Ticker

6/recent/ticker-posts

Don Me Ake Karatun Hausa?




Bisa ga al’adar ɗaliban harshen, ya kamata in ce: don me ake karatun harshe? Sanin cewa, masana sun yi wa harshe tarkakken nazarin da ɗalibi zai ratsa ya samu waraka ga bayanin harshe ko ilimin harsuna, sai na zaɓi in yi bara da Hausa.[1] Haka kuma, ba ina nufin Hausa ba harshen ba ne,[2] buƙatata ita ce, ƙyallaro dalilan da zai sa, mai harshe, ya nazarci harshensa, ko ya nazarci wani harshe a matsayin fagen karatu da neman shahara a ciki. A ganina, gajeren tunanin ‘yan bayan fage ga duniyar ilmi a koyaushe yana nuna musu, wace fa’ida ke cikin karatun harshenka na gado da ka tashi ciki, ka balaga ciki, kuma kana rayuwa a ciki?[3] Masu irin wannan fahintar…
Don Me Ake Karatun Hausa?

Aliyu Muhammad Bunza
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato
Waya: 0803 431 6508

Takarda da aka gabatar a bukukuwan makon Hausa na ɗaliban Hausa, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato, ƙarƙashin kulawar Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato, Ranar Asabar 10-11-2012 a mazaunin Jami’a na dindindin (ETF 3) a ƙarƙashin shugabancin Kwamishinan Yaɗa Labarai Malam Nasiru Ɗanladi Baƙo (Kogunan Sakkwato) da ƙarfe goma na safe.

Gabatarwa:
Bisa ga al’adar ɗaliban harshen, ya kamata in ce: don me ake karatun harshe? Sanin cewa, masana sun yi wa harshe tarkakken nazarin da ɗalibi zai ratsa ya samu waraka ga bayanin harshe ko ilimin harsuna, sai na zaɓi in yi bara da Hausa.[4] Haka kuma, ba ina nufin Hausa ba harshen ba ne,[5] buƙatata ita ce, ƙyallaro dalilan da zai sa, mai harshe, ya nazarci harshensa, ko ya nazarci wani harshe a matsayin fagen karatu da neman shahara a ciki. A ganina, gajeren tunanin ‘yan bayan fage ga duniyar ilmi a koyaushe yana nuna musu, wace fa’ida ke cikin karatun harshenka na gado da ka tashi ciki, ka balaga ciki, kuma kana rayuwa a ciki?[6] Masu irin wannan fahintar tunaninsu ya kasa hango musu cewa, da wane harshe suka yi karatun da suke cin gajiyarsa?[7] Da suka faɗo duniya, da harshen iyayensu suka faɗo, ko iyayensu ne suka koyar da su harshen har suka iya magana da shi? Domin daɗa juna sani ga masu sha’arwar karatun harshensu, da masu ganin ɓeran gida ba ya da mai, ya sa na yi tunanin wannan rubutu ga ɗaliban karatun Hausa cikin sigar tambayar, don me ake karatun Hausa? Burina a nan shi ne, bayanin wannan tambayar ya fito ƙarƙashin hasashen da Aƙilu Aliyu ya yi na cikin waƙarsa ta: “Hausa Mai Ban Haushi.” A faɗarsa:[8]
          Tsuntsu kamata yai da shi ya yi kuka
                   Ya irin na kakanninsa can mai nisa.

Harshen Hausa Da Hausawa A Doron Ƙasa:
A wannan fasali ma, kamata ya yi in ce, mene ne harshe. Da gangan na zaɓi wannan tsarin domin in ƙara kusantar da Hausa a tunaninmu. A hangen masana, ba wani abu ne harshe ba, face sadarwa da ke wakana tsakanin mutum da mutum ta fuskar magana da daidaitaccen lafazi da aka saba da shi. Sadarwa ta fuskar magana ita ce, harshe, kuma ita ce sunan da ake bai wa kowane harshe doron ƙasa.[9] Dabarun sadarwa na ishara, da ƙaƙale, da rubutu, da dabarun al’ada, ana kiransu hanyoyin sadarwa.[10] Idan haka ta tabbata, harsunan duniya duka martabarsu ɗaya ga masu amfani da su.
Harshen Hausa na daga cikin manyan harsunan ‘yan zuriyar Chadi.[11] tana daga cikin manyan harsunan da Afirka ke bugun gaba da su ga kowane misali na martabar harshe.[12] ta yi wa sauran harsuna babakere a Afirka ta Yamma.[13] Ya yi wa sauran takwarorinsa fintikau cikin gida Nijeriya.[14] Ya dakashe wa harsunan Turai kaifi cikin ƙasashen da suka yi kaka-gida (watau Turanci da Faransanci).[15] Ya hana wa harsunan mulkin mallaka salwantar da nahawunsa.[16] Tasirin da addinin Musulunci bai sa Larabci ya durmuyar da kalmominsa na asali ba.[17] Juyin-juya-hali na masu jihadin ƙarni na goma sha tara, bai firgita martabarsa ba ga masu shi, da masu koyonsa.[18] Ya tilasta wa harsuna maƙwabtansa da waɗanda suka riske shi aro cikinsa saboda wadatattun kalmominsa da yalwatacciyar al’adarsa.[19] Ya yi aro irin na ci gaba da wasu harsunan da zumuntar zama ya haɗa su, ba tare da salwantar da kalmominsa na asali ba.[20] A duniyar Afirka, shi ne harshen da ya fi kowane bazuwa, da yaɗuwa, da karɓuwa, da sarƙuwa cikin harsuna, ba tare da zama harshen ƙasa a hukumance ba.[21] Kaɗan daga cikin martabobin harshe Hausa ke nan wanda ya sa masananmu ke cewa, mai maɗi ke talla, mai zuma ido yake sa wa. Wannan zance nasu ya hau ƙololuwar tunanin makaɗa Narambaɗa a faɗarsa:
          Jagora:        Maɗi bai kai ga zuma ba
Yara:           Kowal lasa shi ka hwaɗi
:Kwandon wake bai kai ga
:Damen gero ba
Jagora:        Ɗan akuya ko ya yi ƙahoni
Yara:           Ya san bai yi kamar rago ba
Jagora:        Duw wada ɗan sarki yaƙ ƙasura
Yara:           Kak ka raba shi da bawan sarki
Gindi:          Gorarman Tudu jikan Sanda
:Maza su ji tsoron ɗan mai Hausa

