Littafin Ruwan Bagaja A Ma’aunin Matakan Rayuwar Bahaushe

Amsoshi

Aliyu Muhammadu Bunza


Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya


Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’aduwa, Katsina.


08034316508


mabunza@yahoo.com


OKTOBA 2013TSAKURE


Matakan rayuwar Bahaushe ba su samu kulawar masana da manazarta da d’aliban nazarin Hausa sosai ba. Wannan takarda ta lalubo matakan rayuwar Bahaushe uku: aure, da haihuwa, da mutuwa. Ta d’auki kayan cikin littafin Ruwan Bagaja gaba d’aya ta d’ora su a kan wad’annan turaku uku. An nazarci rawar da suka taka wajen kai littafin zama zakaran gasar 1933. An yi garkuwa da matanonin nassoshin littafi wurare ashirin (20) a k’unshiyar kayan cikin takardar. An gano wurare goma sha uku (13) da aure ya taka rawar gani. An k’yallaro sak’onni goma sha uku (13) da aka isar ta fuskar haihuwa. An tantance wurare ashirin da bakwai (27) da aka yi garkuwa da mutuwa domin isar da sak’o ga masu karatunsa. A jimlace matakan rayuwar Bahaushe sun taka rawar gani a wurare hamsin da uku (53) ana warwarar jigo da sak’ar zaren tunanin sak’on littafin. A kula, gutsattsarin labaran da aka gina littafin gaba d’aya hamsin da biyar (55) ne. sakamakon bincike ya fed’e biri har wutsiya. Da haka, takardar ta yanke hukuncin kowane irin sashe na adabi ana iya kallonsa a matakan rayuwar mutanensa. Yin ko oho da waiwayen matakan rayuwar mutane wajen nazarin ayyukan adabinsu da hikimominsu, kure ne babba ga d’alibai da malamai da manazarta da masana. Da adabi da harshe, duk al’ada ta haife su. Don haka, dole ne a kula da ita idan ana son a fahinci hankalin ‘ya’yanta.

 

https://www.amsoshi.com/2017/11/05/bamaguje-da-dan-akuya-kauna-ko-kiyayya/

 

GABATARWA:


Dalilan da suka sa littafin Ruwan Bagaja ya lashe gasar rubutattu k’agaggun labarai a shekarar 1933 sun cancanci a yi bitarsu.[i] Ba ina nufin bitar dacewar hukuncin alk’alan ko akasin haka ba.[ii] Manufata ita ce, a ji mazan jiya, a saurari mazan jiya, a karanci mazan jiya, a d’ora su a sikelin tunanin zamaninmu.[iii] Yau[iv] kimanin shekaru tamanin da haihuwar littafin amma koyaushe kamar shekarar da ake ciki aka rubuta shi.[v] A hangen manazarta fannoni daban-daban, duk da wani abin da manazarci ke buk’ata, ba a rasa wurin da za a nazarce shi a littafin ba.[vi] Ganin haka, wannan takarda ta himmatu ga lek’en “Matakan Rayuwa”[vii] da yadda aka yi sinadari da su wajen k’ulla zaren tunanin littafin.

 

MATAKAN RAYUWA:


A falsafar al’ada, kowane mutum matakai uku yake hawa a rayuwarsa.[viii] Matsalar da masana da manazarta al’ada suka dad’e suna fuskanta ita ce, tsayayyun hujjojin jeranta matakan.[ix] A tunanin Bahaushe, matakan su ne, aure; da haihuwa; da mutuwa. Tak’addamar da ke nan ita ce, da aure da haihuwa wane aka fara yi a duniya? Idan an bi mahangar addini muhawarar k’urarra ce.[x] Idan aka shimfid’a ta a faifan nazarin al’ada da kimiyya da hankalin tuwo abin zai fi zare tsawo.[xi] A ganinmu d’aliban al’ada, duk wani mutum da ya rayu a duniyar mutane, wad’annan matakai uku su ne turakun rayuwarsa. Ba za su ta’ba riskuwarsa gaba d’aya ba.[xii] Babu yadda zai tafiyar da su gaba d’aya. Ala tilas, kowannensu turken kansa yake da shi, sai an fita turke d’aya, a fad’a d’aya, bi da bi. Don haka muke ganin, komai kaifin tunani da basirar mutum, da zantukansa da rubutunsa da ayyukansa da tunaninsa a kan turakun suke tafiya sau da k’afa.[xiii] A nawa nazari, wad’annan matakan suka taimaka wa Abubakar Imam ga fitar da basirarsa yadda Bahaushe zai saurare shi ya fahince shi.

Kowane irin tubali wani manazarci ko masani ko d’alibi zai yi hasashen da shi aka gani tubalan littafin Ruwan Bagaja; idan bai waiwayi matakan rayuwa ba, bai yi wa nazarinsa susa gurbin k’aik’ayi ba. Masu hangen tubalan ta adabin Larabci, Larabawa na da matakan rayuwa.[xiv] Masu bin diddigin adabin baka, su sani cewa, kowane adabi a kan matakan rayuwa yake shek’e ayarsa.[xv] Babu shakka, duk abin da bakin d’an Adam zai furta ko alk’alaminsa zai rubuta, dole a samu nason matakan rayuwarsa kane-kane a ciki. Tak’addamar jeranta matakan rayuwa ba abin da za a gama ba ne.[xvi] Don haka, zan tattauna su yadda na ambace shi.

AURE:

A mahangar al’ada, aure shi ne amintuwar jinsi biyu mabambanta (mace da namiji) masu rai na zama tare da mik’a wuya ga juna.[xvii] Idan sandararrun abubuwa ne na itace da tsirrai sai an had’a jinsinansu kalmar aure ke tabbata.[xviii] Da mutane da dabbobi da k’wari ana tantance aurensu ta fuskar yadda suke huld’a da juna.[xix] Ma’anar aure takan fad’ad’a zuwa kusantar juna da had’a jiki[xx]. Burin takardarmu gano gurbin aure a mahad’in tunanin Abubular Imam ga k’ulla zaren gutsatsarin labaransa a shahararren littafinsa Ruwan Bagaja.

 

TUNK’A ZAREN TUNANI A KAN MATAKAN AURE:


Zaren tunanin gina labaran littafin Ruwan Bagaja ga aure ya samu tushe. Yayin da Koje[xxi] ya sadu da Imam ya zuba labarai daga safe har magariba (Imam, Ruwan Bagaja. 2:3). Ba a gaya muna labaran da Koje ya bayar ba. Da Imam ya so ya mayar da zubin adashin magana sai ya ce:

Na farko dai in ji maigida, sunana Alhaji Imam. Ubana kuwa wani babban malami ne na Sarkin Sudan. Sunansa Malam Na-Bakin-Kogi. Sai da ya kai dattijo har ya tsufa, ba a ta’ba ko ‘bari ba gidansa. Abin da ya dame shi k’warai ga wagagen littattafai ba mai gado. Amma ko da shike malamin nan ba shi da d’a nasa na cikinsa yana da wani agola, shaid’ani ana kiransa Sak’imu, kome uban nan nawa ya yi masa uwar ba ta godewa, shi yaron ba shi godewa.

(Ruwan Bagaja: Babi na 1, Shafi na 3, sakin layi na 1).

 

Wannan d’an bayanin shi ne tushen littafin. Da za a cire shi, an gurgunta duk abin da zai biyo baya. Imam ya fara gabatar da sunan mahaifinsa. Ishara ce mai nuni da cewa, sai an yi shuka ake zancen tumu.[xxii] Ambaton ubansa da sunan “ubana”, ko ba a kawo sunan mahaifiyarsa ba an san da aure aka haife shi. Bugu da k’ari, aka sake bijiro da wani babban turke daga turakun aure wato samun rabuwar aure ta rashin fahintar juna ko mutuwa. Dalilin haka ne uwar Sak’imu ta zo da d’anta agolan malam (Sak’imu) a gidansa. Da Imam ya so ya k’ara d’aure turken aure sosai, ya nuna bayan Sak’imu ya aikata abin da ya aikata, sai ya ce:

Matan suka yi ‘yan koke-kokensu na al’ada suka bari. (Ruwan Bagaja: Babi na 1, Shafi na 4, Sakin layi na 2).

 

Kalmar matan ta nuna ba mata d’aya ke ga malam ba. Babban dalilin aure na kowane jinsi shi ne samun zuri’a. Bahaushe idan bai samu zuri’a ga mace ba zai k’aro wata domin neman dacewa ko da kuwa matsalar haihuwar daga wajensa take. Wannan wani babban turke ne ga littafin, domin da zaren labarin ya so ya tsinke, sai aka ku’butar da Yak’utatu mahaifiyar Imam yana cewa:

Uwar nan tawa kuwa ana ce mata Yak’utatu. Da ta yi arba’in aka d’aura musu aure da Liman.

(Ruwan Bagaja: Babi na 1, Shafi na 4, Sakin layi na 2).

