Ticker

6/recent/ticker-posts

Katsina: Rumfar Hausa, Gamji Matattarar Tsuntsaye


Burin wannan tattaunawa fito da irin gurbin da ke ga Katsina da Katsinawa a farfajiyar karatun Hausa, a duniyar ilimin Hausa jiya da yau. An waiwayi gurbin ƙasar Katsina cikin ƙasar Hausa da dangantakarta da sauran ƙasashen da Hausawa ke bugun gaba da su. An ƙyallaro haihuwar boko, da yadda Katsina ta agaza wa naƙudarsa, da karɓar biƙinsa da yayensa. Gudunmuwar fitattun marubutan adabi irin su Alhaji Abubakar Imam da takwarorinsa, da addibbai irin su Shata, an kakkaɓe mata ƙura. An harari manyan makarantu bakwai da ke agaza wa karatun Hausa a Katsina. Takardar ta yi nazarin yadda Katsina ta ƙwace kambun karatun Hausa daga shekarar 1967-2014...

----------------------------------------
Daga
Aliyu Muhammadu Bunza
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua, Katsina
-------------------------------------------

Takardar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani na maraba da ɗaliban Hausa sababbi na shekarar, 2014, a sashen Hausa na Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua, Katsina a babban ɗakin taro na Tsangayar Fasaha, na Jami’ar ranar Alhamis 14/08/2014 da ƙarfe goma na safe (10:00am)
TSAKURE
Burin wannan tattaunawa fito da irin gurbin da ke ga Katsina da Katsinawa a farfajiyar karatun Hausa, a duniyar ilimin Hausa jiya da yau. An waiwayi gurbin ƙasar Katsina cikin ƙasar Hausa da dangantakarta da sauran ƙasashen da Hausawa ke bugun gaba da su. An ƙyallaro haihuwar boko, da yadda Katsina ta agaza wa naƙudarsa, da karɓar biƙinsa da yayensa. Gudunmuwar fitattun marubutan adabi irin su Alhaji Abubakar Imam da takwarorinsa, da addibbai irin su Shata, an kakkaɓe mata ƙura. An harari manyan makarantu bakwai da ke agaza wa karatun Hausa a Katsina. Takardar ta yi nazarin yadda Katsina ta ƙwace kambun karatun Hausa daga shekarar 1967-2014, a cikin shekarar 1983 da 2010. A duniyar karatun Hausa, Katsina na da jigajigai (12) da muryoyinsu ke yin zara a wannan ƙarni. An kakkaɓe buzun karatun da waigo irin gudunmuwar Jami’ar UMYUK ga ƙara wa Borno dawaki. An naɗe tunanin takardar da kakkaɓar gara da waiwayen tarihin tabbatar da kasancewar “Katsina Rumfar Hausa, Gamji matattarar Tsuntsaye”. Fatar takardar ka da Katsina da Katsinawa su bari tutar karatun Hausa ta sha ƙura a hannunsu.
Gabatarwa:
Ga al’adar karatu, ɗalibinsa ya yi adalci wajen nuna wurin da ya karɓo shi, da wurin da ake samun sa, shi ne rabin ilmi ga ma’ilmanta, da masu neman ilmi. Na sha tunanin, yadda zan fuskanci Katsina ga ɗan karatuna na ɗalibi, a kowane gehe na leƙo, sai in ga babu masoka haki. A fagen tsarin shugabanci Katsina, M.G. Smith bai rage abin da ɗalibi zai tsinta ba, a ayyukansa biyu, Government in Katsina da The two Katsina. Idan aka hangi Katsina da sauye-sauyenta a zangon tarihi, me Yusuf Bala Usman ya rage da wani ɗalibi irina zai hango? Aikinsa Transformation of Katsina dogon kogi ne mai faɗi. Da na tsura wa birnin Katsina ido a ma’aunin al’ada, sai na ga Malam Munnir Mamman ya riga ya share wa Katsinawa hawaye a ayyukansa biyu masu taken: The Emergence of words in Katsina metropolis da Tarihin Unguwanin Birnin Katsina, 2011. Da na laɓaɓo ga irin karamci da na samu ga Katsinawa na Jami’ar Umaru Musa Yar’adua, na fara kakkaɓe teburin rubutu sai na yi kiciɓis da littafin malam Ingawa, Katsina gidan Kara. Da dai na ga babu wata babbar ƙofa sai na ce, ana wata haka, in ji gwanin rawa da ya faɗi. Kai tsaye na yi wa wannan takarda take: Katsina Rumfar Hausa Gamji Matattarar Tsuntsaye.
