Al’adar Rok’on Ruwa A K’asar Gobir: Daga Riwayar Bakandamiyar Malam Muhammad Umar Kwaren-Gamba

Amsoshi

Dr. Yakubu Aliyu Gobir


Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo Sokoto


Sashen Nazarin Harsunan Najeriya


È08035605024, email: yagobir@yahoo.co.ukTsakure


 

K’asar Gobir wani yanki ne daga cikin garuruwan Hausawa na asali. Garuruwan Hausawa na asali nan ake samun Hausawa na asali wad’anda yanayin rayuwarsu da al’adunsu suka yi daidai da yadda Hausawa ke gudanar da su. Al’adar rok’on ruwa tana daga cikin al’adun da suka mak’ale wa rayuwar Hausawa har bayan da Musulunci ya yi tasiri ga rayuwar tasu. Mak’asudin wannan takarda shi ne fito da yadda Gobirawa ke gudanar da wannan al’adar, ta bakin Malam Muhammad Umar Kwren-Gamba, daga Bakandamiyarsa.

https://www.amsoshi.com/2017/11/05/gaskiya-tunanin-bahaushen-karin-magana/

Gabatarwa:

Al’adun Hausawa sun shedi sauye-sauye da dama, saboda tasirin addinin Musulunci da shigowar bak’in al’adu. Duk da kakka’bar gara da Musulunci ya yi wa wasu al’adun Hausawa, musamman lokacin jihadin Usmanu Danfodiyo, amma har yanzu akwai sauran rina a kaba. Wannan shi ya k’arfafa wasu marubutan wak’ok’in Hausa, irin su Malam Muhammad Umar Kwaren-Gamba, suka tashi tsaye, suka ci gaba da kakka’be sauran rinar da ta rage a kaba. Mak’asudin wannan takarda shi ne fito da wani babban gurbi a cikin al’adar Bahaushe, wato rok’on ruwan sama, daga Bakandamiyar  wak’ar Malam Muhammad Umar Kwaren-Gamba ta Rok’on Ruwa.  An yi k’ok’arin kauce wa bayani a kan ma’anar wak’a da ire-irenta, ganin cewa bayanan sun gabata a cikin ayyukan masana (Yahya, 1997/2001) da ‘Dangambo, 2007) da sauransu. Da farko, ya kamata muk’alar ta fara bayanin wane ne Malam Umar Kwaren-Gamba.

 

2.0   Tak’aitaccen Tarihin Malam Muhammad Umar Kwaren Gamba:


Hausawa sun ce ‘wak’a a bakin mai ita…’ Domin samun cikakken bayani a kan tarihin rayuwar Malam Muhammad Umar, na tattauna da shi kansa da wasu ‘bangaren iyalansa da abokansa da kuma wasu almajiransa. Sannan aka harhad’a wad’annan bayanai:

An haifi Malam Muhammad Umar cikin shekarar 1949 a garin Kwaran-Gamba cikin k’asar Sabon Birnin Gobir. Wato misalin kilomita 20 Kudu maso Yamma daga Sabon Birnin Gobir, a K’aramar Hukumar Mulki ta Sabon Birni, cikin Jihar Sakkwato a Nijeriya. Kuma a nan garin ya tashi har ya girma ga hannun mahaifinsa Malam Umar wanda kuma shi ne limamin garin. Sunan mahaifiyarsa kuwa Halimatu.