 

Da ba a ku’butar da mahaifiyar Imam ba, da zaren tunanin Abubakar Imam ya tsinke.[xxiii] K’ara kawo tubalin aure na Yak’utatu da Liman ya sake raya riwayar ta ci gaba da d’inkewa da ginuwa har k’arshen littafin.

Da gutsattsarin labaran da aka tsara a babi na farko aka tuk’e su. Babin ya k’are, sai aka bud’e sabon babi na biyu. A babin, Imam ya isa birnin Yamel. Tafashen kalangai da gangunan da ke tashi da kakaki da algaita da farai, su suka yi wa Imam maraba a garin. Ya tambayi yara me garin yake ciki. Suka gaya masa:

Mowar sarki aka kawo wa mata yau.

Na ce, “Daga ina?”

Yaron ya ce, ‘yar Sarkin K’aryatun Ni’am aka gama su.

(Ruwan Bagaja: Babi na 2, shafi na 10, sakin layi na 1 – 2)

Da wannan shagalin aure aka yi wa babin turke duk gutsattsarin labaran da suka biyo baya ‘yan rakiya ne.[xxiv] Haka kuma, auren shi ne maganad’inson k’ulla zaren tunanin babi na biyu da uku. Da an yi kuren wannan turken, da fasahar da aka tsaro ta bargaje. Cikin rigimar bikin auren aka zarce zuwa garin Sasa. A can aka gamu da K’wara. Da aka tsere wa K’wara,[xxv] aka had’u da Bak’auye mai jaka.[xxvi] Aka fad’a kurkuku, aka fito aka had’u da mahaukacin rak’umi aka had’a shi da Fulani,[xxvii] har dai aka shiga birnin Ris. Daga haka har labari ya zo na rabuwarsa da Zurk’e. A nan babin ya tsinke ko ya tsaya.

Turken babi na uku garin D’andago aka fara yada zango. Yana shiga garin garin D’andago ya ce:

 

A can na sami wata yarinya, ‘yar wani malami, ana ce mata Jamilatu. Ka san ni da rigima, sai na shiga bid’ar aure. Muka shiga kai toshi, yarinya kuwa ba ta fid da wanda take so ba. Kai, muka yi ta cacar kud’i dai ba haddi. Rannan fa sai na je na gaya wa uban, na ce ya kamata yarinyan nan ta fid da wanda take so, kowa ya huta.

(Ruwan Bagaja: Babi na 3, shafi na 14, sakin layi na 2).

 

A turken aure aka k’addaro da makaftarsa.[xxviii] A turken aka sada shi da Arme.[xxix] Daga nan sana’ar ‘su’ ta shigo don ta sake sada shi da Zurk’e.[xxx] Bayan nutsewarsa a kogi da had’uwarsa da ‘yan ruwa sai garin Baku. Aka k’ulla gutsattsarin labaran Zandoro d’an Zotori. Daga nan aka kawo labarin gawar bawan sarki. Bayan abin da ka aukuwa ya auku, aka ja zaren labarin zuwa babi na hud’u.

Zaren tunanin babi na hud’u da turken aure aka sarrafa shi. Domin kuwa bayan ya tambayi fatake labarin Zurk’e da gawa, aka gaya masa ba a kashe Zurk’e ba an dai d’aure shi, sai ya ce:

Ina yawo a kasuwa ran nan ina tambayar labarin Ruwan Bagaja, sai na ga wata yarinya na ce zan aura. Ashe tana da miji ba ta sonsa ne kawai. Na kira ta muka shirya ta ce in zo yau da dare. Daren kuwa aka yi maraice da ruwa. Cikin ruwan nan mijin ya dawo, ta hura masa wuta yana k’ahon dandi.

(Ruwan Bagaja: Babi na 4, shafi na 19, sakin layi na 7 – shafi na 20, sakin layi na 1)

 

Da neman aure aka k’ulla zaren tunanin wannan babi. Da kuma auren dole ko auren k’iyo aka fara warware jigon babin aka daidaita masa fuska.[xxxi] Duk auren da ba a gina a kan soyayyar ma’aurata ba, k’arshensa a shiga wani hali mawuyaci. A kan wannan tunani ne Abubakar Imam ya sakad’o da matsalar kwartanci da zina.[xxxii] Auren dole na sa mata fita ba da kamun kai ba. Yana sa mace neman mazaje irin wad’anda take so. Da aka fara tunk’a akalar gutattsarin labaran da ke k’unshe a babin. Yunk’urin kore kunya da hukuncin kwartanci ya sa aka gabato da haukar Imam da samun sarautar Wawan Sarki[xxxiii] har ya samu shiga fada sosai aka tuk’e babin daga nan.

Abin ban sha’awa, fasahar babi na biyar da tubalanin aure aka fara gina ta, aka kuma ya’be ta da shi, katangar ta yi k’arfi. Imam a garin Tegi ya fara yada zango. Da masarautar ta yi maraba da shi, sai sarkin garin ya gabatar da damuwarsa ga Imam a kan Sarkin Zaginsa ya ce:

Kai, ni dai Sarkin Zagi ya dame ni. Ba ya ko barina in yi barci.

Waziri ya ce, “Saboda me, ranka shi dad’e?”

Sarki ya ce, ai ka san tun watan jiya matarsa ta mutu. To, tun daga ran da ta mutu har yau, kullum ba ya barci. Da tsakad dare sai ya tashi yana wad’ansu wak’e-wak’e kamar mahaukaci, yana cewa da ma shi mutuwa ta d’auka ta bar matar da ya huta.

(Ruwan Bagaja: Babi na 5, shafi na 22, sakin layi na 1 – 2).

 

Daga cikin aure babu abin da ya kai soyayya dad’i. Tsananin so ke sa ma’aurata d’okin ganin junansu. So na hak’ik’a ke sa ko an rabu a gangar jiki zuciya na k’yallaro juna ka ce tare ake.[xxxiv] Bayan da aka k’ulla babi na hud’u a kan auren dole. Aka zo a babi na biyar, aka tunk’a zaren tunaninsa da auren soyayya wanda mutuwa kad’ai ta raba. Bayan da ta raba, mijin da ke raye ya kasa had’iye takaicin rabuwa da masoyiya. Duk gutsattsarin labaran da aka ambata a babin suna tafiya da wannan tubalin na aure jejjere kamar kashin awaki. Da aka zo rufe babin, bayan an had’a mata da miji fad’a kan gawa sai aka nad’e babin da cewa:

Na tafi wurin ‘yan fura in saya, sai wata mace ta taka mini hannun riga, zan yi magana ta zage ni, ta ce wai, “Lebura fa ba wanda ya fi shi izza.”

Na dubi macen da ta ce mini lebura, na ga ko tsarar k’anwata ba ta yi ba. Na ce, “Ni ban yi sai da mijinki”.

Ta dube ni da fushi ta ce, “K’arya kake yi, Malam Zurk’e ya fi ka, kada ka gama kanka da shi.”

(Ruwan Bagaja: Babi na 5, shafi na 25, sakin layi na 10 – shafi na 26, sakin layi na 1).

 

An k’i sa Imam ya kashe ta mari, da nan labarin ya tuk’e. Aka bijiro da martabar aure, ya sa mata ido.[xxxv] Aka harzuk’a shi ya nemi mijinta. Aka tsokane ta aka gane tana da miji. Aka had’a had’uwarta da mijinta da Imam ya zama tabarmar nad’e babin.

Tunanin Imam a babi na shida bai sauya ba. Da ya shiga garin Miska ‘barayi suka dame shi daga cikin ‘barayin sai da aka kawo Malam Zurk’e. Dalilin kawo shi domin a ji abin da ya faru da shi da matarsa na kore wa kashin Imam k’uda.[xxxvi] Aka gina babin da matsalolin da ke tattare da auren fitinannun mata mafad’ata. Aka bijiro da matsalar rabuwar aure a mataki na biyu wato jidalin mace da musibobinta da take jawo wa mai gida da gidansa. Rabuwar Zurk’e da matarsa ta sa ya zama gwauro har ‘barawo ya ziyarce shi da dare.[xxxvii] Daga cikin shika-shikan labaran babin akwai labarin marin matar Zurk’e wanda su suka d’inke babin sosai suka yi masa turke managarci.[xxxviii]

Babuka biyu, na bakwai da takwas nad’e labaran ne. Babi na bakwai tubar manyan taurarin labaran ne. A babi na takwas, an samu biyan buk’ata an dawo gida. Ko a nan aka tsaya, an san da babu tubalan aure cikin littafin da k’unshiyar ta kasance holok’o. Aure wani babban artabo ne a fafitikar rayuwar Bahaushe. Gwagwarmaya da adawar da ke ciki tsakanin masu nema bayyane yake a auren Jamilatu ‘yar Malam. Ranar d’aura shi wata sabuwar salla ce ga iyaye da amare. Kad’e-kad’e da bushe-bushen da suka game garin Yemel a auren Mowar Sarki da ‘yar Sarkin K’aryatun Ni’am shaida ne a kan haka. Zamantakewar Malam Na-Bakin-Kogi da Sarkin Zagi da iyalansu wani manuni ne ga auren soyayya. An gabatar da matsalar kwartanci da zina domin a fito da hoton auren dole da aka yi wa yarinyar da ta gayyaci Imam da Zurk’e gidan mijinta. Mutuwar aure da sakin aure da zaman gwauranci duk sun taka rawar gani ga nishad’antar da mai karatun littafin.

