Amsoshi

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

NA


MUSA LUKMAN ALK’ASIM


 


KUNDIN BINCIKEN KAMMALA KARATUN DIGIRI NA FARKO (B.A HAUSA) A SASHEN HARSUNAN NIJERIYA, JAMI’AR USMANU ‘DANFODIYO, SAKKWATO


 BABI NA HUD’U


AL’ADUN MUTUWAR MAGUZAWAN KAMBARI


4.0 Al’adun Mutuwar Maguzawan Kambari


A wannan babi za a fito da abubuwa wad’anda suka shafi yadda Maguzawan Kambari suke aiwatar da al’adunsu na mutuwa. A cikin babin an kawo abubuwa da suka shafi jiyar mara lafiya da hanyoyin da ake bi don sanar da mutane ‘yanuwansa. Haka kuma, an yi k’ok’arin kawo yadda Maguzawan Kambari suke kimtsa gawa kafin kai shi rami.

Bayan haka kuma, an fito da muhallin da suke binne gawa tare da yanayin ramin binne gawa da zaman makoki da yadda suke raba gadon mamaci. Haka da bukukuwan da suke yi bayan cika shekara uku da mutuwa da dai duk wani abu wanda ya shafi mutuwarsu.

4.1 Jinya


Da farko idan aka ga rashin lafiya ya yi tsanani, Maguzawan Kambari sukan aje mara lafiya a cikin d’akinsa. Bayan haka, za a samu tsohuwa wadda za ta kula da shi. wannan tsohuwar ita ce za ta kama ba shi magani bi da bi.

Bayan haka kuma, Bamagujen Bakambare ba ya kar’ban magani a cikin gida, in akwai boka a gidan. Ba za a yi amfani da maganinsa ba, sai dai a je wajen wani a nemo. Idan aka yi dace da maganin ciwon da yake fama da shi, idan idan kuwa ba a yi dace ba to shi kenan sai a canza wuri daban don kar’ban magani. Bayan haka, in an yi dace da wurin da aka canza to shi ke nan.

4.2 Fad’ar Mutuwa


Maguzawan Kambari idan aka mutu a cikin gida, a farko sukan kore yara maza da mata k’anana zuwa gidan mak’wafta. Da ganin haka nan za a fahimci an yi mutuwa a gidan. Bayan haka ana samun wasu daga cikin matasan gida masu shekar 20-30, su za su tafi gidan mutane makwafta na kusa da na nesa domin bayyana abin da ya faru da d’an’uwansu. Idan mace ce ta mutu ana sanya tsofaffi mata su kula da ita. Idan kuwa namiji ne ya mutu ana barin maza wurin gawan kafin mutane su taru.

4.3 Kimtsa Gawa


Da farko idan mace ce ta mutu, mata tsofaffi suke mata wanka da ruwa mai kyau. Amma sai an d’umama wannan ruwa ya yi zafi. Bayan haka kuma ana wanke gawa amma ana wankewa ne ba shafa ruwan ake yi ba a jikinsa. Bayan haka idan an gama wanka, ana samun wani zani na gado da ake ce wa arkyalla. Maza kan yi amfani da wannan abu wajen yin walki, mata kan d’aura shi, a jiki. Bayan haka, sai a sanya mai, a yi k’ok’arin kai shi cikin rami.

https://www.amsoshi.com/2017/11/08/barazanar-zamani-kan-magungunan-hausawa-na-gargajiya/

4.4 Muhallin Binne Gawa


Dangane da muhallin da Maguzawan Kambari ke binne gawa, kamar yadda idan wani daga cikin Musulmai ya rasu, ana kai shi a mak’abarta. Bayan wanann su ma Kirista, idan wani daga cikinsu ya mutu, bayan an sanya shi cikin akwati su ma suna da ke’ba’b’ben wuri da suke kaiwa.

Haka su ma Maguzawan Kambari a duk lokacin da babba a cikin gida ya mutu, wasu daga cikinsu suna binne shi ne a cikin zaure. Bayan haka kuma, idan saurayi ne, mafi yawa a jeji kusa da bayan gida suke binne shi.

Wani loakci kuma idan jinjiri ne akan sanya shi a cikin matashin tukunya, bayan an sanya shi sai a sami abu a rufe bakin kamar murfi, daga cisani a mai da k’asa.

4.5 Yanayin Ramin Binne Gawa


        Maguzawan Kambari na samun wad’anda suka manyanta kamar masu kimanin shekaru 40 ko 30 don su je su gina ramin da za a binne gawa. Dangane da zurfin rami, suna gina shi ne yadda zai kawo kusa da cibi. Dangane da fad’in ramin kuma, ya danganta da mamacin, idan wanda ya mutu yana da fad’in jiki za a gina ramin daidai fad’insa.