Malam Muhammad Umar ya tashi gidan ilimi, ya yi karatun Alk’ur’ani mai girma ga mahaifinsa, har ya sauka. Ya kuma fara karatun ilimi duk nan ga mahaifinsa. Lokacin da ya ga ya fara fahimtar karatun ilimin littattafai, sai ya fara begen tafiya makaranta wani gari, domin ya saba da jin karatun mahaifinsa. Yana son ya ji daga wasu malamai. To kamar yadda yanayin zaman Hausawa yake, idan lokacin rani ya kama, wato bayan damana, sukan fita su bar gida, domin babu wani aiki a gida. Wasu sukan tafi neman kud’i, wasu kuma neman ilimi, har sai lokacin da wata damana ta fara, sai su dawo gida. To malam Muhammad ya fara fita zuwa makaranta a irin wannan lokaci a shekarar 1967. Garin da ya fara tafiya shi ne Marad’i a Jamhuriyar Nijar inda ya yi karatu a wurin Malam Illo, a Gusau kuwa ya yi karatu wurin Malam Jelani da Malam Musa Kanoma. A garin Isa kuwa ya yi karatu a wurin limamin Isa. A tak’aice, Malam Muhammad Umar ya rik’a kai-komo tsakanin garin Marad’i da Isa da Gusau don neman iliminsa. Wato wannan shekara ya je Marad’i, wata shekara kuma ya je Isa ko Gusau, har ya samu iliminsa gwargwadon hali.

A shekarar 1976 lokacin da gwamnati ta k’addamar da tsarin U.P.E, an bud’e makarantun furamare da sakandare da dama. Saboda haka an d’auki malamai da dama. Malam Muhammad yana d’aya daga cikin wad’annan malaman. An d’auke shi a matsayin malamin Arabiyya da addinin Musulunci domin ya koyar a furamaren da ke garinsu. Wannan shi ya tilasta masa shiga karatun zamani na Kulliya a inda ya yi kwas na J.I.S a garin K’aura Namoda, S.I.S kuwa a garin Zurmi, daga shekarun 1983 zuwa 1989.

Wani abin sha’awa ga rayuwar Malam Muhammad shi ne, duk yawuce-yawucen da yake yi na neman ilimi yakan samu gabata bisa sauran d’alibai ga malamansa. Misali a Marad’i da Gusau, duk shi ke jan-bak’i idan ana karatu. Wato duk wani wanda za a yi wa karatu, to shi ke jan Larabcin littafin, shi kuma malamin yana fassarawa. Haka kuma, tun zuwan sa karatun Kulliya shi ke jan ragamar d’alibai, tun aji d’aya har suka k’are. Wato ya yi shugaban aji (Monitor), sannan tun a shekara ta hud’u har zuwa k’arshen karatunsa, shi ne shugaban d’alibai wato (Head students). Kai har ma da ya k’are makaranta, shugaban makarantar da malamansa sai da suka nemi aronsa daga k’aramar hukumar mulki ta Sabon Birni a kan ya ci gaba da karantarwa a nan Kwalejin, saboda ganin zai iya don irin k’wazon da Allah ya ba shi, amma hakan ba ta samu ba. Malam Muhammad ya tashi da sha’war wak’a a rayuwarsa tun yana k’arami, kamar yadda yake cewa:

 

Da ma na tashi ina sha’awar wak’a, domin ina karanta wak’ok’in Infiraji na Malam Aliyu da wak’ar Limamin Isa mai suna ‘Allah Na Kira ka Ina K’uzami’.

 

Malam Muhammad Umar, ya fara rubuta wak’a ta farko a lokacin da ya sami kansa cikin k’auna da shauk’in son zuwa wani gari don ya zurfafa karatunsa. Wannan bukata ta zak’ulo da sha’awarsa da rubuta wak’a. Daga wannan lokacin ne ya rubuta baitoci wad’anda ya yi wa lak’abi da ‘Wak’ar Makaranta’. Bai kammala rubuta wannan wak’ar ba sai Allah ya cika masa burinsa na zuwa makaranta. Tun daga wannan lokaci ya ci gaba da rubuta wak’a da Larabci ko da ajami. A duk lokacin da wani abu ya faru a makaranta ko cikin gari, nan take zai zauna ya rubuta ’yan baitoci a kansa. Misali, a lokacin da aka samu k’aramar hukumar mulki ta Sabon Birni, ya rubuta wak’a. ya kuma rubuta wak’ok’in wayar da kan jama’a a kan ayyukan gwamnati, kamar wak’ar ‘Yak’i da Rashin Tarbiyya’ da wak’ar ‘Allurar Riga-Kafi’ da sauransu.