 

HAIHUWA:


Ko itace da tsirrai aka d’aura wa aure buk’ata su samar da ‘yan’yan da za a yi amfani da su.[xxxix] Tubalin haihuwa wani babban tubali ne a matakan rayuwar Bahaushe. Turakun manyan babukan littafin a kan tubalin aka gina su. Wajen yunk’urin warware k’unshiyar tubalan, haihuwa ta taka rawar a zo a gani. A tunanin Bahaushe, haihuwa haske ce, rashin haihuwa duhu ne, mai kashe gida, ta turbud’e tarihin zuriya, da saka bak’in ciki ga mai shi, da danginsa.[xl] Tunanin Bahaushe a kowane sassan adabinsa ‘ya’ya na da babban kaso a kayan cikinsa da sak’onnin da ke tarshe ciki. Idan aure na da muhimmanci, to haihuwa tana gaba da shi. Dalili kuwa shi ne, idan dai sai da aka haihu aka yi aure. To! Wad’anda suka yi aure yaya aka same su? Babban dalilin kowane aure shi ne haihuwa, domin da an rasa haihuwa tarihin aure ya kawo k’arshe.[xli] Wannan matakin rayuwar ya taka muhimmiyar rawa ga gina littafin Ruwan Bagaja da fito da hazak’ar murubucinsa.

Idan ana biye da zaren tunanin wannan takarda, za a ga babi na farko Abubakar Imam ya ambaci mahaifinsa babban malami ne ya ce:

Sunansa Malam Na-Bakin-Kogi. Sai da ya kai dattijo har ya tsufa ba a ta’ba ‘bari ba gidansa.

(Ruwan Bagaja: Babi na 1, shafi na 3, sakin layi na 1).

 

Sanin darajar haihuwa da irin k’imarta a rayuwa ya sa aka fara aza harsashen littafin da ita. Rashin samun ta shi ya ambata da: “Ba a ta’ba ‘bari ba gidansa.” Rashin samun ‘bari ga mai mata fiye da d’aya (hud’u) irin Malam, wata shaida ce ta nuna matsalar daga gare shi take. Duk da yake malami ne, ba a nuna ya yi wani yunk’uri na samun waraka ga matsalar ba. Haka su ma matan, ba su yi wani yunk’uri ba.[xlii] Duk wannan na daga cikin fasahar jan zaren tunanin marubuci. Domin nuna martabar haihuwa sai aka ce:

Amma ko da shi ke malamim nan ba shi da d’a nasa na cikinsa, yana da wani agola, shaid’ani, ana kiransa Sak’imu.

(Ruwan Bagaja: Babi na 1, shafi na 3, sakin layi na 1).

 

Kawo zancen “agola” fito da matakin rayuwar Bahaushe ne na haihuwa.[xliii] An auro mai yaro domin fatar a sami haihuwa. Saboda ta ta’ba haihuwa, an zo da ita gidan, ko ba ta haihu ba, a rik’a yaronta kamar d’a. Da wannan tunanin aka gina fasahar littafin gaba d’aya.[xliv] Da za a cire Sak’imu da dukkanin muradin marubucin an salwantar da shi. Haka kuma, labarin wannan agola shi ne mataki na farko na sak’on littafin Ruwan Bagaja.

Mataki na biyu na sak’on shi ne, rashin lafiyar Yarima d’an sarki. Abin da ya muhimmintar da wannan rashin lafiya shi ne kasancewar Yarima d’an sarki ne. Da yaron sarki ne ko bafadensa ko d’an mak’wabcinsa ko wani basarake daga cikin sarakansa, wanda ba d’an tsatsonsa ba, da abin bai kai haka ba.[xlv] Ai saboda tsananin damuwar sarki na d’ansa ba ya da lafiya ya sa ya ci mutuncin Limaminsa. Cin fuskar da aka yi wa Liman ita ce mafarin fafitikar neman Ruwan Bagaja. Ga yadda aka tubka zaren fasahar:

Wai don yau ana cikin fadanci, Sarki ya ce d’ansa Yarima ba ya da lafiya, sai an kwantar a tayar. Ni kuwa na ce da za a sami Ruwan Bagaja a wani gari, da mutanen garin nan duk sun huta da masassarar zamani.

Daga wai na fad’i ‘yar wannan, sai sarki ya harzuk’a, ya ce wai ba’a ce nake jan shi da ita. Ya ce wai in ba shegantaka ba, da shak’iyancin da na saba, ina na ta’ba ganin wanda ya sami Ruwan Bagaja a duniya?

(Ruwan Bagaja: Babi na 1, shafi na 5 sakin layi na 7 – shafi na 6, sakin layi na 1).

 

Duk wata wahala da aka shiga ta neman Ruwan Bagaja wannan ne musabbabi. Duk wasu gutsattsarin labarai da aka ci karo da su a fafitikar kai-da-kawon manyan taurari da k’ananan, wannan ne dalili. Duk wani sak’o, da fasaha, da azanci da marubucin littafin ya sarrafa a kan wannan dalili ne.

Warwarar jigon littafin Ruwan Bagaja ba za ta yi armashi ba, idan ba a laluba babi na bakwai ba. A babin aka kakka’be wundin karatun arangamar manyar taurarin littafin Imam da Malam Zurk’e. Bayan sun tuba a nan Alhaji ya kashe wansa. Da wannan kisan kan aka kai ga samun biyan buk’ata (d’ebo Ruwan Bagaja). Ga d’an abin da nake son a kula:

Wata rana ne yana cin goriba da dare, sai ya ‘yar da k’odagon da ya gama ci. Ashe an zo da jinjirin d’an Sarkin Aljannu wurin su yi wasa. Abin k’addara sai k’odagon ya bugi kan d’an Sarkin Aljannu d’aya a mad’iga ya fad’i ya mutu. Shi ya sa aka d’auko shin an da nan a halaka shi. (Ruwan Bagaja: Babi na 7, shafi na 36, sakin layi na 4).

 

Haihuwa muhimmanci gare ta ga kowa. Dubi cikin rashin sani aka kashe jinjirin amma Iskoki suka d’au fansa nan da nan. Da ba don k’addarar kashe jinjirin d’an Sarkin Aljannu ba, da samun takobin da za a samu Aljanin da zai kai Imam ga Ruwan Bagaja ba ta yiwu ba. Dukkanin k’unshiyar littafin Ruwan Bagaja, idan ba  a kai ga nasarar samo Ruwan Bagaja ba, ba a yi komai ba an raki bak’o ya dawo.[xlvi]

Gabanin a kai Imam ga Ruwan Bagaja, duk fad’i tashin da ya yi, ba a ba su muhimmanci ba. Da martabar girmama haihuwa aka yi masa sakayya.[xlvii] Abin da ake son wanda aka haifa ya yi, shi Imam ya yi wa wanda ba shi ya haife shi ba, don haka aka saka masa da alheri. Dubi wannan:

Lallai ka cika d’a, tun da ka sai da ranka don uban wani. (Ruwan Bagaja: Babi na 8, shafi na 37, sakin layi na 4).

 

Haka kuma, kyautata wa jinjirin Aljana da uwar Liman ta yi shi ya sa su abota, har Imam ya shigo cikin wannan alfarmar ya ci nasara. Manazarci al’ada bai yi kure ba idan ya ce, mataki na biyu na daidaita k’unshiyar littafin Ruwan Bagaja shi ne matakin rayuwa na biyu, wato haihuwa. Da an bar matakin rayuwa na aure shi kad’ai, da hoton littafin bai fito sosai ba. Da aka kawo matakin haihuwa sai abin ya k’yallaro zukatan masu karatu sosai. Duk da haka, ruhin littafin ba zai bayyana k’arara ba idan ba a waiwayi matakin rayuwa ta uku ba, wato mutuwa.

Bahaushe ya d’auki haihuwa da muhimmancin gaske. Don haka, da wuya a tantance, shin d’a ya fi son mahaifi ko mahaifi ya fi son d’a? Da aka yi harsashen gina zaren tunani da rashin haihuwa, tubali na farko da aka fara gina da shi, shi ne agola. Abin da ake so ga d’a ya zama mai jink’ai da tausayi ga iyaye. Da aka fara gini da shak’iyin agola daga k’arshe aka zo da nagartaccen agola da ya yi abin da ake son d’a ya yi. Da jink’ayin da iyaye ke yi wa ‘ya’ya aka ci nasarar samun Ruwan Bagaja. Haka kuma, da zaren tunanin haihuwa aka gama Sak’imu da ajalinsa kamar yadda malaman duba suka dubo masa. Cikin tsanaki haihuwa ta hana zaren tunanin marubucin tsinkewa yadda aka bud’e da ita, da ita aka kammala.