A sauƙin fahimta da koyo, Hausa ita ce zuma, sauran harsunan Afirka maɗi ne.[22] ta fuskar martaba da ɗaukaka, Hausa damen gero ce takwarorinta na a Kwandon wake.[23] A wajen yaɗuwa, da bunƙasa, a nahiyar duniyar zamaninta, Hausa karon rago ce, mai manyan ƙahoni sauran harsunan ƙarninta bunsurai ne ɗan ƙahonsu na ɗara ne, bai isa karo da manyan harsunan Turai ya kai labari ba.[24] Mai musun  wannan ya tambayi harshen Yarbanci da Ibo da Wolof  da Fulantanci da Kanuri da Asante da Wangara da Kisuwahili zai tabbata, Hausa ce sarauniya, sauran harsuna ‘yan galadimomi ne ba su da bambanci da bawan sarki da za a kira, ya rugo a guje.[25] Waɗannan hasashe-hasashenmu, ana iya kallonsu ta fuskar mamayar da Hausa ta yi wa kafafen yaɗa labarai na duniyar zamaninmu.[26] Mujallun ilman Turawa, da fadakarwa, da jaridu, na duniyar ƙarni na ashirin da ɗaya za su tabbatar da haka.[27]

Ban so in raba bayanin Hausa da Hausawa ba a wannan ɗan rubutun, amma bayani ya tilasta haka. Da Hausa da Hausawa abu ɗaya ne, kamar mutum da sunansa. In aka kira sunansa shi ne, in shi ya faɗi sunansa linzaminsa ne. Hausawa su ne tarsashin jama’ar da ke amfani da harshen Hausa a matsayin harshen uwa, ko in ce harshen haihuwa.[28] Haka kuma, ya kasance ga iyayensu suka gaji harshen, su kuwa iyayensu sun gada daga iyayensu.[29] A al’adar Bahaushe, wanda ya gaji abu iyaye da kakanni ya taki hujjar da zai faɗa a saurare shi.[30] Hausawa a doron ƙasa ba ƙyalle ba ne, idan aka nazarci nahiyoyin da suka mamaye. A gida Nijeriya, sun kafa daulolin da babu wata al’ummar da ke da irin su yawa, da ƙarfin mulki, da tsarin shugabanci, da fice a tarihi.[31] A cikin Afirka ta Yamma, sun yi ale-ale a Ghana da Nijar da Mali da Togo da Benin da Abijan da Saliyo da Borkina da Libiya da Morocco da Tunis da Masar da Sudan da Saudi Arabiya. Cikin al’ummar da ke zaune a duniyar baƙar fata, babu wanda ya kai Bahaushe barbazuwa a duniyar zamaninsa.[32]
A ma’aunin ɗalibta da na karatu, matsayin harshen Hausa da Hausawa a duniyar baƙar fata ya isa ya zama hujja da ɗalibai, da malamai, da manzarta, da masu bincike, na kowane fannin ilmi su tunkare shi. Burin kowane harshe shi ne, ya samu masu magana da shi.[33] Ya mamaye nahiyar da ya tsira.[34] Ya samu karɓuwa ga maƙwabtansa na ciki da na waje.[35] Masu magana da shi, su fantsama a uwa duniyar zamaninsu, da harshen a bakunansu.[36] Idan harshe ya kai ga wannan muradi, duk wata musibar masassara, da za ta sa ya suma, ko ya mutu, ya tsallake ta. Don haka, ko musibar yaƙi da annoba tana raga masa, bale wani baƙon haure da zai zo da tsakiyar rana da ƙarfin soja.[37] Hausa ita ta yi wa kanta gwagwarmaya wanda ke karatunta gajiyarta ne zai ci, ba neman a riƙa ta miƙe tsaye take ba.[38] Tsaye aka taras da ita kamar ‘alif baƙi’ kuma tana saman harsunan zamaninta irin yadda ‘alif ja’ ke saman kowane harafin da aka rubuta.[39] A gai da Alhaji Muhammadu Gambo Fagada[40] da ke cewa:
          Jagora:        Dole nakiya ta yi zaƙi Sanda Ummaru
                             :Don da zuma aka fara yin ta