 

2.1  Bakandamiyar Malam Muhammad Umar Kwaren-Gamba:


Malam Muhammad ya rubuta wannan wak’ar ta rok’on ruwa a shekarar 1983, a lokacin da aka yi  wani fari wanda ya game ko’ina. A cikin  wannan halin ne ya rubuta wak’ar da nufin wa’azi ga al’umma da kuma rok’o ga Ubangiji Allah don samun ruwan sama. Sannan ya ce, ya za’be ta ta zama bakandamiyarsa saboda dalilai guda hud’u kamar haka:

 1. Ita kad’ai ce ta k’unshi manyan nau’ukan jigogi guda hud’u a cikinta. Jigogin       kuwa su ne:  jigon addu’a, jigon tauhidi, jigon gargad’i da kuma jigon   bushara;

 2. Haka kuma akwai ‘yan baitocin da mahaifinsa ya rubuta a ciki. Saboda     haka yana ba wak’ar wani matsayi na musamman. • Sannan sigar da aka tsara wak’ar da ita ta yi daidai ainun da sak’onnin da take d’auke da su. 1. Ya kuma ce da ita mafi yawan mutane suka san shi.


 

Haka kuma, wannan wak’ar an tsara ta kan kwar biyar-biyar ne. Kuma tana da amsa-amo iri biyu a cikinta.  Wato amsa-amon ciki da na waje a kowanne baiti. Misali, a baiti na d’aya:

 

Ya Allah Sarkinmu Rabbana,

Mai ikon komi da ko’ina,

Duk bayi mun shaida naka na,

In wak’ati ya zo na damana,

Muna rok’o Allah ka yo ruwa.

 

A nan, d’ango hud’u na farko, suna k’arewa da ‘na’, shi ne amsa-amon ciki.  Amma d’ango na biyar mai k’arewa da ‘wa’ shi ne amsa-amon waje. Amsa-amon wajenta duk bai d’aya yake tafiya da harafin ‘wa’ har k’arshenta. Amma amsa-amon ciki yana sassakewa ne tsakanin baiti zuwa baiti.  Misali, mun ga cewa a baitin da ya gabata, yana da amsa-amon ciki mai harafin ‘ba’ ne. Misali:

Allah ba tilas gare shi ba,

Mun san ba tamka gare ka ba,

Ba shawara nika so mu ba ka ba,

Rok’o na muka yi muna kira muna tuba,

Allah ka yo ruwa.

 

Haka kuma, wannan wak’a tana d’auke da baiti tis’in da hud’u (94) ne.  Kuma baitocin suna da dangantaka da juna. Wani lokaci ma akan samu za’bi-zarce ko gangara a tsakanin baitocin.  Wato ya zan ba a samun cikakkiyar ma’anar wani baiti sai tare da mai bi masa.

 

3.0  Yanayin Damana a K’asar Hausa


A k’asar Hausa, yanayin damana yakan d’auki kimanin watanni biyar ana ruwan sama. Mafi yawanci ruwan kan fara sauka a watan bakwai na Musulunci (wato Rajab). Shi ya sa Hausawa ke cewa a karin maganarsu: ‘Watan bakwai mak’arar rani, ko babu damana da alamu’. Watan bakwai na Musulunci shi ke daidaita da watan Mayu ko Yuni (watan Turawa) zuwa watan Satumba ko Oktoba. Lokacin marka ko malka (wato watan Agusta) an fi samun ruwan sama mai yawa. Yawan ruwan sama bai yawaita kamar na kudu, kuma bai k’aranta irin na hamada ba (Abdullahi, 2008). A wasu shekaru akan samu ruwan sama da yawa har ya yi ‘barna, a wasu shekaru kuma yakan d’auke da wuri, tun kafin amfanin gona ya nuna (Abdullahi, 2008). A sanadin haka, sai a samu fari. A irin wannan yanayi ne Hausawa kan fita wajen gari domin rok’on ruwa ga Mai Sama’u. Hausawa na gudanar da wannan al’ada ta rok’on ruwa tun a lokacin Maguzanci[i]. Sai kuma suka yi sa’a addinin Musulunci shi ma ya zo da bayanin halaccin rok’on ruwa da kuma yadda ya kamata a yi rok’on ruwan. Saboda, maimakon Hausawa su cirata daga rok’on ruwan Maguzanci zuwa na Musulunci, sai suka hautsina al’ada da addini, wato suka d’auko wasu al’adun Maguzanci suka had’a da na Musulunci[ii]. Wannan shi ya harzuk’a Malam Muhammad Umar Kwaren-Gamba, har ya rubuta wannan wak’a ta rok’on ruwa[iii].

