Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriya
NA
NAZIRU MUHAMMAD ALKALI
BABI NA HU’DU
KWATANCI DA BAMBANCI NA KARIN HARSHEN KATSINANCI DA SAKKWATANCI
4.1 Karin Harshen Katsinanci
Katsinanci kari guda ne daga cikin kare-karen hausar Nijeriya mutane fiye da miliyan hud’u da ke tsohon lardin katsina na jahar kaduna ke amfani da karin shi wannan lardi na katsina ya k’unshi yankuna ko kuma k’ananan hukumomi guda shida wad’anda su kuma suka k’unshi gudumomi ashirin da d’aya wad’anda suka had’a da:- Yankin Katsina da Yankin Kankiya da Yankin Dutsen-ma da Yankin Huntuwa da Yankin Malumfashi da Yankin Mani. Kowane yanki yana da gundumomi a k’ark’ashinsa. Ga yadda kowane yanki yake d’auke da gundumomin:-
Yankin Katsina yana da gundumomi guda bakwai, wad’anda suka had’a da; Katsinar kanta da Jibiya da Tsagero da ‘Batagarawa da Rimaye da Kaita. Shi kuma yankin Kankiya yana da Gundumomi guda uku; wato Kankiya da Ingawa da Musawa. A yankin Dutsin-Ma shi ma akwai gundumomin guda uku; wato Dutsen-ma da Safana da Batsari. A Yankin Futuwa akwai gundumomi irin su; Funtuwa da Bakori da Faskari. Yankin Manunfashi shi kuma yana da gudumomi biyu ne kawai; wato Malumfashi da K’ank’ara. A Yankin Mani akwai gundumomi hud’u; Mani da Mashi da Bindawa da Dutsi
Wad’annan su ne yankuna guda shida wad’anda suke amfani da karin harshen Katsinanci, wad’anda a cikin su aka samu k’ananan gundomomi ashirin da d’aya .
Katsinanci Daidaitacciyar Hausa
Cibi Cokali
Kuyahwa K’oshiya
Ciibi Cibiya
Bedi darbejiya
Dandi gantali
Band’aki bayi
Kwad’d’o makulli
Katihwa katifa
Askunniya k’yaure
wundi keso
kalme fartanya
Adaka Akwati
Hwawa fawa
Idan aka lura da wad’annan misalai zamu ga cewa kamanci da ke tsakanin karin harshen Sakkwatanci yafi yawa fiye da bambancinsu, domin kowa sashen arewa na yankin Katsina shi ne yafi yawa kuma yake d’auke kashi hud’u bisa shidda na yankunan mulkin k’asar kuma shine karin harshen da ya yi dai dai da karin harshen Sakkwatanci a sanadiyar kasancewasu a gefen yamma na k’asar Hausa wannan ne yasa gefen na Katsina da yawaita kuma shine gefen da yafi yawa a k’asar Katsina shi kuma gefen kudu na lardin Katsina shi ne ya fi surki da wasu karuruwa da suka bambanta k’warai da Katsinanci wato Kananci da zazzaganci. Domin idan a lura Hausar harshen kudu ya fi kusa da daidai taciyar Hausa, wadda ita kuma tafi kusa da Kananci da kuma Zazzaganci a kan yadda daidaitaciyar hausa take da Katsinanc
4.2 KARIN HARSHEN SAKKWATANCI
Idan ana maganar karin harshen Sakkwatanci za a ga cewa karin harshe ne mai babban kaso wanda ya k’unshi karuruwan harsunan yammacin k’asar Hausa. Idan aka yi la’akari da ra’ayoyin wasu daga cikin masana wad’anda ke ganin cewa, karin harshe ya kasu kashi biyu wato Karin harshen gabas wanda ya k’unshi Kananci, Zazzaganci, Katsinanci da makamantansu, sai kuma karin harshen yamma wanda ya k’unshi Sakkwatanci, Kabanci, Zamfaranci, Arewanci, da sauran kare-karen harshen yamma. Saboda kasancewar garin Sakkwato a matsayin babbar mahad’a ga sauran karuruwan harsunan yamma. Saboda haka sai masana ilimin kimiyyar nazarin harshe suka za’bi karin harshen Sakkwatanci ya zama jagora ga sauran karuruwan harshen Hausa da suke da alak’a da juna ta fuskar furuci da tsarin sauti da yanayin gini jumla da ma’ana. Akan samu dangantaka ta fagen karin harshe da al’adu da auratayya, addini da kuma kasuwanci. Wasu kad’an daga cikin masanan da suka tofa albarkacin bakinsu game da karin harshen Sakkwatanci su ne:
Hamma'ali, (1985), ya nuna cewa "Sakkwatanci Karin harshe ne na Sakkwato. An samo kalmar Sakkwatanci ne daga sunan garin Sakkwato. Sakkwatanci karin harshe ne na mutanen Sakkwato. Sai dai kuma ba ana nufin Jihar Sakkwato gaba d’aya ba. Wasu na ganin tsagwaron Sakkwatawa su ne, wad’anda ke garuruwan da ke kusa da Sakkwato, wato Zamfarawa, Kabawa da Arawa, musamman wad’anda aka kafa ko ciyar da su gaba, bayan jihadi.
