Ticker

6/recent/ticker-posts

Jiya Ba Yau Ba


Wanda duk ya ga jiya, ya san yau na buƙatar agajinmu. Ganin irin riƙon sakainar kashi da na yau ke yi wa al’adunmu na jiya shi ya tunzura ni rubuta wannan waƙa. Masu gani dole sai an sa su, da masu ganin ba a yi sai da su, sun yi kuskure. Hausawa sun ce, wanda ya riga ka barci dole ya riga ka tashi. Idan za a yi koyi da gabaci ba za a ci wahalar sakamakon bin son rai ba. A ganina, har gobe mazan jiya guntun igiya ne, ko kun ruɓe akwai ranarku. Matasan yau kuwa man kaza ne, in rana ta yi su narke.

--------------------------------------
--------------------------------------

1.                 Da sunan Allah guda Tabara abin bauta,
Mafifici ka buwai Buwai ga buwayarwa.

2.                 Salati ga manzonKa ka umurce mu dukkanmu,
Biyayya muka yi gare Ka babu musantarwa.

3.                 Bahaushe na ce wa zamani babbar riga,
Idan waƙaci ya yi sa ta shi ne wayewa.

4.                 A nau ra’ayi hankali ka sa a saye riga,
Ga fuskarta ake ganin alamar dacewa.

5.                 Irin manyan riguna na da ɗirka-ɗirka,
Wadatattu masu kyau da ƙarfi da daɗewa.

6.                 A da rigar taƙama ga kowa a wadace,
Ya zam mai kunya a ko’ina za ya tsayawa.

7.                 A san ka da kunya a ko’ina wata sutura ce,
Gwanin ban sha’awa da walƙiya mai burgewa.

8.                 Maras kunya ko cikin gidansu abin ƙi ne,
Abokin hulɗa cikin gari za ya rasawa.

9.                 Da an gan ka da shi, akan kira ka a ja kunne,
A ce, hayya! Da kanka in kana son morewa.

10.             Rashin kunya ƙetare ƙafafun magabata,
Anai musu kallon na da, da ba su da ganewa.

11.             A da in babba yana ɗumi ba mai tari,
Ya ƙare jawabi ana shiru ba a muɗawa.

12.             Da ya ce a yi, nan da nan da sauri a gama shi,
Da ya ce a bari, zama guda ba a daɗawa.
13.             Idan ya ce kayya! Ko ƙafa ba a ɗagawa,
Bale ya yi ƙyacci zama guda aka rugawa.

