Ticker

6/recent/ticker-posts

Bambanci Da Kamanci Tsakanin Karin Harshen Sakkwatanci Da Katsinanci (6)

Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriyawww.amsoshi.com

NA

NAZIRU MUHAMMAD ALKALI

BABI NA BIYAR

TAK’AITAWA


A babin farko an yi bayani kan bitar ayyukkan da suka gabata da kuma dalilin yin bincike da kuma hanyoyin gudanar da bincike tare da kuma muhimmancin bincike, haka kuma an nuna tsarin gabatar da aiki. Babban muhimancin wanannan binciken shi ne na kulawa wasu muhimman kalmomi da zantukan Karin harshen Sakkwatanci dan gudun salwantar su, saboda barazanar sauyawar zamani da ake samu kan harsunan duniya da harshen Ingilishi yake yi musu.

Babin na biyu kuma an bayyana ma'anar jumlar Hausa a bisa ra’ayoyin masana, tare da bayyana ire-iren jumlar Hausa da ake da su tare kuma da ba da wasu misalai daga cikin kowace jumla. Misali, a sassauk’ar jumla an nuna cewa, jumla ce da ta k’unshi yankin suna, da kuma yankin abin da aka fad’i game da suna. Haka kuma ita ce jumlar da ke bisa tsarin S.A.K. Jumlar tambaya kuma ita ce, jumlar da ake gina wa don yin tambaya. Jumlar umarni jumla ce da ta k’unshi kalma d’aya rak a matsayin cikakkiyar jumla. Jumlar korewa jumla ce da ke d’auke da wasu kalmomi na musamman da harshen Hausa ya amince da su, domin su zama sharad’i waje nuna irin korewar da aka sanu a cikin sassauk’ar jumla. Sannan su ne a matsayin dokokin da aka shimfid’a wajen samar da ita kafin ta zama jumlar korewa.

Cikin babi na uku a nan ne inda aka bayyana karin harshen Sakkwatanci a bisa ra’ayoyin masana da kuma ire-iren jumlar karin harshen Sakkwatanci, tare kuma da kawo wasu misalai daga cikin jumlolin. A sassauk’ar jumlar Hausa ta yi daidai da ta karin harshen Sakkwatanci, saboda haka ne aka yi bayanin cewa ita ma jumlar ta k’umshi yanki biyu wato yankin suna da kuma yankin abin da aka fad’i a game da suna. Haka kuma ita ma jumlar karin harshen Sakkwatanci tana bisa tsarin S.A.K, daidai da ta sassauk’ar jumlar daidaitacciyar Hausa. Jumlar tambaya ta karin harshen Sakkwatanci ita ma kamar jumlar tambaya take ta daidaitacciyar Hausa, jumla ce da ake yi domin tambaya. Jumlar umurni ta karin harshen Sakkwatanci, ita ma kamar jumlar umurni take ta daidaitacciyar Hausa, ana gina ta ne a bisa tsarin ba da umarni. Jumlar korewa ta karin harshen Sakkwatanci, ita ma kamar jumlar korewa take ta daidaitacciyar Hausa, ana gina ta ne a kan korewa sai dai ta bambanta da ta daidaitacciyar Hausa kad’an. Babi na hud’u shi ne aka tattauna kan wasu mahimman kalmomi da karin harshen Sakkwatanci ya mallaka. Don haka wannan babi ya yi bayanin wad’annan mahimman kalmomi da aka tattauna a zauren Sakkwatanci, an yi tsokaci dangane da abin da ya shafi ma’anar mafayyaciya dangane da ra’ayoyin masana da kuma wasu ‘yan misalai. Haka kuma duk a cikin wannan babin ne aka yi bayanin lokatak’ da ire-irensa had’i da kuma wasu ‘yan misalai. Bayan wannan kuma duk a cikin wannan babi ne aka yi bayanin kalmomin dirka da kuma yadda suke zuwa a cikin karin harshen Sakkwatanci, tare da wasu ‘yan misalai domin fayyace abin yadda yake. Haka kuma, duk a cikin wannan babin na hud’u an yi tsakure game da Sakkwatattun kalmomi dangane da masu bambancin furuci, amma ma’ana d’aya, da kuma masu ma’ana d’aya amma sauti bamban. Saboda haka, wannan babi shi ne babin da ya k’unshi wasu mahimman batutuwa da wannan nazari ya adana su, wato mafayyaciya lokatak’, da kuma kalmomin dirka, yadda suke zuwa a Sakkwatanci da kuma yadda suke zuwa a cikin daidaitacciyar Hausa, da kuma wasu daga cikin Sakkwatattun kalmomi.

 

 

 

 

 

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

Post a Comment

0 Comments