Wasu masana na ganin cewa, Sakkwatanci karin harshe ne na mulki. Dalilin da ya sa suke ganin Sakkwatanci a matsayin karin harshe na mulki shi ne, saboda kasancewar Sakkwato cibiyar daular Usmaniyya. Wadda bayan k’are jihadi ita ce ke fad’a a ji a k’asar Hausa, har zuwan Turawan mulkin mallaka. Bisa la’akari da ra’ayin wannan manazarci ana iya cewa karin harshen Sakkwatanci ya samo asali ne daga ginuwar garin Sakkwato a zamanin jihadin Shehu ‘Danfodiyo, inda aka za’bi garin Sakkwato don ya zama babbar fadar mulki ta masu jihadi. Wannan za’ben da aka yi wa Sakkwato sai ya samar da dama ga mutanen garin Sakkwato na mallakar kalmomi da k’wayoyin sautukan sauran kare-karen harshen da suke mak’wabtaka da garin Sakkwaton wajen ginin kalma da samar da jumla zuwa fahimtar ma’ana da take k’unshe cikin zantukan yau da kullum.
4.3 KWATANTA SAKKWATANCI DA KATSINANCI A MAGANGANUN AZANCI
Magana tana d’aya daga cikin muhimman abubuwan dake bambanta mutane daban daban ko da suna da harshe iri d’aya na magana musamman idan sunkasance ba tare suke zaune ba wato suna da harshe ire d’aya amma zaman nesa ya bam-banta su kamar yadda za muga kamanci da bambanci da ke tsakanin mutane Sakkwato wato Sakkwatawa, da mutane Katsina wato Katsinawa duk da cewar sun kasance a gefen yamma.
4.4 Jerin Jimlolin Da Suka Bambanta Karin Harshen Sakkwatanci Da Katsinanci
Ga Misalai wad’anda zasu k’ara nuna wannan bambanci da Katsinanci ta fuskar magana.
SAKKWATANCI KATSINANCI
Ba Zai je ba An yi mamu fura
Ba Musa na ya sayee shiba An kama wani ya yi sata
Yaushe Ladi za ta tahi Uwaggida ta mari Amarya
Yaushe Zaka taho Ana kid’a
Tashi shai ka da gudu k’ofar gida
Rubuta wanga Malam ya zo makaranta
Tahi makaranta Ana yima yara ta tsuniya
Kurum ka tahi Wannan wafe na na
Wanga Yamareta Wad’annan suke makara
A cikin wad’annnan misali, da muka gani munga cewar akwai bam-banci da ake samu tsakanin Katsinawa da Sakkwatawa ta fuskar magana ta wajen ru’banya bak’ek’e a Sakkwatanci
Ga Misali:
Hulla Hulluna
Kud’d’I Kud’ad’e
Kassuwa Kassuwanni
Mallam Mallamai
Haka kuma akwai inda Sakkwatanci yake le’bantar da maganganunsa.