Martabar Karatun Hausa:
Karkarar da muka fito mun ga matsayin Hausa na zama tsayayyen harshe, wadatacce ga masu magana da shi, yalwatacce ga kalmomi, kuma sananne a duniyar zamaninsa. Ga alama, ɗalibin nazarin ilimin Harsuna zai ce: “Da an ce, martabar karatun harshe abin ya fi amo.” A ganina, an gama kyau tun ranar haihuwa. Da Hausa muke rubutu a kan Hausa muke magana. Da Hausawa da masu sha’awar karatu ko nazarin Hausa muke tattaunawa. Don haka, gara a yi, ga wuta, ga masara, filin wuri dabon Ɗankama. Harsuna duniya ba ta fuskar tsawonsu, ko faɗinsu, ko nauyinsu ko kwalliyarsu, ko wayewarsu, ake kallo a kasancewarsu harshe ba. Haka! Akan kalli wasu daga cikin waɗannan a wasu ɓangarorin ilimin harsuna, amma fa’idojin harshe ga ɗan Adam, wanda zai sa a yi ɗalibtar karatunsa suna da yawan gaske.
Irin tazarar da ke tsakani mai karatun harshe da ɗan kallo tankar tazarar da ke tsakanin mutumin da ke ji da kurma ne. ba a fi kurma sutura, da zati, da taƙama, da cika ido ba. Da an fahinci ba ya ji ya zan rabin mutum. Da wanda ba ya jin abin da ake faɗa, da wanda ke ji ya kasa fahinta, maƙawabtan juna ne. idan aka kwatanta su da mai gani da makaho ba a yi kure ba. Domin da wanda ba ya gani, da mai gani garaye-garaye,[41] da wanda ya kasa ahuma da fahintar abubuwa da yake ganin tazararsu ba ta da yawa. Idan aka kwatanta su, da mai hankali da mahaukaci ana iya yin muwafaƙa. Mai hankalin da ya kasa aiki irin na masu hankali, lokacin da ake buƙatar a auna hankalinsa, a cikin wannan rutsin, sunansu ɗaya da mahaukaci. Dangantakar da ke tsakanin masani harshen da ake magana da shi, da wanda bai san harshen ba, irin ta malami ce da jahili tuƙaƙƙe (watau murakkabi).[42] Komai wayonsa, da wayewarsa, da ƙwarewarsa, ga abin da yake ganin ya ƙware a kai, idan ana magana da harshen da bai sani ba, kamar ana ba gawa labarin sanadiyyar mutuwarta ne a al’adance. Da me labarin ya amfane ta? Wane amfani daga cikin amfanonin maganan mai labarin ya amfana da shi? Kwatanci masani harshe da wanda ya jahilci harshe, irin na baƙo ne da ɗan gari. Yaya za ka kwanta wanda aka haifa cikin gari, ya manyanta ciki, ya san mutanen garin, suka san shi, da wanda bai taɓa sanin gari ba, ya wayi gari a ciki. Bai san kowa ba, kowa bai san shi ba. Bai taɓa ganin kowa ba a garin kowa bai taɓa ganinsa ba? Yadda yake zarar ido irin na sabon makaho. Yake waiwaye-waiwaye irin na baƙon ɓarawao. Haka nan wanda bai san harshe yake ba idan ana hulɗa da harshen a gabansa. Dubi irin damuwa, da tsarguwa, da rashin natsuwar da mace za ta ji a babban birnin da ita kaɗai ce mace, ko namiji zai ji a alƙaryar da shi kaɗai ne namiji. Kwatankwacin haka ne mutum zai samu idan ya baƙunci gari/ birnin da ba a jin harshensu, shi kuwa, kowa ba ya jin nasa.
Tabbas! Kintsuwar mutum, da zamansa kamili, ba ta cika, sai yana iya magana a fahince shi, ko ana magana ya fahinta. Waɗannan abubuwa biyu su ne tubalan da suka gina kowane harshe a duniya. Dole mai hankali ya sake tunanin cewa, wai idan babu harshen sadarwa a duniya yaya hulɗar rayuwa za ta kasance wa ‘yan Adam? Bayanin da za a ba wanda ya yi wannan tambayar shi ne, ya dubi rayuwar tsuntsaye, da ƙwari, da dabbobin garinsu. Mutanen garinsu ba su fi su yawa ba, amma wane tasiri suke da shi a garin? A koyaushe, harshe na da alaƙa ta ƙuƙut da hankali, da mutunci, da martabar ɗan Adam. Ashe, mamakin nazari ko karatun abin da mutum ba ya kasancewa cikakken mutum sai yana da shi, wani duhu ne na ƙoli daga cikin duffan rashin sani. Idan wani ilimi na zama wajibi da kowane ɗan Adam, da wuya bai kasance ilmin sanin harshensa ba. Bisa ga haka, ba sai na gaya wa ɗaliban Hausa su yi karatun Hausa ba. Ga fili ga doki ga wurin suka mai daɗi. Ko ba a faɗi ba ido ya san abin da ke cika masa tumbi.

Hasken Harshen Hausa Ga Ɗalibansa:
Babu shakka, kowane harshe haske ne ga masu magana da shi, da ɗalibansa, da manazartansa, da malamansa. Ɗaliban harshe na kowane zamani, na kowace ƙasa, darajarsu ɗaya, tsawonsu kwatankwacin mashaci yake a ma’aunin nazari.[43] Harshen Hausa wani haske ne ga ɗaliban da ke nazarinsa a kan kowace fuska suka samu rayuwarsu ciki. Ga ɗan abin da na hango na irin matsayin hasken harshe ga ɗaliban nazarinta.
Ɗaliban Hausa, ku sani, Hausa kamar farfajiyar duniya ce da ke shimfiɗe, tattare da mutane, da ƙwari, da dabbobi, da itace, da ƙoramu, da tsaunuka, da rafuka, da tuddai. A cikin wannan yanayin harshe kamar rana yake ko wata. karin harshe zai zamo taurari.[44] Idan babu rana da wata sararin duniya ba ya zaunuwa a wala a ciki. To, ka ƙaddara faɗin duniyar nan, yaya zai kasance, idan an cika shi da bil Adamu, kuma babu wani harshe da ake sadarwa da shi? Ko da harshe ɗaya kacal aka samu duniya, hasken rana ya bayyana ga mazaunanta. Yayin da ranar za ta faɗi, wato idan harshe ya cika ya batse, za a ga wata da taurari sun bayyana cikin dare, wannan kwatankwaci kururuwan harshen ne. wata na nan a matsayinsa na harshe mai wakiltar rana, domin idan harshe ya cika ya batse, ci gaban da ke aukuwa a duniyarsa na ƙara yawaita masa baƙin kalmomi sababbi, da na aro, cikin haka, a samu tasirin wasu tsofaffin kalmomi, sai haskensa ya ɗan dushe, ya tashi daga duniyar rana zuwa darajar wata. Taurarin da ke gewaye da shi kuwa karuruwan haushe ne, da ke tsira bisa ga saɓanin yanayi, da nahiya, da ci gaba, da walwala, da siyasa, da addini, da al’adr da harshe ke haifarwa. Harshe wani dogon haske ne mai game ko’ina da ko’ina irin na rana ga masu nazarinsa. Waɗanda ke magana da shi idan ba su karance shi ba, ɗan hasken da suke da shi nasa bai fice na tazarar da ke tsakanin faɗuwar rana zuwa shigan duhu na haƙiƙa ba.
Hasken harshen Hausa, da amfanoninsa ga ɗalibansa, irin na maji yunwa ne da abinci. Ɗan kallo ga nazarin harshe, wanda bai ɗalibce shi ba, mayunwata ne ga amfanonin da ke cikinsa. Misalin wanda ya ratsi harshe, harshe bai ratse shi ba, kamar maji yunwa ne da ƙishirwa matsananciya, a yi masa wanka da fura da ruwa masu sanyi sosai tsarkakakku, amma a hana shi lasa ko tas daga ciki. Wankan da aka yi masa zai wadatar da shi daga matsalar yunwar da yake ciki? Ga aikin hankali, takaici ma zai ƙara masa. Irin wannan takaici ne ke sa wanda bai karanci harshen Hausa ba, ke mamakin masu sadaukar da kansu suna karatun Hausa. Takaicinsa, yana Bahaushe uwa uba, amma a ce, wai bai san harshensa ba, sai ya je ya ɗalibce shi. Ya manta da cewa, kai ke da gonanka, amma idan ka yi shuka, sai ka ƙi yin noma da sa taki lallai sai ka sha takaici ranar girbi. Sau nawa mutum zai manta da kayansa, waɗanda ya ajiye da hannunsa, a ɗakinsa, sai matarsa, ko yaronsa, ya nuna masa wurin da suke? To! Haka koyon harshenka na farko yake a makaranta. Dalilinmu ke nan, na koyon harshenmu, domin ba a san tabkin da ke makara da ruwa ba. Ai kamata ya yi a ce, mata ta san mijinta ko daji ta gan shi komai taron maza tana bambanta shi.
A ganinmu ɗaliban harshen Hausa, haɗarin da ke cikin rashin koyon harshenmu a matakin nazari, haka yake kamar a ce, ga ƙasa mai ɗimbin arziki, da tsaro, amma ba ta da tsarin mulki da shugabanci. Me za ka ce wa, sabuwar mota da aka shirya gagarumin biki da ita ba ta da kowane irin mai da za ta sha? Yaya rayuwarka za ta ji, idan kana cikin matsananci hali na neman agajin gaggawa, ga ka da sabuwar waya, da kuɗi a hannu, amma babu kowane irin layi cikin wayarka, yaya za ka ji wannan matsalar? Gabanin ka ba ni bayanin irin ƙuncin da kake ciki, fiye da wannan ƙuncin wanda bai zurfafa cikin harshensa nag ado ba yake ciki. Dalilin ɗaliban harshe ke nan, na cewa, kowane ilmi gare ka a duniya, ka yi ƙoƙari ka fahinci sirrin harshenka, in kana son ka ji daɗin duniyar zamaninka. Ma’ilmanci da bai iya sarrafa ilminsa cikin harshensa nag ado, ya shiga cikin ɓatan ɓakatantan domin ya zama buzuzu ga ƙarfi babu dabara, in ji malamin kiɗa Narambaɗa:
          Jagora:        Banza sha’anin maras kare
Yara:           sai kuwwa, sai ko wanda yak kashe
:Ya ce mishi, “Amshi rataya.”[45]
Gindi:          Ya ci maza, yak wan shina shire
:Gamda’aren Sarkin Tudu Alu