 

MUTUWA:

A wajen manazarta al’ada, duk fafitikar da masu rai ke yi a duniya, mutuwa ake yi wa ita. D’an’adam ya k’irk’iro noma domin ya yi wa yunwa barazana.[xlviii] Idan aka k’i noma aka sa wa yunwa ido za ta yi aikinta. Dukkanin yak’e-yak’en da mutanen duniya ke yi, ana yin su ne domin kariya ga abin da ke son yi wa rayuwa barazana.[xlix] Duk tattalin arzikinsu na inganta rayuwarsu ne.[l] Duk tanaje-tanajensu na yi wa rayuwasu kariya ne.[li] Tsananin fasaharsu, da ilminsu, na gano abubuwan da za su ciyar da rayuwarsu gaba ne. Tsarin siyasun rayuwarsu na nema wa zamantakewarsu zaman lafiya ne.[lii] Zaman lafiya kuwa muradinsa rayuwa ta samu sakewa ta wartsake, ta shak’ata, ta yi kamar ba ta mutuwa.[liii] Duk da haka dai, k’arshen kowace rayuwa mutuwa.[liv]

Bisa mizanin al’ada, mutuwa gado ce ga kowane mai rai.[lv] Don haka, tunanin kowane mai rai a zantukansa na baka da rubuce-rubucensa da addninsa mutuwa ke shawagi a ciki.[lvi] Duk da yake ba a son ta, ba a k’aunar ta, ana k’yamar ta, amma dole a tuna da ita. Tuni da ita ke sa a ke’be mata nata gurbi a tunanin masu rayuwa. A k’unshiyar littafin Ruwan Bagaja, da ba a ke’be wa mutuwa babban kaso ba, da kashi ya game, dole a sake rabawa.

Zancen Sak’imu da Malan Na-Bakin-Kogi su ne harsashin ginin k’unshiyar littafin. Babban sak’on da ke k’unshe ga matsalar da Malam Na-Bakin-Kogi ke ciki shi ne:

Ga wagagen littattafai tuli, ba mai gado.

(Ruwan Bagaja: Babi na 1, shafi na 3, sakin layi na 1).

 

Tunanin ana mutuwa ke kawo zancen mai gado. Ga al’ada da addini, ba a gado sai wanda aka gada ya kau (mutu).[lvii] Tunanin za a mutu babu mai gado ya sa aka auro uwar Sak’imu, gudun ka da littattafai su sha k’urar banza.[lviii] Kashe Malam Na-Bakin-Kogi shi ne silalin farko na zaren tunanin littafin. Bayan kisan gillan da Sak’imu ya yi wa Malam bai firgita ba, sai da ya ga mutuwarsa a fili kamar haka:

… Sak’imu ya yi mafarki, ya ga malamin a tsaye. Sai ga wani d’an abu kamar d’an dabino, ya fito daga zakarin malamin. Sai ya ga abin nan yana ta girma har ya kai kamar zaki. Da ya kai haka sai abin ya fad’o masa ya kashe shi.

(Ruwan Bagaja: Babi na 1, shafi na 4, sakin layi na 2)

 

Gaskiyar Hausawa da ke cewa, wanzam ba ya so a jikinsa. Ina laifin masu azancin magana da ke cewa, mutuwa kashe mutane ki mutu? Duk a cikin mafarkin nan, Sak’imu abubuwa biyar ya gani: malam na tsaye, da zakarinsa, da wani abu kamar dabino, da girma kamar zaki, da mutuwa. Mutuwar nan ita ta firgita shi. Ashe idan manazarci al’ada ya ce, da matakin rayuwa na uku (mutuwa) aka shimfid’a zaren sak’ar azancin littafin Ruwan Bagaja bai yi kuskure ba.

Matakan da Sak’imu ya d’auka na kauce wa mutuwa, su suka ba da k’unshiyar littafin da sakamakon da aka samu. Mataki na farko da aka d’auka sai ga mutuwa ta fito k’uru-k’uru:

Da gari ya waye, ya tara malamai don su yi masa duba.

Dukan malamai, kowa ya duk’ufa ya zana ya shafe, ya zana ya shafe. Daga nan sai babban su ya ce, za a haifi wanni yaro a gidan nan, cikin matan tsohon nan da ya rasu shi ne zai kashe ka.

(Ruwan Bagaja: Babi na 1, shafi na 4, sakin layi na 2 – 3).

 

K’ok’arin da Sak’imu ya yi na ku’buta daga tarkon matakin rayuwa na k’arshe (mutuwa) ya sake haifar da wata mutuwar kamar haka:

Abin da ya fi kyau sai in halaka matan hud’u duka masu  takaba, don ka da maganar masu dogwayen geman nan ta zama gaskiya.

Saboda haka ya samu guba, ya yi ta ba su d’ai d’ai suna mutuwa ana cewa bak’in cikin rabuwa da malamin nan ne ya kashe su.

(Ruwan Bagaja: Babi na 1, shafi na 5, sakin layi na 1 – 2).

 

A nan aka rufe shafin matan liman uku. Da ana son a ci gaba da k’ulla zaren tunanin gaba tare da mahaifiyar Imam, aka nuna ita ba ta gidan, tana garin iyayenta wani k’auye can na daban. Duk da haka, sai da aka aika mata nata manzon mutuwa da dokinsa. Aka ba shi damar isa gare ta, ya d’auko ta kan doki, ya shiga daji da ita. Ga yadda aka ruwaito:

Ya aza ta kuturi, ya yi dawa da ita. Ya yi ta kutsa daji da sukuwa, har kusan asuba, sa’annan ya tsaya. Ya d’auki takobi zai kashe ta, sai ya taka wutsiyar wani kumurci, ya sare shi. Nan ya fad’i ya mutu. Doki ya yi dawa da gudu! (Ruwan Bagaja: Babi na 1, shafi na 5, sakin layi na 2).

 

Ku’butar da mahaifiyar Imam ga mutuwa da mutuwar ‘barawon mahaifiyarsa su ne tubalin ginin k’ashin bayan littafin Ruwan Bagaja. Da ba a k’addaro da kumurci ya kashe bak’in bawan nan ba, da shi zai kashe mahaifiyar Imam. Da ya kashe ta, da zaren labarin ya tsinke daga nan. Ku’butar da ita da cikin wata uku shi ya k’addaro zuwan Imam duniya har ya nemo fansa ga muzanta mijin mahaifiyarsa da aka yi. Da wannan aka gina gutasttsarin labaran babi na farko. Zaren labaran ya kai babi na biyu. A babi na biyu, da ana son a sake jan zaren fasaha sai aka kawo had’uwar Imam da K’wara. A had’uwar, da mutuwa aka yi garkuwa. Mutuwar k’arya ta K’wara ita ta ja tsawon gutsattsarin labarai na babi na biyu har aka shiga babi na uku.

A babi na uku, da ana son a d’inke shi sosai, sai aka kawo zancen mutuwa tsakanin Imam da Zandoro d’an Zotori. Ya zo yana yawo da sa yana cewa:

Wa zai amshi sana, in an yi kwana bakwai in zo ya ta’bo kaina?

(Ruwan Bagaja: Babi na 3, shafi na 16, sakin layi na 6).

 

Daga cikin sharud’d’an da ya bayar su ne:

Ya kuwa riga ya ce in na kasa, zai yanka ni, ya ba gunkinsa jinin.

(Ruwan Bagaja: Babi na 3, shafi na 16, sakin layi na 7).

 

Ashe da mutuwa aka yi garkuwa a nan, kuma ita ce ta jawo hankalin ‘yan kallo su zo su ga yadda za a kwashe.

Had’uwar manyan taurari a garin Hindu da mutuwa aka ja zaren labaran. Bawan sarki da aka kashe, Malam Zurk’e ya kai gawar gidan Imam. Imam ya zuk’e, Zurk’e ya kwan ciki ya d’and’ani kud’arsa. Wannan ta sa, Imam gudu ya bar gari, labari ya kai babi na hud’u. Gutsattsarin labaran da suka biyo baya ‘yan rakiyar labarin gawa ne, har labarin ya kai babi na biyar.

A babi na biyar, da mutuwar matar sarkin zagi aka gina shi. Bayan da aka magance haukar kewar da ta kama Sarkin Zagi, kunyata Sarkin Zagi ya sa Imam barin garin Tegi. Gabanin ya kwashe kayansa da mutuwa aka yi korar fagen babin. A gidan da Imam ya sauka, mai masaukinsa ya kashe ‘barawo. Imam ya samo kulkin da ya kaura wa mummuk’en Sarki Zagi yana barci. Da wannan dabarar gawa da mummuk’en Sarkin Zagi, Sarkin Zagi ya shiga kurkuku shekara d’aya.[lix] Barin k’auyen ke da wuya, aka sake k’ulla zaren labarin da mutuwar wani bak’auye da d’an’uwansa yana cewa:

Ina yawo rannan cikin daji sai na ga wani bak’auye na fad’a da d’an’uwansa. Ina kawowa sai na ga guda ya sa kulki ya fyad’e guda ya mutu.

