Ticker

6/recent/ticker-posts

Al’adun Mutuwar Maguzawan Kambari Na Birnin Yawuri (2)

KUNDIN BINCIKEN KAMMALA KARATUN DIGIRI NA FARKO (B.A HAUSA) A SASHEN HARSUNAN NIJERIYA, JAMI’AR USMANU DANFODIYO, SAKKWATO

www.amsoshi.com

NA

MUSA LUKMAN ALƘASIM

BABI NA BIYU

2.0 Bitar Ayyukan Da Suka Gabata


Dangane da bitar ayyukan da suka gabata, masana a kan tarihi, da kuma al’ada sun yi rubuce-rubuce a kan ƙabilar Kambari, na wurare daban-daban. Wasu masana kuwa sun mai da hankali ne a kan harshen ƙabilar Kambari.

Bayan haka, masana sun yi maƙalu daban-daban. Haka wasu sun buga littattafai, dangane da ƙabilar Kambari. Bayan wannan kuma ɗalibai daga wurare daban-daban a jami’o’i da kwalejin ilimi, duk sun yi bincike a kan al’adun Kambari. Wasu daga cikin rubutun da aka gudanar a kansu, sun haɗa:

2.1 Kundaye


Malamai da ɗalibai, da yawa sun yi rubutun kundaye. Waɗannan kundayen sun ke’banta ne a kan al’adun ƙabilar Kambari da harshensu. Ga wasu daga cikinsu:

Muhammad, B. (2011) a cikin kundindiirinsa na farko mai taken: Tasirin Al’adun Auren Hausawa a kan Ƙabilar Kambari.” Wannan kundin yana da alaƙa da wannan nazari, da yake duk a kan Kambarin Yawuri ne aka yi su. Sai dai sun bambanta kasancewar an yi aikin ne a kan al’adun aure ne, kamar ɗaukar amarya da neman aure, da hanyoyin samun aure da sauransu. Ni kuma zan dubi al’adun mutuwar su na gargajiya.

Abdullahi, Z. (2002) a cikin kundin digirinsa na farko, Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato, mai taken: “Kambarin Kwantagora: Tarihinsu da Al’adunsu.” Wannan kundin na da alaƙa da wannan aiki, da yake duk a kan Kambarin Yawuri aka yi su. Sai dai sun bambanta kasancewar an yi aikin ne a kan tahirin Kambarin Kwantagora da al’adun aurensu da haihuwa kamar samun ciki har zuwa ranar suna, da kuma al’adun aure da sauransu. Amma ni kuma zan dubi al’adun mutuwarsu na gargajiya.

Shanga, A. (2006) a kundin digirinsa na farko Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato mai taken Bukin Auren Kambari Auna. Wannan kundin na da alaƙa da wannan nazarin da yake duk a kan Kambarin Yawuri aka yi su. Sai dai sun sha bamban kasancewar an yi  nazarin ne a kan al’adun auren Kambarin garin Auna ne. a cikin aikin nasa ya yi bayani a kan neman aure, yadda ake kai amarya da ɗaurin aure da sauransu. Amma ni zan dubi al’adun mutuwarsu a gargajiyance.

Gado, A. (2007) a kundin digirinsa na farko a Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato, mai taken Tasirin Tsafe-tsafen Kambari da Gungawa na Magani a Kan Hausawa Mazauna Yawuri. Wannan kundi na da alaƙa da wannan nazari domin duk a kan Kambari aka yi aikin. sai dai sun bambanta don an yi nazarin ne a kan tsafe-tsafensu. A cikin wannan aiki, an kawo yanayin ƙasar Yawuri, da tarihin Yawuri da kayayyakin tsafin Kambari da  kuma ire-iren tsafin Kambari na magani. Amma ni zan kalli al’adun mutuwar Kambari ne a gargajiyance.

Auna, H. M. (1992) a cikin kundin digirinsa na farko jami’ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato mai taken Shigowar Harshen Hausa a cikin Harshen Kambari. Wannan kundin na da alaƙa da wannan nazari da yake duk a kan Kambarin Yawuri ne aka yi su. Sai dai sun bambanta kasancewar an yi aikin ne a kan yadda harshen Hausa ya shiga a cikin Harshen Kambari. A cikin kundin ya kawo rabe-raben Kambari dangane da harshensu, da tarihinsu. Amma ni zan dubi al’adun mutuwar Kambari ne na gargajiya.

Mu’azu, M. (1985) a cikin kundin digirinsa na farko jami’ar Usmanu Dnfodiyo Sakkwato mai taken Tasirin Al’adun Hausawa a kan ƙabilun Yawuri. Wannan kundi na da alaƙa da wannan nazarin da yake an ta’ba ƙabilar Kambari. Sai dai sun bambanta kasancewar akan al’adun aure ne da haihuwa aka yi magana kansa. A cikin wannan kundin, an yi bayani a kan ƙabilun Yawuri kamar Dukawa, Shangawa, Gungawa da Kambari. An fito da yadda al’adun Hausawa suka yi tasiri a kansu. Ni kuma zan dubi al’adun mutuwar Maguzawan Kambari a gargajiyance.