Misali
SAKKWATANCI KATSINANCI
Dawaaci Daaci
Swa’bi Sa’bi
Swaataa Sata
Rwaahi Raahi
Twaari Taari
Twaanka Tanka
Zwaari Zaari
Zwaahi Zaahi
Wad’annan misalai su suka nuna cewa akwai bambanci dangane da ru’banya bak’ak’e da le’bantar da wasu a sakkwatanci wanda hakan ba shi a katsinanci.
Wad’anan misalai sune zamu ga akwai bambanci dangae da ru’banya wasulla da bak’ak’e da Hausawan Sakkwato ke yi katsinawa ba su yi sannan da la’bentar da kalmomin da sakkwatawa ke yi katsinawa ba suyi kamar yadda muka gani.
4.5 Kamanci Ta Fuskar Kalmomi Mabanbanta Amma Kuma Masu Ma’ana ‘Daya
Ga Misalai na kalmomi mabambanta amma kuma masu ma’ana d’aya.
SAKKWATANCI KATSINANCI
Tussuwa Zuddwa
Ceniya Can wuri
Toka (sabulu) Sabili
Awo E
Datti Daud’a
Shiyya Unguwa
Ayimuna Ayi Mamu
Wanga Wannan
Kudaku Dankali
Boli Juji
‘Datu Kwad’o
Bakuru k’uli-k’uli
Taggo Riga
4.6 Manunin Shud’ad’d’en Ambato A Katsinanci
Previous Refernce mak’era Katsinanci A daidaitaciyar Hausa ana amfani da-n ko-r don nuna PRM Alai Misali riga-r gida-n. Yin amfani da-r ko-n ya dangane, irin kalmar suna da ke d’aukar PRM d’in. Idan kalmar yana da jinsin namiji kamar kalmar gida to kalmar nata d’auki n-wato gidan. Idan kuma kalmar suna tana da jinsi tamatsari na daidaitaciyar Hausa na yin amfani da r-ko-n haka nan yake a Sakkwatanci amma ba haka yake a Katsinanci ba. Katsinanci yana amfani ne da-I kawai a matsayin PRM Don haka ba bambanci a suftar PRM wadda bambancin jinsin kalmar sune ke haifarwa.
Ga misalai daga Katsinanci kamar yadda aka Kwatanta ta da
SAKKWATANCI KATSINANCI
Bolar Bolal
Butar Butai
Ciyawa Ciyawai
Fartanyar Fartanyai
Fitila Futilai
Gwazar Gwazai
Hwatar Hwaitai
Hwanteka Hwantekai
Kamar yadda muka gani wannan hanya ta amfani da-I a matsayin PRM Katsinawa ne kawai ke aiwatar da shi wajen ma’anarsu ta ya yau da kullum yin magana da wad’annan kalmomi a bisa yadda suke k’ara nuna cewa lalle mutum bakatsine na asali domin sune kawai ke amfani da wad’annan kalmomi a cikin maganarsu.
