Takardar da aka gabatar a taron ƙasa da ƙasa domin karrama Marigayi Farfesa Muhammadu Hambali Jinju mai taken: The Challenges of Teaching African Languages and Association des Auteurs Nigeriens en Langues Nationales (ASAUNIL) due da Nigerian Indegenous Languages Writers Association NILWA suka shirya, ranar 19-21 Febrairu, 2014 a Emir Sultan, Niger Republic haɗe da bukin ranar Harshen Uwa International Mother Language Day (IMLD) da UNESCO ta ƙaddamar
Daga
Aliyu Muhammadu Bunza
Sashen Koyar da Harsunan, Nijeriya
Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua, Katsina
Jahar Katsina, Nijeriya
Waya: 0803 431 6508
K’ibd’au: mabunza@yahoo.com
Gabatarwa
Barazanar da lokaci ke yi wa al’umma ga ci gaban rayuwarsu
musamman idan aka kalli mutuwa a faifan nazari, za a ga ba ƙarami ba ne.
Magabata managarta maɗaukaka mafifita mahanga nesa, da ƙyallaro baya, da suka
yi wa Hausa aikin a zo a gani an fara ƙamfarsu a ƙarninmu[i]. Idan gaba ta fara ba da
baya, baya ba ta da sauran kwanciyar hankali. Kasancewar na gaba idon na baya,
idan ya faku, na baya ya rasa idon ƙyallaro gaba. Matuƙar bagiren da sanuwar
gaba ta sha ruwa nan ta baya za ta tsoma bakinta. To! Idan ta ƙi tsoma bakin za
a ce da lauje cikin naɗi. Danƙwairo ya tabbata mana gaba ta riga ta wuce baya
ke da saura. Idan haka ne, gaba sunanta gaba, na baya na nan baya, sunansa É—an
baya. Magabatanmu da suka assasa karatun Hausa cikin Hausa, sun aza Hausa a
tafarkin cigaba. Nasararsu a fili take ko ba a yi gwari-gwari ba. Taken wannan
takarda kirarin ne gare su, da tabbatar masu da goyon bayanmu bisa ga hasashen
malamin kiÉ—i NarambaÉ—a:
Jagora: Ga abu nan a hwaÉ—i,
Yara : Babu mai hwaÉ—i
Yara : Sai ƙus! ƙus! ƙus! Akai da shi
Jagora: Wa ka hwaÉ—i?
Yara : Kai É—an baka hwaÉ—i,
Jagora: Wai, baya ka ƙwazon tunkuɗe gaba
Yara : Shi Allah ba yarda shikai ba
Yara : Mai sharri shi É—ai yaka biya
Jagora: Kai tashi biri tsohon maɓannaci,
Yara : Karen ‘buki bai É—an shawararka ba,
Yara : Shi maganar giwa yake tsare
Jagora : Ka ce wa biri duk dabbar da ac cikin daji,
Yara : Giwa taka biya.
Jagora: Aaahn!
Gindin: Ya ci maza ya kwan shina shire
Gamda’aren Sarkin Tulu Alu[ii].
Karatun
Boko
Karatun boko ba wahayi ba ne, ba kuma wani keɓaɓɓen ilmi ne da aka keɓe domin
wasu mutane na daban ba. Asalin karatun boko sana’o’i da al’adu da fasahohin da
Allah Ya albarkanci mutane da su, a kowace nahiya ta duniya suke. Hore muna
harshen sadarwa da aka yi shi ya bunƙasa su. Dabarar rubutu da Allah Ya saukar
wa mutane ita ta taimaka ga ƙara yaɗa su da bunƙasa su da taskace su. To! Daga
nan boko ya fara a duniyar mutane[iii]. A wajen Hausawa yake
“Boko”, kowace al’umma da yadda take kallonsa ta fuskar sunan da ta ba shi[iv].
Masana ilmin harsuna da bazuwarsu sun tabbatar da cewa, harshe na bunƙasa, yana
masassara, yana doguwar suma, yana ƙaura, yana balaguro kuma yana mutuwa[v]. Abubuwan da ke bunƙasa
harshe, su ke hana shi masassara. Dalilan da ke sa ya yi masassara su ke
haddasa doguwar suma. Cikin magagin suma ake samun ƙaura ko balaguro. Mutuwar
harshe kwatakwata abu ne mai wuya, amma masana sun tabbatar da shi a rubuce[vi]. Don haka, al’ummomin da
suka fara samun cigaban karatu da rubutu da harshensu na asali a rubuce, suka
yaÉ—a ilmin takarda mai suna “Boko” a Hausa[vii]. Duk wata al’umma da ta
bunÆ™asa da wannan salon adana ilmi a rubuce wannan shi ne tushen “Boko” gare
ta.
Asalin
Magana:
Asalin magana ga kowace al’umam ga harshe ake danganta shi. Harshen É—an Adam ke
sarrafa sautukan da bakinsa ke gurzawa bayan da ƙwaƙwalwa ta gama saƙa
tunaninsu. Asalin basirar a zuciya take gine, ƙwaƙwalwa ke jujjuya su
gwargwadon ƙarfin basirar mai magana. Don haka, basirar magana ta sarrafa
sautuka da ita ake haihuwar É—an Adam[viii]. Masanan da ke da wannan
tunanin sun ce, ai ba É—an Adam kawai ke da harshe ba. Wasu halittu sun fi shi
harshe mai girma, da tsawo, da faÉ—i, amma ba a ba su martabar magana ba. Duk da
irin faÉ—in baki da girmansa da darajarsa ta sarrafa abinci, harshe ya fi shi
daraja da martaba a fagen magana. Harshe ne madugun kula da É—anÉ—ano da jujjuya
yawu a baki. Don haka, a tunanin gargajiya na magana ana cewa harshe “baki”[ix]. WaÉ—annan abubuwa
da aka hanga ya sa nake da ra’ayin cewa, magana ginanniya ce a jikin mai ita
daga wanda ya ƙaga shi. Haka kuma, ita wannan maganar, ita ce ake kira HARSHE.
Dole a girgiza wa masana ilmin harsuna a kan hasashe-hasashensu na asalin
harshe ga É—an Adam. Wasu na ganin asalin amgana daga tsuntsaye da dabbobi ne[x]. Domin tabbatar da wannan
tunanin, sai an tantance, wa aka fara halitta daga cikinsu? Wa ya halitta su?
Ina aka samu labarin wannan halitta? Hasashe-hasashen masana a kan asalin
harshe idan aka É—ora su a kan waÉ—annan tambayoyi uku, za a gane wurin da salka
ke tsatsa. A taƙaice, zamu gane cewa, a tarihin samuwar harsuna, babu harshen
da ya fi wani daraja da É—aukaka. Da akwai wani harshen da za a fifita a kan
wani, da harshen da mutum na farko da ya riga kowa fara rayuwa a doron ƙasa shi
ya kamata a fifita. Wane harshe ne? A wace ƙasa mai shi ya rayu? Wa ya koyar da
shi harshen? Ire-iren waɗannan hasashe-hasashe sai a naɗe ƙasa a dangane ba a
kai ga haƙiƙanin bayanin da za a bai wa mutum a gansar da shi sosai ba. Idan
ana tare da ni a kan wannan za a ga:
·
Masu harshe ke É—aukaka harshe ba harshe ke É—aukaka kansa
ba.
