Amsoshi

Daga


 


 


 


Umar Muhammad Dogon Daji


dogondajiumaru@yahoo.co.uk


Sashen Koyar da Harsunan Faransanci


Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato


Jahar Sakkwato, Nijeriya


 


 


 


Da


 


 


Zaki, Muhammad Zayyanu


muhzayzak@udusok.edu.ng


Sashen Koyar da Harsunan Faransanci


Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato


Jahar Sakkwato, Nijeriya


 


 


Takardar da aka gabatar a taron k’asa da k’asa domin karrama Marigayi Farfesa Muhammadu Hambali Jinju mai taken: “The Challenges of Teaching African Languages and Association” des Auteurs Nigeriens en Langues Nationales (ASAUNIL) da Nigerian Indegenous Languages Writers Association (NILWA) suka shirya, ranar 19-21, 2014 a Emir Sultan, Niger Republic had’e da bukin ranar Harshen Uwa International Mother Language Day (IMLD) da UNESCO ta kaddamarTSAKURE


 

K’asashen Afirka sun had’u da Harsunan Faransanci da Turanci a hanyar mulkin mallaka amma tun kafin zuwan Turawa, akwai al’ummomin Hausawa da ke zaune a k’asashen da Ingila da Faransa suke mulki suna cud’anya da juna ta hanyoyi daban-daban. A cikin wannan kasidar zamu bayyana hanyoyin da harshen Faransanci ya bi a wajen kutsawa cikin harshen Hausa. Daga k’arshe zamu yi nazarin matsalolin da Faransawa Hausawa ke fuskanta wajen magana da harshen Hausa.

 

1.0     Gabatarwa/Shimfid’a:


Harshen Farasanci ana magana da shi a cikin k’asashen Afirika wad’anda Faransa ta mulka. Wad’annan k’asashen kuwa sune k’asar Nijar, k’asar Mali, k’asar Benin, k’asar Togo, k’asar Burikina Faso, k’asar Kwaddebuwa, k’asar Sanigal da sauransu. A duk cikin wad’annan k’asashen, Hausawa suna magana da harshen Hausa amma harshen ya garwaya da harsunan su na k’asa. Misali, a Nijar akwai Hausa daban-daban, kamar Arauci, Damagaranci, hausar Filinge, Adaranci.

A Nijeriya kuwa, akwai Hausawa da ke zaune a arewacin Nijeriya suna magana da harshen Hausa daban-daban, misali: akwai Sakkwatanci, Katsinanci, Zazzaganci, Kananci, Zamfarci da sauransu. Wad’annan al’umomin Hausawa su dad’e suna huld’a da k’asashen yammacin Afirika masu magana da Faransanci ta hanyoyi daban-daban kamar haka:

2.0     Hanyoyin Huld’ar da Aka Samu Tasiri A Kan Juna:


2.1     Auratayya:

Ta wannan hanya da yawa Hausawan Nijeriya suke auren mata daga k’asashen Faransa, musamman daga k’asar Nijar zuwa Nijeriya. Saboda auren mijin ko matar dole ya koyi Faransanci saboda ya ji dadin huld’a da matarsa.

  • Cinikayya:


Shekaru aru-aru, mutanen Nijeriya da Nijar suna kasuwanci tsakaninsu ta hanyar saye da sayarwa da kayayyakin abinci da mota. Ta wannan hanyar, Hausawa ‘yan kasuwa dole su koyi harshen Faransanci ko kuma su gamu da gamon su saboda ana iya juya baki a cucesu.

  • Addini:


Saboda tarurukan wa’azi da k’ungiyoyin watsa addinin Musulunci kamar k’ungiyar Izala da Darik’a da sauran k’ungiyoyi da ke hada jama’a daga k’asashen Afirika wuri d’aya. Masu Faransanci da masu Turanci. Koyon harshen Faransanci ya zama wajibi ga wad’annan k’ungiyoyin addini saboda su yi wa’azin su cikin nasara. A hanyar haka an buda Sunna TV ta duniyar Hausa.

2.4     Siyasa:

Ita ma wannan hanyar tana taka babbar rawa wajen hada kan al’ummomin k’asashen Nijeriya da Nijer. Ta hanyar siyasa, ‘yan siyasa daga k’asashen Faransa da Ingila suna taruwa saboda su kara ma juna ilimi. Fahimtar tsakaninsu ba ta yiyuwa sia in sun jin harsunan junansu. A saboda wannan dalilin dole ne ‘yan siyasa Hausawa na Nijeriya su koyi harshen Faransanci don biyan bukatunsu na siyasa.

2.5     Mawak’a:

Faransanci yana kutsawa a cikin Hausa ta hanyar amfanin da mawak’a ke yi da kalmomin Faransanci a cikin Hausa. Misali Fati Nijar da Shatan Zamani, dukkan su suna amfani da kalmomin Faransanci a cikin wak’ok’in su na Hausa. Misali Mamman Gawo Filinge.

