Amsoshi

 

FATIMA MUHAMMAD UMAR


 

 

https://www.amsoshi.com/2017/11/01/rigar-kaya-mai-dadi/

 

Gabatarwa


Wannan bai kammala har sai an yi dogon waiwaye a kan kafuwa da kuma yad’uwar addinin musulunci a duniya da kuma kafuwar jami’o’i na.

Don haka, wannan littafi mai suna “Sark’a” yana d’auke ne da shafi tamanin. Wanda a cikinsa za a ga yadda ake aiwatar da dabaru iri-iri. Kuma yana d’auke da taurari da dama.

A cikin wannan littafi mai suna “Sark’a” za a ga hoton yanayin kishi da siddabaru. Inda wata mai suna Halima Sark’a take aiwatar da wasu abubuwa na makirci wanda ya sabawa addini. Akwai kuma wani boka wanda shi yake wa Halima aiki tana wannan mummunan hali.

Har ila yau, Musulunci ya fara zuwa Afirika tun zamanin Annabin Rahama lokacin da ya turo tawagan farko ta musulmi masu gudun hijira daga Makka zuwa Habasha a k’ark’ashin jagorancin Ja’afar Ibn Abu-Talib.

Wannan littafi mai suna “Sark’a” wanda Maryam Salisu Kurfi ta wallafa, ta sadaukar da shi ga ‘yan uwanta da abokan arziki da masu nema na a kodayaushe, ta kuma jinjina shi ga Alhaji Mansur Kurfi tare da amaryarsa.

Ma’anar jigo


Jigo na nufin sak’o ko manufa ko bayani ko ruhin da littafi ya k’unsa wanda kuma shi ne abin da littafin ke son isarwa ga mai saurare ko karatu ko nazarinsa.

Warware jigo shi ne fitowa da bayanan da marubucin littafi zai yi a cikin tsarin littafinsa d’aya bayan d’aya. Mafi yawa abubuwa uku ke kawo kwan gaba kwan baya a cikin littafi, sune kamar haka:

 • Rashin k’warewar marubucin littafi

 • Rashin nak’altar abin da ake rubuta littafi kansa sosai

 • Mantuwar marubuci a kan wani muhimmin abu sai can daga baya ya tuna da shi.


Don haka, wannan littafi mai suna “Sark’a” yana d’auke da jigon “Tashin hankali” saboda ire-iren tashin tashinan da ake yi a ciki.

Ma’anar Salo


Salo hanyace da ake bi a isar da sak’on littafi ko kuma a wani k’auli shi ne dabarun jawo hankali da sarrafa littattafai a cikin littafi.

Misali,

Amfani da Hausa mai kyan armashi ta hanyar za’ben kalmomi da jumloli ingantattu kansa a yi kwad’ayi a yi karatun littafi tare da fahimtar jigo cikin sauk’i, kamar:-

A cikin wannan littafi na “Sark’a” an yi amfani da wad’annan abubuwa na salo kamar wato:

 • Aron kalmomi

 • Karin magana

 • Kirari

 • Salon zance cikin zance

 • Labari cikin labari, wad’annan na daga cikin abubuwan da suke sa littafin ya yi kwarjini da farin jini.


Salo ya k’unshi salailai da dama da ake samu cikin littafi, sune kamar haka:

Salon kwalliya:


Salon kwalliya shi ne amfani da wasu za’ba’b’bun kalmomi masu ratsa zuciya da marubucin littafi ke amfani da su cikin hikima da basira domin sakawa mai saurare.

Misali,

“Ba don akwai wata magana”

An yi wannan maganar ne a shafi na goma sha bakwai inda Halima take cewa – ba don akwai wata magana da yanzu ta watse.

Salon Kamance:


Shi ne wajen da marubucin littafi ke kwatanta wani abu da wani domin tantance matsayin abin da ya ke kwatantawa daga abin da ya kwatanta shi da shi.

Misali,

“Da kamar ba zan fad’a mata gaskiyar abin da ya faru ba”

An yi wannan maganar ne a shafi na goma sha bakwai, inda Halima take cewa – gaba d’aya na rud’e, in ban da kame-kame babu abin da nake yi.

Salon Kinaya


Shi ne inda marubucin littafi zai k’ira wani abu musamman mutum da sunan wani abu daban da ba nasa ba.

Misali,

“Abin ga dai da mamaki”

Salon kirari


Shi ne wanda mutum zai yi wa kansa kirari ko kuma ya yi wa wani abu.

Misali,

“Sark’a uwar rikici”

“Ya d’aya tamkar da goma”

“Annoba k’are ‘ya’yan zamani”

“Mai gida mai mota, mai dubbai mai china, dole a ganki a k’yale”.

A wannan ‘bangare, an yi wannan kirari ne a shafi na hamsin da bakwai, da k’awayen Halima ke yi mata.

Zubi da tsari


Wasu manazarta sun fi so a k’ira shi tsari, a nan zubi da tsari sun shafi wad’annan abubuwa, sune kamar haka:

 • Bud’ewa ko rufewar littafi

 • Dabarun k’ulla labari

 • Tsarin babi-babi ko lambobi ko kan labari


Har ila yau, shi wannan littafi mai suna “Sark’a” yana d’auke da shafi tun daga d’aya har zuwa tamanin (80). Wato ya kuma fara da mabud’in tashin hankali da kuma marufinsa shi ne matsayar da aka cimma wannan tashin hankali. Sannan kuma an yi amfani da dabaru iri-iri na k’ulla labari a ciki.

Taurari


Daga cikin taurarin da suka fito na wannan littafi mai suna “Sark’a”, sun had’a da:

 • Nafi’u

 • Halima Sark’a

 • Malam Sani

 • Hajiya Fati

 • Ma’azu

 • Hadiza

 • Baba Sa’idu

 • Hadiza

 • Alhaji Inuwa

 • Hajiya Samira

 • Duduwa

 • Alhaji Lawan


Wato dai babban ko babbar tauraro ko tauraruwa a wannan littafi na “Sark’a” ita ce ko shi ne “Halima Sark’a”. Shi dai yana d’auke da taurari iri-iri a ciki. Kowane daga cikin taurari ga irin rawar da ya taka. Shi dai Malam Nafi’u shi ne mijin Halima na farko sannan Malam Sani kuma abokin mijin Halima ne wato Malam Nafi’u, wannan littafi dai yana tattare da abubuwa da dama na ban mamaki da al’ajabi. Saboda littafi ne wanda tauraruwar ke shirya makirce-makirce iri-iri na ban tsoro, wanda daga k’arshe sai abin ya dawo kanta. Halima Sark’a dai tana yawan zuwa wurin boka suna k’ulla abubuwa. Inda daga k’arshe kuma yazo ya na nadama da iri wannan abubuwan ban al’ajabi da ta k’ulla. Sannan ita Dr. Hadiza ma’aikaciyar asibiti ce wato dakta. Ita ce daktar da take duba Halima a yayin da duk lamari ya ‘bace har ta je ga zuwa asibiti.

Kammalawa


Wannan littafi mai suna “Sark’a” na labaran zube na gargajiya. An rubuta shi ne da jigon tashin hankali. A cikin wannan littafin an kawo ma’anar jigo da salo da zubi da tsari. An kuma kawo sunayen taurarin ciki gaba d’aya.

https://www.amsoshi.com/2017/10/16/hyperbole-peak-stylistic-adornment-hausa-oral-songs/