·
‘Daukaka wani harshe a kan wani harshe bisa hankalin tuwo
wani irin tiƙeƙen jahilci ne da bai kamata a samu masu shi a wannan ƙarni ba.
·
·
Duk harshen da ke da masu magana da shi yana da hujjar
gwada tsawo da kowane harshe, domin babu wani ma’aunin ilmi da ya nuna wani
harshe ya fi wani.
·
Duk wani harshen duniya da baki ake sarrafa sautukansa,
kuma ‘yan Adam ke sarrafa shi ba dabbobi da tsuntsaye da Æ™wari ba. Harshen da
ya ci nasarar samun karɓuwar dabbobi da tsuntsaye da ƙwari babu laifi ya yi
bugun gaba a ji shi. Wanda duk bai kai ga wannan martabar ba, ba ya da wata
hujja ta yin kirari in ba kirarin matsoraci ba.
·
WaÉ—annan ‘yan dalilai guda huÉ—u (i-iv) su suka ba ni damar Æ™aga
sunan wannan takarda da yanke hukunci na kai tsaye cewa: kowane tsuntsu ya yi
kukan gidansu, sai dai, ban ga laifin shege ba, ya yi kukan uban wani domin ya
rasa uba.
Rubutun
Hausa A Tarihi
Gajeren tunanin wasu ke ganin wai, Hausa ba a fara rubuta ta ba sai bayan zuwan
Turawa. Wannan shi ya sa ake tuƙe bokon Bahaushe ga tarihin zuwan Turawa a
Nijeriya ta Arewa. A tarihin bazuwar Bahaushe a duniya, da tarihin bazuwar wasu
al’ummomi Æ™asar Hausa, za mu ce, fara sarrafa harshen Bahaushe a rubuce ya soma
ne tun zamanin:
·
Kakamin Gobirawa na farko da suka fara ratsu ƙasar Hausa
daga Masar. An ce, sun zo da saukakken addini na Nasara. Abin sani shi ne, duk
saukakku addini yana da azancin rubutu[xi].
·
Bazuwar Hausawa a ƙasar Hindi tun gabanin zuwan Turawan
mulli-mallaka yake. Hindi sun daÉ—e da ilmin rubutu da lisafi. Ba za a É—ebe É—anmaha
ba idan aka bi diddijin tarihi[xii].
·
·
Girkawa da suka bazu a uwa duniya, an samu ‘birbishin
shigowar su ƙasar Hausa a birnin Kano. A rijiyar Akwa an samu rubutun Hausa
cikin sautukan Girkanci[xiii].
·
·
Barebari a diddigin tarihin rubuce-rubucensu na tarihin
tafsiransu cikin harshensu, ajaminsu ya fi shekaru É—ari bakwai. Dangantakarsu
da Hausawa irin ta jini da tsoka ce. Tabbas! Ba a rasa wani abu ba, na ba da
misali ba[xiv].
·
A tarihin Bahaushe, tun fil azal, kowace zuriya daga cikin
zuriyarsa tana da tsage-tsagen fuska na gargajiya da za a iya rarrabe ta da
ita. Babu wanda zai musanta kasancewar tsagar fuska rubutu, idan za a bi
diddigin ma’anar rubutu[xv].
·
Wangarawa da suka shigo ƙasar Hausa tun wajen ƙarni na tara
zuwa goma, su kimanin É—ari huÉ—u, a Kano suka yada zango mai tsawo. Da suka
assasa addinin Musulunci, salon karatunsu da ƙidan baƙinsu ne Bahaushe ya ara.
Don haka, ba za a É—ebe É—anmahan rubuce-rubucen harshensu (na Mali) Wangaranci
da aka aka adana Hausa a ciki ba, haka kuma, ba za a rasa Hausa rubuce a cikin
harshensu ba[xvi].
·
Rubutun Ajami da shi Hausa ta yi fice da zara ga dukkanin
harsunan Afirka a kundin tarihi. Don haka, Hausa a rubuce take gabanin bayyanar
boko[xvii].
Harshen da ya kai ga ire-iren waɗannan martabobi ba ya buƙatar dafa kafaɗar
kowane harshe domin ya tashi tsaye. A tsaye aka farar da shi. A tsaye aka san
shi. A tsaye aka rabu da shi bayan da aka sadu da shi. A tsaye aka bar shi,
bayan da aka fice shi. Haƙiƙa babu harshen gida da ya riga shi wayewa a duniayr
rubutu. Yadda duk Turanci ya aro tsarin Romawa a fagen rubutu, haka Hausa ta
aro tsarin Larabawa ta É—ora bisa ga nata. Abin mamaki a ce, É—alibin harshe ke
ganin wai, sai Hausa ta roƙi roƙaƙƙe da roƙo ya rarake domin ta ciyar da
harshenta gaba. Yaushe ne hankalin karatu zai yarda da cewa:
1.
Muna da namu, mu watsar, mu je mu yi aro. Ka ce dai da kuÉ—inmu,
mu ‘boye, mu ciwo bashin da babu ranar biya.
2.
Wace hikima ke ga aron aro? Turawa dai ga Romawa suka aro
rubutu. Muna da namu, muka ƙara da na Larabawa. Me zai sa mu yi daɓin daɓakuna?
- Kai! Ina ganin lokaci ya yi mu sake yin nazarin Rubutun Tafi da
masana suka binciko na Hausa mu yi tunanin inganta shi[xviii].
Hausa A
Karatun Bokon Nijeriya:
Turawan Ingila da suka ga ƙwal uwar bari, dole suka ba da kai bori ya hau, aka
bar Hausa a tsarin ilmin boko. Tun a makarantun firamare, ake fara nuna wa yara
Hausa. A da, a zamanin ‘yan bokon farko da Hausa za a dinga koyar da yaro komai
har zuwa aji huÉ—u da biyar[xix]. Daga nan, idan bakinsa
ya yi taushi, fasaharsa ta ƙaru, a fara sa Turanci. A makarantun Sakandare da
na horas da malamai da manyan kwaleji da jami’o’i duk Hausa na da kaso mai
tsoka. Sai dai, domin a kare mata fikafikai za a sakaɗa ta ƙarƙashin sunaye
irin su:
Department of Languages
Department of African Languages
Department of Language and Linguistics
Department of Literary Studies
Institute of African Studies.
Duk da haka, martabar Hausa ba ta ragu ba. Za a taras malaman Hausa da karatun
Hausa da ayyukan Hausa da gudunmuwar Hausa sun fi yawa a ciki. A da, a karatun
boko Hausa na a matsayin Vernacular[xx], wato harshen marasa
galihu. A wasu lokuta, a sa ta cikin ‘local languages[xxi]’ wai, wasu ‘yan tsirarun
harsuna na ƙwarorin mutane. Idan ana son a kawo misalanta a rubutun ilmi, wasu
su ce, mother tongue[xxii], wasu su ce, first
language[xxiii], ga su nan dai. Duk waÉ—annan
abubuwa an rasa yadda za a yi a muzanta harshen da ake ganin ya gagari a ɗaƙile
shi. Cikin wannan guni da kishi da zunɗe da harara da tsaki da ƙyacci da gwalo
da ƙyashi da hasada, Hausa ta ci gaba da rayuwa da yaɗo da haihuwan nagartattun
‘ya’ya wandon robo daidai da kwankwason kowane irin zamani.