Ƙumshiyar Karatun Hausa:
Manhajar kowane harshe daji ne ba ka da gambu. Idan za a koyi harshe, duk wata albarkar da ke ciki, sai an yi mata fasalin kanta. A nazarin Hausa, muna da: Al’ada da Adabi da Harshe. Waɗannan duwatsun murhu uku, su suka sa karatun Hausa ya zama wani dodo a cikin karatun harsunan duniya. Alal misali, a Turanci akwai Harshe da Adabi, amma babu ‘Al’ada”. A Jamusanci akwai Harshe da Adabi amma babu “Al’ada”. A wajen masu nazarin Hausa, duk wata taska ta rayuwar Bahaushe sai an ƙwalailaice ta, domin ɗalibi ya zamo wayayye ga sanin al’ummar da ya karanta ta kowace fuska.
Muradin Nahawun Hausa, ba iya magana, da rubuta ta, da karanta ta ne babban muradi ba. Muradi shi ne, a iya magana. A iya fahimtar magana. A iya fassarar magana. A iya danganta magana da mai yin ta, da wanda/ waɗana ake yi wa ita, da halayyar da ake yin ta, da lokacinta, da gurbinta. Buƙatarmu a adabui ita ce, ta kasance taskar adana hikimar magabata,[46] ta fuskar adabin baka da rubutacce, domi a waigi jiya, a tsura way au ido, a ƙyallaro gobe. A cikin al’ada ne za mu ga yadda harshe da adabi suka narke cikin sosai, da yadda za a warware su a yau, su zama rumbun arziki ga na gobe. Wanda ya rasa al’ada bai san wurin da ya fito ba, ya manta da wurin da ya dosa.
Idan haka ta samu, ɗalibin da ya karanci Hausa ba Hausawa kawai zai amfana da karatunsa ba domin ba rayuwar Hasawa kawai ya karanta ba. Ya san Hausa da Hausawa ciki da waje. Ya san maƙwabtan Hausawa. Ya san abokan hulɗar Bahaushe. Ya san harshen Hausa, da harsunan da Hausawa ke da zumunta da su, da yadda zumuntar ta kasance. Ya san rayuwar Hausawa, da al’adusu, da al’adun sa suke so, da waɗanda ba sa so. Ya san miyagun al’adu da al’adu na gari. Rashin samun haka a yau ya sa ma’aikatanmu nay au suka zama, ɗaka gumi, waje ɗari, gado kazunzumi, zani ga ƙyaya. Bayan ba sani ba, kuma ba a san ba a sani ba, an sunsune sai da sanin ba a sani ba.