Kwance Ƙullin Fitilun Kalmomi:
Na san ɗalibai ‘yan’uwana za su so su ji, don me aka yi amfani da kalmomin “rumfa” da “Gamji” da “ Matattara” da “Tsuntsaye”? Rumfa dai ita ce mahuta bayan an motsar da jiki an wahala domin a samu. Rumfa ba domin mutum ɗaya aka yi ta ba don kowa da kowa. Katsina wata mahuta ce ga Hausawa da maƙwabtansu da baƙinsu na nesa da na kusa. Da gangan na kawo kalmar “Gamji” domin idan ba a samu sukunin yin rumfa ba, gamji na ɗauke mata ɗawainiyar. Dalilin Bahaushe ke nan da ke cewa: “Gamji babbar inuwa” wanda duk ya ratsi ayyukan da aka yi na tarihi da adabi da walwala da al’ada a kan Katsina, ba zai yi musun kasancewarta “mattatara” ba. A ganin Nufawa, Katsinawa tsuntsaye ne masu wayo “Kenci” ba su taɓa tabbata a ice/bishiya ɗaya. Don haka, suka barbazu uwa duniya, suka bar ƙofofin birninsu a buɗe baƙin arzikin na ta kwarara su amfana a amfana da su. Da fatar an yi wa matambayi susa gurbin ƙaiƙayi.
 Maƙasudi:
Babban maƙasudin wannan bincike shi ne, ya lalubo irin rawar da Katsina da Katsinawanta suka taka a fagen raya ilmin karatun Hausa. Wace rawa suka taka tun daga haihuwar boko zuwa yau da muke ciki a ɓangaren karatun Hausa da harshen Hausa da Hausawa da ya sa aka koɗa birninsu. Rumfar Hausa? Shin gabanin rumfar akwai wata rumfa ko ita ce ta farko? Gagabanin rumfar akwai gamji, ko ita ta ba da damar shuka itacen gamji karatun Hausa a duniyar ilmin Bahaushe? Ban ce na san komai a kan Katsina ba, domin baƙo ɗan shekara huɗu a gari bai isa a ce ya tantance komai sarai a garin ba, sai dai dole baƙo ya gane mai masaukinsa a riwayar Ɗankadi mai zari da ke cewa:
Jigo   : Mata ta san mijinta
          : Ko daji tag gane shi
          : Komai taron maza
Yara  : Tana bambanta shi.
Ka da in cika ku da gafara sa, ba ku ga ƙaho ba, ga yadda na hangi Katsina a fagen ilmi karatun Hausa.
Gurbin Ƙasar Katsina:
Allah Ya zaɓa wa ƙasar Katsina wani irin gurbi wanda ya dace da ita. Tana maƙwabtaka da Kano da ake yi wa kirarin Jalla Babbar Hausa. Ta haɗa iyaka da ƙasar Adar/Maraɗi da ake jin daga nan Hausawa suka ɓullo. Tana da danga da ƙasar Zamfara da ake yi wa kirari dandin Hausa. Maƙwabciyar ƙasar Zazzau ce a tsohon tarihi. Idan ban yi son kai ba, zan ce daga cikin ƙasashen Hausa babu mai irin wannan gurbi a farfajiyar daularsa. Ashe ban yi washi ba idan na kira ta; “rumfar Hausa”.
Abin ban sha’awa, Kano da ta yi ficen bunƙasa a tarihi Katsina ta ba ta tsaro ku binciki tarihin Ɗanwaire. Ƙasar Kabi da ke bugun gaba da sarki Kanta Kotal, a Katsina aka auro mahaifiyarsa. Gobirawa da ke ganin da su da mutuwa uwa ɗaya, Katsina ta koyar da su sanin dabarun yaƙi, ko kun manta da, “A mazaya...”.
Ƙasar Nufe da ke garkuwar ƙasar Hausa a fagen fatauci dole su durƙusa wa Katsinawa. Dakarkari da ke da karin maganar shiga sojan Badakkare, Katsina ce babbar cibiyarsu. Idan za a yi wa tarihi adalci, ba za a musanta cewa, babu ƙasa daga cikin ƙasashen Hausa da ke da wannan babban gaba irin na Katsina don haka iƙirarina na kiran Katsina “Babban Gamji” ba washi ba ne, karatu ne.