(Ruwan Bagaja: Babi na 5, shafi na 24, sakin layi na 4)

 

Da wannan gawar aka had’a Malam Zurk’e da matarsa fad’a da rantse-rantse wanda sanadiyar haka Zurk’e ya yi layar zana ya gudu ya bar garin. Da labarin ya kai babi na shida, a garin Nasarawa da mutuwa aka shimfid’a wundin karatu. Dalili kuwa, mutuwar ‘yar sarki ya sa aka tabbatar da walittakar Imam.[lx] Bayan abubuwan da ke faruwa sun faru aka shiga babi na takwas.

Babi na bakwai, da mutuwa aka yi masa matashiya cewa: TUBAN ALHAJI DA MALAM ZURK’E, ALHAJI YA KASHE WANSA. Duk abubuwan da suka biyo baya cikon sunna ne makaho da waiwaye. A babi na takwas aka nad’e littafin domin a nan ne buk’ata ta biya. Yadda duk al’ada ke kallon mutuwa haka nan aka sarrafa ta a gutsattsarin labaran littafin. An kawo mutuwa ta kisan gilla da gangan.[lxi] An kawo ta k’addara.[lxii] An kawo ta rashin sani.[lxiii] An kawo ta sakayya.[lxiv] An kawo ta tsafe-tsafe.[lxv] An kawo ta k’arya.[lxvi] An kawo ta al’adar rashin lafiya ko tsufa.[lxvii] An kawo ta sunu.[lxviii]

 

SAKAMAKON BINCIKE:


Muradina in fito da wata mazhabar al’ada da ya kamata a dinga kula da ita idan ana nazari da tarken adabi. Nazarin wannan littafin ya gano wurare fiye da hamsin (50) da aka sarrafa matakan rayuwar Bahaushe domin isar da sak’on littafin Ruwan Bagaja. A gurguje an sarrafa matakan aure kamar hake:

 1. Imam da mahaifinsa.

 2. Malam Na-Bakin-Kogi da matansa hud’u.

 3. Auren mahaifiyar Imam da Liman.

 4. Auren Mowar Sarki.

 5. Auren Zurk’e da matarsa.

 6. Auren Jamilatu ‘yar Malam.

 7. Auren da aka yi wa wata yarinya na dole.

 8. D’an Sarki da iyalansa da aka washe wa masai.

 9. Sarkin Zagi da matarsa da ta mutu.

 10. Zurk’e ya rabu da matarsa mafad’aciya.

 11. Matar Sarkin Aljannu.

 12. Matar Imam da ta yi buk’atar ganin iyayenta aka murza zobe.

 13. Auren uban Sak’imu da mamarsa gabanin ta fito gidan.


 

Idan aka waiwayi matakin rayuwa na biyu (haihuwa) za a ga abubuwa kamar haka:

 1. Rashin haihuwar Malam Na-Bakin-Kogi.

 2. Agola Sak’imu.

 3. Haihuwar Alhaji a gidan Liman.

 4. D’an Sarkin Aljannu jinjiri.

 5. Mowar Sarki da ‘yar Sarkin K’aryatun Ni’am.

 6. Yaron Zurk’e Armi.

 7. D’an Sarkin Aljannu da mahaifiyar Liman ta ba ruwa.

 8. Yaron da ya ba Imam labarin auren Mowar Sarki.

 9. Fad’ar Imam na cewa “Yara sun ‘bata gidan da miya.”

 10. ‘Ya’yan Sarkin Aljannu da suka kamo Sak’imu.

 11. Yasifi d’an

 12. Iyayen mahaifiyar Imam da ke wani k’auye.

 13. ‘Yar Sarki da aka je jana’iza.


 

A ‘bangaren matakin rayuwa na uku (mutuwa) muna da:

 1. Mutuwar Malam.

 2. Mutuwar Matan Malam uku (3).

 3. Mutuwar d’an samame (‘barawon mahaifiyar Imam).

 4. Mutuwar ‘yar Sarki.

 5. Mutuwar K’wara ta k’arya.

 6. Kashen wan Liman.

 7. Kashe d’an Sarki Aljannu.

 8. Zakin da ya kashe Sak’imu a mafarki.

 9. Fad’ar malaman duba za a kashe Sak’imu.

 10. ‘Barawon da ya kashe bafaden sarki.

 11. Mai masaukin Imam da ya yi kisan kai.

 12. Bak’auyen da ya kashe d’an’uwansa.

 13. Fad’ar Sarki ga zargin da ake yi wa Zurk’e “ku buge shi sai ya mutu.”

 14. Mutuwar Matar Sarkin Zagi.

 15. Imam ya zama mutuwa.

 16. Fad’ar Zurk’e cewa da bai rabu da matarsa ba ta sa an kashe shi.

 17. Fad’ar Imam a d’akin samarin da ya yi wa sata “Wayyo ya kashe ni!”

 18. Fad’ar Sarkin Zagi cewa da shi mutuwa ta d’auka ba matarsa ba.

 19. Fad’ar Imam cewa na k’wak’wata rairayi na shiga. Na yi na yi in mutu.

 20. Fad’arsa “Ina nan cikin ramin nan ina jiran mutuwa.”

 21. Fad’arsa na “Kafin a zo a kashe ni na rama wa baba.”

 22. Fad’arsa na cewa: “Na yi kamar in ce masa ya kashe ni don in huta da azaba…”

 23. Yasifi d’an Nuhu har ya k’aura.

 24. Fad’ar Sarkin Aljannu: “… ka kashe mini wanda ya kashe d’ana!”

 25. Fad’ar Sarkin Aljannu “In ka d’ebo da yawa ka halaka.”

 26. Fad’ar Sarkin Aljannu ga Imam: “Ka kuru da sun kashe ka!”

 27. Fad’ar Sarki ga Yarima “…mun fi so ya mutu ma yanzu ya huta.” (Ya kashe ‘barawo).


 

Aure ya taka rawa sau goma sha uku (13). An sarrafa haihuwa sau goma sha uku (13). Mutuwa ta kafa turaku ashirin da bakwai (27) a sak’on littafin. Wace rawa aka taka ba da su ba a littafin Ruwan Bagaja?

 

NAD’EWA:


Na tabbata kowane masani ya d’auki alk’alaminsa ba zai rasa abubuwan da zai harara ba na fanninsa a cikin littafin Ruwan Bagaja ba. Duk da haka, kasancewar marubucin mutum mai rai, Bahaushen k’asar Hausa dole a samu nason rayuwarsa a ciki. Da za a tambayi marubucin yadda ya gina zaren tunaninsa na rubuta gawurtaccen littafin da ya yi wa tsara fintinkau! Da wuya ya ambato matakan rayuwar Bahaushe. Don haka d’aliban al’ada muke cewa, mutum ba zai iya yin wani tunani wajen al’adarsa ba. Dole kowane mutum ya yi tunani irn na mutane ko dai irin na al’ummarsa ko irin na wasu. Haka kuma, a kan kowace al’umma zai rayu ko ya rayu, tunaninsa ba zai tsallake matakai uku ba: aure; haihuwa; mutuwa. Rubutun kowa ko fasahar kowa aka d’ora kan wannan falsafar al’ada za a tabbata wurin da babu k’asa ake gardamar kokuwa. Gwargwadon k’wazo da hazak’a da basirar mutum na sarrafa wad’annan matakan a tunaninsa, gwargwadon yadda ayyukansa ke shiga jikin mutane. A fahintata ta d’alibin al’ada, marubucin littafin Ruwan Bagaja k’wazonsa na sarrafa wad’annan matakai na rayuwa a littafinsa, shi ya ba shi nasarar cinye gasar kai tsaye. Tabbas wanda duk bai kalli littafin Ruwan Bagaja a kan wad’annan matakai ba, a karkace ya dube shi, ya sake duba ya gani.

 

https://www.amsoshi.com/2017/11/04/agitation-dialogue-hausa-fulbe-encounters/

MANAZARTA


Abdullahi, A. M. 1998. “Abubakar Imam: Nazarin Tubali da Ginuwar Ayyukansa na Adabi.” kundin digirin PhD, Kano: Jami’ar Bayero.

Abdullahi, B. H. 1981. “Kwatanci Tsakani Salon Ruwan Bagaja da kuma Nagari Nakowa.” cikin D’agel Journal of Faculty of Arts and Islamic Studies, Sokoto: University of Sokoto.

Bunza, A. M. 1991. “Sharhin Ciki da Wajen Littafin Ruwan Bagaja.” Muk’ala - Makon Hausa, Sakakwato: Jami’ar Usmanu D’anfodiyo.

Bunza, A. M. 2006. Gadon Fed’e Al’ada. Lagos: Tiwal Nig. Ltd.

Daura, R. M. 1996. “Jirwayen Al’adun Hausawa cikin Littafin Ruwan Bagaja.” kundin digirin BA, Sakkwato: Jami’ar Usmanu D’anfodiyo.