 

3.1   Al’adar Rok’on Ruwa a K’asar Gobir


K’asar Gobir, babbar masarauta ce ta Hausawa a k’asar Hausa da ke Arewacin Nijeriya. Gobirawa kuwa su ne Hausawa na asali da ke zaune a wurin, mutane ne masu fad’a da tsananin yak’i. A fahintata, wannan ya sa har yanzu duk lokacin da wani ya ambaci Gobir, sai ka ji Hausawa sun ce “Gidan fad’a”. Kuma tarihin yak’e-yak’en Daulolin Borno da Mali da k’asashen Hausa, ba sa kammala sai an ta’bo Gobir, tun ma ba yak’in jihadin Shehu Usmanu ‘Danfodiyo ba. Cikakkiyar k’asar Gobir ta had’a yankin k’asashen Jamhuriyar Nijer da Nijeriya, farawa daga K’onni da Tsibiri da Marad’i, zuwa wasu sassa na Arewacin Nijeriya. Daga cikin sarakunan da suka jagoranci k’asar Gobir akwai Sarkin Gobir Babari, wanda shi ne mahaifi ga Sarki  Bawa Jangwarzo 1789 – 1790, daga nan sai Sarkin Gobir Yakubu 1794-1795 , da Sarkin Gobir Nafata, da Sarki Yumfa. An ta’ba yin wata Saraki mai suna “Inna Gobir”. Ana yi mata kirari da “Inna ’yar Bukuma, gagari maza” (Bunza, 1990:29). Daga cikin Sarakunan Gobir na farko-farko, Bawa Jangwarzo ya fi shahara. Shi ya sa makad’a Maidaji Sabon Birni yake cewa cikin Wak’ar sarkin Gobir Umaru:

 

Ga zamanin Jangwarzo,

Alhaji kura ba ta sauran cizo,

Zaki ba shi da sauran kuka,

Gara ba ta sauran gina.

 

A halin yanzu, manyan masarautun Gobirawa su ne masarautar Sarkin Tsibiri a Jamhuriyar Nijar, mai suna Sultan Abdu Bala Marafa da kuma Sarkin Gobir na Sabon Birni mai suna Alhaji Abdulhamid Balarabe Salihu.

A fannin sha’anin addini, mutanen k’asar Gobir, kamar sauran ’yan uwansu Hausawa, kafin zuwan Musulunci sun dulmuya cikin bautar iskoki. A tsarin bautarsu ta iskoki, Maguzawan Hausawa sun yarda da akwai ubangiji wanda ba a gani kuma ba a kusantar sa sai ta kan iskoki, su kuma iskoki  ba a kusantar su sai ta hanyar ’yan bori da bokaye da shugabannin tsafi (Ibrahim, 1982). Alal misali, a Kano, sun yi bautar Tsumburbura wadda mazauninta na a kan dutsin Dala, a Gobir an yi bautar Inna Doguwa, a Katsina kuma, sun yi bautar Dur’bi ta Kusheyi da tsafin ‘Dantalle a garin Dutsin-ma. A Kwatarkwashi da Tsafe an yi bautar Birkid’i da Magiro (Bunza, 1990).