A cikin karance-karancen boko a Nijeriya, Hausa ta yi yaÉ—o kane-kane cikin
ilmin harsuna. Ta yi babban biga cikin tarihi da walwala da ilmin siyasa. Ta yi
zurfi cikin nazarce-nazarcen kimiyya da ƙere-ƙere da ilmin kiyon lafiya.
Tsare-tsaren tattalin arziki da tsaro da kimiyyar ƙere-ƙere Hausa na ciki
tsundum! Manyan ‘yan boko da suka yi digiri da manyan digirori cikin waÉ—annan
fannonin da bazar Hausa suka yi rawa wajen rubuta kundayen digirorinsu. Butulci
ne babba bayan an ci moriyar ganga a ce mata koren banza. Babbar magana kan ta
ita ce, masu kukan a koyar da Hausa da Turanci sun manta da cewa, hatta da masu
karatun Turanci da Hausa suke garkuwa ga kundayen digirinsu. Wannan ya tabbatar
da kasawar Turanci ga biya wa Hausawan da suka ƙware ga Turanci wadatacen
bagiren bincike. Kaico! Rashin sani ya fi dare duhu. Hausawa sun ce, hankali ke
gani ba ido ba. Haƙiƙa, mai hankali idan ya ga kurma a guje, taya shi gudu zai
yi, ba tsayawa zai yi tambayarsa me ya faru ba? Dalili kuwa, shi ne, shi kurma
gani ya yi, ba ji ya yi ba.
Koyar da
Wani Harshe Ciki Wani Harshe
A fagen ilmi, kowane harshe gashin kansa yake ci. Bisa ga Æ™a’ida, ba za a bai
wa ɗalibi takardar shaidar ƙware wa ga harsunan Afirka ko Asiya ko Turai gaba ɗaya
ba. Dole a ware harshe É—aya da aka koyar da shi a ba shi. Bisa ga tsari, kowane
harshe yana da sautuka da yadda ake furta su. Yana da tsarin furucin sauti da
wasula da yadda za a gwama su, su gina kalma. Haka kuma, ba zai rasa yadda za a
sarrafa kalmomin su ba da jimloli ba. WaÉ—annan albarkatu na harshe kamar zanen
hannu suke kowa da nasa daban. Ko da dukkanin harsuna na duniya sun yi ittifaƙin
a ce wa “ruwa” “suna” ne babu saÉ“ani. To kuwa kowanensu ba “ruwa” zai kira shi
ba. Wani ya ce “water”, wani “ruwa”, wani “maa’u”, wani “miri”, wani “diyan”,
wani ya ce “akwa”, wani “omi” wani ya ce “eyin”[xxiv]. Daga waÉ—annan misalai za
mu ga cewa, koyar da wani harshe cikin wani harshe a ƙarshen dabirtar duk ga
fasara za ta tsaya. A tsarin ilmi, fasara wani harshe zuwa wani harshe, ba shi
ne koyon harshen na haƙiƙa ba, domin masana cewa suka yi, fasara ita ce, ƙoƙarin
bayar da makusanceyar ma’ana, da za a iya fahimtar abin. Don haka suka kasa
fasara zuwa:
1.
a) Fasarar baƙi-da-baƙi
2.
b) Fasarar mai ‘yanci
3.
c) Fasarar nan take
A cikin ilimin fasara, kowace irin fasara masani ya zaɓa, ba zai fito da ruhin
madarar ma’anar harshen asali ba, sai dai a yi hasashe. A Æ™arshe, za a taras da
tsofafin kalmomi da kalmomi na al’ada da kalmomi na fannu/sana’a da ‘boyayyun
kalmomin karin harshe da daÉ—aÉ—É—un kalmomin aro da kalmomin batsa da tsokana da
wasannin motsa jiki da waƙe-waƙe da kirari da karin magana da salon magana da
gatse da barkwanci su kasa samun yalwatacciyar fasara da ta fito da ruhinsu[xxv]. Idan tussan magana na
adabin gargajiya sun lahanta, nahawun kowane ‘bangare na harshe zai samu taÉ“uwa,
a wayi gari kwalliya ta kasa biyan kuÉ—in sabulu. Dubi waÉ—annan ‘yan misalai da
ruhin ma’anonin fasarar da suka samu:
Larabci: Wabilun
Hausa: Ruwa kama da baƙin ƙwarya
Turanci: It rains cats and dogs
Larabci: Laisal khabaru kal iyaani
Hausa: Gani ya kori ji
Turanci: Seeing is believing
A cikin waÉ—annan misalai, rashin samun jituwan kalmomi bi-da-bi wajen fito da
ma’anarsu a harsunan shi ya tabbatar da cewa, ma’anar fasara gajeruwa ce. Wani
harshe ba ya biya wa wani harshe buÆ™ata domin Alhaji ‘Danmaraya Jos cewa ya yi:
Jagora: Yaro ba ya É—aukar yaro
: Sai dai rungumanni mu faÉ—i
A irin hasashen da na gabatar, a É—auka ana son koyar da Bature ko Balarabe ko
Buzu ko Bayarbe Hausa, yaya za a fasara masa waÉ—annan ya samu Æ™oshin ma’ana
wadatacciya yadda Bahaushe zai ji?
- Jarƙaniya
- Tsakin tsakuwa
- Kirɓin gumbar makauniya
- Tumu/daƙuwa/ƙuli-ƙuli/baduhu /zana/kau-da-bara/ƙago/sagau/gaabaa
Idan aka tunkari taskar harshe ta sautuka da kalmomi masu yi wa juna shigan
gizagizai za a samu salon magana, gagara Gwari, ko ƙarangiya. Duk yadda aka
nuna Æ™warewar harshe, fasara ba ta bayar da gansasshiyar ma’ana mai ruhi irin
ta harshen asali. Idan aka bijiro wa Bahaushe da wannan Turanci yaya zai mayar
wa Bahaushe da gami a ji tangam! Irin na mai zuwa Haji da ya gamu da Annabi
(SAW) a ji harafin “f” yadda take kaÉ—awa a Turanci?
- First Friday, February fifteen fifty five further Frances fride four
festival fish for four fathers from France.
Yaya za a bai wa Bature ma’anar wannan. Cikin lugudan harafin “k” yadda yake a
Hausa?
- Da Kalla da abokin Kalla sun ta fi kallon kalangu, sai aka kalle
Kalla mari wajen kallon kalangu, aka gaya wa abokin Kalla, “Maza kalla
gida da gudu ka gaya wa matar Kalla ga Kalla can an kalle da mari wajen
kallon kalangu”. Ya kalla da gudu ya kalla wa matar Kalla kira da cewa, ga
Kalla can an kalle da mari wajen kallon kalangu ta kallo kara, ta kallo da
gudu da kallabi, domin ta kalla wa wanda ya kalla wa Kalla mari wajen
kallon kalangu. Ta kalli taron kallon kalangu domin kallo wanda ya kalla
wa Kalla mari wajen kallon kalangu, da ganin ta da kallanlen kara ya kalla
da gudu, kallo ya koma ga Kalla da abokin Kalla da kallallen karan da ta
kallo domin kalla wa wanda ya kalla wa Kalla mari.
