Amsoshi

 

NA


MUSA LUKMAN ALK’ASIM


 


KUNDIN BINCIKEN KAMMALA KARATUN DIGIRI NA FARKO (B.A HAUSA) A SASHEN HARSUNAN NIJERIYA, JAMI’AR USMANU ‘DANFODIYO, SAKKWATO


 BABI NA UKU


3.0 Shimfid’a


A wannan babi na uku an kawo tarihin Birnin Yawuri a tak’aice. Bayan nan kuma an akwo tarihin k’abilar Kambari da muhallin da suke zaune. Haka kuma an fito da rabe-raben k’abilar Kambari dangane da addini. A cikin wannan babin an ba da ma’anar mutuwa daga bakin masana da kuma alamomin mutuwa. Bayan haka an yi k’ok’arin bayanin abin da kalmar Maguzawa ta k’unsa.

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

3.1 Tak’aitaccen Tarihin Birnin Yawuri


Birnin Yawuri, wadda aka fi sani da tushen Yawuri, masana daban-daban a kan ilimin tarihi sun yi bayanai dangane da kafurwar garin. Haris (1930:42) ya bayyana cewa, garin ya kafu ne kimanin shekaru dubu d’aya da suka wuce. Kuma ya k’ara da cewa sarakuna kimanin d’ari d’aya da ashirin da d’aya sun yi mulki a k’asar.

Mahdi (2013) ya bayyana cewa garin Birnin Yawuri ya kafa tarihinsa ne tun a wajajen k’arni na 13 zuwa 14, haka Sahabi na da ra’ayi irin na Mahdi da Haris. Bayan wannan kuma bayanai sun nuna cewa daga bakin sarki na d’aya har zuwa na talatin da hud’u, duk sun yi sarauta a garin Birnin Yawuri. Garin ya rasa babban masarautansa ne a wajajen shekaru (1858 – 1878) daga bisani ya koma a garin Yawuri.

Dangane da dalilin barin sarkin wannan zamani zuwa Yawuri, wani ra’ayin ya nuna cewa Umamru Nagwamutse d’an sarkin Musulmi Ahmadu Atiku, a lokacin da yake yak’an wuraren da ba su da Musulunci, bayan ya yi yunk’urin zuwa garin Birnin Yawuri sarkin wannan zamani Suleman d’an Ado ya yi shakkan kar da ya riske shi, duk da yake akwai Musulunci a wurin amma bai samu gindin zama ba. Sai wannan sarki ya yi hijira daga Birnin Yawuri zuwa Ikum. Daga bisani sai masarautan ta dawo a Yawuri.

Ummaru Nagwamutse ya fito daga Gwamutse a shekaran (1851). Amma kuma ya shiga k’asar Birnin Yawuri ne a shekarar (1864) bayan sarkin ya yi hijira (Adamu, 2000: 209-296). Birnin Yawuri ya kar’bi sunansa ne  saboda shi ne tushen Yawuri. Don haka ake kiransa da garin birnin Yawuri garin na d’auke da ganuwa, don haka akawai k’ok’fofi guda shida kamar haka:

 1. K’ofar Adama

 2. K’ofar Katsinawa

 3. K’ofar Muta

 4. K’ofar Dur’bi

 5. K’ofar ‘yan Kara

 6. K’ofar Hayin Dawaki


Adamu (2013: 43) ya nuna cewa kafin Amina na Zazzau ta ziyarci Birnin Yawuri, garin na d’auke da ganuwa. Domin Amina ta zo a tsakiyar k’arni na 16. Kafin ta zo mutanen wurin sun gina ganuwarsu.

Bayan haka kuma kasancewar k’abilar Kambari, su ne suka fara zama a wurin, wanan k’abilar na bautar magiro ne. Domin tabbatar da cewa su ne suka fara zama a wurin, akwai sunayen unguwanni a cikin garin Birnin Yawuri. Wad’annan suna a kambarce suke. Haka su ne unguwannin farko a cikin garin. Mafi yawanci babu su a yanzu. Ga sunayen wad’ansu daga ciki:

 1. Unguwar Cicinawa

 2. Unguwar Dankal

 3. Unguwar litaba da sauransu


Haka kuma akwai rafuna, su ma mafi yawancinsu a cikin harshen Kambarci ne. rafin gwantaci da rafin Madiso da rafin Kwankwami da sauransu. Wad’annan k’abilar da suka fara zama a wuri mafi akasarinsu ba Musulmai ba ne don haka suna aiwatar da tsafe-tsafensu don biyar buk’atunsu na yau da kullun. Sukan je rok’on ruwa a duk lokacin da tari ya addabe su. Bayan haka kuma suna kai gumba a matsayin sadaka don samun biyar buk’ata kamar ta rashin haihuwa da sauransu. Ga mahallin kamar haka:

