Ticker

6/recent/ticker-posts

Al’adun Mutuwar Maguzawan Kambari Na Birnin Yawuri (3)

KUNDIN BINCIKEN KAMMALA KARATUN DIGIRI NA FARKO (B.A HAUSA) A SASHEN HARSUNAN NIJERIYA, JAMI’AR USMANU ‘DANFODIYO, SAKKWATO

www.amsoshi.com

NA

MUSA LUKMAN ALƘASIM

BABI NA UKU

3.0 Shimfiɗa

A wannan babi na uku an kawo tarihin Birnin Yawuri a taƙaice. Bayan nan kuma an akwo tarihin ƙabilar Kambari da muhallin da suke zaune. Haka kuma an fito da rabe-raben ƙabilar Kambari dangane da addini. A cikin wannan babin an ba da ma’anar mutuwa daga bakin masana da kuma alamomin mutuwa. Bayan haka an yi ƙoƙarin bayanin abin da kalmar Maguzawa ta ƙunsa.

3.1 Taƙaitaccen Tarihin Birnin Yawuri


Birnin Yawuri, wadda aka fi sani da tushen Yawuri, masana daban-daban a kan ilimin tarihi sun yi bayanai dangane da kafurwar garin. Haris (1930:42) ya bayyana cewa, garin ya kafu ne kimanin shekaru dubu ɗaya da suka wuce. Kuma ya ƙara da cewa sarakuna kimanin ɗari ɗaya da ashirin da ɗaya sun yi mulki a ƙasar.

Mahdi (2013) ya bayyana cewa garin Birnin Yawuri ya kafa tarihinsa ne tun a wajajen ƙarni na 13 zuwa 14, haka Sahabi na da ra’ayi irin na Mahdi da Haris. Bayan wannan kuma bayanai sun nuna cewa daga bakin sarki na ɗaya har zuwa na talatin da huɗu, duk sun yi sarauta a garin Birnin Yawuri. Garin ya rasa babban masarautansa ne a wajajen shekaru (1858 – 1878) daga bisani ya koma a garin Yawuri.

Dangane da dalilin barin sarkin wannan zamani zuwa Yawuri, wani ra’ayin ya nuna cewa Umamru Nagwamutse ɗan sarkin Musulmi Ahmadu Atiku, a lokacin da yake yaƙan wuraren da ba su da Musulunci, bayan ya yi yunƙurin zuwa garin Birnin Yawuri sarkin wannan zamani Suleman ɗan Ado ya yi shakkan kar da ya riske shi, duk da yake akwai Musulunci a wurin amma bai samu gindin zama ba. Sai wannan sarki ya yi hijira daga Birnin Yawuri zuwa Ikum. Daga bisani sai masarautan ta dawo a Yawuri.

Ummaru Nagwamutse ya fito daga Gwamutse a shekaran (1851). Amma kuma ya shiga ƙasar Birnin Yawuri ne a shekarar (1864) bayan sarkin ya yi hijira (Adamu, 2000: 209-296). Birnin Yawuri ya karɓi sunansa ne  saboda shi ne tushen Yawuri. Don haka ake kiransa da garin birnin Yawuri garin na ɗauke da ganuwa, don haka akawai ƙoƙfofi guda shida kamar haka:

1.     Ƙofar Adama

2.     Ƙofar Katsinawa

3.     Ƙofar Muta

4.     Ƙofar Durɓi

5.     Ƙofar ‘yan Kara

6.     Ƙofar Hayin Dawaki


Adamu (2013: 43) ya nuna cewa kafin Amina na Zazzau ta ziyarci Birnin Yawuri, garin na ɗauke da ganuwa. Domin Amina ta zo a tsakiyar ƙarni na 16. Kafin ta zo mutanen wurin sun gina ganuwarsu.