KaÉ—an ke nan daga cikin wahalolin da ba za a kai matsayar yadda za a fice su
ba, idan aka nace ga koyar da mai harshe harshensa cikin wani harshe.
https://www.amsoshi.com/2017/10/21/bitar-karatun-hausa-a-karni-na-ashirin-da-daya-krn-21/
Mafarin
Koyar da Hausa Cikin Turanci
Cikin manyan harsunan duniyar wajen ƙasar Hausa ba Turanci kaɗai Bahaushe ya
fara cin karo da shi ba. Wace martaba Turanci zai gwada wa Larabci da Girkanci
da Latinanci da Hindi da Urdu da Faransanci? Masu waÉ—annan harsuna sun riga
Bature leƙa ƙasar Hausa, sun riga shi sanin albarkatun da ke cikin ƙasar na ƙasa
da jama’a da sauransu. Me ya sa, ba su mamaye harshen Hausa ba, suka maÆ™ure
shi, suka shaÆ™e shi, suka cukuikuye shi a keji, suka hana shi ‘yancin yawo da Æ™afafunsa?
Dalilan da suka sa haka kaÉ—an daga cikinsu, su ne:
1.
Turanci ya zo wa ƙasar Hausa da fuskoki daban-daban. Fuska
ta farko an zo da niyyar buɗe ido cikin rigar leƙen asiri. Wanda duk ke son ya
miƙe ƙafafunsa, ya yi munafunci da azuzanci da makirci da maƙarƙashiya da zagon
Æ™asa ga wata/wasu al’umma, dole sai ya koyi harshensu. Haka kuma, zai tilasta a
koyi harshensa domin ya riƙa jin wainar da ake toyarwa[xxvi].
Wannan shi ne babban mafarin ruɓaɓɓen tunanin.
2.
Muradun Turawa su bazu, al’adunsu su mamaye Æ™asa, a Turance
mutane da harshe da al’ada. Cikin wannan dabarar ce za a cusa musu addinan
Nasara su rungume shi hannu biyu domin an fi ƙarfinsu. To! Cikin rigar addini
za a shimfiÉ—a mulkin mallaka cikin ruwan sanyi. Littafin Allah a hannu dama, a
hannu hagu bindiga, a zuci mulkin mallaka. Haka ko aka yi[xxvii].
- Cunkoson da ƙasashen Turai suka yi da kaya jibge babu masaya. Yunwa
da fatara da rashin aikin yi na yi wa mutane barazana, shi ya haifar da
neman mafaka a ƙasashen Afirka ido rufe. Don haka, an fito cin ranin da
babu ranar komawa, ko’ina aka ga wurin zama za a yi mannanu Æ™uda ya faÉ—a Æ™waryar
alewa. Ashe ke nan, dasirar koyar da Bature Hausa domin ya samu mafaka,
ita ce ta haifar da koyar da Hausa cikin Turanci domin Turawa su amfana da
nahawunta, ba don amfanar da Hausawa ba[xxviii].
1.
Rahotannin da Turawan leƙan asiri ke rubutawa cikin
harshensu suke rubutawa. WaÆ™ilansu da ‘yan barandarsu da suka koya wa harshensu
domin su farauto asirranmu a rubuce a adana musu. Asirranmu cikin harshenmu
suke. Dole a fasara su, a rubuta su cikin Turanci. Mai fasara dole ya ƙware ga
harsuna biyu: harshen asali da harshen bayar da fasara. Tushen koyar da Hausa
cikin Turanci a nan ta samo asali, domin Turawan leƙen asiri su tabbatar da
cewa abubuwan da aka fasara musu a rubuce daidai suke[xxix].
2.
Bayan da ‘yan leÆ™en asiri suka gama aikinsu, tunanin
kutsowa ƙasashen Afirka ya zo a zuciyar Turawa. Tunanin ya haifar da kafa
sansanin koyar da harsunan Afirka a Turai musamman Ingila, Jamus, Faransa da
Rasha. Hausa na daga cikin harsunan da ke sahun gaba a wannan tunanin. Sojojin
yaÆ™i da ‘yan leÆ™en asiri da Mishon da Ma’aikatan hukumar mulkin mallaka aka
fara koyar da su Hausa tun a ƙasashen Turai. Waɗannan abubuwa ba don ceton
harshen Hausa aka tsara su ba, don ceton masu son su cuci Bahaushe ne. Asalin
koyar da Hausa cikin Turanci domin amfanar da Turawan da ke koyon Hausa ne. Kai
da ke da harshenka, wace dambala za ta sa a aro wani harshe a koyar da kai shi,
in ba renin wayo da rashin kishi da rashin sanin ciwon kai da ‘bata tunani da
mayar da gaba baya da ɗaure wa ƙarya gindi ba?
Uzurin
Masu Ra’ayin Aron Hannu:
‘Dalibai da ke da ciwon koyon Hausa cikin Turanci ban ga laifinsu ba, domin
kowa da bukin zuciyarsa. Duk da haka, tilasta mutum ya ciwo bashin abin da yake
da shi, ko ya yi aron abin da ya mallaka, wata irin dambala ce makusanciyar
manomin da ya saya abincin da ya noma da kuÉ—in aljihunsa, ya biya kansa da
kansa. Daga cikin uzurran da masu ganin dole a koyar da Hausa cikin Turanci ke
faÉ—a akwai:
1.
Turanci ne harshen ƙasa, dole kowa ya rungume shi a kowane
aiki da ya danganci hukuma. Karatun Hausa na cikin tsarin hukuma, dole a yi shi
a Turanci[xxx].
2.
Babu wani takamammen aikin nahawu na Hausa da aka yi a
rubuce, don haka, dole a ari na Turanci a isar da saƙo[xxxi].
- Idan ana son a koyar da Hausa cikin Hausa, za a ci karo da
matsalolin fasarar wasu kalmomin ilmi (fannu) da babu yadda za a sarrafa
su zuwa Hausa[xxxii].
1.
Karatun Hausa ilmi ne kamar sauran ilmuka, dole a koyar da
shi a harshen da ake koyar da sauran darusan karatu a makarantunmu. Wai! Yin
haka, zai sa ta samu karɓuwa a fahince ta[xxxiii].
2.
Sun ce, akwai ƙarancin wadatattun kalmomi na Hausa da za su
iya wadatar malamin Hausa ya koyar da Hausa cikin Hausa[xxxiv].
3.
Ana hangen barazanar kimiyya da cigaban ƙere-ƙere zai baro
Hausa da Hausawa a baya idan aka nace da koyar da Hausa cikin Hausa[xxxv].
- Uzurin wasu masu koyar da Hausa cikin Turanci shi ne, malaman da
suka ba su digiri ko suka duba babban digirinsu ba Hausawa ba ne, sun fi
son abin cikin Turanci. Daga nan suka zaƙe suka fi mai kora shafawa[xxxvi].
- A gaskiya, da yawa daga cikin masu son a koyar da Hausa cikin
Turanci ciwo biyu ke damun su. Na farko, a ce sun iya Turanci. Na biyu, ka
da a ce, ba su iya Turanci ba. Na uku, suna ganin sun waye, yin Hausa
gidadanci ne[xxxvii].
1.
