Ticker

6/recent/ticker-posts

Karar Tsana: Gudumar Dukan Watsattsu Ta Abu-Ubaida Sani

... Yayin da na ɗaga kai na dubi cakwalkwalin cakwakiyar da duniyar matasantaka ke ciki a yau, sai na tuna maganar malamina a sakandare da yake cewa: “A concentrated mind is never taken away.” Sai kuma na ce da kaina, kenan “A determined mind is never taken away.” A nan sai maganar mahaifiyata ya dawo mini (sai an kula kashi yake ɗoyi). Ai kuwa nan na gane cewa, babbar hanyar kauce wa tarkon watattsu shi ne samun gudumar dukansu. Gudumar da ta fi dacewa kuwa ita ce KARAR TSANA. Yayin da mutum ya tsani halinsu da salonsu, to lallai salon nasu ba zai taɓa burge shi ba ballantana har ya ji yana ra’ayin ɗanawa....



Abu-Ubaida SANI
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara
Phone No: 08133529736
Email: abuubaidasani5@gmail.com

Bismillahi a farkon zance,
Sunan Allah zan yo sawa.

Na roƙe ka ka ƙaran baiwa,
Domin waƙar in tsarawa.

Ƙara salati gun sa Rasulu,
Manzon nan da ka yo aikowa.

Har da iyalai nasa a jimla,
Har da sahabbai su duka kowa.

Har mabiyansa dukka mutane,
Kan sunnarsa har ran tsaiwa.

Dam ɗin zance yau ya batse,
Ambaliya zai yo tasowa.

Abin da ka ƙunshe yau ya kwance,
Zai ko baje a gani duka kowa.

Ran wanka ba ɓoyon cibi,
Yau zancen ba na sakayawa.

Zan magana ne kan watsattsu,
Siffofinsu za ni faɗowa.

Ko da ka kalle su da tsafta,
Sun sa kaya mai burgewa.

To wannan siffar fenti ce,
Ga ta usul zan yo zanawa.

Kar da kuɗinta ya ko dame ka,
Kyan halinta kawai kai tsaiwa.

Kyawun fuska daban da na zuci,
Zuci ake so ai dacewa.

Runtse idonka in ba ka kamarta,
Siffofinta ka yo ganewa.

Idan da abinci gabanka ka kau sai,
Kar da amai kai yo kwazawa.

Don da ita gwamma ka ga kashi,
Ko kakin da a kai tofarwa.

Kai jama’a muni ga kumatu,
Tamkar bakuru tai cusawa.

Ga goshi ko abin ban tsoro,
Kamar jaki sabon haihowa.

Ga da ma kuwa ba ta da gashi,
Ga sanƙonta yana haskawa.

Siffar kanta ya dutsen guga,
Ya za ai gashi ya tsirowa?

Hancin nan ya gajeren wando,
Kamar kwaɗon da a kai takawa.

Hancin nan fa ƙananan ɓewa-
Tsaf za su iya su wucewa.

Ina tsammanin ya fi na jaki,
Musamman yayin numfasawa.

In ta yi bacci tana minshari,
Kamar inji aka yo tadawa.

Shape ɗin hancin aka ɗauki design,
Ƙofar fada a kai zanawa.

Ka ga idonta kamar ‘yar mage?
Ga su da kwantsa ba wankewa.

Ga bakinta kamar an yi ɓarna-
Nan da wuƙa ga babbar kabewa.

Kwatancen bakin ka san ganda?
Musamman baƙi dake nannaɗewa.

Ka ga haƙoran kamar katafila,
Wanda kacarta ta yo tsinkewa.

Daga nesa ka hanga tamkar kanti,
Na cokala da ake saidawa.

Don sun watse ba su da tsari,
Kamar gyauron da su kai tasowa.

Na ɗan kwan biyu ina ta hasashe,
Yanzu gare ku ko zan furtawa-

Kamar harshenta bature ya kalla,
Farfelarsa ya yo tsarawa.