Bayan haka kuma kasancewar ƙabilar Kambari, su ne suka fara zama a wurin, wanan ƙabilar na bautar magiro ne. Domin tabbatar da cewa su ne suka fara zama a wurin, akwai sunayen unguwanni a cikin garin Birnin Yawuri. Waɗannan suna a kambarce suke. Haka su ne unguwannin farko a cikin garin. Mafi yawanci babu su a yanzu. Ga sunayen waɗansu daga ciki:

 

1.     Unguwar Cicinawa

 

2.     Unguwar Dankal

 

3.     Unguwar litaba da sauransu

 


Haka kuma akwai rafuna, su ma mafi yawancinsu a cikin harshen Kambarci ne. rafin gwantaci da rafin Madiso da rafin Kwankwami da sauransu. Waɗannan ƙabilar da suka fara zama a wuri mafi akasarinsu ba Musulmai ba ne don haka suna aiwatar da tsafe-tsafensu don biyar buƙatunsu na yau da kullun. Sukan je roƙon ruwa a duk lokacin da tari ya addabe su. Bayan haka kuma suna kai gumba a matsayin sadaka don samun biyar buƙata kamar ta rashin haihuwa da sauransu. Ga mahallin kamar haka:

 

1.     Kan daka a unguwar Hajin Daulaki

 

2.     Madutsi a unguwar Sharifai

 

3.     Dallafe a unguwar Dankita

 


Dangane da shigowar Musulunci a Birnin Yawuri, masana tarihi sun bayyana ya shigo ne a wajajen shekaru (1620-1663). Ga sunayen sarakunan da suka yi mulki a cikin garin kafin ta bar cikin ganuwar Birnin Yawuri:



Suna

Shekara

1.

Tafiraulu

1411 – 1433

2.

Kamuwa

1433 – 1450

3.

Bunyagu

1450 – 1480

4.

Sakazu

1480 - 1508

5.

Yawuri

1508 – 1531

6.

Kisagiri

1531 – 1560

7.

Jarabana

1560 – 1572

8.

Gimba

1572 – 1600

9.

Lafiya

1600 – 1601

10.

Kasafaugi

1601 – 1620

11.

Jarabana  (II)

1620 – 1663

12.

Gimba

1663

13.

Kasagurbi

1663 – 1665

14.

Kana

1665 – 1660

15.

Janrina

1660 – 1670

16.

Dutsi

1670 – 1674

17.

Lafiya

1674 - 1675

18.

Kada

1675 – 1689

19.

Gandi

1689 – 1703

20.

Ɗan Ibrahim

1703 - 1714

21.

Muhammadu

1714 - 1723

22.

Lafiya (II)

1723 - 1745

23.

Yanazu

1745

24.

Umar Gandi

1745 - 1748

25.

Suleman Jarabana

1748 - 1770

26.

Alu Lafiya

1770 - 1775

27.

Ahmadu Jarabana Jatau

1775 - 1790

28.

Sha’aibu Madara

1790 - 1790

29.

Mustafa Gazari

1790 - 1793

30.

Muhammadu Albashir Ɗan A’i

1793 - 1838

31.

Ibrahim Dogon Sarki

1838 - 1844

32.

Jibrin Gajeren Sarki

1844 – 1853

33.

Abubakar Jat

1853 - 1858

34.

Suleman Ɗan Ado

1858 – 1878


https://www.amsoshi.com/2017/11/05/tanade-tanaden-tsafin-maguzawa-aladunsu-na-aure-da-haihuwa/

Bayan haka da tafiya ta yi tafiya, Birnin Yawuri aka ba ta uban ƙasa. Ana kiran fadar da sarkin gabas. A yanzu haka ana aiwatar da mulki a wurin. Ga sunayen saurakunan da suka gabata har zuwa yanzu:



Sarki

Shekara

1.

Sarkin gabas Ɗan Tsoho Agizo

1914

2.

Sarkin gabas Isah Uban Masallaci

1923

3.

Sarkin gabas Salihu

1925

4.

Sarkin gabas Yakubu Mai Saje

1927

5.

Sarkin gabas Usman Ango

1950

6.

Sarkin gabas Usman Malam Gange

1955

7.

Sarkin gabas Suleman

1955

8.

Sarkin gabas Attahiru

1956

9.

Sarkin gabas Abubakar Karazube

1977

10.