4.7 Sunayen Mata
SAKKWATANCI KATSINANCI
Hassatu/Hassi Hassatu
Farida Farida
Safiya Safiya
A’I A’I
Nafisa Nafisa
Atika Atika
Maryam Maryam
Zainab Zainab
Ummu Salma Ummu Salma
Nazbatu Nazbatu
Hadiza Hadiza
Habiba Habiba
Ruk’ayya Ruk’ayya
Murja Murja
Ruhwa’atu Rufa’atu
Balkisu Balkisu
Nabila Nabila
Halima Halima
Suwaiba Suwaiba
Hamida Hindatu
Sa’ida Sa’ida
Raliya Raliya
Amina Amina
Salma Salamatu
Mariya Mariya
Zuwaira Zuwaira
Maimuna Maimuna
Aliya Aliya
Haulatu Haulatu
Huwaila Huwaila
4.8 Lak’abin Sunayen Mata
SAKKWATANCI KATSINANCI
Ige Kande
Inno Binta
Maijidda Maijidda
Kubura Kubura
Amira Amira
Ummi Ummi
‘Yarmantu ‘Yarmantu
Barmini Barmini
4.9 Sunayen Ranakku
Jimmai (Jummai:- Ranar Jumu’a)
Lami (Laminde:- Ranar Alhamis)
Talatu (Ranar Talar)
Ladi (Ranar Lahadi)
Asabe (Ranar Assabar)
Larai (Laraba/Tabawa/Balaraba:- Ranar Larba)
4.10 Sunayen Maza
SAKKWATANCI KATSINANCI
Lawal Lawali
Bashar Bishir
Ibro Iro Hali Haliru
Muhammad Muhammad
Musa Kalla
Isa Isa
Usman/Shehu Usman/Shehu
Rabi’u Rabe
Mu’azu Mu’azu
Rayyanu Rayya
Abbas Abashe
Abdulrazak Razak’u
Abdulrrahman Abdulrrahman Abdul-k’adir Abdul-k’adir
Salihu/Sale Salele
Dauda Dauda
Ayuba Ayuba
Yakubu Yakubu
Haruna Haro
Shamsu Shamsu
Mika’ilu Miko
4.11 Sunayen Maza Wad’an Da Da Ake Samu Dangane Da Ranakku
SAKKWATANCI KATSINANCI
‘Dan jumma ‘Dan jumma
‘Dan lami ‘Dan lami
Balarabe Balarabe
‘Dan tala ‘Dan tala
‘Dan tani ‘Dan tani
‘Dan ladi ‘Dan ladi
‘Dan Asabe ‘Dan Asabe
4.12 Lak’abin Sunayen Maza
SAKKWATANCI KATSINANCI
Saddi Sadik’
Na Allah Na Allah
Gadanga Gadanga
Sodangi Sodangi
Shekarau Shekarau
Dangana Dangana
4.13 Lak’abin Sunayen Sarautu
SAKKWATANCI KATSINANCI
Sarki Sarki
Waziri Waziri
Galadima Galadima
Wambai Wanbai
Katuka Katuka
Jarma Jarma
Yarima Yarima
‘Dan Jika ‘Dan Jika
‘Dan Maliki ‘Dan Maliki
Turaki Turaki
Garkuwa Garkuwa
Maina Maina
Mayana Mayana
Hakimi Hakimi
‘Dan Madami ‘Dan Madami
Sarkin Shanu Sarkin Shanu
Sarkin Gabas Sarkin Gabas
Sarkin Noma Sarkin Noma
Sarkin Kudu Sarkin Kudu
Matawalle Matawalle
Tafida Tafida
4.14 Sunayen Sana’o’i
SAKKWATANCI KATSINANCI
Noma Noma
Kira Kira
Gina Gina
Sak’a Sak’a
Hwarauta Hwarauta
Dukanci Dukanci
Wazanci Wazanci
Tauri Tauri
Kokuwa Kokowa
Koli Koli
Jima Jima
Rini Rini
Kiyo Kiyo
Kitso Kitso
Tuwo-Tuwo Tuwo-Tuwo
Su Su
Nad’ewa
A wannan babi anyi tsokaci akan bambanci tsakanin Sakkwatanci da Katsinanci A tak’aice anga manyan bambance bambance da ke tsakanin Sakkwatnci da Katsinanci wad’anda suka had’a. Ru’banya bak’ak’e a wasu jimlolin na Sakkwatanci, Katsinanci baya ru’be wad’annan bak’ak’en. Sakkwatanci ya kan le’banta wasu bak’ak’e musamman a ga’bar farko ta wasu jimloli, Katsinanci bashi le’bantar da bak’ak’en a irin wad’annan kalmomi. Amfani da-1 akwai a matsayin PRM a Katsinanci, Sakkwatanci yana amfani ne da-r ko-n kamar yadda abin yake a daidaitaciyar Hausa.
https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/
1 Comments
[…] Bambanci Da Kamanci Tsakanin Karin Harshen Sakkwatanci Da Katsinanci (5) […]
ReplyDeleteENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.