14.             Da ya yi harar guda ana gane nufinsa,
A ce masa na tuba, na bari, ban ƙarawa.

15.             Idan yai nune, gaban ya ce, an ruga can,
Da girgiza kainai zama akai ba motsawa.

16.             Ba za ka ji an ja ba, in ya ce ya lamunce,
Idan ya kaɗa kai, a dole ne aka fasawa.

17.             Da ya ja layi, aradu ba mai gitta shi,
Da yai wafaati cikin wasiyya aka sa wa.

18.             Idan ya raba gardama, a dole a shashance,
Da ya riski ana faɗa ido yaka ƙwalawa.

19.             Abokan damben da kokuwa za su yi zungum!
Faɗa ya mutu, ba gunagunin zan ramawa.

20.             A cacar baki shiru yakai bai ɗaga baki,
Da jin zarmoɗansa bakuna na kullewa.

21.             Idan ya yi rabo kashin gabanka kake kwasa,
Batun zaɓe, tsallake kashi, ko farawa.

22.             Idan an ga shi zaune, za a je can a ishe shi,
Anai masa barka da yamma sannu da hutawa.

23.             Da safe idan an ga ya fito tarbon hantsi,
A je a yi kwal lafiya da barka da fitowa.

24.             Idan aka hango ya ɗauko kaya bisa kansa,
Tara masa kanu a kai ya zaɓi na ɗorawa.

25.             Lalura duka babba ba ya roƙon a taya shi,
Gabaci aka wa da gaske ko bai godewa.

26.             Faɗin sunanai ƙiri-ƙiri cin fuska ne,
Bale laƙabi wa mutum ya ce zai furtawa?

27.             Kiran sa akai “baba” ko’ina aka tar da shi,
Gabaci yab ba shi zamani bai ƙwacewa.

28.             Zama mai hali zama da ilmi duka oho!
Da an ga samanai da hurhura sai duƙawa.

29.             Talakka ya zamto walau da mulki duka daidai,
Gabaci aka wa da shekarunsa na tsohewa.

30.             A rauni uban mai kuɗi ya ce za shi gara shi?
Dugaduggainai ka agajinsa ga ɓoyewa.

31.             A yau me yas samu zamaninmu na ƙarninmu?
Gabaci an sa shi tagumi bai da sakewa?

32.             Yana kallo an aje shi gefe an manta,
Kaman jiya ba ta agaza wa yau ba ga tasowa.

33.             Idan ba jiya yau da wa ake labarinta?
Haƙiƙan ita tay yi yau da gobe ga tsarawa.

34.             Idan ba jiya, babu gobe, jibi a bar zance,
Bale citta, da gata, shekaran jiya, ƙarawa.

35.             Da yanzu, da in an jima, da ɗazu, batun yau ne,
Idan ba jiya, lisafinsu yau, ba shi fitowa.

36.             Ashe wanda ya rayu yau, daren jiya yar rayu,
Na gobe daren rayuwarsa yau, jiya zai cewa.

37.             Tunanin jiya, in na yau ya ce, ba ya kula shi,
Ya ɗirku cikin ɗemuwa da wauta da ɓacewa.

38.             Fasahar jiya, in na yau ya ce zai ture ta,
Dabarar yau ko da tagumi taka ƙarewa.

39.             A wayonmu na yau, a sa matasa gaba ɗungum!
Tunaninmu saboda shekarunsu na tasawa.

40.             Ina suka taso? A hannuwan wa suka rayu?
Dashen asali dag gare shi reshe ka tsirowa.

41.             Idan tushen ya ruɓe batun rassa ba su,
Da ganye da fure da ‘yan ɗiya ba tartsowa.

42.             Da me ɗan yau zai gwada wa ɗan jiya wayewa?
Tuwon jiya aka zazafe na yau sai lecewa.

43.             A ba kurma rediyo da me yaka saurare?
Makaho ya yi bidiyo da me zai kallawa.

44.             A sa ɗan yau madugu mazan jiya na zaune,
Idan hanyar ta yi turunƙu wa aka sa wa?

45.             Dabarun yaro fagen faɗa ai ta karawa,
A nakkasa ƙarfi a sha wuya har shurewa.

46.             Mazan jiya makasar faɗa suke dinga faɗaɗe,
Bugu ɗaya, in dai a faɗi, in ko rugawa.

47.             Da an faɗi fagen faɗa batun ya kai ƙarshe,
Idan an ruga da an tsaya ba a daɗawa.

48.             Matashi lotto gare shi mai rata babba,
Dare duka burinsa gobe zai daɗa holewa.

49.             Mazan jiya kwana da zullumin yau ko gobe,
Da sun sara gatarinsu ɗai suka dubawa.

50.             Mazan jiya ko sun yi kuskure don jama’a ne,
Na yau don son ransu ne da burin burgewa.

51.             Na da, in an ƙaryata su sai zub da hawaye,
Su kwashi kawaici jiɓi ya dinga tararowa.

52.             A yau, ƙarya an aje ta wayo da ƙwarewa,
A shaara ta a soka rantsuwar ƙin ƙarawa.

53.             Ɓarawo kunya ka sa ya ƙaura ya salwance,
Ya bar al’ummarsa rayuwatai da macewa.

54.             Ɓarayin yau su ka mai kiɗi su ka maroƙa,
A kunyata kunya ta kunyace da kuranyewa.

55.             Ɗiya matan da saboda tsabar kunyarsu,
Ɗiyansu na farin uwar miji ke goyawa.

56.             Mazajen jiya don riƙon amana da nagarta,
Rikazin ƙasa kwag gino shi bai fara taɓawa.

57.             A yau aljifai ake ta yanka masalatai,
Cikin coci a tungune shi bai iya sheƙawa.

58.             Da duk an ka sake wa yara-yara amanarmu,
Gidaje da abin hawansu ɗai suka gyarawa.

59.             Ku dubi matasan da sun ka ja ragama yanzu,
Ido rufe sata ƙiri-ƙiri ba ɓoyewa.

60.             Su kwaso ƙazanta su kai a coci, masallatai,
A sa limamai da malamai muzancewa.

61.             A sa su halin karnuka da manyan kuraye,
Da su aka cuta da addu’ar sasantawa.

62.             Mazajen da, ba a ba su mulki su yi daru,
Su kai ga iyalai da ‘yan uwa ai ta hayewa.

63.             Kanawa ka faɗin aradu mun ga Alu Babba,
Yana sarki layya bai da ragon yankawa.

64.             Abu Mai Raɓa na Bello Sakkwato mulkinsa,
Talakkawanai ka layya bai da na yankawa.

65.             Halan kun manta da Murtala jiya yar rayu?
Da yan mutu ƙosai akai gidansu na saidawa.

66.             Gawon ya yi riƙon ƙasa yana yaro ringis!
Da yai raran dukiya Odiji ya turawa.

67.             A tsarinmu na yau ina kuɗi za su yi rara?
Da Nazaƙi da Annaboro su ka fasaltawa.

68.             Tunanin jiya bai barin na yau kwana sosai,
Jini ka hawa zullumin abin da ka tasowa.

69.             Idan jiya ta gyaru, yau tana da abin cewa,
Idan yau ta barkace na gobe ka kokawa.

70.             Sanin jiya yas sa na yau ka kuka don gobe,
Hawaye su ƙwafe ganin ido na ta ragewa.

71.             Matasa in ban da ku batun cigaba ba shi,
Ku girmama na gabanku in kuna son morewa.

72.             Rawar kai na ganin muna da ilmi da takardu,
Mu ce wa gabacinmu ba sani ba sabawa.

73.             Na baya yana baya ko kwaranga yat taka,
Mazan gaba a gigirce sun riga shi ga hangawa.

74.             Idan an ce baba an gama an kai ƙarshe,
Da an ce ɗan ɗa uba ake fara kulawa.

75.             Fa tammat Allah Ka ba mu ladar tsarin ga,
Aliyu Muhammad na Bunza ne mai ratsarawa.


                                                Aliyu Muhamamdu Bunza
                                        Sashen Koyar da Harsuna Nijeriya
Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’aduwa
Katsina.
Lahadi 12/01/2014
Arkilla, Wamakko L.G. Sakkwato

Post a Comment

1 Comments

Post your comment or ask a question.