Shehu, M. (2005) a kundin digiri na farko a Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sakwkato mai taken: Tasirin Al’adun Auren Hausawa a Kan Gungawa. Wannan nazarin na da alaƙa da wannan aiki da yake duk akan Ƙabilar Yawuri ne aka yi su. Sai dai sun bambanta kasancewar an yi aikin ne a kan al’adun aure. a cikin wannan kundi an yi bayanai irin neman aure, da baiko da sadaki da ɗaurin aure, duk sun yi tasiri a kan auren Gungawa. Amma ni kuma zan dubi al’adun mutuwar Maguzawan Kambarin da ke cikin wannan yanki na Birnin Yawuri ne.

2.2 Bugaggun Littattafai


Masana tarihi da yawa, sun yi rubuce-rubuce a kan Kambari. Wasu daga cikinsu sun mai da hanakali ne akan tarihin Kambari, wasu a kan harshensu. Ga waɗansu bugaggun littattafai:

Mahdi, A. (2013) The Rise and Fall of Yawuri Kingdom and Maginga. Wannan littafin yana da alaƙa da wannan nazari, da yake duk a kan tarihin Kambarin Yawuri ne aka yi. Sai dai sun bambanta kasancewar an yi aikin littafin ne a kan tarihin Yawuri, da yanayin ƙasar Yawuri da tarihin Kambari. Bayan haka kuma cikin littafin an kawo shigowar Musulunci a ƙasar da yadda aka gudanar da mulki a ƙasar da  sauransu. Amma ni zan dubi al’adun mutuwar Kambarin ne a gargajiyance.

Sahabi, A. (2000) The Brief Histroy of Yawuri Kingdom. Wannan littafin yana da alaƙa da wannan nazari da yake duk a kan tarihin Kambarin Yawuri ne aka yi. Sai dai sun bambanta kasancewar an yi wannan littafin ne a kan tarihin Yawuri da yanayin ƙasar Yawuri da abin da ƙabilar Kambari suke bautawa, da shigowar addinin Musulunci ƙasar da yanayin tsarin gudanar da mulki daular da dai sauransu. Ni kuma zan dubi al’adun mutuwar Kambari ne a gargajiyance.

Yasin A. da wasu (2014) A Short History of Yawuri Kingdom. Wannan littafi na daga cikin jerin littattafan da aka buga a kan tarihin Kambarin Yawuri. Sai dai sun sha bamban da wannan aiki domin an yi littafin ne a kan tarihin Yawuri a ciki an kawo tarihin Kambari, da yanayin ƙasar Yawuri da muhallin da ƙabilar Kambari suke zaune, a cikin ƙasar. Bayan haka littafin ya kawo yadda aka gudanar da mulki a ƙasar, da shigowar Musulunci a ƙasar, da sauransu. Amma ni zan dubi al’adun mutuwar Maguzawan Kambarin ne a gargajiyance.

2.3 Maƙalu


Abubakar Y, Journal of Islam in Nigeria ‘Bol 1 No 1, 2015. “Islam in Yawuri Emirate to the End of 20
th Century.” Department of History, Usmanu Danfodiyo Uni’bersity, Sokoto. Wannan maƙalan na da alaƙa da wannan nazari da yake duk a kan Yawuri aka yi su. Sai dai sun bambanta kasancewar an yi aikin ne a kan adddinin Musulunci a ƙasar Yawuri da tsarin dokar malammai na Musulunci da yadda ƙungiyar Jama’atul Nasril Islam ta yaɗa addini a ƙasar da sauransu. Amma ni kuma zan dubi al’adun mutuwar Kambari ne a gargajiyance kafin su kar’bi addinin Musulunci.

2.4 Hujjar Ci Gaba da Bincike


        Idan aka yi la’akari da ƙumshiyar bitar da aka yi na ayyukan da suka gabata, za a fahimci cewa an yi nazarce-nazarce masu dama a kan ƙabilar Kambari. Daga cikin waɗannan nazarce-nazarceakwai waɗanda suka shafi al’adunsu na aure akwai tsafe-tsafensu. Haka kuma akwai waɗanda suka dubi tarihinsu da na wurin zamasu da kuma irin bambance-bambancen harshe da ake samu a tsakaninsu. Wasu kuma sun dubi irin tasirin al’adu da ake samu a tsakaninsu da Hausawa. To sai dai wani muhimmin abu da za a yi la’akari da shi shi ne, babu wani nazari ko bincike da aka gudanar da ya dubi al’adun Kambari na gargajiya wanda suka shafi mutuwa.

Ganin yadda mutuwa take da tasiri a rayuwa da kuma irin tanadin da ake yi mata a kowace al’umma, muka ga ya dace a yi wannan nazari domin a cike babban gi’bin da aka bari.

2.5 Naɗewa

Wannan babi an yi ƙoƙarin kawo abubuwa da suka haɗa da bitar ayyukan da suka gabata, irin kundaye. Haka an kawo bugaggun littattafai masu alaƙa ta kusa da wannan aiki tare da hujjar ci gaba da bincike.

Post a Comment

0 Comments