Ticker

6/recent/ticker-posts

Rawar Da Dabbobi Ke Takawa A Wajen Gina Wasu Sassan Rubutattun Adabin Hausa

NA

IBRAHIM ABUBAKAR ARGUNGU

DA

RABIU ALIYU RAMBO
SASHEN HAUSA
KWALEJIN ILIMI TA ADAMU AUGI ARGUNGU
MAKALAR DA AKA GABATAR A
YAURI JOUNAL OF ARTS AND SCIENCE (YAJAS)

TSAKURE

A al’adance dabbobi suna taka muhimmiyar rawa ga al’umar Hausawa. Hausawa sukan yi amfani da dabbobi a al’amuransu na yau da gobe, kamar a fagen aikin gona da fatauci da tsaro da tafiyar da mulki. Haka kuma a bangaren Adabin Hausa, musamman rubutaccen adabi. A cikin wannan muk’ala za a dubi littattafan Ka Ko yi Karatu da Ka Kara Karatu da Ka Yi ta Karatu wad’anda da su Jean Boyd da Ahamed Ingawa suka rubuta domin su fito da irin wuraren da aka yi amfani da dabbobi a k’ok’arin k’ulla zaren labari saboda cimma wata manu. Haka kuma mun yi amfani da littafan Magana Jari Ce littafi na farko da na biyu a k’ok’arin samar da adabin da aka gina ta amfani da dabbobi.Domin rayuwar d’anadam bata iya gudana sai da dabbobi domin tare Allah ya yi su don su amfani juna.Shi kuma adabi hoto ne na rayuwa.Kenan ba yadda za a d’auko hoton rayuwar al’umma ba tare da dabbobi ba.

GABATARWA


Mafi yawancin abubuwan da ke bayan k’asa idan ka dube su da kyau za ka ga wasu abubu wa ne aka had’a aka samar da su. Kasancewar adabin Hausa wata gona mai fad’I, mai kuma d’auke da abubuwa da yawa, in ka yi masa dubin k’wak’waf sai ka iske yana d’auke da d’imbin abubuwa da dama da suka had’u suka gina sassan Adabin. Wasu daga cikin abubuwan da suka had’u suka gina Adabin Hausa sun had’a da mutane da dabbobi da aljannu da tsuntsye da k’wari da wurare da kayayyaki. Kowane ‘bangaren adabi ana iya samun wasu abubuwa da suke su ne tubalen gininsa. Misali idan aka d’auki tatsuniya, za a taras wuraran da aka fi ambata su ne  kogo ko k’ungurmin daji ko wani gari mai nisa ko gulbi ko fadama ko marmaro ko mafitar rana ko k’wai ko d’ankwatashi ko tufafi ko abinci ko garge ko tukane da sauransu da yawa.

Dabobi wasu halittu ne wad’anda Allah ya yi a bayan k’asa masu rai da ke da bambanci da wata da ba ita ba, wannan shi ya sa Hausawa ke masana da tsofaffi suke amfani da su a wajen tsara labarai  domin a samu gina al’uma ta gari, ta hanyar nuna wauta ko dabara ko jaruntaka ko hikima domin yara su kwaikwaye su ko su  k’aurace musu. A cikin wannan muk’ala za a dubi yadda masana suka yi nazari a kan ma’anar Adabi tare da fito da ire-irensa da kuma gajerun labarai da aka yi amfani da dabbobi a wajen gina su a cikin littattafan Ka Koyi Karatu  da Ka K’ara Karatu  da Ka yi ta Karatu  da Magana Jari Ce littafi na farko da na biyu.

MA’ANAR ADABI


Masana sun tofa albarkacin bakinsu kan abin da suke ganin shi ne ma’anar adabi. Wasu suna ganin “wannan kalmar tana nufin abubuwan da suka shafi al’umma. Wani lokaci “adabi” yakan k’unshi har irin nazarin da ake yi wa rayuwar al’uma baki d’aya. (Danganbo da Yahaya, (1986).  Ganin yake yi adabi madubi ne mai d’auke da hoton rayuwa baki d’aya.(shafi na 99). Don haka, adabi wata hanya ce ta amfani da harshe a sarrafa shi ta fuskoki daban-daban na hikima da fasaha ya zama tamkar wani mak’unshi ne na al’adu wanda kuma zai taimaka wajen karantar da matasa gargajiyarsu.  Wasu gungun masana a nasu ra’ayi cewa suka yi: idan aka natsu waje d’aya, aka kwantar da hankali za a ga cewa adabi yana d’aukar fuska biyu ne.

v    Fuska ta farko, sarraffafen harshe ne wanda ya k’unshi wata balaga ta musaman, mai ayyana basirori da hikimomin al’umar Hausawa.

v    Fuska ta biyu; hanya ce ta fayyace yadda Hausawa suke sarrafa aikace-aikacen fasaharsu domin samun sauk’in aiwatar da ayyukan yau da gobe.