2.6     Wasannin Kwaikwayo:

Harshen Faransanci yakan kutsa cikin Hausa ta hanyar wasannin kwaikwayo wad’anda suka yawaita su ka watsu a cikin k’asashen Afirika masu magana da Faransanci.

 

 

2.7     Kafafen Watsa Labarai:

Ta wannan hanyar Faransanci yakan kutsa cikin harshen Hausa musamman ta hanyoyin gidajen rediyo, da talabijin da kuma jaridu ta wak’e bada rahoton abin da suka faru a k’asashen yammacin Afirika. Misali Jamila Tangaza ta gidan rediyon Ingila wato BBC. Ta kan yi amfani da Faransanci a cikin rahotanninta na yau da kullum. Kamar Barmu Arzika, da Chima Ila Youssouf da ke kawo rahotanni daga Nijar ma’aikatan gidan rediyon BBC.

2.8     Ilimi:

Da dad’ewa gwamnatocin Nijeriya suke huld’a ta hanyar ilimi tsakanin su da k’asashen yammacin Afirika masu magana da Faransanci ta hanyar sauyin d’alibai da malammai. Malammai da makaranta daga Nijeriya ya zama tilas gare su, su koyi harshen Faransanci domin su fhaimci karatun su da aka tura su suyo. Ta wannan hanya, Faransanci zai kutsa a cikin Hausarsu. A lokacin da zasu koyi harshen, sun riga sun iya harsunan Turanci da Hausa.

https://www.amsoshi.com/2017/10/01/tsarin-cincirindon-sifa-na-hausa-da-ingilishi/

2.9     Mak’wabtaka:

K’asar Nijeriya tayi iyaka da k’asashe hud’u masu magana da harshen Faransanci. Wad’annan k’asashe kuwa su ne: Chadi, Kamaru, Nijer da Benin. Shi Faransanci ya kutsa a cikin Hausa ta hanyar iyakokin jahohin Sakkwato, Kabi, Katsina, Maiduguri da Kano a arewancin Nijeriya. Misali jahar Sakkwato ta yi iyaka da k’asar Nijer a bakin boda da ke garuruwan Illela da Kwanni. Ita kuwa jihar Kabi tayi iyaka da k’asar Nijer a garuruwan Kamba, Dolekaina da Gaya.

2.10   Kiyon Lafiya:

Hausawan Nijeriya sukan koyi harshen Faransanci ta hanyar kiyon lafiya. Musamman idan suka ziyarci asibitocin k’asashen Faransa da ke garin Galmi a k’asar Nijar ko asibitin da ke garin babbarke a k’asar jamhuriyar Benin. Ko ma babbar asibitin da ke Yamai. Duka wad’annan cibiyoyin da ke bukatar dole Bahaushe ya tafi domin neman lafiyarsa suna zama mafarin kutsawar Faransanci a Hausar Bahaushen Nijeriya.

2.11   Tsaro:

‘Yan Nijeriya da ke aikin kayan sarki misali sojoji, kwastan, imagreshin da masu farfarun kaya. Duk ayukkansu na bukatar su ziyarci k’asashen yammacin Afirika. A inda mafi yawancinsu da ke magana da Hausa sukan ci karo da Faransanci ya kutsa cikin harsunan da suka iya na Nijeriya, musamman harshen Haus ako Yarbanci ko Iyamuranci.

 

2.12   Sarauta:

Shi ma ta hanyar sarauta, akwai masarautun gargajiya da ake nad’awa a cikin Nijeriya wadda take da alak’a da k’asar Nijar. Misali, sarautar sarkin Katsina ta samo asalinta ne daga sarautar sarkin Katsinan Maradi da ke jamhuriyar Nijar. Don haka wad’annan sarautu, sarakunan gargajiya na k’asashen Hausawan Nijar da Nijeriya sukan ziyarci juna musamman lokuttan bukukuwan salla da sauran al’adun gargajiya. Wanda ya sa dole harshen Faransanci ya kutsa cikin harshen Hausa domin su tabbatar da mulkin gidajensu na sarauta.

2.13   Bauta:

Har wa yau attajirai daga Nijeriya sukan sayo bayi daga k’asashen renon Faransa domin su zama barorinsu a cikin gidajensu. Ta wannan hanyar Faransanci ya samu kutsawa a cikin harshen Hausa.

2.14   K’aura:

Ma fi yawancin Hausawa su kan yi k’aura zuwa k’asashen yammacin Afirika a inda suke zama su yi cud’anya da Faransawa. Ta wannan hanya kuwa Hausawa su takan gurbata da Faransanci. Ko kuma su Faransawan su yi kaura zuwa k’asashen Hausa, misali mutanen k’abilar Bararoji, Zabarmawa da Azbinawa da Buzaye sun cika garuruwan Hausawa makil inda suke gadi, sayar da ruwa, wankin takalma, shayi, dunkin da sauransu. Ta hanyar zaman su a cikin Hausawa ya sa Hausar su ta gurbata da harshen Faransanci. Kamar yadda zamu iya gani a cikin wannan allon. Mafi yawancin kalmomin da Hausawan Nijar mazauna Maradi ke amfani da su.