Bincike ya tabbatar da har gobe sarautar Maraɗi ana ce da ita “Sarkin Katsina” sarautar cibiyar Zamfara ‘Gusau’ sunanta Sarkin Katsinan Gusau. A taƙaice, kudancin Katsina daga Katsina zuwa Karaɗuwa da Zamfara ƙasar Kwatarkwashi da Tsafe suna cikin Katsinar Laka. Dukkanin daulolin da muke da su ƙasar Hausa, Gobir, Kebbi, Kano, Zazzau, da sauransu babu mai irin wannan babban baki na laso zango uku bayan cibiyar a masarautarsa sai Katsina. Da na harari wannan leshi na ƙasar Katsina ban ga na yi cika baki ba da na kira ta “Gamji Matattarar Tsuntsaye”.
Haihuwar Boko:
Bature ba da girma da arziki ya kai boko ƙasashen da ya mallaka ba. Boko cikin fitina ya zo, tsaitsaye aka karɓe shi, tsaitsaye aka bayar da shi. Manufarsa cusa harshe da al’adu da addinin Yahudu da Nasara a ƙasashen da suka mallaka. Duk da haka, Hausawa kan ce, da ɗan gari akan ci gari. Da ‘Hausa’ aka fara boko a Nijeriya ta arewa musamman ƙasar Hausa. Makarantun boko da suka yi fice a ƙasar Hausa su ne: Makarantar Nasarawa, Kano da makarantar Sakkwato 1905 da ta Katsina Middle School, 1922. Da karatu ya fara shiga ran ‘yan makaranta babu littattafan karatu, dole aka shirya gasar neman littattafai. A gasar, 1933 Katsina ta limanci bokon Nijeriya da littafin Ruwan Bagaja na Malam Abubakar Imam. Wannan littafin shi ya kai Katsina da Katsinanci wurin da dugadugan Katsina bai taka ba. Bugu da ƙari littattafan Abubakar Imam Magana Jari Ce 1-3 da Ƙaramin sani Ƙuƙumi da Kayi ta Karatu da Ka Ƙara Karatu, su suka fara fitar da karatun Hausa a duniyar ilmi. Da waɗannan karatun Hausa ya samu karɓuwa a ilmin boko, duk wani masani da malamin Hausa da bazarsu yake taka rawa. A iya sanina ya zuwa yau, ba a yi kwatankwacin su ba. Na yarda da Ɗan’anace da ya ce:
Jagora         : Mai son miya ya auri tsohuwa
                   : Mai son shimfiɗa ya auri budurwa
                   : Mai son ɗan ƙwarai ya auri isassa.
Takwaransa a fagen rubutun waƙoƙi ya ce:
A nemo manya al’amarin da yai tsawo
Zaman babban yatsa ko ba ta cin tuwo
          Ta iya ɓare malmala.
                             (Waƙar Siyasa, A.M. Bunza 1997).
Har gobe, masana adabin Hausa suna bugun gaba da Iliya Ɗan Mai Ƙarfi na Amadu Ingawa. Zaɓi Naka na Munir Mamman ba ƙaramar rawa ya taka ba. Turmin Ɗanya da Tura Ta Kai Bango, na Suleman Ibrahim Katsina sun cancanci yabo. Ibrahim Sheme, ba ƙaramar gudumuwa ya bayar ba a cikin littafin ‘Yar Tsana ba. Bilkisu Funtuwa, ta fito da ‘Ya’yan Hutu da Mugun Zuma da Duniya Rawar ‘Yanmata. Waɗannan rubuce-rubuce a ko’ina ake nazarin Hausa a binciken Hausa da koyar da Hausa za a ga a kan gaba suke. Don haka suka zama wata azara ko ginshiƙi ga rumfar da Abubakar Imam ya haƙa. Idan Katsina ta kasance haka a nazarin Hausa, to a yi wa Narambaɗa ɗa’a:
Jagora  : Shigifa in babu azara
             : Kuma babu ginshiƙi
             : Ai kun san sai ta tuɗe
             :  Mi aƙ ƙarfin shigifa
             :  Ba su ba?
Gindi    :  Na yaba ka da girma Abdu ƙanen Maidaga
             :  Kan da mu san kowa
             :  Kai mun ka sani Sardauna.

Adabin Baka:
Da aka fara karatun Hausa da Adabin Baka aka fara share fage domin shi ya haifar da rubutacce. A tunanin ɗaliban tarke adabi sun ce, waƙa tafi amo da shahara da shiga zuciyar ma’abuta adabi. A nan, Katsina ta yi tsayin daka na ganin ta zama rumfar Hausa. Da an ce waƙa in an kawo sunnan Alhaji Muhammadu Shata Katsina dole a yi shiru maƙoƙo ya fito a bakin zabiya. Abin ban sha’awa, mafi yawan mawaƙan baka irin su Kurna, Narambaɗa, Alu Ɗandawo, Salihu Jankiɗi, Sarkin Taushin Sarkin Katsina, Ɗanƙwairo, Gero Zarto, Sa’idu Faru, da suka yi fice a waƙoƙin fada, duk a gidajen suka rasu a nan aka rufe su. Alhaji Muhammadu Shata  kawai aka kai gidan uban gidansa (Mai daura) aka rufe shi. Wannan wani tarihi ne na karatun Hausa da babu wanda ya gabaci Katsinawa da shi. A gai da Narambaɗa da cewa:
Jagora         : Ɗan bajimi shi ka zama bajimi,
                   : Yai bobakali yai tozo
                   : Ɗan akuya na kallo.