 1. Kan daka a unguwar Hajin Daulaki

 2. Madutsi a unguwar Sharifai

 3. Dallafe a unguwar Dankita


Dangane da shigowar Musulunci a Birnin Yawuri, masana tarihi sun bayyana ya shigo ne a wajajen shekaru (1620-1663). Ga sunayen sarakunan da suka yi mulki a cikin garin kafin ta bar cikin ganuwar Birnin Yawuri:


SunaShekara
1.Tafiraulu1411 – 1433
2.Kamuwa1433 – 1450
3.Bunyagu1450 – 1480
4.Sakazu1480 - 1508
5.Yawuri1508 – 1531
6.Kisagiri1531 – 1560
7.Jarabana1560 – 1572
8.Gimba1572 – 1600
9.Lafiya1600 – 1601
10.Kasafaugi1601 – 1620
11.Jarabana  (II)1620 – 1663
12.Gimba1663
13.Kasagurbi1663 – 1665
14.Kana1665 – 1660
15.Janrina1660 – 1670
16.Dutsi1670 – 1674
17.Lafiya1674 - 1675
18.Kada1675 – 1689
19.Gandi1689 – 1703
20.D’an Ibrahim1703 - 1714
21.Muhammadu1714 - 1723
22.Lafiya (II)1723 - 1745
23.Yanazu1745
24.Umar Gandi1745 - 1748
25.Suleman Jarabana1748 - 1770
26.Alu Lafiya1770 - 1775
27.Ahmadu Jarabana Jatau1775 - 1790
28.Sha’aibu Madara1790 - 1790
29.Mustafa Gazari1790 - 1793
30.Muhammadu Albashir D’an A’i1793 - 1838
31.Ibrahim Dogon Sarki1838 - 1844
32.Jibrin Gajeren Sarki1844 – 1853
33.Abubakar Jat1853 - 1858
34.Suleman D’an Ado1858 – 1878

https://www.amsoshi.com/2017/11/05/tanade-tanaden-tsafin-maguzawa-aladunsu-na-aure-da-haihuwa/

Bayan haka da tafiya ta yi tafiya, Birnin Yawuri aka ba ta uban k’asa. Ana kiran fadar da sarkin gabas. A yanzu haka ana aiwatar da mulki a wurin. Ga sunayen saurakunan da suka gabata har zuwa yanzu:SarkiShekara
1.Sarkin gabas D’an Tsoho Agizo1914
2.Sarkin gabas Isah Uban Masallaci1923
3.Sarkin gabas Salihu1925
4.Sarkin gabas Yakubu Mai Saje1927
5.Sarkin gabas Usman Ango1950
6.Sarkin gabas Usman Malam Gange1955
7.Sarkin gabas Suleman1955
8.Sarkin gabas Attahiru1956
9.Sarkin gabas Abubakar Karazube1977
10.Sarkin gabas Jibrin Na Wando1986
11.Sarkin gabas Mannir Suleman2006

 

Wannan shi ne tak’aitaccen tarihin Birnin Yawuri, domin tarihin garin kandama ne.

3.2 Tarihin Kambarin Birnin Yawuri


Adamu (2013) ya bayyana cewa k’abilar Kambari sun fito ne daga Makka. Suna d’aya daga cikin k’abilar da annabin rahama ya kora wad’anda ke bauta wa gunki. Haris (1930) ya bayyana da cewa babu ainihin lokacin da za a tabbatar da zuwansu. Amma ana hasashen cewa tsakanin lokacin da aka ba annabi Muhammadu (S.A.W.) annabta (611AD) da kuma lokacin da ya koma ga mahaliccinsa (632 AD). a wannan lokacin ne suka yi hijira suka samu kansu inda suke a yau.

Wannan k’abila na Kambari ana samunsu wurare da yawa a cikin jahar Neja da kuma kudancin Kabi, a cikin gunduman Ngaski. Kambari k’abila ce da ke da harshensu na Kambarci. Kuma mutane ne bak’ak’e amma ana samun farare a cikinsu ta launin jiki. Haka kuma, ba su rufe jikinsu da tufafi baki d’aya. Amma bayan tasirin Hausawa da kirista ya yi naso a gare su, da kuma tasirin addinin Musulunci har wad’anda ba su kar’bi wannan addini ba, suna amfani da tufafi a maimakon walki ko kuma ganye.

Matan Kambari ba su d’aukan kaya bisa kai sai dai a bisa kafad’a. Haka kuma suna goyon ‘ya’yansu ne a k’ugu ba saman baya ba kamar Bahaushe da kuma wasu k’abilu. Bakambare bai cika zama cikin gari ba. Rayuwarsu ta ke’banta ne a jeji, kuma ba su yin kasuwanci. Maguzawan Kambari sun dogara ne a harkan noma da kiwo, a dalilin haka ne ake bin su da kirari kamar haka:

Kambari dawa ‘yan zaki,

Ga gidanku ga na maciji,

Kun sha rura maciji ya sha.