Ire-iren Adabi

Masana sun karkasa adabin Hausa zuwa gida biyu manya: wato adabin gargajiya da adabin zamani. Adabin gargajiya kuwa sun karkasa shi zuwa gida hud’u wato zube, wak’a, wasa da azanci. Rubutacen adabi kuwa ya kasu kashi uku wato zube,wasa, da wak’a.  Don haka adabi hoto ne na rayuwar al’umma baki d’aya. Akan jadawali zai kasance kamar haka:

 

 






Adabi

 

 

 

 

 

Adabin Gargajiya                                                               Rubutaccen Adabi

 

 











 

Zube        Wak’a             Wasa         Azanci                       Zube           Wak’a          Wasa











 

Tatsuniya  - Wak’ok’i   -  Wasanin dadali – Kirari                K’agaggun     Rubutattun       Wasan

Labarai     -  W/Makada-  Tashe                - Zambo              Labarai            Wak’ok’i        Kwaikwayo

Tarihi        -  W/Mata    -  Raye-raye       -  Ba’a

Tarihihi     -   W/Dandali -                         - Habaici

Kissa         -                        -                         -  Karin Magana

Hikaya       -                        -                         -  Salon Magana

Barkwanci -                        -                         -  Zaurance

-                        -                         - Sara

-                        -                          - Gatse

-                         -                         - Al’mara

 

Idan muka dubi wad’annan rukunonin za mu ga cewa kowane rukuni yana cin gashin kansa sai dai ‘yar dangantakar da ba a  rasa ba tsakanin wasu rukunoni.

Yawanci dabbobi sun fi taka rawa sosai a rukunin adabin bakan zube domin nan ne ake zuba bayani rututu.Wannan ya sa  akan yi amfani da su ko dai a fad’akar ko a nishad’antar ko kuma a fito da wani abu da ake son al’uma ta amfana da shi na gyaran rayuwarta ta yau da gobe. ‘Bangarorin Adabi da aka fi amfani da dabbobi domin a nuna wa mutane wani abu mai kyau ko maras kyau su ne a wajen labarai ko tatsuniya ko hikaya ko almara da dai sauran ‘bangarorin Adabi.

A makarantu firamari malamai irin su Muhammadu Ingawa da Abubakar Imam da Ali Haidara da Jean Boyd sun shirya littattafai masu d’auke da gajerun labarai masu karantarwa domin yara su san yadda za su yi zaman duniyarsu. Yawancin wad’annan labaran an gina su ne ta amfani da dabbobi domin yara su yi saurin fahimtar su.A cikin littafi na biyu na Ka Koyi Karatu akwai labarai kamar :

- Gada da ‘yarta

-  Kaza da Giwa

- Kwad’i Biyu

Labarin kwad’i biyu: Wad’ansu kwad’i guda biyu suka fad’a cikin k’waryar madara, suka kasa fita. Suna ta iyo har  ya gaji ya ce

“yau kwanana ya k’are” sai ya bar k’okari ya nutse ya mutu. Amma d’ayan ya yi ta yi, ta wurin motsinan da yake yi har mai ya taru. Sa’anan ya hau bisa curin mai ya yi tsalle ya fita. Allah ya ce “tashi in taimakeka”.Ingawa(1972).Shafi na 6-7

Wannan labari yana nuna muna duk wani hali da ka shiga kada ka yanke k’auna ga samun nasara. Babu shakka mai k’ok’ari da k’wazo yana tare da samun nasara ga al’amuransa.