Wasu sun ce, wai! Hausawa sun kasa tsayi su yi wani
takamammen aiki na yadda za a fuskanci karatun Hausa cikin Hausa. Dole idan
yadda aka so ba ta samu ba, a yi yadda ba a so, a zauna lafiya[xxxviii].
2.
Wata hujjar rashin hujja ita ce, wai akwai harsunan
Nijeriya barkatai da babu littattafan da za a koyar da su da harshensu na
asali. Idan aka ce, a koyar da Hausa cikin Hausa, su kuwa yaya za su yi? Domin
a daidaita tunanin haÉ—a kai, sai a koma Turanci gaba É—aya, in ya so a yi marus,
haihuwan guzuma É—a kwance uwa kwance[xxxix].
3.
Ga alama, hatta da malaman Hausa akwai masu jin taƙaicin
Hausa saboda sauƙin ta, da saurin fahintarta da ake yi. Zama ɗaya a iya ta, a
fahince ta, a samu manyan digirin ƙoli ciki, abin na ci musu tuwo a ƙwarya. Da
an bijiro da maganar koyar da Hausa cikin Hausa, sai idanu su yi ja, a dinga
tayar da jiyoji, da karya gumi, hasada ta rufe ido, a dinga zubar da hawaye wai
wasu za su ci arziki cikin ruwan snayi. Kaico! Ai rabon kwaÉ—o ba ya hawa sama[xl].
Ban ce, waÉ—annan su ne kaÉ—ai ra’ayoyin masu ganin a koyar da Hausa da Turanci
ba. Duk da haka, su na iya kalatowa da rairayowa yayin da nake fafitikar harhaÉ—a
wannan muƙala. Ko da da wasu daban, mu a Nijeirya ta Arewa waɗannan su ne
jigajigan hujjojin. Idan muka yi riƙo da hujjojin su irin hasashen wasu abubuwa
da na yi wa taken:
Hasarorin
da Aron Hannu zai Haifa
A tsarin koyar da harsunan duniya, ba baƙon abu ba ne harshe ya ɗauki nauyin
kansa a fagen koyar da duk abin da ya shafe shi. Baƙon abu shi ne, koyar da
nahawun wani harshe cikin nahawun wani ba shi ba. Idan aka ce, a nace ga aron
hannu, dole a shirya karɓar hasarar da ba za a san ranar gama jajenta ba. Abin
da mu É—aliban harshen Hausa da malamanmu suka hanga shi ne, za mu yi hasarar:
1.
i) Ruhin harshenmu na asali da ke ƙunshe cikin nagartattun
kalmomin gado. A Æ™arshe, kalmomin da suke gama gari ga ma’ana kawai za a riÆ™a
amfani da su a watsar da waÉ—anda sai ‘yan gado suka sani. Da sannu harshenmu ya
shiga cikin harsunan da ake yi wa suna “harsunan da ke cikin haÉ—arin salwanta”.[xli]
2.
ii) Sautukan harshenmu da suke taÆ™adaru ga waÉ—anda ba ‘yan
asali ba, irin su tagwayen baƙaƙe da wasula da baƙaƙe masu ƙugiya za a durƙusar
da su. Yadda duk aka samu dabarar samar da su saboda ana son magana da rubutu
da Hausa a wancan zamani, haka za a ragaitar da amfani da su idan Turanci ya
karɓi tutar koyar da nahawun Hausa[xlii].
Allah Ya tsare mu Ya tsare wuyan raƙuminmu in ji Buzu da ya ga mai maƙoƙo.
iii) Za a ci amanar karuruwan harsunan Hausa da suka
taru suka gina harshen Hausa suka shimfiɗa daular ƙasar Hausa. Cikin ƙoƙarin
daidaita Hausa ta dace da buƙatun gwannati a fagen koyarwa da daidaita
ma’anonin kalmomi da za su yi canjaras da na Ingilishi dole a kushe wani karin
harshe a kan wani. Idan na asali su salwanta Hausa ta yi hasarar su[xliii].
1.
iv) Bunƙasar harshe da ƙara ɗaukakarsa da yaɗuwarsa tana
tare da tsarin salon rubutunsa da yadda za a adana shi a rubuce. Idan za a
koyar da Hausa cikin Turanci rubutun Turanci zai É—aukaka na Hausa ya rushe a
farfajiyar ilmi, daga nan sai sare-saren salwanta. Me ya É—aukaka harsunan Turai
ba salon rubutu da aka adana su da shi ba[xliv]?
2.
v) Harshen Hausa da al’adun Hausawa sun zama wa Turawa alaÆ™aÆ™ai
tun zamanin cinikin bayi da mulkin mallaka. Duk ƙasar da ta ratsi duhun
jahiliyyar mulkin mallaka za ta yi hasarar harshenta da nagartattun al’adunta
da asirranta. Wannan maƙasudin ya kasa cin gira a ƙasar Hausa. Duk da Turance
Hausawa da aka yi da bokonta su, da bautar da su, da rikiÉ—a musu addinai, an
kasa murÆ™ushe harshensu da al’adunsu na gargajiya. Babu abin da ya taimaka wa
Hausawa a kan haka face riƙo ga harshensu damaƙui. Yau da rana tsaka, bayan mun
ci nasarar yaƙi, a ba mu kuturun bawa, kurma, maƙaho, mahaukaci gigitacce da
shi. Matuƙar aka bai wa Turanci amanar koyar da Hausa to, Turanci ne ake
koyarwa ba Hausa ba[xlv].
3.
vi) Sunan wata babbar hasara ‘banta-É“akatantan, ba a ga
tsuntsu, ba a ga tarko. Masu koyar da Hausa cikin Turanci matuƙar ba Turawa ba
ne, ba nagartaccen Turanci É—an asali za su koyar da yara ba, yaye-yaye ne cikin
kuri da gayanci, a wayi gari yara ba su iya nahawun Turanci ba, su manta da
nasu na asali na Hausa. Bahaushe na cewa, ba ka bayar da abin da ba ka da.
Turanci ba harshenka ba ne, ya ya za ka aro shi ka koyar da masu harshe
harshensu da harshen da ba nasu ba? Da kai, da su, duka baran uwar Nuhu kuke
yi. Assha! Wannan ita ce musibar da ke damuwar ɗaliban nazarin Hausa a ƙarƙashin
wannan ruÉ—aÉ—É—en sabon tunani[xlvi].
vii) Fahintar harshe a ilmi shi ne, a naƙalci nahawunsa a
magana da sarrafa shi a rubuce cikin ƙoshin kalmominsa na asali. Idan za
a koyar da Hausa da Turanci É—alibin Hausa zai yi hasarar É—imbin kalmomin Hausa
masu wadatattun ma’ana ya faÉ—a cikin Æ™addarar Æ™ila-wa-Æ™alan Turanci. Idan aka
shiga wannan yanayi babu makawa sai an yi saki zari kama tozo. Wanda ya karanto
harshe ya rasa wadatattun kalmomin da zai yi rubutu ya isar da saƙo a cikinsa
bai amfanar da harshen da komai ba. Amfanar da harshe shi ne, raya kalmominsa,
da adana su a adabi da rubutu. In babu ƙira me ya ci gawai? Masassara ke nan
daga nan sai doguwar suma sai baƙuntar kushewa[xlvii].
viii) Wata hasara ita ce, renon takaici cikin takaici a rayar da
takaici. Turanci kishiyar duk wani harshe ne da ya yi wa mulkin mallaka. Turawa
kuwa ba su taɓa ganin kan wanda suka mallaka da gashi. A koyaushe uban gida son
yake a ce, bawansa ya riƙa kwaikwayonsa domin ya tabbata bawa. Da wace hujja za
mu rayar da harshen wasu wanda da shi aka zalunce mu, mu watsar da namu? Koyar
da Hausa cikin Turanci rayar da harshen Ingilishi ne da daƙusar da martabar
Hausa da Hausawa. Haba! Lokaci ya yi a doki garwa belbelu su tashi su san wurin
da dare ya yi musu.