Gindi          : Na yaba ka da girma
                   : Audu ƙanen Maidaga
                   : Kan da mu san kowa kai mun ka sani Sardauna.
Karatun Hausa A Katsina:
Sanin asalin rumfar da Katsina ta yi wa karatun Hausa a arewa, ya sa na ga ya kyautu a ƙyallaro wannan bagiren. Bayan makarantun Firamare da na gaba da su da ake karatun Hausa akwai makarantun ilmi mai zurfi da Hausa ta baje kolinta a ciki irin su:
i.                   Jami’ar Umaru Musa Yar’adua Katsina
ii.                 Jami’ar Musulunci ta Katsina
iii.              Federal College of Education, Katsina
iv.               College of Education Dutsin-ma
v.                 Bala Usman College of Legal Studies, Daura
vi.               Katsina Polytechnic
vii.            Federal University, Katsina (Muna Fata)
Jami’ar (UMYUK) da FCE, Katsina suna ba da digirin Hausa. Jami’ar Musulunci an saka Hausa cikin darussanta. Sauran kuwa suna ba da shaidar NCE, Federal University, muke fatan a buɗe sashen domin ɓarin waina/ masa cikin zuma ba ɓanna ba ne. A nan kaɗai za mu ga cewa, Katsina ta ɗaure wa Hausa gindi har da wuya domin yanzu haka, ma’aikatar kulawa da ilmin Jami’a ta ba da izinin a fara babban digiri M.A. da M. Phil da Ph.D a Jami’armu. Wannan ya sa Katsina ta zama ta (4) a Jami’o’in duniya da ake koyar da Hausa.
Muryar Katsina a Duniyar Karatun Hausa:
Idan an ce duniyar karatu, da an kai Jami’a an kai sin-waw-raa-taakuri in ji Bagarden allo. A tsarin ilmin Jami’a da alƙalami da littafi da kujera da allo da allin karatu ba su kai ƙima da darajar digirin First Class ba. A ɗan nawa tunanin ya kyautu a kira ta “Fintinkau” domin ita ce kan takardar kowa baya yake. A irin tsarinmu na Jami’a, ba a bayar da ita sai ga ɗalibin da aka tabbatar da cewa, ko an daka cikin turmi da su cikin masu fita. Ka ce, Shata a fagen waƙa ko Shago a fagen dambe, ko Daƙƙwale a wasan Tauri, ko Ɗantagaro a filin sata, ko Muhammadu Duguru a sana’ar gini, ko Ɗantata a zancen kuɗi, ko ka ce Fir’auna a fagen mulki, ko Manzo Muhammadu (SAW) a gurbin Annabawa. Mai digirin “Fintinkau” haka haskensa ke bayyana a cikin tsara.
A tarihin karatun Hausa na duniyar Hausawa, Bakatsine ya fara karɓar wannan digiri a birnin Kanawa, Jalla Babbar Hausa, a Jami’ar Bayero Kano, 1983. Sunan Shagon, Malam Aminu Lawal Auta Katsina. Ya yi digirin M.A 1986, PhD, 2008. Abu Kaman ƙaddara in ji Buzu da ya sha kayen raƙumi, sai ga shi, an buɗe Jami’ar Umaru Musa Yar’adua, 2006. A shekarar 2010 ta yaye ɗalibanta na farko. A sashen Hausa wani Ɗandunawa ya sake bayyana mai suna Abdurrahman Faruk ya yi wa digirin “Fintinkau” zama ɗaya kamar yadda baƙauye ke yi wa busasshen biredi. A kula da waɗannan jawabai:
i.                   An fara karatun Hausa a Nijeriya a 1967
ii.                 Yau shekaru Arba’in da bakwai 47 ana karatun Hausa a Nijeriya
iii.              Jami’o’in da suka yi fice da karatun Hausa, ABU, BUK, UDUS da Maiduguri
iv.               Daga 1967-2014 digirin Fintinkau biyu (2) kwai aka samu a duniyar bokon arewa kuma waɗannan buwayayyin duk Katsinawa ne.
