Fassarar Wasu Kalmomin Kiwon Lafiya: Nazari Kan Asibitin Koyarwa Ta Jami’ar Usmanu Danfodiyo (Usmanu Danfodiyo University Teaching Hospital Uduth) Da Asibitin Kwararru Ta Sakkwato, Asibitin Daji (Specialist Hospital Sokoto) (6)

     KUNDIN BINCIKEN KAMMALA KARATUN DIGIRI NA FARKO (B.A. HAUSA) A SASHEN KOYAR DA HARSUNAN NIJERIYA, JAMI’AR USMANU ‘DANFODIYO, SAKKWATO

    NA

    ABUBAKAR ZAHARADEEN MAINIYO

    07031168630

    BABI NA BIYAR: TAKAITAWA DA KAMMALAWA

    5.1 Tak’aitawa


    Wannan bincike mai taken: "Fassarar Wasu Kalmomin Kiwon  Lafiya: Asibitin Koyarwa ta Jami'ar Usmanu ‘DANFODIYO(Usmanu ‘DANFODIYO University Teaching Hospital UDUTH) da Asibitin K’wararru ta Sakkwato,(Specailist Hospital Sokoto) Asibitin Daji. Nazari ne wanda ya yi k’ok’arin fassara wasu kalmomin kiwon lafiya kamar sunayen cututtuka da kayan aiki da kuma sassan asibitocin kiwon lafiya biyu da ke cikin garin Sakkwato.

    Aikin ya gudana ne a cikin babi  biyar. Babi na d’aya wanda shi ne  gabatarwa, ya kawo bitar ayyukan da suka gabata da hujjar ci gaba da bincike da manufar bincike da hanyoyin gudanar da bincike da kuma farfajiyar bincike. Babi na biyu ya kawo tak’aitaccen tarihin samuwar fassara da ma’anar fassara da nau’o’inta da kuma muhimmancin fassara. Babi na uku ya yi k’ok’arin kawo tak’aitaccen tarihin Asibitin Koyarwa Ta Jami’ar Usmanu ‘DANFODIYO,( Usmanu ‘DANFODIYO University Teaching Hospital UDUTH) da Asibitin K’wararru Ta Sakkwato (Specialist Hospital Sokoto) . Babi na hud’u kuwa ya yi k’ok’arin fitowa da sunayen cututtuka da kayan aiki da sassan asibitoci da kuma fassararsu. Babi na biyar shi ne tak’aitawa da kuma kammalawa.

     5.2 Kammalawa


            Kasancewar aikin fassara wani muhimmin ‘bangare ne na ilimi a cikin rayuwar al’umma da kuma sanin muhimmancin kiwon lafiya, su ne suka haifar da gudanar da wannan bincike na fassara wasu kalmomin kiwon lafiya da suka had’a da sunayen cututtuka da kayan aikin kiwon lafiya da kuma wasu sassan kiwon lafiya a cikin asibitoci guda biyu da ke garin Sakkwato Asibitin Koyarwa Ta Jami’ar Usmanu ‘DANFODIYO (Usmanu ‘DANFODIYO University Teaching Hospital UDUTH) da Asibitin K’wararru Ta Sakkwato (Specialist Hospital Sokoto).

    La’akari da cewa mafi yawan al’umma da ke ziyatar wad’annan asibitoci  Hausawa ne,  kuma da Hausa suke magana ya sa ma’aikatan asibitocin da  kalmomin asibitin suke k’ok’arin fassara wasu sassan kula da lafiya da  cututtuka da kuma hanyoyin kula da majinyata da harshen Hausa domin sauk’ak’a sadarwa.

    Wannan aiki wani k’arin taimako ne ga irin wannan k’ok’ari ga  wad’annan asibitocin domin sauk’ak’a huld’a da sadarwa a tsakanin ma'aikata da marasa lafiya a asibitocin. Binciken ya fassara kalmomi kimanin  guda 100 da suka shafi sashen kiwon lafiya,da sukahad’a da  sunayen cututtuka da kayan aikin kula lafiya da sassan koyar da kiwon lafiya na asibitocin biyu da ke garin Sakkwato. Duk da haka ba za a ce wannan aiki ya tattara kalmomin kula da kiwon lafiya gaba d’aya ba, na ba asibitoci za a rasa wasu abubuwa  da yawa da bai ta’bo ba.Daga cikin sunayen haka kuma ba za a rasa bambanci ba tsakanin fassarar sunayen cututtuka ana yadda a cikin wannan yanki ake kiransu ko fassarr su  a wasu sassa na Hausawa da ba yankin Sakkwato ba dalilin bambancin karin harshe.
    www.amsoshi.com

    1 comment:

    1. […] Fassarar Wasu Kalmomin Kiwon Lafiya: Nazari Kan Asibitin Koyarwa Ta Jami’ar Usmanu Danfodiyo (Usma… […]

      ReplyDelete

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.