A cikin litafi na uku kuwa akwai gutattakin labarai kamar :

- Kare da Kura da Damo (a shafi na 3)

- Kurege da Bushiya (a shafi na 6)

- Dila da Zalbe (a shafi na 8)

- Ungulu da Shaho (a shafi na 10)

- Hana wani hana Kai (a shafi na 16)

- Yi taka tsantsan da Duniya (a shafi na 18)

- Sannu ba ta hana zuwa (a shafi na 30)

A cikin littafi na hud’u mai suna Ka yi ta Karatu akwai jerin labarai da aka yi amfani da dabbobi wajen k’aga su kamar:

- Karan- banin K’auyen hanya

- Hankaka Mai hikima

-  Dila sarkin Dabara

- Komai ka samu gode Allah

- Samu ya fi iyawa

- Gasar Neman Aure

- Maciji da Kunama

- ‘Beran ‘Birni da ‘Beran Daji

- Nahana Sarkin Rowa

- Banza Girman Mahaukaci K’arami mai wayo ya fi shi

A makarantun gaba da firamari musaman a manyan azuzuwan d’alibai suna nazarin wasu k’agagun labarai da ke a cikin littatafai kamar su:

- Shaihu Umar

- Iliya ‘Dan Mai k’arfi

- Ruwan Bagaja

- Gand’oki

- Da’u Fataken dare da dai sauransu.

A cikin wad’annan labarai akan samu inda masu litattafan sukan k’ulla zaren labarinsu ta amfani da wata dabba wato Kura ko Doki ko Kare da dai sauransu.

A cikin litafin Shaihu Umar an  fito mana da irin rawar da kura ta taka domin ganin cewa labarin ya d’ore. Misali:

“Bayan ‘barawo ya sace Umar ya tafi da shi  wani gidan gona ya yi bacci, shi kuma  Umar ya samu wani kwando ya shige.  “Ba a jima ba sai na fara jin gurnanin wani abu mai ban tsoro a bayan d’aki ashe gurnanin kura ne, da ta fito farauta ba ta samo komai ba har asuba, babu wani sayi mai aminci ko tufanya ma babu a k’ofar d’akin da muke. Da kura ta zo k’ofar d’akin sai ta tsaya tana shawara ko ta shiga ne ko ta koma. Gari kowa ya kusa wayewa sai ta yi  k’uru ta shiga ta samu mutumin nan a bakin k’ofa ta tsaya ta kansa tana jin inda nufashinsa yake fita sai na ga ta kafa masa hak’ori a mak’ogoro ba wani jinkiri ko wahala sai na ga ta raba kansa da jikinsa misali kamar mutum ya samu almakashi ya datse ganye sabon toho. (Abubakar T B,( 1966).Shafi na 22.

Kashe wannan ‘barawo da kura ta yi ya sa zaren labarin ya k’ara k’ulluwa har aka gane inda Umar yake, aka ci gaba da ba da labari. Wannan ya k’ara fito muna da irin gudunmuwar da dabbobi suke k’ara bayarwa wajen gina adabin Hausa.

Idan aka dubi labarin Iliya d’an mai k’arfi za a ga irin k’ok’arin da dokinsa ya yi a wajen karo da mazaje da Iliya ya yi a lokacin gwagwarmayarsa. Misali kafin had’uwar Iliya da Falalu  sai da Iliya ya yi wa Dokinsa K’walele kirari ya na cewa:

“K’walele Dokin Iliya k’walele Dokin yak’i ba ni saisheka ba ni kuwa ba da aronka! K’walele ya yi haniniya kamar ya san abin da Iliya ke fad’a daga nan Iliya ya gyara ya d’auko sirdi ya aza ya d’aure tamau ya sa’bi kulki, ya rataya takobin wargaj,i ya d’au mashi da kwari da baka ya zabura ya nufi wajen Falalu”

A yak’in Iliya na k’arshe waldima ya sake neman taimakon Iliya da ya taimaka masa kan Sarki abokin gaba bisa ga yak’in da za su yi.