Elias, T. O. 1957. “Hausa Marriage in Nigeria.” A K’uarterly Magazine of General Interest. No. 53, Lagos: Federal Government of Nigeria Eshibition Center, Marina.

Garba, A. 2002. “A Stylistic Study of Hausa Classical No’bels: Shaihu Umar , Ruwan Bagaja and Kitsen Rogo.” PhD thesis, Kano: Bayero University.

Guga, S. B. 2010. “Hoton Sarauta a Cikin Littafin Magana Jari Ce na Abubakar Imam.” kundin digirin MA, Zariya: Jami’ar Ahmadu Bello.

Gwarzo, Y. T. da wasu 2005. Aure a Jihar Katsina. Katsina: Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al’adu.

Hassan, S. 2013. “Nazari a kan Mutuntaka da Adabi: Tasirin Abubakar Imam a Magana Jari Ce.” kundin digirin PhD, Zariya: Jami’ar Ahmadu Bello.

Ibrahim, M. S. 1985. Auren Hausawa: Gargajiya da Musulunci. Zariya: Hausa Publication Center.

Imam, A. A. 1966. Ruwan Bagaja. Zaria: NNPC.

Imam, A. A. 1978. (Ruwan Bagaja) The Water of Cure. Zaria: NNPC

Kafin-Hausa, A. A. 1985. “Nazarin wasu daga Rubuce-rubucen Marigayi Abubakar Imam.” Muk’ala, Zariya: Sashen Harsunan Nijeriya da Afirka.

Madauci, I. da wasu 1968. Hausa Customs. Zaria: NNPC.

Magaji, A. 2002. “Wasu Al’adun Hausawa: Yanaye-yanayensu a K’asar Katsina.” kundin digirin PhD, Kano: Jami’ar Bayero.

Mairukubta, H. 1999. “Jego da Reno a K’asar Hausa: Tsokaci kan Hausawan Kabi.” kundin digirin MA, Sakkwato: Jami’ar Usmanu D’anfodiyo.

Malumfashi, I. A. M. 2005. “Kama da Wane ba Wane ba! Kakka’bo Littafin Ruwan Bagaja daga cikin Taskar Adabi.” cikin Birniwa, H. A. da wasu (editoci) D’und’aye Journal of Hausa Studies. ‘Bol. 1. No. 2, Sakkwato: Jami’ar Usmanu D’anfodiyo.

Malumfashi, I. A. M. 2009. Adabin Abubakar Imam. Sokoto: Garkuwa Media Ser’bices.

Mora, A. 1985. “Wani ‘Bangare daga Tarihin Rayuwar Marigayi Alhaji Dr. Abubakar Imam da Aikace-aikacensa Daga 1911-1981.” Taron K’ungiyar Ha’baka Hausa, Zariya: Jami’ar Ahmadu Bello.

Mora, A. 1989. Abubakar Imam Memoirs. Zaria: NNPC.

Nyamwaya, D. and Parkin, D, 1987. Transformation of African Marriage. United Kingdom: Manchester University Press.

Ottenberg, P. and Simon (ed) 1960. Cultures and Ethics of Africa. USA: H. Wolf Book Mtg. Con., Inci.

Pweddon, N. 1977. “Thematic Conflict nad Narrati’be Technik’ue in Abubakar Imam’s Ruwan Bagaja.” PhD thesis, Madison: University of Wisconsin, USA.

Sallau, B. A. 2011. “Rad’a Suna Jiya da Yau.” Cikin Himma Journal of Contemporary Hausa Studies. Katsina: Umaru Musa ‘Yar’aduwa University.

Sarkin Sudan, I. A. 2008. “Jiya Ba Yau Ba: Waiwaye a kan Al’adun Matakan Rayuwar Maguzawa na Aure da Haihuwa da Mutuwa.” kundin digirin PhD, Sakkwato: Jami’ar Usmanu D’anfodiyo.

Smith, M. G. 1957. “The Hausa System of Social Status.” In Africa. ‘Bol. d’d’’bii. No. 1

Tambuwal, M. S. 2001. “Mutuwa a Idon Bahaushe: Nazari daga wasu K’agaggun Labaran Hausa.” kundin digirin BA, Sakkwato: Jami’ar Usmanu D’anfodiyo.

Temple, C. L. (ed) 1965. Notes on the Tribes, Pro’binces, Emirates and States of the Northern Nigeria. London: Frank Cass and Company Ltd.

Tra’bitt, L. 1973. “Attitudes and Customs in Childbirth Amongst Hausa Women in Zaria City.” Sa’bana. No. 2 ‘bol. 2, Zaria: Ahmadu Bello University.

Umar, M. B. 1980. Al’adun Haihuwa a K’asar Hausa. Zariya: Hausa Publication Center.

Umar, M. B. 1987. Dangantakar Adabi da Al’adun Gargajiya. Kano: Triumph Publishers.

Usman, M. 1998. “Tarsashin Adabin Baka a Magana Jari Ce.” kundin digirin MA, Zariya: Jami’ar Ahmadu Bello.

White, H. 1980. “Literature and Social Action: Reflection on the Reflection Theory of Literary Art.” New Literary History. ‘Bol II, No. 2. The John Hopkins University Press.

Yahaya, I. Y. 1989. “The Literary Works of Alhaji Abubakar Imam in Perspective.” Harsunan Nijeriya d’i’b. Kano: Bayero University.

Yunusa, M. M. 1985. “Kasancewar Tatsuniyar Ruwan Bagaja Tushen Littafin Ruwan Bagaja na Dr. Abubakar Imam.” kundin digirin BA, Sakkwato: Jami’ar Sakkwato.

[i] Don samun cikakken bayani a dubi: N. Pweddon, 1977, “Thematic Conflict and Narrati’be Technik’ue in Abubakar Imam’s Ruwan Bagaja, un published PhD, University of Wisconsin – Madison.

[ii] Na yaba da aiki ak’alan, don haka nake son in tabbatar da gwarzonsa ya yi gwarzo a ko’ina za a gwaje shi, musamman idan aka d’ora alk’alancinsu a kan faifan al’ada.

[iii] A zamaninmu da ilmi ya kai k’ololuwar bunk’asa har yanzu ba a samu littafin da ya dushe hasken littafin Ruwan Bagaja ba. Buk’atarmu a sake nazarin k’unshiyarsa, na baya su ga k’wazon na gaba. Haka kuma, a bi wannan salon ga nazarin sauran sassan adabi domin a ciyar da ilmi gaba gwargwadon ci gaban zamaninmu.

[iv] Yau, ina nufin shekarar 2013, da littafin ya share shekara tamanin a duniyar bokon arewacin Nijeriya. Kamata ya yi a ce an yi tunanin irin wannan aiki tun shekarar 1983 da ya cika rabin k’arni.

[v] Takardun da za a samu a kan wannan bincike su za su tabbatar da wannan hasashe nawa. Cikin harsunan Nijeriya, babu mai rubutaccen adabin da zai iya gwada tsawo da na Hausa. Da manazarta Hausa sun sa himma da yanzu an wuce haka.

[vi] Na tabbata da lauyoyi da masana walwala da tarihi da tattalin arziki da kiyon lafiya da addini da harsuna da ilmi da kimiyya da falsafa, kowannensu na da ta cewa a littafin. Wannan ya nuna, tunanin da ke k’unshe cikin littafin sun zarce na shekarun marubucinsa, a lokacin da ya rubuta shi yana d’an shekara ashirin da hud’u (24). Wannan ya nuna tunanin mutanen k’arnin da ya gabace mu ya fi namu kaifi da fasaha da hangen nesa. Ta tabbata da tsohuwar zuma ake magani.

[vii] Ban ga wani aiki da aka ta’ba yi a Hausa da ya gabaci wannan ba. Don haka, wannan zakaran gwajin dafi ne. A taya ni gyara, ba ni na kashe zomo ba rataya aka ba ni.

[viii] Da haihuwarsa yana yaro, sai ya girma ya zama saurayi in ya balaga ya yi aure ya zama mutum. Yin aure ya sa ya hau mataki na d’aya. In ya haihu ya shiga mataki na biyu. In ya mutu ya shiga na uku da ba a sake wani mataki bayan shi.

[ix] Har yanzu masana ba su kai ga matsayin shin aure aka fara yi ko haihuwa? In aure aka fara, wa ya haifi wad’anda suka yi auren? In kuwa haihuwa aka fara, ta wace fuska aka haihu? Ga su nan dai!

[x] A addinin Musulunci da Kirista da na Yahudu, an aminta da Adamu da Hawwa’u su ne mutane na farko. Alk’ur’ani ya ce, daga hak’ark’ari (awwazun) Adamu na k’asa aka halicci Hawwa’u.

[xi] A kimiyya da al’ada, ana k’ok’arin a kore addini a halittar mutane. Mr. Darwin ya fara hasashen daga birai aka fara har aka waye aka koma mutane. Wannan tatsuniyar an shara ta cikin Tarikh ‘bol. 1, No. 3.