4.6 Yadda Ake Binne Gawa


        Da farko bayan an gina rami, ana d’aukansa ne a sanya a cikin ramin. K’afarsa na duban gaba, sannan kuma kansa na duban Yamma. Bayan haka kuma fuskan ko dai ya dubi kudu ko kuma arewa. Amma kafin a sanya shi sai an shimfid’a tabarmar kaba a k’asan rami.

Bayan haka, daga nan kuma sai a zuba masa kud’i a cikin ramin ko kuma kayansa. Ana gitta itace masu d’an girma a saman ramin. Bayan nan sai a samu zana  a sanya a saman itacen. Daga bisani a mayar da k’asa, sanan a d’a’be da makuba.

Bayan haka sukan zuba giya lokacin da ake da’be ramin. Haka sai a umarci jikan mamaci ya k’etara ramin sau uku. Bayan an gama, sukan yi abin da suke kira duba, amma sai bayan kwana uku da mutuwa. Sukan yi amfani da wani abu ne, da suke kira k’odago domin sanin wanda ya kashe shi. Kuma suna ba shi sak’o kamar haka:

Idan kashile ne ya kashe ka, to ka yafe idan kuwa mutum ne  ka biyo hakinka bayan ka dawo fatalwa.

Ga kuma yadda suke fad’i da yaransu:

Kamar bammad’a wulenu ko kashile in ko bambad’a wulenu mitoo hakimi kashile wulutmitoo munoo.

Bayan haka kuma, idan Bamaguzan Bakambara ce, ta mutu akan samu jikanta ta gefen uwa, a bata kaza. Idan ta rik’e kazar sai ta buga bisa kabarin da aka binne ta. Amma jikan ba ta da damar cin naman kazar, sai dai wasu.

Bayan haka, Maguzawan Kambari suna kai kayan mamaci a mararrabar hanya. Akan ba jikan wanda ya mutu goran duma a zuba gari a ciki, tare da ludayi. A duk lokacin da ake yin tafiya zuwa mararraban hanya, idan ya ci karo da wani mararrabar hanya sai ya d’ibi garin da hannun hagu, ya zuba har sai an kai wurin da aka saba kaiwa.

Haka kuma, idan namiji ne, sai bayan kwana uku da mutuwa sannan akwashe kayan a ba da kyauta. Saura kuma a kai mararraban hanya, kamar riga da kwacciyan shuka da kasko. Idan kuwa mace ce, ana kai kaya kamar kujera da tsintsiya da tulu da kuma takalma da sauransu.

4.7 Zaman Makoki


Maguzawan Kambari a duk lokacin da wani daga cikinsu ya mutu sukan taru a gidan wanda abin ya shafa wato sukan taru a gidan mamaci domin taya wanda abin ya shafa bak’in cikin rashin da ya same su. Bayan sun dawo daga wurin binne mamaci akan aje tulun giya a k’ofar gida. Duk wanda zai shigo cikin gida sai ya d’ibi giyar ya sha. Wannan giyar da suke sha, shi ne ke kore musu zafin rashin da suka yi na d’an’uwansu.

Bayan haka kuma abokan zama kan kawo musu abinci da giya don su ciyar da masu zaman makoki. A lokacin da ake zaman makoki matar mamaci takan zauna ne ta mek’e k’afarta. Duk ladabin da ke ga Maguzawan Kambari a duk loakcin da suka gamu da juna, sukan kai har k’asa ne domin girmamawa. Duk da haka, matan mamacin ba ta daikon mik’e k’afarta balle ma ta tashi. Bayan haka kuma, takan sayi giya da kud’in da ake taimaka mata da su. Wannan kud’in da su ne take sayen giya ta kama zubawa a bisa kabarin da safe da yamma har sai ta kwana uku.

https://www.amsoshi.com/2017/10/20/mene-ne-bori-fashin-bakin-maanarsa-cikin-taskar-harshe-adabi-da-alada/

4.8 Lafuzzan Gaisuwar Mutuwa


        Dangane da lafazin da ake amfani da shi a wajen gaisuwar mutuwa, kamar yadda kowace, k’abila ke amfani da wasu ke’ba’b’bun lafuzza wajen amsar gaisuwa, su ma haka suke yi. A duk lokacin da wani daga cikinsu ya mutu, wad’annan lafazin wajen gaisuwar mutuwa ne kawai ake amfani da shi.

Haka Maguzawan Kambari na amfani da lafuzza wajen amsar gaisuwa a duk lokacin da wani daga cikinsu ya mutu. Bayan haka akan sami ‘yan uwa na kusa da kuma abokan zama, hak akuma da ‘yan uwansa na jini. Duk wad’annan suna taruwa a gidan mamaci don amsar gaisuwar da ake musu. Maguzawan Kambari suna amfani da lafuzza kamar haka:

Ashe haka Kashile ya yi nashi ikon?

