Ticker

6/recent/ticker-posts

Lokacin Abu A Yi Shi In Ana Son A San Shi



1.                 Mu gode Allah ɗaya mai komai
Da yay yi komai a lokacinai,
Yay yi hukunci bisa yardaTai,
     Ga lokaci wa ka karkare shi?.

2.                 Bisa yardaTai ya ƙago bayi,
Ga ƙassai ga sama’u Ya yi,
Da fasullan shekara da yay yi,
     Na lokaci ba a gurgasa shi.

3.                 Shi dai waƙaci a kiyaye shi,
In ya zo ba a tunkuɗe shi,
Mai iƙirarin ya gurgusa shi,
     Kar ku yi shakka ga ƙaryata shi.

---------------------------
Aliyu Muhammad Bunza
-------------------------------

1.                 Mu gode Allah ɗaya mai komai
Da yay yi komai a lokacinai,
Yay yi hukunci bisa yardaTai,
     Ga lokaci wa ka karkare shi?.

2.                 Bisa yardaTai ya ƙago bayi,
Ga ƙassai ga sama’u Ya yi,
Da fasullan shekara da yay yi,
     Na lokaci ba a gurgasa shi.

3.                 Shi dai waƙaci a kiyaye shi,
In ya zo ba a tunkuɗe shi,
Mai iƙirarin ya gurgusa shi,
     Kar ku yi shakka ga ƙaryata shi.

4.                 Mai ƙwazon kan ya zo ya leƙo,
Wai zai ruga ya sa ya sheƙo,
Haba! Idan kai yana da sanƙo,
     wa zai gashi ya sutarta shi?

5.                 Gaggawa ba ta sa a girma,
Komi nakinka in gaya ma,
In waƙaci ya yi babu dama,
     Komai shi za shi bayyana shi.

6.                 Bari doro don kana da kuɗɗi,
An shiga mulki ana ta faɗi,
In waƙaci ya yi babu daɗi,
     Zama guda za shi toskana shi.

7.                 Ilmi bai tsere lokaci ba,
In ka same shi zan ka tuba,
Daina kirari kana ta ƙaba,
     Ko an ce: “Wane ba awa shi”.

8.                 Bil’ama ya so ya ƙure Musa,
Ganin karatunsa ya yi nisa,
Tabara yab bi shi har maƙosa,
     Da lokaci an ka dambala shi

9.                 Da lokaci yay yi an ka kammai
Mala’iku an ka sa su jimai,
Bugu guda an ka yo gaba nai,
Nahawunai an ka yamutse shi.

10.             Ga shi rugun zaune an ka nuno,
Sunanai an ka ce ya zano,
Yay yi ta wayon biɗan ya gano,
     Amma yak kasa rubuta shi.

11.             Kun san Ƙaruna ya yi suna
Da lokaci yat taho na ƙuna,
Gaban mutane a tsakan rana,
     Ƙasa ta kammai ta adana shi.

12.             In mai mulki bai manta ba,
Bai yiwa Fir’auna ƙwarjini ba,
Da lokaci yay yi bai kula ba,
     Cikin ruwa an ka birkice shi.

13.             Duk mai cewa ƙarfi ya zo,
Ya bar tsoro yana ta ƙozo
In waƙaci ya yi babu gwarzo,
     Zama guda za a murƙushe shi

14.             Ku dubi tsarin maza na farko
Da shirye-shiryen da sun ka ɗauko,
Da lokaci yay yi sun ka sauko,
     Kamin ya biya ya kakkaɓe shi.

15.             Ɗan boko in ya sa agogo,
Kaman ya tusgo da shi ya rugo,
Kan ajima in ya je ya rego,
     Nan waƙaci za shi ba shi haushi.

16.             A yau ina altaɗar da jaki?
Kuɗinsu da sun wuce tumaki,
A yanzu sun zan adon musaki,
     Waƙaci tilas a girmama shi

17.             Waƙaci kwas san irin halinai,
In ya ga ya fara isalinai,
Miƙa wuya zai yi kar ya farmai,
     Ya sa shi mala ya maƙure shi.