Har da ko nata salon karkarwa,
Yayin gulma da shegen tsiwa.

Ban ma fara kwatanta giranta,
Don ko babu da nai dubawa.

Ka ga wuyanta kamar na aro ne,
Can ya danƙara bai miƙewa.

Kunnen nan ko ya faifan goro,
Wanda samansa ake saidawa.

Kwatancen cikinta katifar mayu,
Nan muninta ya yo tarewa.

Da dai ka san kabarin ɗanwada,
Siffar kenan ba ka rabewa.

Ka ga ƙafarta ya tsinken bawul,
Sandar sabulu ta fi shi direwa.

Sai ma ka dubo daga nesa,
Kamar lauje sukai bauɗewa.

Kuturta cuta ce da daga Allah,
Ita ga ƙazanta tai samowa.

Gajera ce kuwa ‘yar ɗif ga ta,
Ga shi baƙinta kamar shafawa.

Tamkar an shafa mata fenti,
Duna ɓaleri ƙirin aka cewa.

Ko ƙwan wutarka na nan da haske,
In ta doso zai yi dushewa.

Ka ga salon tafiyar ‘yar iskar?
Ga fa kwatance kai ganewa-

Ka san ƙaguwa na bauɗewa,
Salonsu guda a wurin takawa.

Idan ta yi sauri sukan bambanta,
Tamkar agwagwa take komawa.

Ga ko hanunta kamar katako,
Shi taurinsa daban da na kowa.

Fatar jikinta irin ta guza ce,
Sak tsarinsu da nai dubawa.

Kaushin ƙafarta yana amfani,
Ta yi bajinta ban ɓoyewa.

Ai wata rana ana kan aiki,
Ana fasa titi don gyarawa.

Sai katafilar tasu ta ɓaci,
Ga shi ana son ai ƙarewa.

Ai ita goganyar da ta taso,
Wucewa ɗai tai ba dawowa.

Duk kuwa titin sai da ya ɓarje,
Katafila ranar tai hutawa.

Ranar an ga abin mamaki,
Fasonta ko ya burge Turawa.

Na ji Bature yana gulmarta,
Cikin Turanci yake furtawa:

I have never seen a robot,
So active ya wanan ɗan baiwa.

I thought first it was a gorilla,
The way na gan shi yana takawa.

Oh! Technology is advancing,
Where on earth a kai ƙerawa?

Ni ko na ce masa is not a robot,
That is faso je kai dubawa.

Allah ya yi hani ga mazaje,
Su taɓi mace ko shafawa.

Na san taɓinta ko babu halaki,
Ko alwala ba ya karyawa.

Idan ba ka farga ba ma ta taɓe ka,
Gadon bayanka ta yo shafawa.

Za ka kai bugu ne da sauri,
Da niyar dai ka yo maujewa.

Kai a zatonka gwadan-gwale gwada,
Shi ne bayan ya yi ɗalewa.

Babbar matsala na nan yawunta,
Idan ƙaddara tai yo gittawa.

Sai ka ji an ce an yi disaster,
To yawu ne tai tsittarwa.

An ce gado tai na fitsari,
Nan a gado da dare tsulawa.

Wai da Maliya ba shi da aibu,
Ruwansa garau akan kurɓawa.

Sai da uwarta ta tsula fitsari,
Yai sanadinsa na gurɓacewa.

Idan ka gan ta kamar goggo ne,
Shi da ita ba a fa rabewa.

Na samu ubanta a kwanan baya,
Ga shi shawara nai bayarwa.

Ka san yana da kuɗi har na banza,
Amma ga Allah bai godewa.

Sai dai a tara ba a kyauta,
Balle zakka bai fiddawa.

To da ma fa kuɗi na haramun,
Ba albarka mun shaidawa.

Kullum sai kuka na talauci,
Babu wadatar zuci daɗawa.