Bazar
Hausa a Farfajiyar Ilmin K’arni na 21
A tsarin karatun Hausa na matakai masu zurfi an haÉ—u a kan ‘bangarori uku.
Al’ada, Adabi da Harshe. Kowanne daga cikinsu wani babban kandami ne da za a
iya yi wa suna, daji ba ka da gambu. Tattare da haka, a imaninmu na É—aliban
Hausa da malamanmu masu kishin cigaban harshenmu, duk aikin da aka yi a kan
wata fasaha ta harshen Hausa ko Bahaushe, Hausa aka yi wa aiki kuma aikin na
nan a cikin farfajiyar karatun Hausa. Ai ba Hausa kaÉ—ai ce harshe a Afirka ba.
Ba ita kaÉ—ai ce harshe a Nijeriya ba. Ba ita kaÉ—ai ce harshe a Nijeirya ta
Arewa ba. Ba ita kaɗai ce harshen da ake amfani da shi a cikin ƙasarta ba. Me
ya sa ta fi su saura kere a fagen ilmi? Idan dai mun aminta da, karen da ya yi
cizo da gashinsa ake magani. To! Duk wani ƙwazon Bahaushe aka sarrafa cikin
ilmi, Hausa ce ake yi wa aiki, ma’aikacin kuwa, Hausa ce ya karanto. Ku biyo
ni, amma ku taya ni duba baya makaho ya so tsegumi:
1.
i) A ‘bangaren harshen Ingilishi da Ilmin Harsuna fitattun
kundayen manyan digirin Ph.D da Hausawan da suka karanto Ingilishi suka yi a
kan Hausa sun ninka waÉ—anda aka yi a kan Turanci yawa. Mafi yawan Hausawan da
suka karɓi digirin Ph.D na Turanci harshen Hausa suka yi wa hidima[xlviii].
2.
ii) Haka kuma, waɗanda suka karɓi digirin Ph.D a fannin
Ilmin Harsuna Hausawa da wasu maƙwabtansu Hausa suka yi wa hidima[xlix].
iii) Malaman Hausa na farko da suka assasa karatun
Hausa ba Hausa suka karanta ba, amma ita suka yi wa hidima a kundayensu na
Ph.D. Suka dawo suka sauya akala don kishin Hausa.[l]
1.
iv) Sassan ilmi na fasaha irin Tarihi da Tattalin Arzika da
walwala da sauransu. An yi fitattun ayyuka a kan Hausa da Hausawa[li].
2.
v) A kimiyya, an samu ayyuka da kimiyyar gine-gine da
lissafi da sauransu[lii].
WaÉ—annan aikace-aikace, sun isa su tabbatar da cewa, Hausa ta cancanci a koyar
da ita cikin Hausa, domin Hausawan da suka ilmantu a fannoni daban-daban, da
ita suka yi bara ga ayyukkansu. Ban yi zaton akwai wani harshe daga cikin
harsunan Nijeriya da yake da wannan fice a duniyar ilmin wannan ƙarni ba irin
Hausa. Ba wai harshen Hausa ba, yau babu wani fanni na ilmi da zai buwaya a
Hausantar da shi ba, sai dai idan ba a so ba[liii].
Bazar rawar Hausa cikin Hausa ta ci nasara a farfajiyar ilmin ƙarninmu. A halin
yanzu, masu takardun shaidar Difloma da Ensi’i (NCE) a Hausa sun nunka na
kowane harshen Nijeirya da ake koyo a matakan. Ban yi na babban mahaukaci ba,
idan na ce, masu babbar takardar shaidar digiri (BA) na Hausa da digirin ilmi a
‘bangaren Hausa B.A ed (Hausa) sun fi na kowane harshe yawa a Nijeriya. Babu
shakka, ƙididdige masu digirin ƙwarewa na MA da Ph.D a Hausa, sai an nemi
tiamakon hukuma. A matakin koyo na ƙarshe, Hausa na da Farfesoshi fiye da
talatin ‘yan Æ™asa, kuma ‘yan gida Hausawa da ke a Jami’o’i da Cibiyoyin nazari
da bincike daban-daban[liv]. WaÉ—annan dalilai su suka
tilasta a koyar da Hausa cikin Hausa domin babu abin da Hausa ta rasa.
Hausa Cikin Hausa:
Babban matsalar da ke haddabar harsunan cikin gida ita ce, hana musu ‘yancin
taka rawarsu da kansu a fagen koyonsu da koyar da su da rubuce-rubucen da ya
shafe su. Farfesa Dalhatu Muhammadu Zariya[lv] na daga cikin
jigagan ganin dole Turanci ya sake wa Hausa mara a koyar da Hausa cikin Hausa.
Yekuwarsa ta samu karɓuwa ga fitattun ɗalibansa, Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya da
Farfesa AbdulÆ™adir ‘Dangambo[lvi]. Irin gudunmuwar da suka
bayar na Æ™wato wa Hausa ‘yancin koyar da ita cikin Hausa ita ce gajiyar da muke
ci a yau. A nan, tilas a anbaci Farfesa Muhammadu Hambali Junju, wanda saboda
tsananin kishinsa ya rubuta Rayayyen Nahawun Hausa[lvii].
‘Dalibansa Dr. Ahmadu Bello Zariya da Farfesa Salisu Ahmad Yakasai kowanensu ya
fito da littafin nahawun Hausa cikin Hausa[lviii]. Domin raya harshen Hausa
cikin Hausa, Malamin Malaman Hausa, Farfesa Dauda Muhammad Bagari, ya wallafa
gawurtaccen littafin nahawu mai take Bayanin Hausa. WaÉ—annan
ayyuka sun rufe bakin masu ƙorafin rashin kayan aiki.
Hausa cikin Hausa ta yi tasiri a kundayen karɓar digirori na BA da MA da PhD.
Jami’o’in Bayero da Ahmadu Bello da Usmanu ‘Danfodiyo da Maiduguri sun yi abin
a zo a gani. Babban digirin farko na PhD da aka fara cikin Hausa shi ne na
Farfesa Sa’idu Gusau (1989) na biyunsa shi ne, na Aliyu Muhammad Bunza, (1995)
na uku, Farfesa Ibrahim Aliyu M. Malumfashi (1999). Daga bayansu an sami fiye
da kundayen PhD talatin cikin Hausa. Wannan ya nuna an samu cigaba sosai, kuma
cigaban sai daɗa ƙaruwa yake yi. Babu shakka, wannan na ba da haske gare mu
cewa, fafitikar da ake ciki ta tabbatar da koyar da Hausa cikin Hausa, haƙa ta
kai ga wadataccen ruwa. Abin da ya rage shi ne, a sake fito wa Turanci
Hausance, a fara tunanin gabatar da darusan ilmin da ake tinƙaho da shi a ƙarninmu
cikin Hausa.