18.             In jiya ne kay yi naka loto,
To bari yau masu yi su ƙoto,
In ka ce dole za ka gitto,
     waƙaci ko za shi ba ka kashi.

19.             Shi waƙaci bai jira ga kawo,
Kuma take ya gama da kawo,
Bai rigima bai faɗa da tsawa,
     A hankali za shi hukunta shi.

20.             Ku dubi kyawon abu na sabo,
Kaman a lasa idan ka dubo,
In waƙaci yas shigo ya tarbo,
     A kai shi Juji a jikkita shi.

21.             Ƙuruciya in tana da gauni,
Da shekaru za a  sa ta rauni,
A zo zama dole sai da, ‘wai ni’!
     Tashi sai an kakkama shi.

22.             Mai karfin hankali fasihi,
Ka iske ya dambale wa kihi,
Shekaru sun shige da zurhi,
     Wahmi ya fara sunsuna shi,

23.             Dubi irin zaƙunon budurwa,
In waƙaci za shi ba ta kewa,
Haurun su zube ga gantsarwa,
     Haibar fuska a tamuƙe shi.

24.             Lotto muddin yad darkako,
Kowat tarbe shi ba shi ƙarko,
Zama guda zai mutuwar kasko,
     A kai shi daji a turbuɗe shi.

25.             Rana haskenta in ya ɓullo,
Hantsi kowa yake ta kallo,
Kan agajenin karin kumallo,
     Waƙaci shi za shi rarrabe shi.

26.             Mai cewa ya iya kwatse shi,
Mai doron sun ƙware taɓo shi,
Mai cewa mu ka yi kiro shi,
     Waƙaci muka sa shi hukunta shi.

27.             Tambayi mai kakkaɓi da kauɗi,
Nuna zaƙewa gwanin zumuɗi,
Leɓo kakan kwaɗai da lauɗi,
     Da mucciya an ka zungure shi.

28.             Mai cewa, yanzu ba kamata
Waƙaci ya mai da shi ƙwatata,
Har ya zan yanzu bai da gata,
     Waƙaci ya ida kalmishe shi.

29.             Mai turo yara ƙaryata mu,
Wurin karatu a kunyata mu,
Waƙaci yaz zo ya faranta mu,
     Yau yaran su ka ƙaryata shi.

30.             Tambayi Ɗankama goga masu,
Uban samaƙi mai ‘yan gasu,
Da lokaci za shi suɗaɗa su,
     Zama guda an ka ba su kashi.

31.             Kai waƙaci ka yi ba ta kashi,
Masu gidajen ƙarau gilashi,
Ga su ƙuyaya su yanka kashi,
     A sa ƙasa ai ta rurrufe shi.

32.             Masu hawa raƙuma dawaki,
Da dubun kaji cikin akurki,
Yau abu ya zan kamar mafarki,
     Duk wakaci ya kacaccala shi.

33.             Manyan girma ‘yan alfarma,
Jarummai masu ji da fama,
In waƙaci ya yi babu dama,
     Da hawaye za su kammala shi.

34.             Maganar banza rashin azanci,
A ba ka girma ka sa bananci,
In waƙaci ya taho da ƙunci,
     Da mu da kai, wa ka tsallake shi?

35.             Da lokaci za a shirya komai,
Da shi ake kammalar da komai,
In ba shi ba shiri na komai,
     Domin shi za shi barkata shi.

36.             Komai waƙaci garai sananne,
An ka gina kansa ayyananne,
Komai fitina ta tufananne,
     Ƙyale waƙaci shi toskana shi.

37.             In ka ji an ce, mutum da kaifi,
Komai sai ya yi ci-da-ƙarfi,
In waƙacinai ya zo da zafi
     Zama guda za shi murƙushe shi.

38.             In an ce, wane shi ka tashe,
Ya ɗauko lokaci gasasshe,
Waƙaci zai sa shi dallasshe
     Sai ka ji shu har an manta shi.