Na ce tun da talauci ya kam mai,
Ya ɗaure shi bai motsawa.

Ya ɗauki ɗiya yai gidan dabbobi,
Ya ce ai biri ya zo saisarwa.

Amma shegen bai ji batu ba,
Sai da ƙwaƙwalwa ake ganewa.

Amma daga baya da na duba,
Ba shi da laifi nai ganewa.

Tsoro ya ji in har ya tafi,
Har shi ma za ai kamewa.

Ku tare- kutare! Ga tsohon goggo,
A keji shi za ai dannawa.

Har daga baya a ƙarfafa zance,
A nemi haɗin guiwar Turawa,

Su kai shi Amerika su sa ɗakin lab,
Experiment za su yi dubawa.

Abin dai ya ɗaure musu kayi,
Yadda biri yaka zantawa.

Ga furucinsa ko sak da mutane,
Sai dai ba ma’anar kamawa.

Kai! Da na duba uwar ‘yar banza,
Sai nai kurum ina ta tunawa.

Na ga dalilin da ake ta hasashe,
Ra’in nan da ake zanawa-

Asalinmu birai ne, sannu-a-sannu-
Har mu ka zam mun yo sauyawa.

Har muka samu sifa ta mutane,
Yanda a yanzu muke duka kowa.

Tabbas zuriyarsu ce aka duba,
Wannan theory a kai tsarawa.

Mu leƙa tarihin danginsu,
Labari zan yo bayarwa.

Akwai wani can tsohon kakansu,
Da Turawa suka yo kamawa.

Suka kai shi ƙasarsu wanda a sannan,
Ta fi Amerika ginin burgewa.

Da ya dube su ya bankama tusa,
Gininsu da dama yai rugujewa.

Injinansu duk sunka yi tsatsa,
Ruwansu na sha yai gurɓacewa.

Dabbobi da yawa sun mace,
Wasu da dama sun arcewa.

Ɗai daga cikinsu ko shi ne bodari,
Shi Nijeriya yay yi tahowa.

Ka san ya shaƙo ita iskar,
Ita ce yanzu yake fiddawa.

A nan ne zan ja in dasa aya,
Kayan haushi nai ƙyalewa.

Abu-Ubaida wanda ya yi ta,
Ɗan Sani ga mai dubawa.

Garinmu Misau ne can ko na taso,
Jahar kuwa Bauchi ban ɓoyewa.

Nai godiya kana na ƙara,
Gare shi Ilahu maƙagin kowa.

Na yi salati gun manzonmu,
Da sallallami na yo ƙarawa.

Ɗari da shida ne baitocinta,
Hamdalla na yo ƙarewa.

Tsokaci

“Sai an kula kashi yake ɗoyi!” Ina tunanin na fara jin wannan karin magana ne wurin mahaifiyata. Haƙiƙa za a iya cewa wannan batu gaskiya ne. Abin da mutum ya sanya a ransa kawai shi ke damun sa. Misali, yayin da mutum ya ƙwallafa son wani ko wani abu a ransa, to duk abin da masoyin nasa ya aikata zai kasance abin burgewa a gare shi. Za ta yiwu wannan ne dalilin da ya sa Bahaushe ke cewa: “So mai kau da ganin laifi.” Sani Sabulu ma cewa ya yi: “Ƙauna ba ta gano wahala.” A ɓangare guda kuma, yayin da mutum ya ɗauki karar tsana ya ɗora wa wani ko wani abu, to kuwa duk wani motsi na abin da ya tsanar nan, zai kasance abin ɓacin rai ne a gare shi. A taƙaice dai, abin ba zai taɓa burge shi ba kamar yadda Bahaushe ke cewa: “Mai son ganin laifinka, ko da ruwa ka faɗa sai ya ce ka ta da ƙura.”