Daga cikin al’adun Gobirawa na tsafe-tsafe akwai na rok’on ruwan sama, idan sun samu musibar fari. A cikin wannan al’adar, suna cakud’a al’adar Maguzanci da ta Musulunci. Malam Muhammad Umar Kwaren-Gamba ya fad’a mana yadda suke wannan al’adar a cikin Bakandamiyarsa, a baiti na 32 – 34, yana cewa:

 

 1.        Dan haka malammai ku tsawata


Dan Allah mata su bar fita

Kaburjeje da sifar mahaukata

Irin haka nan nasa a k’untata

Ma, al’umma Allah shi k’i ruwa.

 

 

 

 1. Sai ka ga mata sun fita gari


Tsirara sai kuwwa iri-iri

Ga kuma gonakki cikin fari

Ka ji dad’a sa’bo iri-iri

Wad’anda ka sa ma ba a yin ruwa.

 

 1. Ko can in sa’bonmu yai yawa


Sai a sako fari ba a yin ruwa

To kuma in kuka fara d’emuwa

Kuna kuwwa zindir kuna rawa

Kuna ‘bacin Allah ina ruwa.

 

Wannan d’abi’a ta fita tsirara, akan yi ta ne a lokacin da aka samu fari, ruwan sama suka d’auke tsakiyar damina, da sunan wai rok’on ruwa ne ake yi ga Allah. Za a biyo titi cikin gari kamar masu yin zanga-zanga. Mata sukan fito da rigunan mazansu, su kuma mazan su fito da tufafin mata (kuma duk tufafin wad’anda suka tsufa, ba masu kyau ba). Wad’ansu matan kuwa sai su yi shigar irin sana’ar mazansu. Wato, idan misali mijin d’an tauri ne sai ta yi sifar ‘yan tauri, idan kuwa makad’i ne, sai ta d’auko gangar ta rik’a kid’awa suna rawa. Suna furta wad’ansu kalmomi na batsa da sa’bon Allah. Suna rausayawa, suna yin goho, suna gwada wa Allah duburarsu, cewa dole shi yo ruwa. Ga abin da suke furtawa:

Kaburjeje burje!,

Haba Allah dibo!,

Kwarkwarar munta zindir!,

https://www.amsoshi.com/2017/11/05/hausa-cikin-hausa-martabar-hausawa-da-mai-karatun-hausa/

A wad’ansu wurare cikin k’asar ta Gobir abin ya d’an sa’ba da yadda ake yi a wasu wuraren. Wasu kuma sukan tafi da tsoho wanda ya tsufa tukuf, a gindin itacen gawo ko gidan Inna Gobir (matattarar ’yan bori da mata masu zaman kansu). Sukan kewaye tsohon, suna cewa Mai Sama’u ya yo musu fitsari ko su kashe tsohon nan. Wasu matan kuma, sukan fita daji suna sanye da tufafin mazansu ana tafe ana cewa:

“Allah yo ruwa!,

Anai maka burjak’ k’asa!”

Idan sun had’u da namiji sai su yayyaga masa tufafi su mayar da shi tsirara, wai ya yi izgili, wai ana fari me ya kai shi fita daji wajen aiki? Wato kamar bai damu da halin da ake ciki ba. Wad’annan d’abi’un su ne Malam Muhammad Umar Kwaren-Gamba ya yi kira ga malamai cewa, su tsawaci masu aikata su, domin suna k’ara fushin Ubangiji Allah, maimakon ma a samu ruwan, sai a k’ara samun tsanani cikin sha’anin fari. Sannan ya kawo muna bayanin irin yadda ya kamata a yi a Musulunci, idan har aka samu wannan matsala.  Yana cewa a baiti na 31:

 

 1. In fari yaz zo yadda za mu yi


Rok’on Allah an kace mu yi

Akwai sallah nan wadda za mu yi

Da istigfari an kace mu yi

Muna tuba Allah shi yo ruwa.