39.             Gwani ga ƙira da masu noma
Da ‘yan farauta da masu koma,
In waƙaci ya yi sai su koma
     Kaman da ɗai ba su aikata shi.

40.             Waƙaci da rabo suna da sauri,
Komai ƙwazon rabo da sauri,
Sai waƙaci ya yi zai yi kuri,
     A buɗe hannu a rungume shi

41.             Ba a taɓa yaƙi da lokaci ba,
An ka yi nasarar kara da shi ba,
Bai taɓa lattin zuwa wuri ba,
     Bale a girsai a hukunta shi.

43.             Ka bar ganin wai kana da girma,
Don haka tilas ake raga ma,
Da lokaci ya yi in gaya ma
     Girman duk zai warwatse shi.

44.             Ina bika madugun azanci,
Da shi da suda uwar habarci,
Da lokaci yat taho da ƙunci,
     Tsakan faƙo sun ka yanka kashi.

45.             Dubi taɓaɓɓen ga jiɓananne,
Da shi da wawan ga toskanne,
An ce kawunsu tufanannen,
     Yau waƙaci ya tozarta shi.

46.             Sukuntumau mai ƙullin ƙarya
Da Kakkaɓi mai bakin kurya,
TuwOnsu yau ya koma gaya,
     Da lokaci yaM muzanta shi.

47.             Komai nutse ruwa in ji Kabawa,
Tudu ake tarbon gaggawa,
In yan mace ciki ya zan gawa,
     Ga tunkuɓa aka dako nai shi.

48.             Mazambaci duk ku tabbatar mai,
Yana da waƙacin da za a kammai,
A karanto mai a fallasa mai,
     Bayan kunya a hukunta shi.

49.             Mahassadi mantuwa ka kammai,
Rabon mutum wa ka tunkuɗe mai?
Ubangijinai ya ƙaddaro mai,
     Waƙaci ne, wa ka tunkuɗe shi?

50.             Ka reni yaro ka suturta shi,
Da ya ga an fara girmama shi,
Kai zai duban ka mutunta shi,
     Hadda faɗar ba ka girmama shi.

51.             Ya za ni bari a cutata min,
A sa ƙiyayya a ƙuntata min,
Don waƙaci ya ɗan hasko min,
     Ake bukatar a daƙile shi.

52.             An hau karaga an yi ta sara,
A mumbari an hau ba gyara,
A dandali kullum barara,
     Wai waƙacina a turmuje shi

53.             Muƙaddami da ka wannan sara
Yau waƙaci ya mai sai gara
‘Yan aikensa ka ci mai gyara,
     Shi gilma rai su ƙi gaskanta shi.

54.             A lokacinsu na ɓannan suna,
Da shi da Bagudu ɗan Maigona,
Da Bangaje mai ƙaurin suna,
     Da Ginshimi mai kan ramboshi.

55.             Ba sa tadar sunan kowa,
Magibaci wa zai yin kewa,
Mahassadi mai kushe gawa,
     Kaɓɓa bakaniken gilɓoshi.

56.             Mu tuba mu duka tun ba mu zo ba,
In jama’a ba su yafe ma ba,
Akwai tumulli ba ƙarami ba,
     A ƙulla dambe da mai tarkoshi.

57.             A lokacin da kake dai ka yi,
Da lokacin sakayya yay yi,
A ɗebe zancen samun sanyi,
     Kama a tad’inu a bar manta shi.

58.             Duk wani mai hankali shirarre,
Ya san zancen ga babu kore,
Kai ko mai hankali gajere,
     Waƙaci bai fara makkasa shi.

59.             Allah roƙon na Bunza gata,
Wurinka ko na taho da rata,
Da lokaci yay yi min na ƙeta,
     Ka yi min ahuwa, a kunyata shi.

                                  Aliyu Muhammadu Bunza
                                  Jami’ar Usmanu Danfodiyo
                                  Sakkwato,
Asabar 26/07/2014
Ramadan 29/1435/1A.H.
Arkilla Sakkwato
9:18pm


Post a Comment

0 Comments