Idan dai aka ɗebe ƙyashi da hassada. Da Hausa addini ne, to, Katsina annabinsa yake. Idan kuwa wata ƙasa ce, Katsina shugaban ƙasa yake. Idan kuwa mun ce, harshe ne, kuma ilmi ne, dole mu aminta da cewa, Katsina ce rumfar da za a je a baje kolin litattafan karanta shi domin can kanbum yake har yanzu babu wanda ya ƙwato shi. Wayyo! Na so Katsinawa ku ba ni dama mu yi bitar karatun nan na Narambaɗa:
Jagora         : Amadu dubi mazan gaba
                   : Dubi na baya

Yara            : Ka duba dama ka duba hauni
                   : Ka san jama’ar ga da an nan

Yara            : Ƙyauye da birni ba su da jigo sai kai,
Jagora         : Maɗi bai kai ga zuma ba
Yara            : Kowal lasa shi ka hwaɗi
Yara            : Kwandon wake
                   : Bai kai ga damen gero ba
Jagora         : Ɗan akuya ko ya yi ƙahoni
Yara            : Ya san bai yi kamar rago ba

Jagora         : Duk wada ɗan sarki
                   : Yak ƙasara
Yara            : Kak ka raba shi
                   : Da bawan sarki

Gindi          : Gogarman Tudu jikan Sanda
                   : Maza su ji tsoron ɗan maihausa
Jigajigan Katsina A Duniyar Karatun Hausa:
A fagen karatun Hausa a Jami’o’inmu za mu ga Katsina ba wai ba ce. Abin ban sha’awa, masana Hausa na Katsina ka ce zaɓa mata aka yi a fannonin da suka shahara. A ɓangarorin karatun Hausa uku ga yadda Katsina ta yi rumfa Hausa ta zauna ta huta:

Harshe:
Farfesa Isma’il Junaidu (Abuja)
Farfesa Munir Mamman ABU, Zaria
(Marigayi) Dr. Wurma ABU, Zaria
Dr. Aminu Galadima Ɓatagarawa, UMYUK
Dr. Tanimu ‘Yar’adua (BUK)
Adabi:
Dr. Aminu Lawal Auta (Fintinkau) BUK
Farfesa Ibrahim Aliyu Malumfashi, KASU, Kaduna
Dr. Mustapha Safana, UMYUK
Al’ada:
Dr. Ahmad Magaji, BUK
Dr. Bashir Sallau Sarkin Aska, UMYUK
Wasan Kwaikwayo:
Malam Adamu Ibrahim Malumfashi,
Dr. Ahmed Ɗanmaigoro FCT Katsina,
Farfesa Isma’il Junaidu shi ne garkuwansu.  Duk da haka, a cikin masana ilmin harsuna na Hausa Farfesa Munir na ɗaya daga cikin masananmu masu hannu duka dama. Ya san harshen Larabci, ya san Turanci, ya san Hausa kuma ga shi da shahadar koyar da ilmin (education). Bugu da ƙari, marubuci ne sosai, yanzu haka litattafansa uku suna shawagi hannun makaranta. Idan dai za a yi bayanin adalci daga cikin farfesoshinmu na adabi. A fannin rubuce-rubucen ƙagaggun labaru, dole a cire hula idan an ambaci Ibrahim Aliyu Malumfashi. A fagen, a yanzu, ba ya da takwara, babu ƙani, babu abokin wasa. Don tsananin wayon Bakatsine, sai ya dafa kafaɗar barden Hausa Alhaji Abubakar Imam, ya yi PhD a kan ayyukansa. Dole a girgiza wa Limamin makarantar Malam Bambadiya a duniyar yanar gizo. A fagen al’ada Dr. Ahmad Magaji Malamin Malammai ne. Su dukkansu, Malam Adamu Ibrahim Malumfashi shi ya shayar da su mama. Wanda duk ya karɓi shahaɗar Hausa Jami’ar ABU, ya ce bai san Malam Adamu ba, ban ga dalilin rashin ƙaryata shi ba. A iya sanina a yau, a duniyar karatun Hausa, babu malami ƙwararre a wasan kwaikwayo kamar sa. Idan aka harari ɗan li’irabina da kyau za a tabbatar da cewa a fagen karatun Hausa Katsina da Katsinawa suna hawan doron tunanin Ɗan’anace ga Shago:

Jagora         : Wanda bai ga damben Shago ba
                   : Na da sauran kallo
                   : Ya za ka duniya kamar bai zo ba,
                   : Kamar zuwan kare ga aboki
                   : Ko ya ƙaura ba a gafarta mai
                             (Waƙar shago).
