Ticker

6/recent/ticker-posts

Al’adun Mutuwar Maguzawan Kambari Na Birnin Yawuri

KUNDIN BINCIKEN KAMMALA KARATUN DIGIRI NA FARKO (B.A HAUSA) A SASHEN HARSUNAN NIJERIYA, JAMI’AR USMANU ‘DANFODIYO, SAKKWATO

www.amsoshi.com

NA

MUSA LUKMAN ALƘASIM

BABI NA ƊAYA

1.0 Gabatarwa

Al’ummar Kambari al’umma ce da ake samu a wasu sassa na jahar Kabi da kuma jahar Neja. Kambari ba su da wata al’umma da suka kusance su ko suke mu’amala da su kamar Hausawa. Wannan kusanci ya bayar da damar hulɗa a tsakanin ƙabilu guda biyu ta fuskoki da dama. A halin da ake ciki, kusan a ce babu fannin rayuwar da Hausawa da Kambari ba su haɗa ba. haƙiƙa wannan kusanci shi ya ba da damar tunanin aiwatar da wannan aiki.

Manazarta sukan kalli alamomi da yawa ta fuskoki guda biyu. Wato rayuwarsu ta gargajiya wadda suka gada kaka da kakanni, da kuma rayuwar da suka sami kansu bayan da suka sami tasirin wata rayuwar ta daban kamar ta addini da zamani. A wannan nazari an yi ƙoƙarin nazartar wata rayuwa ta Kambari ne ta gargajiya. Tunanin yin haka ya fito ne bisa la’akari da cewa, rayuwar da aka fara yi, ita takan bayar da haske a gane irin sauyin da aka samu daga lokaci zuwa lokaci. Haka kuma an zaɓi mutuwa ne domin ganin cewa tana daga cikin matakan rayuwar al’umma, wanda ke jan hankalin mutane wajen tabbatar da al’ada da kiyaye su.

An yi tunanin amfani da kalmar Maguzawa ne saboda la’akari da sunan da ya fi tasiri da ake kiran Hausawa da ba Musulmai ba kuma suna bin addininsu, da rayuwarsu ta gargajiya. Ganin akwai irin wannan rayuwa a al’umar Kambari shi ya sa nazarin ya laƙaba musu irin wannan suna na Hausawa.

A taƙaice wannan aiki ya ƙunshi babuka guda biyar. Babi na farko shi ne gabatarwa. Babi na biyu aka kawo bitar ayyukan da suka gabata. A babi na uku aka bayar da tarihin Kambari da haske a kan muhallinsu. A babi na huɗu aka yi nazarin al’adunsu na mutuwa. Babi na biyar kuma ya zama kammalawa.

1.1 Manufar Bincike

Wannan binciken na da manufofi da suka haɗa da; da farko a gano yadda Kambari ke gudanar da al’adunsu na mutuwa a gargajiyance wanda ya ƙunshi yadda Maguzawan Kambari ke jinya da kuma kimtsa gawa. Bayan haka kuma, a gano yadda suke raba gadon mamaci bayan ya mutu da kuma muhallin da suke binne gawa da yadda suke aurar da matan mamaci. Ahaka kuma binciken ya gano yadda Maguzawan Kambari ke zaman makoki, da kuma yadda suke aiwatar da bukukuwan mutuwa.

Bayan wannan kuma, manufar wannan aiki shi ne, a binciko waɗannan al’adun ta yadda za a iya kwatanta su da rayuwar mutanen da suke hulɗa da su musamman na zamantakewa kamar Hausawa.

Haka kuma, wata manufar a nan ita ce, a yi nazarin al’adunsu na mutuwa don ya ba da haske da zama harsashen duban yadda rayuwarsu ta Musulunci da ta Kiristanci take.

Bayan wannan, nazarin zai ba da haske ga ɗaliban da ke da niyyar yin kwatankwacin irinsa a wasu al’ummu. Haka kuma, a samar da waɗannan al’adu a rubucce musamman ganin akasarin Kambari sun fara barin gargajiya zuwa musulunci da kuma addinin Kiristanci. Rashin yin haka zai sa al’adun su ɓace.

1.2 Muhallin Bincike

An keɓe wannan nazari ne a wannan muhalli na Birnin Yawuri, saboda kasancewarsa muhallin Kambari. Duk da kasancewar akwai tasirin Hausawa a wannan wurin har yanzu ana samun Maguzawan Kambari da ke gudanar da al’adunsu a gargajiyance a wannan muhalli.n. keɓe wannan wuri a matsayin muhallin bincike zai taimaka wajen tattara bayanan da ake nema.

Haka kuma an keɓe wannan nazari ga al’adun mutuwa kawai. Wato binciken ba zai taɓo sauran sassa na matakan rayuwa ba kamar aure da haihuwa.

1.3 Dabarun Bincike

An bi hanyoyi daban-daban don gudanar da wannan binciken. Ba shakka a duk lokacin da mutum ya ci karo da irin wanann bnciken, to lallai dole ne sai ya zama matambayi. Kamar dai yadda Hausawa ke cewa: “Matambayi baya ɓata.” Danane da haka, an bi hanyoyi daban-daban domin samun bayanai iri-iri don kammala wannan bincike.

Bayan haka, an ziyarci ɗakin karatu lokaci zuwa lokaci don samun bayayani game da ayyukan da aka gudanar a kan Kambari don samun bayanai ko abubuwa, waɗanda za su zama abin dogaro ko taimakawa a wannan aiki. An sami irin na malamai da kuma ɗalibai ‘yan uwana. Masu alaƙa da wannan bincike na al’adun Maguzawan Kambari ko kuma mai alaƙa da wannan bincike da za su taimaka.

Haka kuma, an yi hira da waɗannan mutane Kambari domin jin ta bakinsu dangane da abubuwan da suka sani game da Maguzawan Kambari. Haka daga cikin dabarun da suka taimaka wajen samun nasarar wannan bincike akwai ziyartar muhallin da waɗannan mutane suke gudanar da ire-iren waɗannan al’adu da suka shafi mutuwa.

1.4 Kammalawa

Wannan babin, sharar fage ne na aikin wanda ya ƙunshi gabatarwa. Haka kuma, da manufar bincike, da muhallin bincike. Bayan haka, an yi bayanin dabarun da aka yi amfani da su don gudanar da wannan bincike.

Post a Comment

1 Comments

Post your comment or ask a question.