 

A wannan baiti malam Muhammad ya yi mana ishara da irin yadda ake son a yi rok’on ruwa na shari’a, kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya tabbatar a cikin  Hadissai da dama[iv], da kuma irin yadda ya kamata a aiwatar da wannan sallah da neman gafara ga Allah Ta’ala. Idan za a yi sallar rok’on ruwa, ana fita bayan gari inda ake sallae Idi ko masallacin Juma’a, ana son a fita da kaya tsofaffi da k’ank’an da kai zuwa ga Allah Mad’aukaki. A yi nafila raka’a biyu, a yi hud’uba ga mutane da su ji tsoron Allah, su tuba daga zunubansu, kuma su daina sa’bon Allah. Sannan a yi adu’a a rok’i Allah ya saukar da rahmarsa.

Malam Muhammad ya ci gaba da tsawatar irin mutanen can da ke aiwatar da wannan mugunyar al’ada ta fita zindir da kama maras kyau, da kuma yi wa Allah izgili. Ta hanyar kawo tarihi na Annabi Nuhu da mutanensa a lokacin da suka yi wannan sa’bon Allah, da kuma yadda Allah ya zubo musu azaba. Malam Muhammad ya kawo wannan k’issar kamar yadda ta tabbata a cikin Alk’ur’ani mai girma.  Mawak’in ya yi wad’annan bayanai ne musamman daga baiti na 35 zuwa na 38:

 

 1. Kun ga irin halin da kuka yi,


Shi fa mutanen Nuhu sun ka yi,

Shi tuba yacce su zo su yi,

Ga Allah suka ce sun k’i ba suyi,

Shi tai shi fad’o Allah shi k’i ruwa.

 

 1. Da Nuhu ya tabbata sun k’i jin kiran,


Shi, wudda suwa’an dai suke kira,

Sai Nuhu shi yar rok’i gafara,

Ga Allah yacce La tazar minal kafirina dayyara,

Allah sako ruwa.

 

 1. Ba fa rowan rahama ba an ka yi,


Bale wata shibka ko su tai su yi,

Ruwa na azaba dai ake ta yi,

Saboda yawan sa’bon da sun ka yi,

An ka kasha su sarai cikin ruwa.

 

 1. Shi Nuhu tuba yab bid’a su yi,


Ga Allah suka kafirta ba su yi,

Kira ga gumaka dai suka ta yi,

Kashe su cikin d’ufana an ka yi,

Sai Nuhu shi d’ai abisa ruwa da baya tai jirgin su ba ruwa.

 

Wannan kissa ko tarihin halakar da jama’ar Nuhu (AS), wani misali ne da Malam Muhammad ya kawo domin gargad’i da kuma lurar da mu jama’ar wannan zamanin cewa, irin wancan abu da ya faru ga mutanen Annabi Nuhu (AS) yana iya aukuwa gare mu matsawar ba mu bar wannan mummunan sa’bo ba.  Ga dai baitin da ke tsawatar al’umma kamar yadda mawak’in ya kawo shi:

 

 1. Halan mu dan an ba mu lamuni


Mun ka d’imauce wanga zamani

Ga matan aure muna gani

Suna kuwwa zindir da hautsine

Suna ‘bacin Allah shi yo ruwa.

 

A wannan baiti, kalmar lamuni na wak’iltar wasu hadissai ne, wad’anda suka yi bayanin cewa mu jama’ar Annani Muhammad (SAW) Allah ba zai rik’a kama mu nan take ba kan wani sa’bo da muka yi gare shi ba.  Ya yi muna lamuni sai ranar tashin k’iyama ranar tonon asiri, sannan a yi wa kowa hisabin abin da ya aikata a zamansa na duniya.  Ba kamar sauran al’ummomi da suka wuce ba, wad’anda da zaran sun aikata wani mummunan sa’bo, nan take sai a aiko da Mala’iku su kife su ko su yi musu azabar bala’i.

Daga nan sai ya ci gaba da kiran jama’a gaba d’aya da a tashi tsaye a yi gyara a kuma rok’i Allah da ya sauko da rahamarSa ga bayinSa.  Wannan rok’on shi ne tun daga baiti na 42 har zuwa na 52.  Musamman a baiti na 50 in da yake nuna a koma ga Allah ga komi ba sai bid’ar ruwan sama ba.