Sakamakon
Nazari:
Martaba da darajar ilmi na kowane fanni iri É—aya ce, amfaninsa a fahince shi a
amfana da shi. Daga cikin abubuwan da suka tanye ƙasashe masu tasowa ga cigaba
akwai matsalar harshen da ake bayar da ilmukan da ke sa ci gaba. Tilasata wani
baƙon harshe a matsayin harshen ƙasa da ƙoƙarin kururuta shi da fifita shi ga
harsunan gado shi ya tauye banƙasar ilmi a ƙasashen da suka yi wa harsunan
mulkin mallaka mabayi’a ta har abada. Wannan É—an Æ™warya-Æ™waryan bincike ya
hango:
1.
Buƙatar sake jaddada koyar da Hausa cikin Hausa da rubuta
kundayen binciken Hausa cikin Hausa. A fara tunanin bayar da kyauta ga kundin
PhD mafi rubutuwa a tantagaryar Hausa
2.
Akwai bukatar farfaɗo da, ko kafa hukumar fasara mai ƙarfi
da za ta kula da ayyukan fasara na ciyar da fasara ayyukan kimiyya da ƙere-ƙere
da kiyon lafiya domin a sama wa ‘ya’yanmu nagartaccen ilmi.
- Binciken ya hango, babu harshe daga cikin harsunan Nijeriya da ke da
masana da manzarta a fanninsa irin Hausa. Hausa ita ce kan gaba ga
dukkanin harsunnan Nijeriya. Babbar matsalar kawai ita ce samun marasa
kishinta daga cikin maciya gajiyarta.
1.
Akwai buÆ™atar buÉ—a sassan karatun Hausa a jami’o’in Æ™asashen
Afirka ta Yamma musamman Nijer da Benin da Togo da Ghana da Senegal da Bokina
da Mali. Yin haka, zai bai wa wasu ƙananan harsuna marasa galihu farfaɗowa idan
suka dafi kafaÉ—ar Hausa. Yadda za a sayar da wannan hajar shi ne, kiran tarukan
ilimi na Hausa a ƙasashen domin su ji irin wainar da ake toyawa.
2.
A halin yanzu, a wannan ƙarni, lalurar koyar da Hausa
cikinTuranci ta kau. Zancen rubuta kundin binciken Hausa cikin Turanci bai taso
ga manazarci Hausa ba a sashen da ake koyar da Hausa ba. Duk malaman Hausa su
tashi tsaye na ganin an kawar da duk wata matsalar da za ta yi wa koyar da
Hausa ikin Hausa barazana.
NaÉ—ewa:
Hausawa na
cewa, babu mai nunin gidansu da hannun hagu. Lallai ƙafafun wani ba su yi wa
wani tafiya. Hakiƙa, kayan aro ba sa ado, domin komai ta daɗe ƙarshen ruwa
kware. Na yarda da faÉ—ar, tare da ni aka ci, ya fi gaba gare ni aka ci amfanin
hanji. Tarihin saduwar Bahaushe da Turanci ba mai daÉ—in sauraro ba ne, domin
kare jini biri jini aka rabu. To! Rabuwar da aka yi dutse hannun riga ina
amfanin a ci gaba da renon musabbabinta? Buƙatar harshen na zama harshen ƙasa,
ko harshen ilimi, dole ya kasance yana da jama’a na asali masu yawa da masu
sha’awarsa. Haka kuma, ya kasance mai wadatattun kalmomi da za su wadatar a
kowane bagire ake leƙo shi. Samun daidaitaccen tsarin rubutu wata martaba ce da
ake so gare shi domin ilimi da siyasar rayuwa dole sai da rubutu. Me Hausa ta
rasa a cikin waÉ—annan sharuÉ—a? Me Turanci zai yi wa Hausa doro a nan? Babu wani
harshe na duniya da kalmominsa suka wadaci buƙatar zamaninsa. Babu harshen da
ya bunƙasa ba tare da are-aren kalmomi da ƙirƙire-ƙirkirensu ba. Babu harshen
da zai shiga zukata da hukuma ba tare da zawiyyar boko ba. Duk wani harshe da
duniya zamaninsa ta ji zarmoÉ—arsa, sun yi auren zobe da ‘yan jarida. Duk wani
baƙon harshe bai san budurcin Hausa ba. Larabci ya tarar da ita ɗakin mijinta.
Rubutun ajami ya riske ta da tagawaye. Turanci da jikokinta ya gan ta. Samari!
Ka da a ci ka da burga, idan za ka yi aure, ga shawaran makaÉ—a ‘Dan’anace:
Jagora: Mai son miya ya auri Tsohuwa
: Mai son shimfiÉ—a ya auri budurwa,
: Mai son ɗan ƙwarai ya auri isassa.
(Waƙar Shago)
Na zaÉ“a maka isassa ita ce “Hausa”. Isassa na iya kasancewa da kowace irin sifa
kake so.
MANAZARTA
Abdullahi, M.D. 2011. A Study of Writing and Development of TAFI,
Fatima Publishing, Katsina.
Adamu, M. 1975. Hausa Factor in West African History, Zaria: ABU,
Press.
Amfani, A.H. (da wasu) 2012, Champion of Hausa Cikin Hausa A
Festschrift in Honour of Dalhatu Muhammad, ABU Press, Zaria.
Bagari, D.M. Bayanin Hausa, Rabbat, Morocco.
Bangbose, A. 1977. Language and Nation: The Language Question in Sub-
Saharan Africa, Edingburgh, University Press.
Birnin-Tudu, S.Y. 1990, “Nazari Kan Rubutun Ajami a K’asar Hausa,”
Kundin digirin MA, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sokoto.
Bivar, A.D.H. 1960. “A dated Qur’an from Borno” Nigerian Magazine,
No.
65, Lagos: Federal Ministry of Social Development, Youth, Sprots and Culture,
Lagos.
Bunza, A.M. 2000, Rubutun Hausa, Yadda Yake Da Yadda Ake Yin Sa,
Don Masu Koyo Da koyarwa, Ibrash, Lagos.
Bunza, A.M. 2008, NarambaÉ—a, Ibrash, Lagos.
Bunza, A.M. 2013. “Don Me Ake Karatun Hausa?” Cikin Harsunan
Nijeriya, Volume XXIII, 2011-2013 CSNL, BUK, Kano.
Clarke, P.B. 1982, West Africa and Islam, London.
Dressler, W. 1981, “Language Shift and Langauge Death, a Protean
Challenge for the Linguist”. Folia Linguistica.
Dorian, N.C. 1981a, Language Death: The Life Circle of a Scottish
Gaelic
Dialect, Philadelphia.
East, R.M. 1952. A Vernacular Bibliography for the Languages of
Northern
Nigeria. Zaria: NNPC.
Fagge, U.U. Ire-Iren Karin Harshen Hausa Na Rukuni, Benchmark
Publishers Limited, Kano.
Fischer, S.R. 2000. A History of Writing, Reaktion Books.
Galadanci, M.K.M. 1976, An Introduction to Hausa Grammar, Longman
Nigeria.
Gazali, K.A.Y. 2005, The Kanuri in Diaspora, The Contributions of
Kanen-
Borno ULAMA to Islamic Education in Nupe and Yorubalands, CSS
Press, Lagos.