[xii] Ba za a ta’ba haihuwar mutum da mata su zo duniya tare da d’aurarren aurensu. Haka, ba za a haifi mutum tare da mutuwa ba. Sai dai ta riske shi a cikin ciki, ko lokacin da zai fad’o, ko bayan ya fad’o duniya. Don haka d’aliban al’ada muke son a yi nazarinsu a rarrabe kamar yadda aka san su a rarrabe.

[xiii] Da an yi aure, haihuwa za a sa wa gaba gadan-gadan. Cikin haife-haife ma’aurata ke tsufa a fara tunanin barin duniya.

[xiv] Matakan rayuwarsu irin na Bahaushe ne babu wani bambanci. Alfu lailatan wa laila. Da Muk’aamatul Hariiri. duk a kan matakan rayuwa aka gina su. Masu ganin a can fahintar ta samo asali, to su san da cewa, ko a can bisa ga matakan rayuwar masu adabin aka gina k’issoshi kuma Imam ya sarrafa su a matakan rayuwar Bahaushe.

[xv] Masu ganin daga tatsuniyar Ruwan Bagaja aka ciro shi, sun yi canjaras! Dalili kuwa babu tatsuniyar Bahaushe da ba ta hawa a kan matakan rayuwarsa. Don haka, wak’a d’aya ce ake rerawa da muryoyi daban-daban.

[xvi] An ce, wannan tak’addama ta ta’ba aukuwa a kacici-kacicin Bahaushe da ke cewa: Da k’wai da kaza wa ya riga wani zuwa duniya? In ka ce, “k’wai” a ina ya fito? In ka ce, “kaza” a ina ta fito? An ta’ba tabka irin wannan muhawara tsakanin Sarkin Gardi K’yank’yashe na Giwa-ta-zo da Sarkin Sarkin Gardi Bela na k’asar Argungu. K’yank’yashe ya fara kirari ya ce:

K’yank’yashe:  Ai sai an kai ga k’yank’yashe

:Sannan bela ka bayyana!

Bela ya yi kuwwa ya ce:

Bela:                 Sai bela ta ci ta wuce

:Sannan aka kai ga k’yank’yashe

Gindi:               Sa maza gudu

:Sa arna sake shawara

[xvii] Dole sai sun aminta su kwanta tare aure ke tabbata.

[xviii] Idan za a aurar da icen mangoro ko gwaba sai an dasa wani cikin wani. Idan dabino ne, sai an buga masa kilili. Had’a su da ake yi tare, d’aya ya yi barbarar d’aya shi ne aure na itace da tsirrai. Me ya bambanta wannan da auren ‘yan Adam in ba kad’e-kad’e da bushe-bushe da biki ba? Duk dai ma’anar a k’ara miya, ba a k’oshi ba.

[xix] Da an ga dabbobin daji mace da namiji tare babu tsangwamar juna an san mata da miji ne. In an ga d’a, a ce ga d’ansu, ko da kuwa na wani uba ne ba na wanda aka gani ba.

[xx] A wajen wasan dambe, idan an yi arangama an rungume juna, sai a ce an yi “amarya”. Ke nan, had’uwa a gama jiki, a rungume juna, ko don murna ko don soyayya ko don buk’ata ko don wata wuya ko wani abu can daban, shi ne aure a harshe. Auren duk da bai samu kai ga irin wannan matakin ba, ba aure ba ne ko a al’adance ko addinance.

[xxi] Wani motsattsen mutum ne da aka yi a zamanin Shaihu d’an Ziyazinu ana kiransa Koje Sarkin Labari. Haukarsa ba ta zagi ba ce, ba ta duka ba ce, ta jin labari ce da bayar da shi. (Ruwan Bagaja: Babi na 1, shafi na 1, sakin layi na 1). Duk da haka, a hak’ik’anin gaskiya, an yi wani mahaukaci a Katsina kimanin shekara d’ari da suka gabata mai suna Koje. Imam suna yara suna biyar sa da ‘yan wak’e-wak’e idan ya fito a kasuwa. Da yake ya tsufa k’warai tun a zamanin su Abubakar Imam dole a samu cikinsa cike da labarai mabambanta. Ga alama a wannan magarya ya d’aure akuyarsa.

[xxii] A al’adance, Bahaushe da ya fad’i sunan mahaifinsa ba a neman sunan mahaifiyarsa an dai san dole mace ta haife shi. Haka kuma, da an ji sunan uba, an san da aure aka haife shi. a al’adar Bahaushe, da uba ake kuri don haka suke cewa, kyawon d’an k’warai ya d’auko ubansa.

[xxiii] Da ya ci nasarar kasheta tana da cikin Imam na wata uku. Imam kuwa shi ya je ya samo Ruwan Bagaja. Da an kashe uwarsa yana ciki magana ta k’are. Mak’ok’o ya fito a bakin zabiya.

[xxiv] Nan ne Imam ya shiga shagalin aure sosai ka ce na d’iyansa na farin ne. Da haka ya samu shiga fada, har ta kai ko neman sarauta ake yi gare shi ake kamun k’afa.

[xxv] An cinye dukiyarsa ya so ya kama Alhaji Imam da wayo, Imam ya nuna, kamin ka ga biri, biri ya ganka. Da K’wara ya ce ya mutu, Imam na shakka. Da ya gan shi baki bud’e, sai ya ce, an ce, K’wara ba sa mutuwa baki bud’e. Halinka da wawa, sai ya rufe bakinsa. Nan Imam ya gane da lauje cikin nad’i, ya tsere.

[xxvi] Aka kar’be wa Bak’auye kud’insa, aka kai shi gidan Yari, wai, ya lak’a wa Imam (‘barawo) sata. Bak’auye bai k’are fursuna ba sai da Imam ya tarar da shi da wani laifi na sata, irin wanda ya lak’a wa Bak’auyen. Hak’ik’a ko bayan tiya akwai wata caca.

[xxvii] An zagi Fulani domin su zo a yi fad’a. Su ba su sani ba, mahaukacin rak’umi ya tsare masu zaginsu, mafita suke nema. Suna zuwa sai rak’umi ya ce, ga abokan fad’a, aka shiga yi wa iska adashi.

[xxviii] An nuna magafta suka yi masa asiri ya makafce domin ya kasa su ga auren Jamilatu ‘yar Malam

[xxix] Da ya makafce, ya sami wani yaro mai tsananin hak’uri wai shi ‘Armi’. Yaron ya rik’a yi masa jagora, saboda sabon makafta wuyan zama da shi. Ya dace da yaro mai hak’uri, komi aka yi sai ya yi damo.

[xxx] Zurk’e ya yi sanadiyyar ya fad’a kogi ya had’u da ‘yan ruwa. Daga nan aka shiga duniyar tatsuniya har aka kai ga samun nasarar d’ebo Ruwan Bagaja.

[xxxi] Domin an nuna yarinyar da Imam ya gani ya ce yana so, ta nuna ba ta da miji. Imam ya gano tana da miji, son sa ne ba ta yi. In haka ne kuwa, auren dole aka yi mata. Don haka take fita irin ta budare ba kamun kai neman wanda take so daidai da ita.

[xxxii] Yarinyar dai k’azama ce, bayan ta kira Imam, ashe ta gayyato Malam Zurk’e. Ga kuma miji tana da shi. Wane k’azanta ya fi haka? Tir! Da mugun hali na ‘bata mutunci da zuri’a.

[xxxiii] Idan Imam bai haukace ba, hukunci mai tsanani za a yi masa. Haukarsa ta k’arya ta sa aka ba shi sarautar Wawan Sarki. Fadar Katsina ta dad’e da Wawan Sarki. Watak’ila wannan ce ta yi naso ga rubutun Imam kasancewarsa d’aya daga cikin sarakunan Sarkin Katsina na lokacinsa.

[xxxiv] Kewar matarsa ya sa ya haukace bayan ta mutu. Hak’ik’a kusan kashi goma (10%) na mahaukata, za a ga tushen haukarsau daga mata ne. In dai sun kasa aure, ko an raba su da matansu ko matansu sun mutu ko an kar’be musu mata. Irin wannan hauka a Larabci ake cewa namiji mai ita Uutuu. A kanta ne aka gina shahararren labarin nan na Larabci “Majanun Laila”.

[xxxv] Al’adar Bahaushe ce ba a fad’a da matar aure sai dai a yi da mijinta. Dalili shi ne, wace d’aukaka k’ato zai samu idan ya yi fad’a da mace? Na yarda da makad’a Bawa D’an’anace da ke cewa:

Jagora:  Ka da ka kashe Na’ila wanzami na!

:Shi ka yo muna gyara

:Ka ga kashe Na’ila bai yi wuya ba

:Kamar a tunkud’e turmi

:Kamar mutum ya mari budurwa

Yara:                 Don ka mari macce ba garari ba

[xxxvi] Imam shigan mahaukata ya yi ya tsorata Malam Zurk’e. Duk da haka bai kamata namiji ya ji tsoron namiji ba har da kore wa kashin k’ato k’uda gaban uwar gida. Duk zamantakewar aure ce ake warware jigo da ita.