Eh haka Kashile ya yi.

Wanda bai k’i zuwa ba, ba ya k’i komawa ba.

Ga yadda suke fad’a a cikin harshensu.

Sututo socesad’o ashe kashile kayatun kan.

Kashile kayenai.

Bu’uya kutuba, Bu’uya kutuba, Bu’uya kuboluba.

Ana ta maimaici.

4.9 Gado


Maguzawan Kambari, a duk lokacin da wani daga cikinsu ya mutu. Idan ya bar gado, suna barin gadon shanu, itace, da akuya, da galman noma da filaye na noma, da sauransu. Da farko idan namiji ne babba a cikin gida wato cikin iyalan mamaci, ana ba shi kaso fiye da na kowa. Bayan nan kuma, sai a ba mai bin sa har zuwa ga d’an auto k’arami.

Bayan haka idan mace ce, babba to ana duban mai binta sai a ba shi kaso fiye da nata. Daga bisani sai ta biyo bayansa har zuwa ga d’an auta. Bayan haka kuma, idan ya kasance namiji ne babba, wanda ke bi masa mace ce, ana ba ta kaso fiye da na wad’anda ke bi mata.

Maguzawan Kambari suna bambanta maza da mata ne wajen gado saboda namiji da ak bari shi ne magajin gida. Don haka a duk lokacin da wata ta zo da wani matsala, wannan namijin shi ne zai magance mata matsalanta.

Matan Maguzawan Kambari, suna ba matan mamaci gadon mijinta, amma sai sun yarda za a gaje su a nan gidan mamaci, wadda ba ta yarda ba, ba ta da gado sai dai ‘ya’yanta. Ana ba su gadon ne fiye da na autan gida. Idan kuwa mace ce ta mutu ana ba mijinta gado, in ba su da ‘ya’ya ana ba mijin kaso mai yawa fiye da na kowa. Sai kason da ke bin nasa, shi ne na uban yarinya. Idan kuwa suna da ‘ya’ya ana ba ‘ya’yan kaso mai yawa fiye da na kowa, mijinta sai babanta da uwanta.

Bayan haka, idan mace ko namiji suka mutu ba su da ‘ya’ya, da farko idan mace ce ta mutu, ana ba iyayenta gadon ta da kuma mijinta, amma na ubanta ya fi yawa. Amma uban bai da damar mallakan gadon shi kad’an, kuma ba za a raba ba. ana amfani da gadon ne a cikin gidan, idan shanu ne kowa na da damar amfani da su wajen noma, haka idan lalura ce, cikin gadon za a yi amfani da shi. Haka kuma abin yake idan namiji ne ya mutu ba ya da ‘ya’ya, ana aiwatar da gadon ne kamar yadda ya gabata a gadon mace.

4.10 Takaba


        Dangane da takaba (wanda a harshensu suke kira wotosunno), a wajen Maguzawan Kambari, idan mace mijinta ya mutu za ta yi kwanaki da yawa kamar wata hud’u kafin ta koma gidan mahaifinta. Daga nan ‘yan uwan mamaci za su ci gaba da kula da ita ta gefen ciyarwa da shayarwa da sauransu. Matan Maguzawan Kambari ba su da wani tsari na sai ta yi jinin haila na wani adadin lokaci. Bayan wannan ba ta daman ta’ba kayan sa domin Maguzawan Kambari suna raba gadon wanda ya mutu. Don haka ba ta da daman ta’bawa domin akwai masu gadonsa bayan ita.

Idan tana takaba akwai wasu hani da aka tanadar mata ta yi, ga su kamar haka:

 1. Idan tana takaba ba a barin ta ta yi ayyuka kamar noma da zuwa itace.

 2. Idan tana takaba ba ta zuwa rafi.

 3. Idan tana takaba ba ta yin girki.

 4. Idan tana takaba ba ta yawo iya kanta cikin gida, ko k’ofar gida

 5. Idan tana takaba ba ta yin wasan k’anin miji

 6. Idan tana takaba ba ta yin dariya k’warai kamar dariyar k’eta sai dai murmushi.


4.11 Auren Matan Mamaci


Maguzawan Kambari suna da hanyoyin da suke bi domin aurar da matan mamaci. Da farko bayan ta gama takaba ta koma gidan iyayenta ko magabata daga cikin ‘yan uwanta, sukan yi shawara da ita a kan ta fad’i wanda hankalinta ya fi kwantawa da shi a cikin ‘yan uwan mijinta wad’anda ta ji tana iya auran shi. Ana ba ta wani d’an lokaci don ta yi shawara. Haka kuma a gidan mijinta da ya mutu, su ma ‘yan uwansa suna shawara a kan wanda ya kamata ya bi ta ya aura.