Da Me Hausa Za Ta Ciyar Da Mu Gaba?
Amfanonin karatun harshe ga mai karatunsa bayyane suke ba sai an lalaba ba. Masu tunanin ganin, wai harshenmu na gado bai da rawar da zai taka a cikin wayayyen zamani irin namu, sun yi wa Hausa sanin damisar Bunu.[47] Duk wani ci gaba da ɗan Adam zai yi tinƙahi da shi, na kowane zamani, da harshe aka assasa shi. Harshen ne ginshiƙin duk wani ci gaba da kowace ƙasa ke bugun gaba da shi. Babu ƙasar da ta ci gaba, ba ta da harshen ƙasa! Babu ƙasar da ta bunƙasa, ba ta amfani da harshenta ba wajen ilmantar da ‘yan ƙasarta. Idan haka yake, harshen ne ginshiƙin da ya tangale kowace dabara ta ciyar da ƙasa gaba. Ga abin da Narambaɗa ke cewa ginshiƙi:
          Jagora:        Shigifa in babu azara
:Kuma babu ginshiƙi
:Ai ka san sai ta tuɗe
Yara:           Me aƙ ƙarhin shigifab ba su ba.
Gindi:          Abdu ƙanen mai daga
:Kan da mu san kowa
:Kai mun ka sani Sardauna

Da mai halitta ya halicci halittarSa ta farko magana ya fara koyar da ita. Sai da baki ya biyu da magana aka fara zancen sanin yadda za a yi bautar wanda ya yi halitta. Harshe shi ne ci gaba da ya fi kowane ci gaba fice daga cikin ci gaban ɗan Adam. Wanda ya karanci harshe shi ne sarkin sarakuna cikin masu ilmi da basira’[48] domin da harshe ne za a yi hulɗa ta zamantakewa. Da harshe za a yi addini kowane irin addini ne a doron ƙasa. Da harshe ne za a yi tunanin matsugunnin da ya fi cancanta a zauna a rayu. Da harshe za a tsara dubarun zaman lafiya, da dokokin ƙasa, da tsarin mulki da hukumar da za ta tsare martabar dokoki, ta hukunta waɗanda suka saɓa mata. Ai wannan ita ce hujjar cewa, mutum ba zai zama alƙali ba, a kowace ƙasa ta duniya, face yana sa ƙosasshen ilmin harshen da ake zartar da shari’a da shi.[49] Haka kuma, ba za a yi wa mutum hukunci ba, face yana fahintar harshen da ake yi masa hukunci da shi dalla-dalla.[50] A taƙaice, karatun Hausa zai agaza wa wannan ƙasa tamu ga dukkaninb abin da ya shafi; tsaro, da yaƙi, da sulhu, da kowane tsari na gudanar da dokokin ƙasa.
Hudowar demokraɗiyya wani tsintuwar guru cikin suɗi ne ga masu karatun Hausa. Nijeira ta Arewa, babu siyasar da za ta yi, ba da harshen Hausa ba, kuma duk siyasar da ta juya wa Hausa baya tana rigayan rana faɗuwa. Tattalin arzikin kowace ƙasa da harshe aka gano shi, da shi ake haƙo shi, in na haƙowa ne, da harshe ake nemo shi, a taskace shi, a amfana da shi. Yaƙe-yaƙe, da ta da zaune tsaye, da ke ci wa duniyar ƙarni na ashirin da ɗaya tuwo a ƙwarya, bay au aka fara su ba, hasali ma, an yi has ashen za su faru, kuma ga su, sun wakana. Bakin duk da ya yi has ashen faruwarsu, shi ya tanadi yadda za a magance su. Ashe ke nan, idan aka rasa harshe, zaman lafiya ya ƙare ga al’umma. Gidajen Rediyo da Talabijin da Jaridu na duniya da ƙasa sun isa abin ba da misali.[51]
Masana tarihi, da walwala, da harshe, sun tabbatar da gudummuwar harshe ga bunƙasar kimiyyar da duniyar mutane ta samu. Mafi yawan ƙasashen da suka buwaya da kimiyya, da harshensu suke amfani. Idan sun ga wani abin buƙata cikin wani harshe, sai su fassaro shi cikin harshensu na gado, su sa zaren tunaninsu na gado. Ai musulmi suka fara ƙirƙiro har jirgin sama, da ilimin lisafi, wasu ‘yan mu-muka-iya suka fassara fasahar cikin harshensi aka bar musulunci da hamma kawai. Ƙasashen Hindu da Bulgaria da Masar da Saudiyya da Spain da Rasha duk ta tafarkin amfani da harshensu ne suka samu fice da ƙwarewa ga fannonin kimiyyar yau da ake auna ci gaban kowace ƙasa das u.[52]

Naɗewa:
Hausawa na cewa, mugun gatarinka, ya fi sari ka ba ni. Ni a fahintata, ƙwai a baka ya fi kaza a akurki. Ƙoƙarin kai na hannu gida, shi ne dabara, da wayo, gabanin da dawo a kama na dawa. Ala tilas, mu yarda da cewa, da dahuwam da bandam da suya duk gashi ya fi su sanin asirin wuta. Ba kushe abin da ba ka sani ba, za ka yi, kai dai, in ba san gari ba saurari daka. Duk da haka, a kiyaye, da jin daka, da kukan zakara, duk shiga gari ya fi su. Tuni muna sane da cewa, in ka ji namu da mai shi. Don haka, a kiyaye, mai hankali ba ya nunin gudansu da hannun hagu. Mu dai taka rawa gwargwadon takenmu, domin, in da wani ya yi rawa aka ba shi kuɗi, in wani ya yi duka zai sha. In bayan rashin sani ya fi dare duhu, wa zai daka wa cikinsa wuƙa ya yi kirari? Mu dai muna tare da makaɗa Narambaɗa:
          Jagora:        Da a ce ku gai da ɗan mai taru
:Gara a ce mai taru
Yara:           Kwak kashe kihinai
:Sai shi nasa goranai
Gindi:          Na riƙa ka da girma Audu ƙanen mai daga
:Kan da mu san kowa
:Kai mun ka sani Sardauna.