 

 1. Rabbi muna rok’on ka gafara


Cikin son Rahma ba mu hank’ura

Ga rok’o nai Allah maji kira

Kai muka rok’o kai muke kira

Ga komi ballanta bid’ar ruwa.

4.0 Nad’ewa


Marubata wak’ok’in Hausa sun taimaka wajen daidaita sahun imanin Hausawa da tsarkake zukatansu daga miyagun d’abi’u da al’adu. Al’adar rok’on ruwan Hausawa na d’aya daga cikin al’adun da suka samu kansu a hautsine tsakanin gargajiya da Musulunci. Bakandamiyar Malam Muhammad Umar ta tabbatar muna da haka. Hausawa na cewa: ‘Da rashin kira karen bebe ya ‘bata.’ Yawaita karanta wannan wak’a ta rok’on ruwa, musamman a kafofin watsa labarai, ya taimaka k’warai wajen kawar da wannan al’ada ta kaburjeje-burje a k’asar Gobir da sauran yankunan k’asar Hausa. ‘In kunne ya ji gangar jiki ta tsira’.

 

 

Manazarta


Augie, A.R. (1984), “The Gobir Factor in the Social and Economic History of the Rima Basin c. 1650 – 1808 A.D.”, PhD Thesis. Zaria: Ahmadu Bello University.

Barira, I.B. (2008), “The Contributions of Some Selected Gobirawa Scholars to the Development of Islam in Sokoto and Zamfara States”. M.A. Dissertation. Department of Islamic Studies. Sokoto: Usmanu Danfodiyo University.

Dumfawa, A. A. (2003), “Wak’a a Tunanin yara” Kundin digirin PhD, Sakwkato: Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo.

‘Dangambo, A. (2007), ‘Daurayar Gadon Fed’e Wak’a, (Sabon Tsari) Kano: Amana Publishers Limited.

Ibrahim, S.M. (1982) “Dangantakar Al’ada da Addini: (Tasirin Musulunci Kan Rayuwar Hausawa)”. Kundin Digiri na Biyu: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Kano. Jami’ar Bayero.

Rahimuddin, M. (1984), Muwatta Imam Malik, (Translated with Exhaustive Notes). Lahore. Pakistan: Institute of Islamic Culture.

Gobir, Y.A. (1993), “Malam Muhammad Umar kwaren-Gamba da Wak’ok’insa.” Kundin Digiri na Farko, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Sokoto: Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

Gusau, S. M. (2011), Adabin Hausa A Sauk’ak’e, Kano: Century Research and Publishing Limited.

Tsiga, I.A. (1985), “Sarkin Gobir Bawa Jangwarzo.” Kano: Hausa Publications Centre.

Yahya, A. B. (1997), Jigon Nazarin Wak’a. Kaduna: Fisbas Media Services.

Yahya, A. B. (2001), Salon Asirin Wak’a, Kaduna: Fisbas Media Services.

 

[i] Aliyu Muhammad Bunza. Laccar Aji, Kwas 710, 2000.

[ii] Maguzawa sun saba da birkice tufafi da sanya tsofaffin tufafi da kuma mata su sanya kayan mazansu idan za su je rok’on ruwa. Musulunci kuma ya yarda idan za a yi sallar rok’on ruwa a birkice tufafi, ciki ya dawo waje, da sanya tsofaffin tufafi, da niyyar k’ask’antar da kai ga Allah Mad’aukaki, amma bai yarda mata su sa tufafin mazansu ba.

[iii] Tattaunawa da Malam Muhammad Umar a Cikin Masallacin Juma’a, Sabon Birni, ranar Talata, 10/06/2001.

[iv] Duba cikin littafin Muwatta Imam Malik, Hadisi na 441 – 443.

1 comment:

 1. […] Al’adar Rok’on Ruwa A K’asar Gobir: Daga Riwayar Bakandamiyar Malam Muhammad Umar Kwaren-Gamba […]

  ReplyDelete