Amsohi

Anas Darazo


08039275299


Juwainas@gmail.com


 

So kamar wuta yake wurin zafi,

Kamar ya zaki yake wurin k’arfi,

Har ya zarce aska wurin kaifi.

 

Sun kira shi tsuntsu mai tashi,

Idan ya zo ka ji shi na k’amshi,

Idan ya so ya yi gaba abun haushi.

 

Akwai damina akwai rani,

Akwai kala-kala akwai launi,

So na canzawa hakan na gani.

 

Sarki ne shi gwanin mulki,

Ka hau shi da gudu kamar doki,

Zai bautar ka kullum kana aiki.

 

Idan ka damu da shi ya dame ka,

Idan ka gudu sai ya same ka,

Idan ka je gare shi ya tsere ka.

 

Damusa yake ba sabo,

Ba ya tsufa kullum kamar sabo,

Zuwan sa ba shiri kamar ha’bo.

https://www.amsoshi.com/2017/10/20/barkwanci-a-matsayin-kafar-samar-da-zaman-lafiya-a-tsakanin-alummu-nazari-daga-wasannin-barkwancin-katsinawa-da-gobirawa/

Yana ladabtar da mai yin sa,

Yana hukunta ma'abotansa,

Babu tausayawa a tsarinsa.

 

Shi gaskiya ce kamar k’arya,

Akwai shi amma yana ‘buya,

Idan ka duba gaba to yana baya.

 

Haske ne shi wajen kallo,

Wuri yana haske da ya ‘bullo,

Isowar zai koma duhu yama gwalo.

 

Wurin nema mawuyaci ne,

Idan ka nemi sayan sa tsada ne

Ka nemi kyautarsa rowa ne

 

Idan ka rik’e da k’arfi ya koka ma,

Idan ka rik’e kad’an ya zulle ma,

Shi fa wurin ruk’onsa  ba dama.

 

Idan ya karb’e ka ka more,

Zai zauna k’alau ba bore.

Ba ka ma so a ce ya k’are.

 

Ba ruwansa da girmanka,

Ba ya lissafin yawan karatunka,

Ya kasa gane tsarewa irin taka.

 

Ina ruwansa kai yaro ne?

Ko kuwa kai d’in babba ne?

Ai shi fahimtarsa an manne.

 

Ina rok’on Allah ya yafe ni,

Ya hana so wahalshe ni,

Da ni da ku ya ikhwani.

 

Soyayyarka Allah ka k’ara min,

Ta Baban Alkasim ka ninka min,

Ta mak’iyanka ina fata ka yaye min.

 

Allah dad’e ni son iyayena,

Tausayinsu ya cika k’albina,

Da su da dukkan masoyana.

 

Zan ja burki haka da baitina,

Baiti sha takwas ne a wak’ena,

Na sha tara zai zama suna na.

 

Anas Darazo ne mawakinku,

Aboki kuma d’an uwa naku,

Mai so ku so shi mai son ku.

 

 

 

https://www.amsoshi.com/2017/10/30/nazarin-littafin-kibiya-ratsa-maza-na-abdulaziz-sani-madakin-gini/