MANAZARTA

Adamu, M. (1975) Hausa Factor in West African History. Zaria: ABU Press.
Aliyu, A. Fasaha Aƙiliya. NNPC, Zaria.
Bunza, A. M. (2008) Narambaɗa. Wallafar Lagos: IBRASH, Publishers.
Bunza, A. M. 2012: “In ba ka San Gari ba Saurari Daka: Muryar Nazari Cikin Tafashen Gambo”, kammalallen bincike ba a wallafa ba.
Bangbose, A. (1977) Language and Nation: The Language Ƙuestion in Sub-Saharan Africa. Edingburgh, Uniɓersity Press.
Crystal, D. (1970) The First Dictionary of Lingusitics and Phonetics. London.
Fagge, U. U. (n.d.) Ire-iren Karin Harshen Hausa na Rukuni. Benchmark Publishers, Ltd.
Jespersen, O. (1965) The Philosophy of Grammar. New York: The Norton Library www.norton&comapany.com
Mai’aduwa, Y. A. (1982) “Harshen Hasusa a Jarida, kundin digirin BA, Kano: Jami’ar Bayero.
Maiyama, U. H. 2008: “Sata a Zamantakewar Hausawa: Nazarin Waƙoƙin Ɓarayi na Alhaji Muhammadu Gambo Fagada”, kundin digirin PhD, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Mamman, M. (2012) Essays in Hausa Grammar and Linguisitics. Zaria: ABU Press.
Musa, M. R. (1988) “Hatsin Bara: Kafofin Watsa Labarai na Al’adun Hausawa”, kundin digirin MA, Kano: Jami’ar Bayero.
Omar, S. (2012) “Hijirar Modibbo Kilo daga Sakkwato zuwa Makka”, Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Salilhi, Z. D. (1986) “Jaridun Hausa: Haɓakarsu da Gudummuwarsu kan Harshe da Al’adun Hausawa”, kundin digirin MA, Kano: Jami’ar Bayero.
Sakkwato, A. B. (2011) Ginin Jimlar Hausa: Jagora ga Mai Nazarin Harshe.
Sani, M. A. Z. (2011) Gamayyar Tasrifi da Tsarin Sautin Hausa. Zaria: ABU Press.
Tayson, L. (2006) Critical Theory Today: A User Friendly Guide. London: Routledge Taylor and Francis Group.
Trudgill, P. (1974) Sociolinguistics: An Introduction. Penguine Books.
Usman, B. (2008) “Hikimar Magabata: Rayuwar Alhaji Usmaru Nasarawa Wazirin Gwandu”, kundin digirin PhD, Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Yakasai, S. A. (2012) Jagoran Ilimin Walwalar Harshe. Sokoto: Garkuwa Media Serɓices.
‘Yar-adua, T. M. (2008) The Syntactic and Semantic Aspect of Hausa Ƙuantifiers. Kano: Clear Impressions, Ltd.