A wannan loakaci da ake ciki, iyayen mamaci ko kuma ‘yan’uwansa kan je gidan matan mamaci domin bayyana musu cewa, sun yi shawara a kan wanda zai aure ta, ya mai da ita. Haka su ma iyayenta za su ce su ma sun ba ta lokaci ne ta yi shawara, amma ba ta fad’i wanda take so ba. bayan wannan za a so jin ta bakinta, idan ta yarda sai a d’aura musu aure a mai da ita gidan da ta fito. Idan k’anin mijinta ne ya aure ta, ya gaji matan wansa. Haka kuma idan wansa ne to ya gaji matan k’aninsa.

Bayan haka, idan ba ta amince ba, sai a ba ta daman auren duk wanda ta ke so, ta aura. Maguzawan Kambari suna da tsarin wanda ya kamata ta aura da wanda bai kamata ta aura ba. wato wad’anda suke haramta ta aura da kuma wad’anda suka halatta ta aura.

Wad’anda Ya Kamata Ta Aura 1. K’anin mijinta

 2. D’an kawon mijinta

 3. Baban mijinta na da d’a ta na iya aurensa


Wad’anda Bai Kamata ta Aura Ba 1. Ba ta auren wan mijinta

 2. Ba ta auren baban mijinta

 3. Ba ta auren kawon mijinta


4.12 Bukukuwan Mutuwa


A al’adan Maguzawan Kambari, bayan mutum ya mutu da shekara uku, ana yi masa bukin mutuwa. Haka kuma idan mace ce ana yi mata bukin bayan shekarar hud’u da mutuwa.

Matakin farko da suke bi shi ne, sanya ranar aiwatar da wannan bukin. Bayan haka kuma, sai a raba goro wajen ‘yan’uwa na kusa da na nesa. Daga nan kuma sai a tanadi abincin ciyar da mutane, da kuma giya don abu ne mai muhimmanci ga Bamagujen Bakambare. Bayan haka kuma, jikan mamacin mace ko namiji kan yi kiwon rago, wannan ragon shi ne za a je da shi wajen bukin.

Maguzawan Kambari, suna tarayya ne da mata wajen yin wanann bukin. Suna yin wanan bukin ne a gidan wani babba daga cikin iyalansu. A wannan gidan ne ake gina d’akin magiro. Wannan ragon da jikan mamaci ya yi kiwo, ana yanka shi a zuba wa d’akin magiron jinin ragon. Haka kuma ana yanka kaza, amma ana yanka ta ne ta baki sai a zuba jinin ga d’akin magiro sai a gyara naman a ci wajen bukin.

A duk lokacin da za a yi wannan bukin ana kiran makad’i. Wannan makad’in shi ne ke yin kid’i su kuma mata da maza suna rawa. Bayan wanan kuma, a cikin wannan shekara ne, na uku Maguzawan Kambari suke zuwa a wurin kabarin mamaci, sai makad’in ya tsaya tsakiyar mata da maza suna zagayan kabarin ta baya-baya.

Bayan haka kuma, ‘yan uwan mamacin daga wurare daban-daban suna kawo ma ‘ya’yan mamaci kyautan gero, da dawa, da gyad’a da sauransu. Maguzawan Kambari, suna yin wak’a lokacin da makad’i ke yi musu kid’a. Wannan wak’ar alhini ne suke nunawa na rashin d’an uwansu. Ga abin da suke cewa a cikin harshensu na Kambarci:

Lafa maringima lukadiboso,

Litukai ulacele alaba yawali’a,

Ya waliba aliyayyee ya ci kai,

Watale.

Wannan wak’ar ita ce suke mamaitawa lokacin da suke rawa, makad’in na yi musu kid’a. A cikin wak’ar nasu, suna nuna yadda mutuwa ke da zafi, da rad’ad’i, a zukatansu. Domin kuwa sun san idan ya mutu ba ya dawowa, kuma dawowan da suke tunanin zai yi, ba a matsayin siga ta mutum zai dawo ba don haka sun rasa shi har abada.

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

4.13 Nad’ewa


        A wannan babi, an yi k’ok’arin tatauna abubuwan da suka shafi yadda Maguzawan Kambari ke yin jinya, lokacin da wani daga cikinsu ya kamu da rashin lafiya. Haka kuma, an bayyana yadda suke fad’ar mutuwa, da kimtsa gawa da muhallin binne gawa.

Babin ya kawo yanayin ramin binne gawa, da yadda ake binne gawa da kuma zaman makoki, da lafuzzan gaisuwar mutuwa. Haka kuma, babin ya kawo yadda Maguzawan Kambari ke raba gadon mamaci. A babin an fito da yadda matar mamaci ke gudanar da takaba. A k’arshe an kawo yadda ake aurar da matan mamaci, da kuma yadda Maguzawan Kambari ke gudanar da bukukuwan mutuwa.