Ticker

6/recent/ticker-posts

Fassarar Wasu Kalmomin Kiwon Lafiya: Nazari Kan Asibitin Koyarwa Ta Jami’ar Usmanu Danfodiyo (Usmanu Danfodiyo University Teaching Hospital Uduth) Da Asibitin Kwararru Ta Sakkwato, Asibitin Daji (Specialist Hospital Sokoto) (5)

KUNDIN BINCIKEN KAMMALA KARATUN DIGIRI NA FARKO (B.A. HAUSA) A SASHEN KOYAR DA HARSUNAN NIJERIYA, JAMI’AR USMANU ‘DANFODIYO, SAKKWATO

NA

ABUBAKAR ZAHARADEEN MAINIYO

07031168630

BABI NA HUD’U: KALMOMIN KIWON LAFIYA TARE DA FASSARARSU

4.0 Shimfida


A babi na uku an kawo tak’aitaccen tarihin Asibitin Koyarwa ta Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato (Usmanu Danfodiyo University Teaching Hospital, UDUTH) da kuma Asibitin K’wararru ta Sakkwato, wadda ake kira Asibitin Daji (Specialist Hospital Sokoto). Tare da tsare – tsare da sassan kowace daga cikin asibitocin.

Wannan babi na hud’u ya kawo wasu daga cikin kalmomin kiwon lafiya a cikin harshen Ingilishi tare da fassara su a cikin harshen Hausa. Haka kuma babin ya kawo sunayen wasu cututtuka da wasu  sassan asibitocin da ake nazari akan  su da kuma wasu kayan da ake amfani da su a wajen  gudanar da  aikin asibiti.

4.1 Kalmomin Kiwon Lafiya Tare da Fassararsu


        Wasu daga cikin kalmomin kiwon lafiya a cikin harshen Ingilishi tare da fassararsu a cikin harshen Hausa da suka had’a da kalmomin:

4.1.1 Sunayen Cututtuka

IngilishiHausa
AbortionZubar da ciki
AidsSinadarin cutar karya garkuwar jiki
AllergiesBorin jinni
AsthmaCiwon xaukewar numfashi
CancerCiwon daji
EczemaQyasfi
EpilepsyFarfaxiya
EwingKumburin qashi
EchovirusQuraje
EarchesCiwon kunne
FibrosisRuvavviyar majina
HaematobiumCiwon daji na mafitsara
HerniaGuiwa
HIVCuta mai karya garkuwar jiki
Heart attackBugun zuciya
HypertentionHawan jini
Hypertitis BCiwon Anta
 Low blood sugarCiwon qarancin suga cikin jini
InfluenzaMurar yara
Guinea warmCiwon kurkunu
BoilMaruru
Ebola FeverZazzavin ibola
Lassa feverZazzavin lasa
LeprosyCiwon kuturta
MeaslesGaida/qyanda
MaleriaZazzavin cizon sauro
MeningitisCiwon sanqarau
InfertilityRashin haihuwa
Otfi mediaKumburin kunne
Tetanus ToxiodCiwon tsinkau-tsinkau
PolioCutar Shan inna
OstercercomaSanqarar qashi
ObesityCiwon qiba
PneumoniaCiwon haqarqari
Heart transplantDashen zuciya
FractureKariya
PilesFitar baya
Pulmnary tuberculosisCiwon tari
RabiesCizon kare
DialisisWankin qoda
HepatomegalyCiwon kumburin Anta
BilharziaFitsarin jini
Seborrtiotic dermatitisAmosanin kai
Typhoid feverMasassarar shawara
TalipesCiwon duddugen qafa
Peptic ulcerGyambon ciki
EpidemicMaibaushe/annoba
Spinal cord injiuryCiwon qashin baya
Toddlers diarrheaZawon yara
Rectal prolapsed CiwonAtuni
PheumatismCiwon sanyin qashi
StrainTargaxe
Sickle cellsCiwon Amo sanin jini
Patial alopecialSanqo