Dangane da abin bauta kuwa, suna bauta wa gunki ne da farko, bayan yin hijiransu daga Makka, sai daga bisani suka koma bauta wa magiro. Wannan magiro iska ne domin ba su ganin shi ido da ido. Kuma sun yi masa ginin d’aki ne na laka. K’abilar Kambari sun bayyana cewa sukan gane gittawarsa a wani lokacin da suke yin bauta. Kuma sun yi imani da shi domin idan fari na rashin ruwa ya addabe su Kambari kan je wurin d’akin don rok’onsa da ya ba su ruwan sama.

3.3 Muhallin K’abilar Kambari


Dangane da muhallin k’abilar Kambari kuwa, ana samun Kambari a wurare da yawa musamman a cikin jahar Neja, a k’asar Kwantagora. Wad’annan k’auyuka sun had’a da Ibeto, Auna da Nasko. Haka kuma ana samun Kambari a Tungan Mangoro da Sulka, da Kura, da kuma Wando da dai sauransu.

Bayan haka kuma a cikin jihar Kabi a gunduman Ngaski ana samun k’abilar Kambari sun yi kaka gida. Kamar a k’auyukan Ngaski akwai Agwara da Lofa, da tungan goguwa da sauransu. Bayan wannan kuma a k’auyukan Birnin Yawuri ana samun k’abilar Kambari. Wad’annan muhallin da ake samun su sun had’a da Kwana, da Kambuwa da Kambu da K’ara Gashi da Tungan Koruwa, da Laka da dai sauransu.

Bayan haka idan aka dubi taswiran jahar Kabi, a cikin littafin Adamu (2000) za a ga cewa k’abilar Kambari na Ngaski da na Birnin Yawuri duk suna layi na 9042 da 110N daga kudu. Haka kuma suna layin 40 da 50 daga gabas da layin Ikwaito.

 

3.4 Rabe-raben Kambari


Dangane da rabe-rab’ben Kambari, za a iya kallon su ta fuskoki guda uku. Da farko rabuwa ta gefen muhalli. Haka kuma akwai rabe-raben k’abilar Kambari dangane da karin harshensu kamar Kambari Akimba da Kambari Abadi, suna da bambancin karin harshe a tsakaninsu. Haka kuma Kambari Awunci da Kambari Agadi suna da bambancin karin harshe a tsakaninsu da dai sauransu. Duk wannan bambancin bai hana su jin maganar junansu ba. Sai dai kawai bambancin kalmomi.

Bayan wannan kuma, sai rabe-raben Kambari ta gefen addini. Wannan rabe-raben za a iya kallon su gida uku kamar haka:

 1. Maguzawan Kambari

 2. Kambari Musulmai • Kambari Kirista


Maguzawan Kmabari, wannan kaso na d’aya daga cikin k’abilar Kambari. K’abila ce da ke bautar Magiro (iska). Haka kuma ba su rufe jikinsu da tufa baki d’aya. Bayan haka giya bai zama haramtacce a wurinsu ba. haka suna cin mushe duk al’adunsu na mutuwa da na aure da haihuwa ya bambanta da Kambari Musulmai da kuma Kambari Kirista.

Kambari Musulmi, dangane da shigowar Musulunci a k’asar Birnin Yawuri. Masana irin Adamu (2013) da Sahabi (2000) duk sun bayyana cewa, Musulunci ya shigo k’asar ne a shekaran (1620-1663). Don haka bayan Musulunci ya samu gindin zama a k’asar Yawuri, sannu a hankali k’abilar Kambari Maguzawa suka kama shiga addinin Musulunci.

Wannan kaso na Kambari Musulmai sun bambanta da Maguzawan Kambari. Da farko suna da bambanci ta gefen tufa, domin sanya tufafinsu tamkar na Musulmai ne. Haka kuma giya ta haramta gare su. Bayan haka kuma, tsarin neman aure, da sanya suna bayan an haihu duk al’adun da suke aiwatarwa sun koma irin na tsarin addinin Musulunci. Bayan haka, a duk lokacin da wani daga cikinsu ya mutu suna yi masa sallah da duk abin da Musulunci ya tanada.

Kambari Kirista, wannan kaso ne daga cikin rabe-raben k’abilar Kambari dangane da addini. Su wad’annan Kambari su ne suka bar addinin gargajiya kuma ba su shiga addinin Musulunci ba. bayan haka yanayin shigarsu ya koma irin shigar Kirista. Haka kuma, idan wani daga cikinsu ya mutu suna sanya shi ne a cikin akwati akasin yadda suke yi a gargajiyance.