3.0     Matsalar da Kutsen Faransanci ya Haifar ga Hausa:


A saboda wad’annan bambance-bambancen hanyoyin da ke sama, Bahaushe mai koyon harshen Faransanci zai iya gamuwa da matsaloli kamar amfani da kalmomi da kuma amfnai da sunayen abubuwa daban-daban a cikin Hausar sa ta yau da kullum kamar haka:


Kalmomin HausaKalmomin Faransanci
1.Mak’ulliCle
2.Madaukin MakulaiPorte-cle
3.Takarda aiko wasik’aEnveloppe
4.Lan-holdaAmpoule
5.Wil-kobaJante
6.Daki a cikin gidaChmbre (maison)
7.Tip na mota ko mashinChambre (a air)
8.Kan pampoRobinet
9.AureMariage
10.Sa kaya kala d’aya da takalma da hulaMariage (habillement)
11.Buroshi na hakura ko na wankin takalmiBrosse
12.Maunin maiLitre
13.Yaro d’an makaranta firamareEleve
14.Abin sa hotunaAlbum
15.‘Dan TawayeRebel
16.Kayan kid’in zamaniGuitare
17.Ledar shinfid’awa k’asaParterre
18.Kud’in alawanse na ‘yan makarantaAllocation
19.Abin shan madarar jariraiBuberon
20.Gyarna jarabawaCorrection
21.WayaTelephone
22.Kyallen shafar zufaMouchoire
23.Dutsin gugaFer a repasser
24.Buga karaurawaSonner (verb)
25.Karatu a gidaLecon
26.GamColle
27.Matstsen wandoCollant
28.Jarrabawar d’aukar aiki ko shiga wata makarantaConcours
29.AlbashiSalaire
30.Abin ajiye abinci kada ya huceThermos
31.Lamar kiraBiper
32.KashiyaComptable
33.Harsashen bindigaCartouche
34.Barikin sojiCampagnie
35.SarkaChaine
36.Gidan ruwaChateau
37.Wajen d’auka ko sayarda kasettDiscotheque
38.Dakin karatuBibliotheque
39.Shago sayarda littafiLibrairie
40.Shagon sayarda maganiPharmacie
41.Hayar dakiLouer
42.Makarantar koyon tukin motaAuto ecole
43.Takardar bari a wuceLaissez-passe
44.Ku kama kunnenkunAux Oreilles
45.Kud’in JabuFaux-billet
46.Hoto fatalwaCliche
47.Vitamin maigina jikiVitamine
48.Farkon wani abuFoundation
49.Abin askiRasoir
50.Engimin machine ko motaMoteur
51.ChazaChargeur
52.Kanfen ‘yan siyasaCamp grie
53.KilomitaKilometre
54.Abin sawa ga kunneEcoteur
55.Dan karamin littafen rubutaCarnet
56.KulochiAmbriage
57.Faifan kilochiDisque
58.Gidan giyaBar d’ambriage
59.MasukiHotel
60.Salat ganyen da ake ciSalade
61.Choi garyen da ake ciChou
62.KarasCarotte
63.Dankalin turawaPomme de terre
64.InshoraAssurance
65.K’aramar bindigaPistolet
66.Abin sa ruwaTonneau
67.K’Aramar motar hayaTaxi
68.K’aramar jikkar hannuMalletee
69.Iskan gasGaz
70.Man manyan motochiGasoil
71.Mai na mota (fetur)Essence
72.FirijinFrigo
73.Wasik’aLettre
74.‘Dan majalisaDepute
75.Kayan sarkiTenue
76.Ano (sakaya kala d’aya)Uniforme
77.ShataletaleRond point
78.Wurin tsayawaStop
79.SignalClienton
80.Jar wutaFeu rouge
81.Babbar makaranta sakandaraiLycee
82.Makarantar horon malamaiEcole normale
83.Zanen gadoDrap
84.SocketteeMultiprise
85.Kwanon abinci d’ayaPlat
86.BokitiSeau
87.Zanen kofaRideau
88.Dogon hutun yara ‘yan makarantaVacances
89.Na d’ayaPremier
90.Na k’arsheDernier
91.Takardar shedar jarabawaBulletin
92.UwaMaman
93.ShugabaChef
94.RadiyoRadio
95.WakiliDelegue
96.Wurin gyarna motaGarage
97.Rufaffin takalminSoulier
98.ChasisChassis
99.ManjagaraRateau
100.Mai gyarna wutaElectricien
101.Sa wutaInstalation
102.AlmakashiCiseau
103.KatifaMatelas
104.Sakon kud’iMandat
105.Shagon ajiye kayaMagasin
106.GalamBidon
107.MachinMoto
108.KandurBougie
109.AjiClasse
110.MakarantaEcole

 

 


111.Karamin kapet
112.Littafen rubutu
113.Littafen karatu
114.Biro
115.Blackboard
116.Tabur
117.Signboard
118.Tudu da kware