Ticker

6/recent/ticker-posts

Kifi Na Ganin Ka Mai Jar Homa!



Waƙar ƙwar biyar ce, babban amsa amonta “ƙe”. An gina ta da baitoci talatin da uku (33) an kammala ta Alhamis 16/01/2014 da ƙarfe 11:05 na dare a Arkilla, Wamakko jihar Sakkwato. Babban abin da ke hana wa ruwa gudu a rayuwar ‘yan Adam ita ce hassada. Jiyewa mutane, da ƙin su da ɓata su da kushe cigabansu da rena ƙwazonsu da wulakanta nasarorinsu da shafa musu kashin kaji duk hassada ke haifar da su. Ɓata lokacinka na ƙoƙarin nuna cikas ga wani ba kai ba, shi zai ba da damar a gano babban cikas da ke a ƙirjinka na hassada. Me zai hana idan ka san ba yabawa za ka yi ba, ka sa wa bakinka takunkumi? Da ka bi wannan shawara, ka huta, an huta da kai.
---------------------------
Aliyu Muhammad Bunza
-----------------------------
1.       Na kiri wahidun Ƙahirun mai taimaka,
          Mai hikima da baiwa Gwani mai ɗaukaka,
Wanda ya san iraadarKa duk bai ja maka,
Komai Kah hukunto ga bawa Maiduka,
          Shi kan mumini bai da ja haka zai riƙe.

2.       Don haka Kay yi horonmu kar mu yi hasada,
Kar mu bi wanda Kab ba da ƙeta da za’ida,
Ko ramin mugunta shi faɗi cikin gada,
Mun kwanta cikin koguna tamkar kada,
          Mun dahe masunta a gurbi sun suƙe.

3.       Ranmu ya ɗauki zafi da duk muka ankara,
Babu zato na hairi da duk muka yunƙura,
Murnar cigaban ɗan’uwanmu ya faskara,
In aka zan abokai zama bisa yaudara,
          Fuska dariya zuciya ta turnuƙe.

4.       Shi mai hasada ba ya son ya ga martaba,
Gun kowa baƙin ransa dai ya ji an yaba,
Ransa ya turnuƙe bai shiru don jarraba,
Sai ya soka mugun kalamin ‘yan daba,
          Yai tsini da baki ya tamuƙe mummuƙe.

5.       Fatatai ya zan babu, babu wurin zuwa,
In aka zo garai ko akwai bai basuwa,
Zai tayye ku yawon biɗa bisa ɓassuwa,
In ya ga za a samu faɗa zai tassuwa,
          Don kowa ya taɓe ya zan abu ya tuƙe.

6.       In ya ga ya rasa ƙulle-ƙulle iri-iri,
Babu zama tsayi kodayaushe cikin shiri,
Yau Uttazu na gobe zai zama ɗan zari,
Mummunar katawarsa dole biɗan tsari,
          Take jiɓi ya tartso jiki duka zai jiƙe.

7.       Bari kuri da ɗan ƙoƙarin da kai masa,
Ko ladabi na ƙauna da kai kaka yo masa,
In ya ga mai yabo gun ka ba ya taya masa,
Sai ya ƙago illa wurin ya yi fallasa,
          Cin zarafi na kowa yana gaba zai zarƙe.

8.       Ba ya kula aboki da wa balle ƙane,
Ya bi ta malami shugaba nasa ya rine,
Babu gwani ga mugu ku tambayi Altine,
In ya ga ɗaukaka zai zamo masa ɗan zane,
          Kan da ka ce kwabo duk idanu sun jiƙe.

9.       Fatatai hasara ga wanda ya ɗaukaka,
Ya fi da son gidajenmu babu abin daka,
Nomau na bara don a ba shi, shi sa baka,
Matan tajirai na ta ga-ruwa sussuka,
          Masu gari su koma ga tallar sassaƙe.

10.     Muddin an ka zauna batun wasu ɗai a kai,
In wani zai wuce an ka gan shi a soke kai,
In aka gai da shi yaw wuce aka ta da kai,
Sharhin babu daɗi idan suka sod da kai,
          Ɗan abu ɗan ƙalilai su mai sai tuttuƙe.

11.     Kak ka sake jiki don ganin ya sake maka,
Bi shi da hankali don ganin bai ja maka,
Dakonai biɗan in da za shi fito maka,
Muddin kas sake mai jiki ya shige maka,
          Ba ka da hus asirranka tun tuni ya haƙe.

12.     Kowane lokaci shi ganin daidai yake,
Komai an ka ce bai ganin haka nan yake,
Ka yi kaɗan ka san karkatarsa ina take,
Duk wada kun ka ƙulla da shi ka ga ya fake,
          Ko kan kuskure kay yi mai abu zai haƙe.

13.     Ga fuska sakakka kamar ta mu’amala,
Sai kun zauni juna a kwana mujadala,
Haƙƙinai da kowa shi kan yi muƙabala,
Wanda ya san musiɓar da an ka yi Karbala,
          Bai haɗa zanga-zanga ya ce ciki zai laƙe.

14.     Masu ganin a yau duniyar haka nan take,
Sun yi kure zaman muminai bamban shike,
Tabbata ko zaman adilai bai ɗai yake,
Sai an yada zango Fulani ka mauɓike,
          Wanda ruwa ka ci ko takobi zai riƙe.

15.     Wanga zama gidan duniya mu yi hattara,
Ran ga na zamani mai rawa bisa ƙaddara,
Kan da mu ankaro yanzu na an gangara,
Wanda ya kwan kushewa ina yaka jin kira?
          Duk wani ƙulle-ƙullen mutum nan zai tuƙe.

