident and Emergency Department) da Sashen kula da binciken jini (Haematology Department) da Sashen awon fitsari da sashen awon ciki (Antenatal Care) da Sashen kula da k’wak’walwa (Neurology Department) da Sashen kula da cimaka da abinci ga marasa lafiya (Nutrition Department) da Sashen d’akunan biyan kud’i (Amenity Department) da Sashen ajiye bayanai na marasa lafiya (Medical Record Department) da Sashen wankin k’oda (Dialysis Department) da Sashen kula da masu ciwon daji da Sashen kula da tsaron asibiti (Security Department) da Sashen kula da k’ananan yara (Pediatric Department).
Ta fuskar tsari kuwa asibitin Koyarwa ta Jmi’ar Usmanu ‘DANFODIYO Sakkwato. Kowane Sashe yana da tsarin gini na daban kuma tana da k’ofa biyu ta shigowa da fita da masallaci da wajen ajiye ababen hawa motoci da babura.
3.2 Tak’aitaccen Tarihin Asibitin K’wararru ta Sakkwato (Specialist Hospital, Sokoto)
An kafa asibitin k’wararru ta Sakkwato shekarar 1932, kuma Gwamna Nijeriya na lokacin mulkin Turawa mai suna Lord Luggard ne ya gina wannan asibiti domin kula da lafiyar al’umma a garin Sakkwato.Wannan asibitin tana da manyan sassa da suka had’a da Sashen Gudanar wa na Asibiti (Admin da Sashen duba marasa lafiya (Medical Ward) da Sashen kula da majinyata (Patient out Medical Department) da Sashen d’akunan bincike (Laboratory Department) da Sashen ba da magani (Pharmaceutical Department) da Sashen yara k’anana (Pediatric Department) da kuma Sashen tsaro na asibiti (Security Department).
Ta fuskar tsari asibitin tana da k’ofa biyu manya na shiga da fita sannan da wurin ajiye ababen hawa mooci da babura kuma kowane Sashe da na shi gini na daban.
3.3 Nad’ewa
Wannan babi na uku ya kawo tak’aitaccen tarihin Asibitin Koyarwa ta Jami’ar Usmanu ‘DANFODIYO Sakkwato (Usmanu Danfodiyo University Teaching Hospital UDUTH) da kuma Asibitin K’wararru ta Sakkwato (Specialist Hospital, Sokoto) wadda aka fi sani da Asibitin Daji.Babin ya kawo tarihin da kuma sassan da suka k’unsa, tun lokutan da aka kafa su. Bugu da k’ari babin ya kuma kawo tsare – tsaren kowace daga cikin asibitocin.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.