[1] Bangbose, A. (1977) Language and Nation: The Language Ƙuestion in Sub-Saharan Africa. Edingburgh, Uniɓersity Press.
[2] Na san akwai taƙaddama tsakanin manazarta Harshe da Adabi kan cewa, Hausa harshe ne ko ƙabila? A wajen Hausawa, Kalmar Hausa na da ma’noni da yawa. Tana da ma’anar ‘azanci’ ga wanda ya ƙware ga Magana. Tana ɗaukar ma’anar ‘dabara’ wajen sarrafa abu. Tana ɗaukar ma’anar ‘habaici’ wajen gugar zana ga su nan dai.
[3] To, idan haka ne, wace fa’ida ke cikin karatun harshen da ba naka ba, ba na uwarka ba, ba na ubanka ba? Da wace hujja za ka karanto harshen da ko da ka zo gidanku/ garinku ba ka da abokin labari da shi? Waɗannan abubuwa suna nuna raunin tunanin masu rena harshensu na gado.
[4] Bangbose, A. (1977) Language and Nation: The Language Ƙuestion in Sub-Saharan Africa. Edingburgh, Uniɓersity Press.
[5] Na san akwai taƙaddama tsakanin manazarta Harshe da Adabi kan cewa, Hausa harshe ne ko ƙabila? A wajen Hausawa, Kalmar Hausa na da ma’noni da yawa. Tana da ma’anar ‘azanci’ ga wanda ya ƙware ga Magana. Tana ɗaukar ma’anar ‘dabara’ wajen sarrafa abu. Tana ɗaukar ma’anar ‘habaici’ wajen gugar zana ga su nan dai.
[6] To, idan haka ne, wace fa’ida ke cikin karatun harshen da ba naka ba, ba na uwarka ba, ba na ubanka ba? Da wace hujja za ka karanto harshen da ko da ka zo gidanku/ garinku ba ka da abokin labari da shi? Waɗannan abubuwa suna nuna raunin tunanin masu rena harshensu na gado.
[7] Duk wani harshen da ka yi karatu da shi, in ba naka ne na gado ba, na wani ne, to shi ko da ya raina harshensu da wane za ka yi karatu? Don haka babu ƙasƙantaccen harshe kowane harshe, harshe ne, kuma amfaninsu da muradinsu ɗaya ne.
[8] A dubi littafin, A. Aliyu, Fasaha Aƙiliya, NNPC.
[9] Domin tantance ma’anar harshe a dubi, Crystal, D. (1970) The First Dictionary of Lingusitics and Phonetics. London. Haka kuma akwai ƙarin bayani a cikin, Yakasai, S. A. (2012) Jagoran Ilimin Walwalar Harshe. Sokoto: Garkuwa Media Serɓices. Shafi na 2.
[10] Don ƙarin bayani a dubi, Musa, M. R. (1988) “Hatsin Bara: Kafofin Watsa Labarai na Al’adun Hausawa”, kundin digirin MA, Kano: Jami’ar Bayero.
[12] Don haka ne a shekarar 1979 aka yi tunanin saka Hausa ɗaya daga cikin harsunan da za a iya magana das u a Majalisar Dokokin Duniya (United Nation)
[13] A faɗin farfajiyar Afirka ta Yamma Hausa ita ce fitaccen harshen da babu ƙasar da babu masu magana da ita. Wurin da ta yi babakere shi ne, ita kaɗai ce ta yi fice a kafofin yaɗa labarai na duniyar zamaninta. Kafofin yaɗa labarai na BBC da ƁOA da Jamus da dai sauransu.
[14] A gida Nijeriya muna da kimanin harsuna fiye da 400. Abin sha’awa, babu harshen da ya samu karɓuwa da hukuma kamar Hausa. ‘Yan bokon da ke da digirin BA da MA da PhD na Hausa sun fi kowane ‘yan bokon da suke karatun sauran harsunan Nijeriya a duniya.
[15] Buƙatar harsunan Turai su ne, su taushe harsunan da ba su ba, su hana su fice a ƙasashen da suka mallaka. Turanci da Faransanci sun kasa su sake ƙafafunsu sosai a ƙasashen Nijeriya da Nijar da Ghana da Mali da Borkina saboda hurjin kyanwa da Hausa ta yi musu.
[16] Yadda Turanci ya ci zarafin nahawun Ibo da Yaruba, bai ci zarafin nahawun Hausa haka ba. Wataƙila saboda Hausa ba gare shi kaɗai ta dogara ga are-aren kalmomin da ba ta da su ba. Hausa ta yi aro a Faransanci da Larabci da sauran maƙwabta harsunan ciki da waje. Tasirin nahawunta da ta gada kaka da kakanni Turanci bai ci nasarar ruguza shi ba.
[17] A zauruka kawai ake amfani da kalmomin fannu na Larabci a cikin koyarwar da ake yi wa ɗalibai. Are-aren kalmomin da Hausa ta yi ga Larabci ya fi yawa a fagen addinin Musulunci.
[18] Mujaddadi Ɗanfodiyo da mataimakansa sun yi rubuce-rubucen waƙoƙi da litattafai da yawa cikin harshen Hausa. Wannan shi ya ƙara wa Hausa ɗaukaka a idon masu sha’awar addinin Musulunci. Fitaccen aikin Hausa da aka yi cikin ajami a ƙarni na goma sha tara shi ne, Markabul Awwamu, na Muhammadu Tukur.
[19] Masana ilimin harsuna na ganin saboda yalwatar kalmomi ya sa harshen Hausa ya fi kowane harshe na yankinsa sauƙin koyo da fahimta.
[20] Baƙin kalmomi da Bahaushe ya aro na maƙwabtan harsuna da ke gewaye da shi da na baƙin haure yawa gare su. Duk da haka, wannan ba ta cuta wa harshen ba, saboda Bahaushe ba ya aro sai ya tabbatar da babu abin cikin harshensa. Idan kuwa ya yi aro yana Hausantar da ita ta yadda ko mai ita na asali ba ya iya gane kalmarsa ce aka aro.
[21] Kiswahili ke bugun gaban yawan mutane masu magana da shi domin farfajiyarsu shi kaɗai ne harshen da aka yi wa kaciya. To! Hausa duk da yawan da take da shi da karɓuwar da ta yi, babu ƙasar da aka keɓe ta a matsayin harshen ƙasa. Da Nijeriya ta yi haka da Afirka gaba ɗaya ta koma Bahausa. Wai duk ƙoƙarin ga na Hausa, na Hausawa ne ba da hannun hukuma ba.
[22] Zaƙin maɗi da zuma ba a kwatanta su da Hausa babu harshen da zai gwada tsawo da ita a cikin ƙarnin da muke cike a yau.
[23] Ga al’ada, wake ya fi gero tsada, amma gero ya fi wake daraja a ma’aunin Bahaushe.
[24] A tambayi Igbo a shekarar 1987 Jami’ar Nsukka ta tilasta a riƙa magana da harshen Igbo a Majalisar Ƙoli ta Jami’ar (Senate). Dalilinsu shi ne, sun fahinci in ba a yi hattara ba, Turanci zai kashe harshen Igbo gaba ɗaya. Da baya, Yarbawa suka fara yin irin wanna tunanin.
[25] Malamin kiɗi, Narambaɗa ya ce:
Jagora: Duk waɗa ɗan sarki yak kai
:Ɗan sarki aka ce mai
:Don sarki ka kira nai
:Shi sheƙo da gudu
Yara:    Ai mai jirgi ka fito
:Mai gora sai wahalab banza
Gindi:   Tura haushi ɗan Amadu
:Ɗan Sanda na Alƙali
[26] Hausa na da tasha a BBC da ƁOA da Jamus da Sin da Iran da Masar da Libya. Babu wani harshe daga cikin harsunan Nijeriya da Afirka ta Yamma da ke da wani shiri ko na sati ɗaya a shekara ne a ciki in ba Hausa ba. Ashe ko Kiswahili da ta mamaye ƙasashe da yawa ba ta samu wannan haske ba.
[27] Don ƙarin bayani a dubi, Salilhi, Z. D. (1986) “Jaridun Hausa: Haɓakarsu da Gudummuwarsu kan Harshe da Al’adun Hausawa”, kundin digirin MA, Kano: Jami’ar Bayero., da Mai’aduwa, Y. A. (1982) “Harshen Hasusa a Jarida, kundin digirin BA, Kano: Jami’ar Bayero.