Sarkin gabas Jibrin Na Wando

1986

11.

Sarkin gabas Mannir Suleman

2006


 

Wannan shi ne taƙaitaccen tarihin Birnin Yawuri, domin tarihin garin kandama ne.

3.2 Tarihin Kambarin Birnin Yawuri


Adamu (2013) ya bayyana cewa ƙabilar Kambari sun fito ne daga Makka. Suna ɗaya daga cikin ƙabilar da annabin rahama ya kora waɗanda ke bauta wa gunki. Haris (1930) ya bayyana da cewa babu ainihin lokacin da za a tabbatar da zuwansu. Amma ana hasashen cewa tsakanin lokacin da aka ba annabi Muhammadu (S.A.W.) annabta (611AD) da kuma lokacin da ya koma ga mahaliccinsa (632 AD). a wannan lokacin ne suka yi hijira suka samu kansu inda suke a yau.

Wannan ƙabila na Kambari ana samunsu wurare da yawa a cikin jahar Neja da kuma kudancin Kabi, a cikin gunduman Ngaski. Kambari ƙabila ce da ke da harshensu na Kambarci. Kuma mutane ne baƙaƙe amma ana samun farare a cikinsu ta launin jiki. Haka kuma, ba su rufe jikinsu da tufafi baki ɗaya. Amma bayan tasirin Hausawa da kirista ya yi naso a gare su, da kuma tasirin addinin Musulunci har waɗanda ba su karɓi wannan addini ba, suna amfani da tufafi a maimakon walki ko kuma ganye.

Matan Kambari ba su ɗaukan kaya bisa kai sai dai a bisa kafaɗa. Haka kuma suna goyon ‘ya’yansu ne a ƙugu ba saman baya ba kamar Bahaushe da kuma wasu ƙabilu. Bakambare bai cika zama cikin gari ba. Rayuwarsu ta keɓanta ne a jeji, kuma ba su yin kasuwanci. Maguzawan Kambari sun dogara ne a harkan noma da kiwo, a dalilin haka ne ake bin su da kirari kamar haka:

Kambari dawa ‘yan zaki,

Ga gidanku ga na maciji,

Kun sha rura maciji ya sha.

Dangane da abin bauta kuwa, suna bauta wa gunki ne da farko, bayan yin hijiransu daga Makka, sai daga bisani suka koma bauta wa magiro. Wannan magiro iska ne domin ba su ganin shi ido da ido. Kuma sun yi masa ginin ɗaki ne na laka. Ƙabilar Kambari sun bayyana cewa sukan gane gittawarsa a wani lokacin da suke yin bauta. Kuma sun yi imani da shi domin idan fari na rashin ruwa ya addabe su Kambari kan je wurin ɗakin don roƙonsa da ya ba su ruwan sama.

3.3 Muhallin Ƙabilar Kambari


Dangane da muhallin ƙabilar Kambari kuwa, ana samun Kambari a wurare da yawa musamman a cikin jahar Neja, a ƙasar Kwantagora. Waɗannan ƙauyuka sun haɗa da Ibeto, Auna da Nasko. Haka kuma ana samun Kambari a Tungan Mangoro da Sulka, da Kura, da kuma Wando da dai sauransu.

Bayan haka kuma a cikin jihar Kabi a gunduman Ngaski ana samun ƙabilar Kambari sun yi kaka gida. Kamar a ƙauyukan Ngaski akwai Agwara da Lofa, da tungan goguwa da sauransu. Bayan wannan kuma a ƙauyukan Birnin Yawuri ana samun ƙabilar Kambari. Waɗannan muhallin da ake samun su sun haɗa da Kwana, da Kambuwa da Kambu da Ƙara Gashi da Tungan Koruwa, da Laka da dai sauransu.

Bayan haka idan aka dubi taswiran jahar Kabi, a cikin littafin Adamu (2000) za a ga cewa ƙabilar Kambari na Ngaski da na Birnin Yawuri duk suna layi na 9
042 da 110N daga kudu. Haka kuma suna layin 4da 50 daga gabas da layin Ikwaito.