Rawar Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua:
Wannan Jami’ar ta taimaka wa karatun Hausa ba ga bunƙasa kawai ba, ta ba shi martabar da ba a taɓa ba shi ba a tsawon shekara 47 da ake koyar da Hausa. Da farko dai, da aka buɗa ta da Hausa aka buɗa tattare da sanin ana maƙwabtaka da Jami’o’i uku da suka yi fice a Hausa. Na biyu, shugabannin Jami’ar tun kafa ta ya zuwa yau, sun bai wa Hausa damar bunƙasa da mamaye duk sassan da ake karatun Hausa a duniyar  zamaninmu. Za a tabbata haka idan aka dubi jerin masana da malaman da suka yada zango a Jami’ar da sunan koyarwa kamar haka:
Farfesa Lawal Ɗanladi Yalwa
Farfesa Isa Mukhtar
Farfesa Sa’idu Gusau
Farfesa Ahmad Baba Tela
Faefesa Muhammad Lawal Aminu
Farfesa Haruna Abdullahi Birniwa
Farfesa Ibrahim Aliyu Malumfashi
Farfesa Munir Mamman
Farfesa Salisu Ahmad Yakasai
Farfesa Atiku Dunfawa
Farfesa Aliyu, Muhammad Bunza,
Malam Adamu Mulumfashi
Dr. Aminu Lawal Auta
Dr. U.U. Fage
Dr. Ummu Ado Abbas
Dr. Ahmad Magaji
Dr. Ahmad Ɗanmaigoro
Dr. Magaji Tsoho Yakawada
Dr. Ibrahim Tsoho Yakawada
Dr. Ibrahim S.S
D. Wurma
Tattare da kasancewar Jami’ar Umaru ‘yar Jinjira idan aka auna nauyin malamanta na Hausa za a ga abin ba da wasa aka assasa shi ba. Malaman Hausa na sangaron daban-dabn na koyon Hausa a Jami’ar su ne:
1.                 Dr. Bashir Aliyu Sallau (Sarkin Aska) BA,MA,PHD (BUK) - Culture
2.                 Dr. Aminu Galadima Ɓatagarawa BA, (ABU) MA(UDUS)phd(ABU) - Language
3.                 Dr. Almustapha Shu’aibu Safana. BA, MA, (UDUS) phd (DUK) - Literature
4.                 Malam Sirajo Ibrahim, BA, MA (UDUS) - Language
5.                 Bashir Abu Sabe BA, MA, (UDUS) (Ph.D in progress Cairo) - Literature
6.                 Ado Abdulrahaman BA,(BUK) MA (UDUS) (Ph.D in progress Cairo) - Culture
7.                 Malama Zainab Isa BA, MA, (ABU) - Literature
8.                 Malama Salima Sulaiman, BA, (ABU) - Language
9.                 Malam Abdulƙadir Ɗan Alhaji BA,MA - Language
10.             Malam Abdulrahman Faruk BA, (UMAR) 1st class – Literature
11.             Malam Aminu Ibrahim, BA,MA - Culture
12.     Malam Murtala Adamu, BA, (BUK) MA (ABU) - Literature
Daga cikin malaman goma sha biyu da muke da su, uku suna da digirin Ph.D, takwas na da digirin MA, ɗaya yana da Fintinkau kuma yanzu haka yana MA a UDUS. Haka kuma, uku ne fannin al’ada, huɗu a harshe, huɗu a adabi. Haƙiƙa tsarin malaman da fannoninsu ya yi tangam mai zuwa Haji ya gamu da Annabi (SAW). Tirƙashi! Lallai Katsina rumfar Hausa ce.
MALAMAI MASU ZIYARA
1.                 Farfesa Manir Mamman
2.                 Farfesa Ibrahim Aliyu Malumfashi
3.                 Farfesa Lawal Ɗanladi Yalwa
4.                 Farfesa Aliyu M. Bunza.
5.                 Dr. Aminu Lawal Auta
6.                 Dr. Ummu Ado Abbas
Ina tabbata muku, babu Jami’ar da ake karatun Hausa a duniya da ta samu albarkar malamai masu ziyarar koyarwa irin tamu. Wannan Wani ƙarin armashi ne ga karatumu da takardun shaidar da ake bayarwa a nan. A ganina, yana ɗaya daga cikin dalilan da su ka sa yaron da ya ci digirin “Fintinkau” aka ce, a tabbatar da ita, domin ya sha nonon Farfesa goma sha ɗaya da daktoci goma. Don haka, babu sauran kukurunkudu Inyamiri ya harbe kurciya. Jerin tsarin masanan da suka yada zango Jami’ar Umaru ya cancanci a kira Katsina da Jami’ar “Rumfar Hausa”. Na tabbata Katsina gamji ce matatarar tsuntsaye, domin duk wani masani ya yi ƙoto, a nan zai zo ya yi tuƙe.