[28] Masana na amfani da harshen ‘uwa’ wasu su ce ‘harshen farko’ ko ‘harshen haihuwa’ wajen tabbatar da harshen asali na mutum. Ina da fahintar cewa da za a tsayar da ɗaya, a ce, ‘harshen gado’ da zai fi fice.
[29] Wannan shi ne ra’ayin Mahdi Adamu Ngaski, don ƙarin bayani a dubi, Adamu, M. (1975) Hausa Factor in West African History. Zaria: ABU Press.
[30] Al’adar Bahaushe ta rinjayar da uba ga gado don haka a ganin Bahaushe harshen uba shi ne harshen haihuwa wato ‘harshen gado’ ba na uwa ba. Ai don haka ne nike da ra’ayin a kira shi ‘harshen gado’ kawai a huta.
[31] Daulolin sun haɗa da Gobir da Kabi da Zamfara da Zazzau da Katsina da Kano da Maraɗi wasu masana tarihi sun ce da Yawuri. Babu al’ummar da ke da irin waɗannan dauloli a cikin al’ummomin Nijeriya da Afirka ta Yamma.
[32] Babu wani tudu da tsibiri da kogi da rafi na cikin farfajiyar Afirka da ba a samun Bahaushe. Kai har cikin ƙasashen Asiya Hausawa sun yi zaman yawace-yawace tun ana zuwa aikin Haji a ƙasa, don ƙarin bayani dubi, Omar, S. (2012) “Hijirar Modibbo Kilo daga Sakkwato zuwa Makka”, Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
[33] Idan ba ya da masu magana da shi, ba ya da karnan farauta. Idan ya rasa karnan farauta ya rasa suna, harshen da ba ya da suna ba za a ce da shi harshe ba. A ƙa’idance kowane harshe a duniya yana da suna.
[34] Daulolin da muka ambata na ƙasar Hausa duka Hausa ce harshen ƙasa gare su. Maƙwabtansu ma Hausawa sun shaƙa musu Hausa, wasu sun koma Hausawa.
[35] Idan waɗanda aka Haifa da harshe su kaɗai ke iya magana da shi, ba ya dogon rai. A birnin Makka, idan ka ga yadda mutanen Pakistan da Indiya da Rasha ke magana da Hausa, ka zaci kana a Shahuci Kano. Haka ake son harshe, ya zama ana iya koyonsa cikin sauƙi.
[36] Dr. Ɗahiru Argungu na Sashen Harsunan Turai na Zamani ya ba ni labarin cewa: lokacin da yake karatun digirinsa na PhD a Uganda a Intarnational Islamic Uniɓersity in Uganda,a Mbale suka yi kiciɓis da mai sayar da nama tsire da balangu. Da suka tambaya, suka tarar da Hausawan Sakkwato ne da ke zaune a can tun yaƙin duniya na (farko ko biyu?). Ni ma na taɓa tsintuwar wani Bakano a Ingila da yawon karatun allo ya kai shi Borno daga nan sai Sudan sai Masar sai Ingila, ya share shekaru 40 a London.
[37] Irin yadda Ingilishi ya yi wa Hausa shigan kutse a daulolin ƙasar Hausa bai so ya bar ta da hakin susa ba. ‘yar sa’ar da ya ci, ‘yan boko masu ido ɗaya suka rungume shi da hannu biyu suka watsar da Hausa, da baya suka dawo da rakiyarsa dole.
[38] Harshen Hausa da al’adun Hausa sun kai wurin da karatun Hausa ba ya iya zuwa can ko da mafarki. Tun gabanin a yi tunanin ƙaƙalo boko a duniya Bahaushe ya riga ya shiga uwa duniya da Hausa da al’adun Hausawa. Mai koyon Hausa a yau, kansa ne yake taimaka wa, ya samu abinci ba Hausa yake taimakawa ta samu ɗaukaka ba. Hausa ta riga ta cira mai niya ya tashi ya bi.
[39] ‘Alif ja’ da jar tawada ake rubuta shi. ‘alif baƙi’ kuma da baƙar tawada. Don haka ne ya sa Bahaushe ya yi musu suna da irin launin tawadar da ake rubuta su.
[40] Gambo fitacccen makaɗin sata ne, cikakken sunansa Alhaji Muhammadu Gambo Fagada. Domin samun cikakken tarihinsa da waƙoƙinsa a dubi, Maiyama, U. H. 2008: “Sata a Zamantakewar Hausawa: Nazarin Waƙoƙin Ɓarayi na Alhaji Muhammadu Gambo Fagada”, kundin digirin PhD, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
[41] Idan ganin mutum na yi yana ɗaukewa irin na tsohuwar fitilar hannu ana ce da irin ganin, gani garaye-garaye. Masu tallar aya na tallar ta da cewa:
Aya ruguza aya!
Garinmu babu makaho
Sai dai mai gani garaye-garaye.
[42] Shi jahili tuɓaɓɓe, bai sani ba, bai san bai sani ba. A yi daidai a yi faɗa da shi, in an yi kuskure ya ba da tukuici.
[43] Tinƙahon kowane harshe a duniya shi ne yawan jama’ar da ke magana da shi. A ilimin harsuna ta fuskar ƙwayar sautuka da furuci da kalmomi da jimloli kowane harshe yana da su yana da yadda ake tafiyar da su. Don haka batun fifiko bai taso ba a nan.
[44] Irin hasken wata shi ke sa a dinga ganin taurari ba masu haske sosai ba. Haka harshe yakem idana ya ƙasura sai ya fara batsewa, ya haifar da karuruwan harshe barkatai.
[45] A wata fassara Makaɗa cewa yake:
Jagora: Mai kare ka farauta
:Maras kare sai
:Ya tayas a kasha
Yara:    A bar shi nan sai haɗiyar miyo.
[46] Wannan ne dalilin da ya sa wani haziƙin ɗalibi ya yi bincike a kan wani fitaccen rumbun adabi, ya sa wa kundinsa suna: Usman, B. (2008) “Hikimar Magabata: Rayuwar Alhaji Usmaru Nasarawa Wazirin Gwandu”, kundin digirin PhD, Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo. A dube shi sosai, za a tabbatar da iƙirarin da muke yi.
[47] Sanin damisar Bunu shi ne sanin da ba tabbatacce da. Bunu ya ce, ya san damisa yana ba da bayanintam ya ce, ƙarama ce, ‘yar firit, mai gashi irin na kyanwa, yaronsa na cewa, yawwa! Baba ka gane damisa. Ya ƙara bayaninsa cewa; mai manyan ƙahoni. Yaro ya ce:’Wayyo! Baba ba ita b ace.”
[48] Duk wani ilimi da ɗan Adam zai nema a duniya da harshe zai neme shi, da harshe za a bayar da shi. Wannan shi nem dalilin faɗata na cewa wanda ya karanci harshe shi ne sarkin sarakuna.
[49] Ashe gaskiyar jami’o’innu da ke tilasta waɗ alibi samun cikakken karatu a Turanci gabanin a ɗauke shi ya karanci shari’a (Law). Alƙalanci babban matsayi ne, da sai wanda ya san kansa fa harshen ake shari’a da shi.
[50]  Wannan ya nuna dole mai hankali ya tashi tsaye ya koyi harshensa da wasu harsuna da ke kusa da shi.
[51] Musibar da ta auku tsakanin Hutu da Tutsu da ta yi sanadiyyar hasarar sama ga mutane miliyan ɗaya da ake son yanzu a kwantar da ƙurar gidan Rediyon BBC ya buɗe musu tasha ta musamman da harshensu.
[52] Dubi irin matsalar da ke ga koyon sabon harshe, wai a cem idan mutum na son karatun digiri wajensu sai ya karanci harshensu. A Bulgaria sai an koyi harshe. A Russia sai an koya a France sai an koya, ga su nan dai.

Post a Comment

0 Comments