Haka kuma al’adun aurensu duk ya koma irin na Kiristanci. Domin kafin shiga wannan ‘bangare hanyoyin mallakan mace da d’aurin aure da zanen suna duk sun canza. Sun koma irin koyarwan addinin Kirista.

3.5 Ma’anar Maguzawa


Dangane da ma’anar maguzawa, masana sun bayar da ra’ayoyinsu dangane da su wane ne Maguzawa. Abdullahi I.S.S. (2008) ya bayar da ma’anar Maguzawa da cewa:

Maguzawa: “Hausawan asali wad’anda ba mululmi ba, wad’anda addininsu na gargajiya ke jagorancin rayuwarsu.”

Don haka idan aka duba\i ma’anar da ta gabata dangane da Maguzawan Hausawa. Ana iya cewa Maguwazan Kambari su ne, Kambarin asali wad’anda ke bin al’adun gargajiya, musamman wad’anda suka sa’ba wa addinin musulunci.

3.6 Ma’anar Mutuwa


Bahaushe ya aro kalmar mutuwa ne daga harshen Larabci wato (almautu). Sai daga baya ya Hausance kalmar ta koma mutuwa. Amma akwai sunayen da yake yi mata, wad’anda ba su da alak’a da Larabci. Wad’annan sunayen kuwa sun had’a da rasuwa da fad’uwa da wucewa da kau da tuni da shek’awa da k’aura da kuma gangarawa da sauransu.

Wad’annan sunayen su ne Bahaushe kan kira mutuwa da su kafin ya kar’bi addinin Musulunci. Bayana ya kar’bi addinin Musulunci sai lafuzzansa suka sauya ba kamar da ba. bayan haka sai ya canza mata suna. Wad’annan sunayen sun had’a da mutuwa da hariyar gabas da kwanta dama da kuma hutawa da sauransu. Ma’anar mutuwa daga bakin masana:

Abdullahi, I.S.S. (2008) ya bayyana ma’anar mutuwa da cewa:

“Rasa rayuwa ko barin aiki ga abu mai rai ko maras rai mutum ne ko dabba ko tsiro ko wata halitta ko kuma wani abu mai amfani da yadda ake ganin alamun ba zai ta’ba dawowa ba, yadda yake a da ba kafin k’addarar rasa rayuwar ta auka masa.”

K’amusun Hausa na Bayero (2006: 354) ya ayyana ma’anar mutuwa da cewa:

“Rasuwa ko k’arshen ran mutum ko dabba, ko kuma duk wani abu mai rai.”

Ta la’akari da k’unshiayr wad’annan ma’anoni a tak’aice ana iya cewa “mutuwa na nufin, k’arewar rayuwar dun wani abu mai rai, dabba ko mutum ko kuma tsiro bayan rayuar wannan abu.”

 

3.7 Alamomin Mutuwa


Dangane da alamomin mutuwa, akwai alamomin da ake gani a duk lokacin da ake tunanin ya kusa mutuwa ko rai ya kusa d’aukewa. Wasu daga cikin alamomin sun had’a da; a dubi idonsa in aka ga bai motsa ba wato kintSawa. Bayan haka ana duba idadunsa idan aka ga fari ya rinjayi bak’in k’wayan idonsa.

Wata alama kuma ita ce sauyawar jiki. Ana aza hannu a jikinsa idan aka ji zafi ko kuma jikin ya yi sanyi to lallai ana tunanin mutuwa ya tabbata gare shi. bayana wanann kuma sai yin shak’uwa wato za a ga yana yin shak’uwa bi da bi, har ya kai ya kama yi kad’an-kad’an. Bayan haka kuma ana duban ramin mak’ogoro, ko kuma zucciya idan aka ga bai halba ba, ba shakka mutuwa ta tabbata a gare shi.

Bayan haka ana duban yatsan k’afarsa babba, idan aka ga ba ta motsa ba wanann ba shakka alamar mutuwa ta bayyana gare shi. A gargajiyance idan duk wad’annan alamomin sun tabbata za a buga wani abu ko a yayyafa mai ruwa idan kuma aka kira sunan shi aka ce Tanko, ko Musa bai amsa ba, tolallai ya mutu.

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

3.8 Nad’ewa


Wannan babi na uku babi ne da aka yi k’ok’arin kawo abubuwa kamar tarihin birnin Yawuri a tak’aice da kuma tarihin k’abilar Kambari tare da muhallinsu. Bayan haka kuma, an kawo ma’anar mutuwa daga bakin masana da ma’anar Maguzawa. Haka an kawo alamomin mutuwa. Wanann babi na iya zama gudummuwa a wannan bincike.