“ Iliya ya harzuk’a zuciyarsa ta cika da hushi. Dokinsa kuma haka Iliya ya tashi da hushi ya k’ara gyara d’amara ya ja majayin sirdi ya rataya takobinsa da mashi ya sa’ba kulkinsa ya hau K’walele.  Kafin su soma tafiya sai K’walele ya ce: shugabana Iliya ka yi hak’uri da tafiyarnan a yau ka yi yak’e-yak’e da yawa duka kai ke cin nasara amma a yau na ga babu sa’a sosai ribar mu kad’ance sai dai kuma abin da mad’aukakin Sarki ya yi. Na ga abukan gaba sun hak’a rami guda uku dominka na tabatta zan iya haye rami na farko da na biyu amma ba zan iya haye na uku ba ina rok’on ka ka yi hank’uri sai gobe” (Ingawa, 1970.Shafi na 45-50)

Can zuwa k’arshen labarin Iliya dai ya yi nasara, a wannan labarin an yi amfani da Doki domin a k’ulla zaren labarin.Haka kuma,wannan labarin na nuna irin muhimmancin Doki ga rawuwar Dan-adam musammam yadda Dokin ya taimaka ma Iliya wurin yak’e-yak’ensa ya na cin nasara.Shawarar da Dokin ya ba shi na cewa yau ba nasara  yana nuna soyayya da k’auna da ke tsakanin dabbobi da mutane musammanga masu k’yautata masu.

Haka ma idan muka dubi tatsuniyar Gizo da Namun Daji inda marubucin ya fara da cewa:Gatanan Gatananku. Gizo ne dai yana son ya ci nama ,amma bas hi da shi,ya rasa yadda zai yi,sai y a ce a ransa,bari in yi wata dabara-----------.Yahaya I Y (1971) Shafi na 1-8.

Wani ‘bangaren labari da aka yi amfani da dabbobi domin gina labarai iri –iri saboda fad’akarwa da nishad’antarwa shi ne a cikin litattafan Magana jari ce. Wasu labarai da aka yi amfani da dabbobi domin a k’ara ha’baka Adabi sun had’a da:

-         Labarin Wani Bororo da ‘Dan Sarki

-         Labarin Auta d’an Sarkin noma da namun jeji

-         Labarin wani aku da matar Uban gidansa

-         Labarin kyanwa da ‘bera

-         Labarin wani jaki da sa

-         Fara koyon mulki da baki kafin ka koyi mulki da hannu

-         Banza girman mahaukaci k’arami mai wayo ya fi shi

-         Labarin Sarkin busa

-        Raina kama kada ga gayya

Misali .A cikin labarin Auta Dansarkin Noma da Namun Daji. A cikin wannan labarin  an mutuntar da dabbobi inda aka nuna zamantakewarsu da kuma hud’d’ar su da mutane inda su ka nuna damuwarsu da yadda mitane ke kashe su .Bayan sun yi taro domin sanin mafita bias ga wannan mastalar inda sarkinsu zaki yake cewa:

“To yaya za mu yi kun sani fa Allah abin tsoro ne, mutumma abin tsoro ne”

Imam (2001).Shafi na 26

A cikin litafi na biytu kuwa akwai labarai da aka gina ta amfani da dabbobi: Misali.

- Yaro tsaya matsayinka kada zancen ‘yan duniya ya rud’e ka

- Labarin Sarkin Noma da ‘ya’yansa

- Labarin Wani Sarki da yaronsa

- Allah na taimakon wanda yataimaki kansa

- Labarin Amjadu da Asadu

- In maye na da hankali ba ya fidda maitarsa a fili

Misali; A cikin labarin Amjadu da Asadu,labarin ya nuna muna yadda aka yi amfani dabbobi a k’ok’arin fansar rayuwar Amjadu da Asadu a lokacin da sarki ya umurci bawansa Hauni da ya je daji ya kashe su ,inda labarin ya nuna cewa:

“Da suka iske shi,ashe dawan da wata zakanya mai ‘ya’ya,doki ya sa hauni ya haye mata   ba sanannen ciki .Zakanya ta durmushe shi za ta kasha,sai ga yaran nan.Amjadu ya sa gaya-wa-jini-na-wuce,ya sare zakanyar Hauni ya kubuta yana kad’uwa”.Iman(2002)Shafi na 153

A cikin wannan labarin munga yadda Amsadu da Amsadu suka taimaki Hauni duk da yake cewa an umurce shi ne ya kashesu amma a k’arshe sai gashi su suka k’ubutar da shi.Ganin wannan sai Hauni ya yi nadama bisa ga ayyukkansa na baya inda yake cewa:

“Bari ta ku ma ,daga wannan na tuba das are mutane .ku k’yale ni,ni na san abin da na gani.Ku dai ku tafi ,in kuna da sauran shan ruwa,to,in ko ba ku da shi ,kuma wannan ba da jinina ba”.Imam( 2002).Shafi na 153

Fa’idar amfani da dabbobi a cikin rubutaccen adabi

Babu shakka akwai fa’idojida dama da ke akwai ta amfani da dabbobi a cikin k’agaggun rubutun adabi ,wasu daga cikinsu kuwa sune:

Domin a fito da wasu halaye na kirki saboda saboda mai karatu ko nazari ya yi koyi das u .Idan kuma aka fito da wani mugun hali na wata dabba ana sun mai karatu ko nazari ya guje mata.