3.4 Rabe-raben Kambari


Dangane da rabe-rabɓen Kambari, za a iya kallon su ta fuskoki guda uku. Da farko rabuwa ta gefen muhalli. Haka kuma akwai rabe-raben ƙabilar Kambari dangane da karin harshensu kamar Kambari Akimba da Kambari Abadi, suna da bambancin karin harshe a tsakaninsu. Haka kuma Kambari Awunci da Kambari Agadi suna da bambancin karin harshe a tsakaninsu da dai sauransu. Duk wannan bambancin bai hana su jin maganar junansu ba. Sai dai kawai bambancin kalmomi.

Bayan wannan kuma, sai rabe-raben Kambari ta gefen addini. Wannan rabe-raben za a iya kallon su gida uku kamar haka:

 

1.     Maguzawan Kambari

 

2.     Kambari Musulmai

 

  • Kambari Kirista


Maguzawan Kmabari, wannan kaso na ɗaya daga cikin ƙabilar Kambari. Ƙabila ce da ke bautar Magiro (iska). Haka kuma ba su rufe jikinsu da tufa baki ɗaya. Bayan haka giya bai zama haramtacce a wurinsu ba. haka suna cin mushe duk al’adunsu na mutuwa da na aure da haihuwa ya bambanta da Kambari Musulmai da kuma Kambari Kirista.

Kambari Musulmi, dangane da shigowar Musulunci a ƙasar Birnin Yawuri. Masana irin Adamu (2013) da Sahabi (2000) duk sun bayyana cewa, Musulunci ya shigo ƙasar ne a shekaran (1620-1663). Don haka bayan Musulunci ya samu gindin zama a ƙasar Yawuri, sannu a hankali ƙabilar Kambari Maguzawa suka kama shiga addinin Musulunci.

Wannan kaso na Kambari Musulmai sun bambanta da Maguzawan Kambari. Da farko suna da bambanci ta gefen tufa, domin sanya tufafinsu tamkar na Musulmai ne. Haka kuma giya ta haramta gare su. Bayan haka kuma, tsarin neman aure, da sanya suna bayan an haihu duk al’adun da suke aiwatarwa sun koma irin na tsarin addinin Musulunci. Bayan haka, a duk lokacin da wani daga cikinsu ya mutu suna yi masa sallah da duk abin da Musulunci ya tanada.

Kambari Kirista, wannan kaso ne daga cikin rabe-raben ƙabilar Kambari dangane da addini. Su waɗannan Kambari su ne suka bar addinin gargajiya kuma ba su shiga addinin Musulunci ba. bayan haka yanayin shigarsu ya koma irin shigar Kirista. Haka kuma, idan wani daga cikinsu ya mutu suna sanya shi ne a cikin akwati akasin yadda suke yi a gargajiyance.

Haka kuma al’adun aurensu duk ya koma irin na Kiristanci. Domin kafin shiga wannan ɓangare hanyoyin mallakan mace da ɗaurin aure da zanen suna duk sun canza. Sun koma irin koyarwan addinin Kirista.

3.5 Ma’anar Maguzawa


Dangane da ma’anar maguzawa, masana sun bayar da ra’ayoyinsu dangane da su wane ne Maguzawa. Abdullahi I.S.S. (2008) ya bayar da ma’anar Maguzawa da cewa:

Maguzawa: “Hausawan asali waɗanda ba mululmi ba, waɗanda addininsu na gargajiya ke jagorancin rayuwarsu.”

Don haka idan aka duba\i ma’anar da ta gabata dangane da Maguzawan Hausawa. Ana iya cewa Maguwazan Kambari su ne, Kambarin asali waɗanda ke bin al’adun gargajiya, musamman waɗanda suka saɓa wa addinin musulunci.

3.6 Ma’anar Mutuwa


Bahaushe ya aro kalmar mutuwa ne daga harshen Larabci wato (almautu). Sai daga baya ya Hausance kalmar ta koma mutuwa. Amma akwai sunayen da yake yi mata, waɗanda ba su da alaƙa da Larabci. Waɗannan sunayen kuwa sun haɗa da rasuwa da faɗuwa da wucewa da kau da tuni da sheƙawa da ƙaura da kuma gangarawa da sauransu.