Kalmar watattse a wannan bagire ta zo da manufar duk wanda ya ɓata kuma yake ƙoƙarin ɓatarwa. Kenan dai muna iya cewa, watattsiya ita ce wanda ta ɓata kuma take ƙoƙarin ɓatarwa. Akan samu irinsu, musamman a yanzu da wakilan sheɗan suke ƙara yawaita. Ma’ana a zamanin da har saɓo ya zama kwalliya da burgewa a cikin al’umma. Rashinsa kuma ya zama ƙauyanci da rashin wayewa.

 Saboda haka:
Ƙarya ta zama sinadarin zance
Ashare-ashare suka zama kwalliya a cikin zance
Batsa ta zama gishirin zance
Namiji na iya kiran mace ‘ƙawata’, kuma ya ce shi ba ‘ɗan daudu’ ba ne
Fitar da tsiraici ga mata ya koma abin yau da kullum
Waɗanda maza suka fi son cuɗanya da su, su ne matan da ke yawo da tsiraici waje
Shaye-shaye ya koma abin ado da nishaɗi tsakanin maza da mata
Kasuwar zina ta yi tashin gwauron zabi
Yaudara tsakanin ‘yammata da samari ta zama ruwan dare
Samari da ‘yammata suka zama kurame ga sautin gaskiya, makafi ga walƙiyar gaskiya sannan kutare ga karɓarta.

Yayin da haushi zai rufe ka, sai wani ko wata ya riga ka cewa: “Amin” yayin da aka ambaci: “Allah ya sa mu shiga aljanna.” An san cewa imani a zuci yake, amma ko ba komai ai: “Alamun ƙarfi yana ga mai ƙiba.” Kuma ma; “Labarin zuciya a tambayi fuska.” To ma wai, me laifin “ko kana da kyau ka ƙara da wanka?” A taƙaice dai, halayen matasa a yau sai dai a maimaita abin da jakin dawa ya faɗi yayin da ya ga na gida, wato: “Allah wadarai naka ya lalace.” Wani ƙarin kayan haushi shi ne, kowane matashi addu’arsa ita ce samun mata ta gari. Haka ma budurwa addu’arta kenan samun miji na gari. Na taɓa ji wani malami yana tambaya: “To wa zai auri waɗanda kuka yi ashararanci da su? Waɗanda kuka ɓata wa rayuwa, kuka ɓata wa lokaci?”

Yayin da na ɗaga kai na dubi cakwalkwalin cakwakiyar da duniyar matasantaka ke ciki a yau, sai na tuna maganar malamina a sakandare da yake cewa: “A concentrated mind is never taken away.” Sai kuma na ce da kaina, kenan “A determined mind is never taken away.” A nan sai maganar mahaifiyata ya dawo mini (sai an kula kashi yake ɗoyi). Ai kuwa nan na gane cewa, babbar hanyar kauce wa tarkon watattsu shi ne samun gudumar dukansu. Gudumar da ta fi dacewa kuwa ita ce KARAR TSANA. Yayin da mutum ya tsani halinsu da salonsu, to lallai salon nasu ba zai taɓa burge shi ba ballantana har ya ji yana ra’ayin ɗanawa.

Wannan waƙa ban shirya ta kan wata mace takamaimai ba. Sannan babu wanda ta ɓata mini rai kafin na fara rubuta ta. A taƙaice dai, na yi ƙoƙarin bayyana matakan da na ɗauka wa kaina ne, wanda kuma muka yi tarayya da mutanen da ke jan zaren tunani irin nawa. Wato matakan kau da kai daga aikin banza, da “yanka wa kare ciyawa” da zaman kashe wando da makamantansu. A cikin waƙar, na nuna irin hoton da zuciyata ta ɗauka ta adana a matsayin siffar duk wata watsattsiya. Kuma hakan ne ya sanya, dukkanin caffa da zararsu kan kawo wa watana kan zama na banza, da yardar Ubangiji. Daga ƙarshe sai abin ya kasance: “Ko a jikina wai an tsakuri kakkausa.”

Post a Comment

0 Comments