Rumfar Katsina ga Hausawa:
Ban ce, ina yarda da dukkanin abubuwan da masana tarihi da al’ada da walwala suka ce game da asalin Hausawa ba. Rashin yardata ba hujja ba ce, amma kuma hankalin karatu na alalin Bahaushe dole ya taɓo:
(i)                           Daura, wadda Hausawa ke yi wa kirari, tushen Hausa. Komai raunin tarihin Daurama yana nan a kundace, da duk aka lalubo asalin Bahaushe sai an kakkaɓo shi. Da an kakkaɓo shi dole a ambaci katsina.
(ii)                         Ba ni cikin waɗanda suka yi imani da zuwan Bayajida shi ne asalin Hausawa. Duk da haka, ban musanta kayan tarihin da ke rijiyar kusugu ba, kuma ban ƙaryatar da ziyarar Bayajida a ƙasar Katsina ba.
Sarautar  Daurama tana da alaƙa da sarautar Sarauniya Amina ta Zazzau da Inna ta Gobir da Magajiya da ake naɗa wa ƙasashen Hausa daban-daban, wanda ya haifar da Karin magana, aikin Magaji ba ya hana na Magajiya. Wannan duk, wata rumfa ce Katsina ta yi na zaunawa a huta, a sake bitar asalin Bahaushe da harshensa.
A kowace fuska aka ɗauko tarihin Bahaushe, a kan kowane irin rai za a ɗora shi Katsina ba ta ƙyalle.
Rumfar Katsina ga Addinin Bahaushe:
          A tarihin addinan gargajiya Katina ta agaza wajen adana al’adu na Bahaushe a da, da suka zama wani furen kallon hasashen addinan da suka ratsa ƙasar Hausa. A gargajiyance, ƙasar Mulumfashi da Kainafara Arnan Birci da Matsafar Jino ta Ƙasar Ƙanƙara wasu taskoki ne ga ƙasar Hausa da masu karatun Hausa. Matsafar Jino matattarar Kabawa da Gobirawa da Katsinawa da sauran maƙwabta ce. An ce, ita ce tushen kafa garin “Acida” na cikin jihar Sakkwato.
A fagen saukakkin addinai, idan aka dubi tarihin hulɗar Katsina da ƙasashen waje, tun gabanin ƙarni na sha tara akwai abin cewa. Ga alama, hulɗar kasuwanci Katsina da ƙasashen Larabawa ya yi sanadiyyar shigowar addinin Nasara da Yahudu.
Binciken da Babajo ya yi (2012) da na Shobhana Shaukar, Christian Origins in Muslim Northern Nigeria, (c. 1890-1975) da aka wallafa (2014) sun tabbatar da haka. Ke nan, rubutun boko da Hausar boko sun riga karatun boko shigowa birnin Katsina. Tarihin Musa Aya da ke Liverpool, a Ingila, ya tabbatar da wanzuwar rubutun boko a Katsina tun gabanin ƙarni na sha tara. Musa Aya madugun cinikin bayi ne da ya makara a liverpool, Ingila. Na shaidi kayayyakinsa da na je can.
Babu wani masani da zai tantance lokacin da aka fara rubutun ajami a Katsina. A duniyar Bahaushe, da an ambaci Bahaushe a kan Ilmin addini dole a gabatar da Wali Ɗanmasani da Wali Ɗanmarina. Waɗannan Katsinawa ne, kuma su suka mamaye ƙasar Hausa. Duk da yake ba a taskace tarihinsu da kyau ba, kamar yadda aka yi wa na Kano Tarikh Man bi Kano Min Auliya’il Laahi na Hausai Baukar Adakawa, ba. Husmiyyar Masallacin Gobarau ya isa zama cewa Katsina rumfa ce ga ƙasar Hausa da Hausawa.
Babu abin da ke hana wa harshen salwanta kamar rubuta. Katsinawa suka fara yi wa Hausa agaji da rubutu da harufan boko. Gare su aka fara adana ajami ta fuskar fatauci. Abin ban sha’awa, a Katsina aka fara fito da wani sabon salon rubutun Hausa, wai shi Rubutun Tafi. Wataƙila, wanda ya jahilci abin zai ga wata rigima ce aka jawo ta mayar da gaba baya. Da na sa natsuwa na karanta aikin sosai, na ga wata lamba ce aka ƙara wa Bahaushe daga cikin lambobin daraja ga harshensa da mutuncinsa. Ala tilas mu girgiza wa Injiniya ga wannan ƙoƙarin.