Waɗannan sunayen su ne Bahaushe kan kira mutuwa da su kafin ya karɓi addinin Musulunci. Bayana ya karɓi addinin Musulunci sai lafuzzansa suka sauya ba kamar da ba. bayan haka sai ya canza mata suna. Waɗannan sunayen sun haɗa da mutuwa da hariyar gabas da kwanta dama da kuma hutawa da sauransu. Ma’anar mutuwa daga bakin masana:

Abdullahi, I.S.S. (2008) ya bayyana ma’anar mutuwa da cewa:

“Rasa rayuwa ko barin aiki ga abu mai rai ko maras rai mutum ne ko dabba ko tsiro ko wata halitta ko kuma wani abu mai amfani da yadda ake ganin alamun ba zai taɓa dawowa ba, yadda yake a da ba kafin
ƙaddarar rasa rayuwar ta auka masa.”

Ƙamusun Hausa na Bayero (2006: 354) ya ayyana ma’anar mutuwa da cewa:

“Rasuwa ko
ƙarshen ran mutum ko dabba, ko kuma duk wani abu mai rai.”

Ta la’akari da ƙunshiayr waɗannan ma’anoni a taƙaice ana iya cewa “mutuwa na nufin, ƙarewar rayuwar dun wani abu mai rai, dabba ko mutum ko kuma tsiro bayan rayuwar wannan abu.”

3.7 Alamomin Mutuwa


Dangane da alamomin mutuwa, akwai alamomin da ake gani a duk lokacin da ake tunanin ya kusa mutuwa ko rai ya kusa ɗaukewa. Wasu daga cikin alamomin sun haɗa da; a dubi idonsa in aka ga bai motsa ba wato kintSawa. Bayan haka ana duba idadunsa idan aka ga fari ya rinjayi baƙin ƙwayan idonsa.

Wata alama kuma ita ce sauyawar jiki. Ana aza hannu a jikinsa idan aka ji zafi ko kuma jikin ya yi sanyi to lallai ana tunanin mutuwa ya tabbata gare shi. bayana wanann kuma sai yin shaƙuwa wato za a ga yana yin shaƙuwa bi da bi, har ya kai ya kama yi kaɗan-kaɗan. Bayan haka kuma ana duban ramin maƙogoro, ko kuma zucciya idan aka ga bai halba ba, ba shakka mutuwa ta tabbata a gare shi.

Bayan haka ana duban yatsan ƙafarsa babba, idan aka ga ba ta motsa ba wanann ba shakka alamar mutuwa ta bayyana gare shi. A gargajiyance idan duk waɗannan alamomin sun tabbata za a buga wani abu ko a yayyafa mai ruwa idan kuma aka kira sunan shi aka ce Tanko, ko Musa bai amsa ba, tolallai ya mutu.

3.8 Naɗewa

Wannan babi na uku babi ne da aka yi ƙoƙarin kawo abubuwa kamar tarihin birnin Yawuri a taƙaice da kuma tarihin ƙabilar Kambari tare da muhallinsu. Bayan haka kuma, an kawo ma’anar mutuwa daga bakin masana da ma’anar Maguzawa. Haka an kawo alamomin mutuwa. Wanann babi na iya zama gudummuwa a wannan bincike.

Post a Comment

2 Comments

  1. Umar Alassan Kamaru11 April 2018 at 10:33

    Assalamu alaikum gaisuwa tare da fatan alhairi zuwa gare ku tabas bude wannan shafi da kukayi domin bunkasa karshen Hausa tabas abin farincikine don haka nema ina matukar sun Hausa da kuma iya rubuta ta.

    ReplyDelete
  2. Abu-Ubaida Sani11 April 2018 at 15:26

    MWa'alaikumussulam. Muna farin cikin kadancewa da kai. Mun gode.

    ReplyDelete

Post your comment or ask a question.