 

4.1.2 Wasu Daga Cikin Kayan Aikin Asibiti


Dole ne ya kasance a asibiti akwai kayan aiki. Haka su ma wad’annan asibitoci su na da kayan aiki kamar haka;

IngilishiHausa
SphygmomanometerNa’urar awon jini
ThermometerNa’urar awon yanayin zafin jiki
Metor, peak-flowNa’urar awon yanayin iskar da ake shaqa
StethoscopNa’urar sauraren sauti da ake sa wa a kunne
Drip standQarfen sarkafa ruwan jiki
CylinderBututun shaqar iska
Suction machineNa’urar tsotse majina
Weighing machineNa’urar awon nauyin jiki
StrelizerNa’urar gasa kayan aiki
Wheel chairKeken xaukar marasa lafiya
N. Gtuse/Naso-gastrilee tubeKayan wankin miki
Forceps dressingQarafun wankin miki da xinki
Needle holderQarfen da ake riqe allurar xinki
Surgical bladeRezar tiyata
TroleyQarfen xauko kayan aikin diresin
GallipotTasar diresin
OxygenNa’urar da iska ta numfashi
Hospital bedGadon asibiti na marasa lafiya
Operation lampFitilar fixa
Operation bedGadon fixa
Crep bandageBandeji na qyale
Cutting bandageBandeji na qaxa
crutchesSandunan koyon tafiya

 
 4.1.3 Sunayen Sassan Asibitoci na kula da Lafiya
Ingilishi Hausa
Antenatal CareSashen kula da lafiyar masu ciki
Accident and Emergency DepartmentSashen  kula da marasa lafiya masu had’ari na gaggawa
Amenity DepartmentSashen kula da marasa lafiya na biyan kudi
Eye Nose and Throat (ENT)Sashen kula da masu ciwon kunne da hanci da mak’oshi
EncologyKula da masu ciwon daji
Family MedicalKula da lafiyar iyali
Dental DepartmentSashen hak’ora
Dialysis DepartmentSashen wankin k’oda
General Out Patient DepartmentSashen duba marasa lafiyar da ba a kwantar ba
Medical Out Patient DepartmentGanin likita
Medical Records DepartmentSashen da ake aje bayanan marasa lafiya a asibiti
Neuro SurgerySashen fid’ar k’wak’walwa
NutritionSashen kula da ingantaccen abinci ga marasa lafiya
Microbiology DepartmentSashen awon cututtuka
Haemathodlogy DepartmentSashen awon jinni
HisthologySashen bincike a kan abubuwan da aka duba daga sassan jiki
PaediatricsSashen kula da yara
Pharmacy DepartmentSashen magani
TraumaSashen kula da hatsari na gaugawa
TransfussionSashen bayar da jini
Surgical DepartmentSashen fid’a
Surgical Out Patient DepartmentSashen kula da marasa lafiya da aka yi wa aiki  da aka sallama
Ophthalmology DepartmentSashen kula da idanu

4.2 Nadewa


Wannan babi na hud’u mai taken fassarar wasu kalmomin kiwon lafiya daga harshen Ingilishi zuwa harshen Hausa ya kawo fassarar wasu kalmomi da  ake samu a Asibitin Koyarwa ta Jami’ar Usmanu ‘DANFODIYO (Usmanu ‘DANFODIYO Teaching Hospital UDUTH) da Asibitin K’wararru ta Sakkwato (Specialist Hospital Sokoto). Kalmomin sun had’a da sunayen cututtuka da sunayen kayan aikin asibitocin da kuma sunayen sassa daban-daban na asibitocin. Babin ya kawo kimanin kalmomi guda d’ari (100) wad’anda suka danganci kiwon lafiya a wad’annan asibitocin biyu da aka yi nazari a kan su.
www.amsoshi.com 

Post a Comment

0 Comments