Sake Kafa Tutar Katsina a Duniyar Karatun Hausa
Idan muka yi la’akari da ‘yan abubuwan da aka tattauna za a ga Katsina na buƙatar Katsinawa su sake zama su kare ta. Ta da harshen da ya fi Hausa amo. Karin harshenka aka fara rubutun Hausa da shi duniyar ilmi ta Hausawa. Karin harshen Katsina ya fara wanzuwa a karatun Hausa, don haka babu yadda za a salwantar da shi komai kishin mai kishi. Lokaci ya yi ga Katsinawa su kafa wata babbar gidauniya ta:
(i)               Fassaro dukkan ayyukan da aka yi a kan Katsina daga wasu harsuna (Turanci da Faransanci da Larabci) zuwa Hausa. Manyan ‘yan boko Katsina da suka yi kundayen digirinsu na uku PhD a kowane fanni, a zauna a fassara su zuwa Hausa yadda Bahaushen Katsina zai amfana da su.
(ii)             A yi tunanin sake taron masana na musamman a yi bitar asalin Hausa da harshensu.
(iii)          A tabbata Jami’ar Tarayya ta Dutsin-ma ta buɗa Sashen Hausa domin Katsina ce cibiyarta, ya kyauta a ce ta amfani cibiyarta fiye da yadda za a amfanar da ‘yan ci rani.
(iv)    Ɗaliban Hausa na NCE da BA da MA da MPh da phD a riƙa yi musu tallar Katsina a ƙudurin kundayen bincikensu. Yin haka zai ƙara amfanar da Katsina da Katsinawa ga cibiyoyin karatu da aka girke farfajiyar ƙasarsu.
Kashedi
Ɗaliban nazari da karatu da Hausa, mai t5unanin Hausa ta takkwallai ce, don haka ya zo a ba shi takkwalin digiri, ya sake shawara zomo ba ya kamuwa daga kwance. Mai ganin ya zo sashen Hausa ya kwashi ɓagas ya yi tattara, kowa ya ci zomo ya ci gudu. Mai ganin ya rasa abin da zai yi, ya zo ya yi Hausa, ya yi ɓatan ɓakatantan ba ya ga tsuntsu ba ya ga tarko. Mai zaton ba sai ya yi karatun harshen iyayensa zai ci jarabawa ba me ya raba shi da gidansu? Ya zauna can mahaifansa su ba shi shahada ya kai gwamnati ta ba shi aiki. Fatarmu samun ɗalibai da ke sha’awar karatun harshenmu haziƙai da za mu yaye su ba duniya mamaki. Ba mu ce, mun fo kowa ba, amma babu shakka, ba mu ga karatun da ya fi namu ba, a bokon da ake yi duniya.
Naɗewa
An takura ni ƙwarai da ba ni ƙurarren lokaci daga jiya Laraba zuwa yau Alhamis 13/03/2014 na gabatar da bincike mai ma’ana. A ɗan rangadin da wannan takarda ta yi, a duniyar karatun Hausa Katsina ce gamji. Irin gudummuwar da ta bayar ya sa na kira ta “Rumfar Hausa” A yau 2014, Gwamnan Jihar Katsina, kaɗai ake kira da Sarkin Yaƙin Hausa. Haka kuma, shi ne Sarkin Fulanin Zamfara domin asalinsa Bajagwade ne daga garin Shema Ƙaramar hukumar Suru, Jihar Kabi, Muhammadu Shata kuwa, daga Sanyinna ta Sakkwato. Janar Buhari daga Borno. Fitattun gidaje irin su gidan Malam Sallau Kumasi sun yi fice a wajen Katsina, su suka wayar da Asante, garin Gamaiji da sarautun gargajiya na Ghana Katsinawa suka assasa su.
Larabawa na Alwajad irin su Abu Algais jikokinsu suka haskaka katsina. Fitattun Unguwanni irin su Farin Ɗadi da Albaba da Tanatinke da ‘Yansiliyu Larabawan Gat da Gadamus da Insala suka share musu wurin zama. Fitattun ƙwararru a Katsina sun kai suna Katsina wajen ƙasar Hausa. ƙwararru daga wajen Hausa sun yada zango a Birnin Katsina. Wannan shi ya ɗaukaka Katsina da Katsinawa da harshen Hausa, Hausa ta samu babbar Rumfa a Katsina. 

Post a Comment

0 Comments