16.     Hasada ta yi suna da dambe a rumfuna,
Ta ishe malamai limamai bisa alluna,
Sun yi arangama ta ci manyan riguna,
Ba laya garat, ga ta ba ta da karfuna,
          Liman ƙwam guda tak kare masa mummuƙe.

17.     ‘Yanboko suna zaune banza ta ishe,
Tak kame ƙafafunsu tas saka kurkushe,
Ta kariye gaɓoɓi wuya ya yi tomashe,
Tsufar dundumi ga gani tuni ya dushe,
          An zama wanzaman cin amanan mummuƙe.

18.     Al’amarin zaman duniya wada nas sani,
Kowa an mutum dole za a yi mai tuni,
In ya jiya ya take tudun da-na-sani,
In ya ƙiya abin nan ya zan lezan zani,
Ƙarshen ƙaiƙayi masu shiƙa zai tuƙe.

19.     Jikokin butulci ƙiyayya hassada,
Cin zarafi da giba shaƙiƙan hassada,
Ƙememe da rowa li’umman hassada,
Zamba da cin mutunci da ƙeta da za’ida,
          Kun ji ɗiyan gida Ƙoƙi mugun garsaƙe.

20.     Dole zama na gaba da Ƙizumu Ɗangiye,
Makirci shirin zurmuguɗɗu da yaf faye,
Komi an ka ƙulla da shi sai ya haye,
Kai ke ba shi, shi zai zama maka makaye,
          Jirgin danƙaro yunƙurinka raƙe-raƙe.

21.     Wanda ya ƙi ka yab bayyana maka kaj jiya,
Ko ya faɗa cikin dandali wani yaj jiya,
Bai ƙaunarka komai kukai ka yi anniya,
Nisance shi jaye jikinka da anniya,
          Baki ba shi hurin wuta in ta suƙe.

22.     Wanda wuta ta ƙuna gawai tsoro yake,
In ya ga ɓirɓishin ƙyanƙyashe kaɗa kai yake,
Hadda tuwo hayaƙinsa tsoro nai yake,
Tun a wuyar da yas sha kwatanta abin yake,
          Ba shi barin a kwasai kaman wani sassaƙe.

23.     Wanda ya so ka shure ka bar mishi duniya,
Ko hijira ka kwashe ɗiyanka da zuriya,
Fatatai ka bar godabe ka shigo ƙaya,
Allah Ya kiyaye ka kutsa haramiya,
          Yau aniyarsa ta hau jiki nasa ta laƙe.

24.     Mai ramin mugunta rufe shi ka bar haƙo,
Kai kuma mai asuta taho kwashe haƙo,
Mai tsawwa na sharri aje su ka bar jiƙo,
Ga darasi gwanin harda kun ƙi tsayi riƙo,
          Me ya rage ga murhu wutar ciki ta suƙe?

25.     In abu ya ɓata hankali kuma yab ɓata,
An shiga ƙaddara hankali ya karkata,
Take ya tura mai shi ga aikata barkata,
Sai ya ga ya fi kowa garinsu mutuntaka,
Ransa ya dinga girma gudan wani tuttuƙe.

26.     Ciwon hassada can cikin ƙirji yake,
          In ya zaburo can ga harshe zai fake,
Leɓɓa na kaɗawa kamar wani fiffike,
Ga fuska sakakka kamar daidai take,
          Kan a jima kumatun kana ishe sun jiƙe.

27.     In ya yi tambaya ci gaban wani yaj jiya,
In ya yi dariya ko hasara tab biya,
In ya yi tagumi ya ji ƙanshin jan miya,
Can a gidan maƙwabtan da yaƙ ƙi da anniya,
          Ƙanshin ya rufe zuciya tasa ya suƙe.

28.     Bai ƙyamar ya cuta wa masu biya masa,
Bai da gwani idan giiba ta motso masa,
Bai tada ga kowa idan ya kula masa,
Kai ko babu gashi yanai masa kalmisa,
          Muddin ya ga jingar tana cika mummuƙe.

29.     Malammai na tafsiru ku da ka tarjama,
Kak ku biye wa Shaiɗan ku kama taƙaddama,
Har aikin ibada ya koma gardama,
Sannu a hankali in abin yag gunduma,
          Dole a ɗebe riga wuya in ta jiƙe.

30.     Kar ku mayar da ilmi ya zan rigar ƙaya,
Ko rikici da sunna irin na gidan haya,
Cin fuska da raddi ga amsar tambaya,
Gugar zana kullun habaicin fariya,
          Shaiɗan ya ci riba gudan wata garsaƙe.

31.     Mai ni’ima ka zan addu’ar neman tsari,
Kibiyar hasada in tana kawo hari,
Ba ta da magani ban da ayoyin tsari,
Allah Ya umurce mu don haka ban bari,
          Ƙul’uzzai ka soke musibar tuttuƙe.

32.     Nai shukura ga Allah gwani mai ɗaukaka,
Gafarce ni Allah Gafuurun Maiduka,
Nai maka godiya tun da kai mini ɗaukaka,
Kai mini arzikin kai ga tsabar sussuka,
          Ai mini tukkuɗina da nono in haƙe.

33.     Tammat sai salati ga Annabi Ahmadu,
Mai waƙanku shi ne Aliyu Muhammadu,
Cutar hasada ni Alu nika wa gudu,
Na yi zama da Legas da Altine Bagudu,
          Ba magana ta cuta da mun ka ji ta laƙe.

                  Aliyu Muhamamdu Bunza
                  Sashen Koyar da Harsuna Nijeriya
Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’aduwa Katsina. Jahar Katsina
Sakkwato, Arikilla
Alhamis 16/01/2014  11:05 na dare

Post a Comment

1 Comments

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.