Da yake mafi yawan labara nana gina su ne domin nishad’antarwa ko cusa wani tunani na musamman ga yara da sauran al’umma,santa dabbobi na sa yara su yi saurin fahintar sak’on da ake sosu fahinta.

Rayuwar d’an adam ba ta iya gudana sai da dabbobi domin tare Allah ya yi su domin su amfani juna,shi ko adabi hoton rayuwa ne baki d’aya.Don haka ba yadda za a d’auko hoton al’umma ba tare da an had’a tad a ta dabbobi bad a suke rayuwa tare .Don haka zamantakewa tsakanin mutane da dabbobi zaman taimakanni in taimakeka ne.

Haka kuma  yana daga cikin fa’idar amfani da dabbobi a cikin rubutaccen adabi shi ne cewa dabbobi suna da sauk’in mutuntarwa a wajen k’aga labarai.Za mu iya ganin wannan a fili idan muka yi nazarin labarin Auta ‘Dan Sarkin Noma Da Namun Daji .A cikin littafin Magana Jari Ce littafi na farko,inda za mu ga an mutuntar da tsarin zamantakewar dabbobi tamkar na mutane.

 

 

 

 

Nad’ewa


Awannan muk’alar mun yi k’ok’arin bayyana yadda rayuwar d’anadam bat a iya gudana sai da dabbobi domin tare Allah ya yi su don su amfani juna .Shi kuwa adabi hoto ne na rayuwa baki d’aya,ma’ana ba yadda za a d’auko hoton rayuwar al’umma ba tare da had’a ta da dabbobi ba. Don haka ,wannan muk’alar ta yi k’ok’arin yin nazari ne akan wasu rubutattun adabi musamman wasu labarai a cikin littafan Ka Ko yi Karatu da Ka K’ara Karatu  da Ka yi ta Karatu  da Magana Jari Ce littafi na farko da na biyu. A cikin wanna muk’alal mun yi k’ok’arin kawo ra’ayoyin masana akan ma’anar Adabi da ire-iren adabin Hausa wato adabin gargajiya da adabin zamani. mun kuma yi k’ok’arin fito da wasu k’agaggun labarai da muke ganin an yi amfani da dabbobi iri-iri a wajen tsara su. mun kuma kawo wasu misalai na wuraren da aka yi amfani da dabbobi a wajen gina wasu sassan adabin   Hausa musamman rubutaccen adabi.Haka kuma muk’alar ta yi k’ok’arin kawo fa’idar amfani da dabbobi a cikin ributaccen adabi.

Alhamdu lillahi

https://www.amsoshi.com/2017/11/09/muhimmancin-dabbbi-wajen-habaka-aladun-hausawa-kebabben-nazari-daga-wasu-littattafan-adabin-hausa/

Manazarta


Abubakar, T.B. (1966) Shuehu Umar N.N.P.C Zaria

Imam, A. (2001) Magana Jari ce Littafi na farko N.N.P.C Zaria

Imam, A (2002) Magana Jari ce Littafi na biyu N.N.P.C Zaria

Ingawa, A. (1970) Iliya d’an Mai karfi N.N.P.C Zaria

Ingawa, A., Haidara A. Boyd J. (1972) Ka koyi karatu sabuwar hanya N.N.P.C Zaria

Ingawa, A., Haidara A. Boyd J. (1972) Ka koyi karatu sabuwar hanya N.N.P.C Zaria

Dangambo A, da Yahaya I . (1986) Jagoran Nazarin Hausa N.N.P.C Zaria

Yahaya, I. (1971) Tatsuniyoyi Da Wasanni O.U.P Ibadan.

 

Post a Comment

1 Comments

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.