[xxxvii] Ya nuna matar ‘yar bala’i ce dole ya rabu da ita. Wannan shi ya ba ‘barayi damar su ziyarce shi domin sun san gidan na mutum d’aya ne, babu mai agaji in sun shiga da yawa. Ka ga ashe da aure aka yi garkuwa rashin sa ke sa a ce wa mutum gwauro.

[xxxviii] Wannan labari ya yi tasiri sosai a k’asar Hausa wajajen shekarun 1962 – 1980, ka ce shekarar abin ya wakana. Katsinawa su ce, Bakano ne ya yi haka. Kanawa su ce, Bazazzagi ne ya yi.

[xxxix] Da Bahaushe ya tabbata ko ya yi aure ba ya samun ‘ya’ya, ba zai kashe lokacinsa da dukiyarsa na yin aure ba. Kowace irin biyan buk’ata za ka hanga a cikin aure, haihuwa ta fi ta. Don haka auren da babu haihuwa ke ba Bahaushe tausayi.

[xl] Watak’ila don samun damar kama hankalin alk’alan gasar ya sa Imam ya gina labarinsa a kan rashin haihuwar Malam Na-Bakin-Kogi.

[xli] Matan Hausawa da yawa ko suna son miji rashin haihuwa na sa su fito su nemi gidan haihuwa komai k’ask’ancinsa su zauna. Haka shi ma namiji, ko mace ta wuce sa’arsa, idan ya san tana haihuwa yakan auro ta domin ya samu.

[xlii] Da wuya a samu mata ba su shiga bokaye a kan haka ba. Domin ba a son su shiga bokaye aka nuna babban malami ne. Haka kuma, da an bari sun shiga bokaye da an ‘bata zaren tunanin marubucin.

[xliii] A k’asar Hausa, ‘yan uwa na ba d’an uwa ko ‘yar uwa yara rik’o, in sun san ba sa haihuwa, domin a natsar da su. Wasu yaran har su girma ba za su tantance ba wannan ne mahaifinsu ko mahaifiyarsu ba. Da yawa yaran akan yi musu suna da ‘d’an’ kamar; D’anmanu, ‘Yarladi, D’anjimma, ‘Yarmairogo ga su nan dai. Wai a danganta su ga marik’ansu domin marik’an su ji sanyi a rai.

[xliv] An ko rik’i Sak’imu kamar d’a. Domin son da ake yi masa ya zama nagari har tsare shi aka yi wata uku ko ya horu ya shiryu. Da yake k’addara ta rigayi fata, haka nan aka k’are da shi, kare jini biri jini. Allah ba ka da dole.

[xlv] Ai da aka nuna Sarkin Zagi ya haukace, Sarki sa ya yi a yi masa maganinsa ya daina damuwarsa da hana shi barci. Da aka buge masa mummuk’e d’aure shi aka yi. Da aka kashe Bafaden Sarki ba a kashe Zurk’e ba.

[xlvi] Tun daga sunan littafin mai karatu zai fara d’okin ya ji yaya za a samo ruwan? In ba a samo su ba za a ji labarin bai kammala ba. Yaya ruwan suke? Me ake nufi da su? Wane wuri za a tarar da su? Wad’annan tambayoyin cike suke a k’irazan masu karatun littafin matuk’ar ba a yi musu susa gurbin k’aik’ayi ba, za su ji kwalliya ba ta biya kud’in sabulu ba.

[xlvii] Ya girmama wanda ba shi ya haife shi ba, amma yana aure da mahaifiyarsa. Ina laifin Ak’ilu Aliyu da ke cewa:

In da fahinta da kula ba da musu ba,

Dole ma’auri iya a ce mishi baba.

[xlviii] Da babu noma sai k’arancin abinci. Da k’arancin abinci sai yunwa. Idan yunwa ta bayyana mutuwa ba ta nesa.

[xlix] An san yak’i kisa ake yi. Duk abin da ya sa yak’i domin kare rayuwar wasu wad’anda ba su ji ba, su gani ba, a kashe su. Dole a yi garkuwa da mutuwa a kare mutuwar walak’anci.

[l] Idan rayuwa ba ta inganta ba cutuka za su biyo ta. Daga nan sai annoba ta bayyana.

[li] A ko’ina aka tanadi tsaro ba don kaya ko k’adara ake yin sa ba, ana yin sa ne domin rayuwar masu kayan da k’adarorin da rayuwa ta samo. Duk tsaron da ya kasa kare rayuwa, ba tsaro ba ne, tsawo ne.

[lii] Sai da zaman lafiya rayuwa ke da amfani. In an rasa zaman lafiya, rayuwa ta k’are amfanin mai ita sai sauraren lokacin da za ta k’are ake yi.

[liii] Idan Bahaushe ya samu wani abin raha, ya yi dariya, yakan ce, kaico! Na yi dariya kamar ba ni mutuwa. Wai! Halin duniya na yau rai, gobe an mutu, ya sa Yaro Hore mai kid’an noma ke cewa:

Jagora:  In nit tuna halin duniya,

Yara:                 Take raina ya yamutce!

Gindi:               Aiki yai ma dad’i k’warai

:Gungaman noma D’anbala

[liv] Dole kowane mai rai ya yi kuka da ranar da zai bar duniya. Littafin Allah ya ce, “Kowace rai mai d’and’ana mutuwa ce.” Tunawa da ranar bak’in ciki ya sa Hali Rayya Makad’a ke cewa:

Jagora:  Wayyo! Duniya ‘yal baya

:Kob bi ta taki bai kai waje.

[lv] Masu wasan dambe sukan yi kirari da cewa:

“Kunya muka tsoro

Mutuwa ta zama gado”

[lvi] Kowane irin adabi aka d’ora kan matakan rayuwa, za a ga an fed’e shi cikin tsanaki. Hausawa na cewa, da rashin tayi akan bar arha. A gwada a gani. Wurin da babu fili ake gardamar kokuwa.

[lvii] Idan mutum ya rayu da d’ansa, d’an nasa ya d’auko irin halayensa muddin suna raye su duka, sai dai a ce, ya d’auko uban. Ba za a ce ya gado shi ba. Idan uban ya mutu, kai tsaye za a ce ya gado shi. A addinin Musulunci, sharid’in gado na farko shi ne mutuwar wanda za a gada da rayuwar wanda zai yi gado bayan mutuwar wanda za a gada.

[lviii] Ba wai wagagen littattafai ake son a gada ba, ilmi ake son a samu d’a mai shi. Mai ilmi zai gaji littattafan ba jahili ba. Da jahili ya gaje su, za su koma masara ko shinkafa, a yi tuwo, a kai wa masai kayanta.

[lix] Tsoron da Imam ya ke ji na kar Sarkin Zagi ya k’are hursuna ya dawo ya ce, sai ya rama. Don haka ya gudu, ya bar garin. Da an samu shaidu da Sarkin Zagi ya fuskanci hukuncin kisa.

[lx] Imam ya san shi ba waliya ba ne don haka ya tabbatarwa mai karatu cewa shi, tik’ar gudu ya yi. Halinka da rashin sani, ya fi dare duhu. Jahilai ba su hango ba, har fad’ar suke yi “masu abin.” Haka ake ko yanzu, malamai sun mayar da mabiyansu tamkar makaman farautar cefane sun kasa ganewa in an yi yunk’urin lurar da su malaman su yi ta jifan mutane da jafa’i da k’asafai, jahilai su yarda cikin rashin sani.

[lxi] Wadda Sak’imu ya yi Malam Na-Bakin-Kogi.

[lxii] Wadda mai masaukin Imam ya yi wa ‘barawo da gawar da aka yaudari Sarkin Zagi aka buge masa mummuk’e ya yi hursuna shekara d’aya.

[lxiii] Irin wadda aka kad’a d’an goruba a kan d’an Sarkin Aljannu ba da sani ba. Nan ya mutu, Aljannu suka d’auki fansa ba da jinkiri ba.

[lxiv] Irin wadda Imam ya yi wa wansa.

[lxv] Irin wadda Zandoro d’an Zotori ya ce zai yi wa wanda ya kar’bi sansa bai iya ta’bo kansa ba.

[lxvi] Irin mutuwar da Jamilatu da ta K’wara. Duk a kan shiri aka yi su kuma Imam aka yi wa su, ya gano.

[lxvii] Irin wadda Sak’imu ya ce Malam Na-Bakin-Kogi ya yi. Ya ce cikin dare ya cika, wa zai musanta haka ga wanda ya tsufa? Nan kuwa Sak’imu ya kashe shi da takobin yak’i.

[lxviii] Irin wadda aka yi zato ga matan Malam Na-Bakin-Kogi bayan da Malam ya rasu

3 comments:

 1. […] Littafin Ruwan Bagaja A Ma’aunin Matakan Rayuwar Bahaushe […]

  ReplyDelete
 2. […] Littafin Ruwan Bagaja A Ma’aunin Matakan Rayuwar Bahaushe […]

  ReplyDelete