Jinju, M.H. 1981, Rayayyen Nahawun Hausa, NNPC Zaria.
Miller, W. 1971. “The Death of Language or Serendipity Among the
Shoshani.” Anthropological Linguistics 13:114-120.
Omar, S. 2013, Modibbo Kilo, ABU Press, Zaria.
Oyetade, S. 2007. “Language Endangerment in Nigeria.” Perspectives on
Akolo Languages of the South-West” Dorian, N. (ed) International
Journal of Society and Language, 184, pp. 169-184.
Rufa’i, A. 1977 “Grammatial Agreement in Hausa”. PhD Thesis
Georgetown University, USA.
Rodney, W. How Europe Underdevelop Africa.
Sakkwato, A.B. 2011 Ginin Jimlar Hausa, Jagora ga Mai Nazarin Harshe,
Mathi Production Sakkwato.
Sani, M.A.Z. 2011, Gamayyar Tasrifi da Tsarin Sautin Hausa, ABU,
Press
Zaria.
Spender, D. 1980. Man Made Language, London Rutledge and Kegan
Paul.
Tsafe, B.A da Sadi, S.A. 2010 Hanyar Binciken Ilmi a Hausa, Farin
Batu
Press Gusau.
Ubah, C.U. 2001, Islam in Africa-History, Baraka Press, Zaria.
Yakasai, S.A. 2012. Jagoran Ilmin Walwalar Harshe, Garkuwa Media,
Services Sokoto.
Yar-Aduwa, T.M. 2008, The Syntactic adn Semantic Description of the
Hausa Quantifiers, Clean Impression Ltd, Kano.
Zariya, A.B. 1981, Nahawun Hausa, NNPC, Thomas Nelson, Nigeria
Limited.
ZaruÆ™, R.M. Aikatau a Nahawun Hausa.
[i] .
Rashin Farfesa Muhammad Kabir Galadanci da Farfesa Ibrahim Yaro Yahya da
Abdullahi Kafin
Hausa da Habib Alhassan Gusau da Malam Zarruƙ da Mahbub Alƙali da Malam Isa
Kurawa
(Kakan Malaman Hausa) da Farfesa Muhammadu Hambali Junju ba ƙaramar giɓi ta
bari ba ga
fagen nazarin Hausa.
[ii] .
Don ƙarin bayani a dubi, Bunza, A.M. Narambaɗa, IBRASH, Lagos.
[iii] .
A hasashen masana irin Farfesa Mahdi Adamu Ngaski Kalmar “boko” ‘yar gida ce,
tun fil azal
Bahaushe na da “biri boko” da “amaryar boko”. Don haka, boko na nufin “Æ™arya”.
A hangen É—aliban É—alibansu irin su Aliyu Bunza, kamar “boko" Baturiya ce,
asalinta daga Kalmar “book” ne da ake yawanta ambata a makarantar.
[iv] .
A mafi yawar al’umma na Afirka da Asiya da wasu Æ™asashen Larabawa ana ce da shi
“ilmin
takarda”. Hausawa ma, É—an takarda suke ce wa ‘yan boko gabanin Kalmar boko ta
karɓe tuta.
[v] .
A dubi, Dorian, N.C. (1981a) Language Death: The Life Circle of a
Scottish Gaelic dialect,
Philadelphia.
[vi] .
A dubi, Dressler, W. (1981) “Language Shift and Language Death, a protean
challenge for the
Linguist”. Folia Linguistica 15:5-25.
[vii] .
Ba Hausawa keÉ—ai ke da shi ba. Akwai shi a Igbo da Kanuri da Yoruba da Igala da
Nupe da duk
harsunan Nijeriya da suka rungumi Turawa.
[viii] .
Nassin AlÆ™ur’ani Ya tabbatar da cewa, Allah Ya Æ™agi É—an Adam kuma Ya saka shi a
zuriyar
zuriya da ya arzuta su da harsuna domin su san junansu.
[ix] .
Idan ya ƙware da iya tsara magana ko yana da yawan surutu akan ce yana da
“baki”.
[x] .
WaÉ—annan ra’ayoyin suna komawa ga irin fahintar da Darwin ya yi wa halittar É—an
Adam ta cewa
daga birai aka fara. A dubi Tarikh vol. 1 No. 3.
[xi] .
A dubi, Alhaji Sa’ad Haruna Gobir, (1982) Kunna Ya Girmi Kaka. Ingantaccen
Tarihin Hausa.
[xii] .
A dubi, Sa’adiyya Omar, 2013, Modibbo Kilo ABU, Press, Zaria.
[xiii] .
‘Dan Masanin Kano Yusuf Maitama Sule ya yi hira da gidan Rediyon BBC, 1982 da
2000 ya
ambace shi. Mal. M.S. Ibrahim ya ƙarfafa maganar da shi da Farfesa Ibrahim Yaro
Yahaya.
[xiv] .
Mun gano wannan a wani binciken haÉ—in guiwa da na yin a wani masanin ajamin
Barebari
Dmitry da muka haÉ—u a SOSA, 1997. Mun samu tabbacin haka a wani K’ur’ani da
muka samu a
hannun Wazirin Gwandu na yanzu (2014) takardun rubutun K’ur’anin sun kai
shekara É—ari bakwai
a tarihi.
[xv] .
Don ƙarin bayani a dubi, Bunza, A.M. Rubutun Hausa Yadda Yake da Yadda
Ake Yin Sa don
Masu Koyo da Koyarwa. IBRASH, Lagos.
[xvi].
Don ƙarin bayani a dubi, Clarke, P.B. 1982. West Africa and Islam,
London da C.U. Uba, 2001
Islam In Africa-History, Baraka Press Zaria.
[xvii] . Don
Æ™arin bayani a dubi, Birnin Tudu, S. (1990) Nazari Kan Rubutun Ajami a K’asar
Hausa, M.A.
UDUS.
[xviii] . A dubi,
Musa D. Abdullahi, A Study of Writing and Development of TAFI,
Fatima Publishing,
Katsina.
[xix] .
Hira da Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari, Shugaban ƙasar Nijeriya a Jamhuriyya
ta biyu a
gidan Talabijin na Tarayya Sakkwato (2010).
[xx] .
A wata fasara ana cewa “Vernacula” harshen bayi.
[xxi] .
Da an ce wa abu “Local” a Turanci an so a Æ™asÆ™antar da shi a takura faÉ—insa da
bazuwarsa.
[xxii] . Ana
faÉ—ar haka domin ana ganin ga uwa ake fara koyon harshe. A wajen Turawa wani
awon renin
wayo ne ga harshen da ba a ganin kansa da gashi.
[xxiii] . Idan an
ji haka a fagen nazarin harsuna na ilmi ake faÉ—ar haka.
[xxiv] . WaÉ—annan
misalai duk daga cikin harsunan Nijeriya aka ciro su. Ina ga an ce a samo
misalai daga
sauran harsunan? Za a ga iya adadin harsunan, iya adadin sunan ruwa da za a
samu.
[xxv] . Ko
an yi fasara mai kyau ma’anar ba ta shiga jikin mai harshen fasara kamar yadda
za ta shiga
jikin mai harshen asali.
[xxvi] . Da aka
matsa kashe Turawan mulkin mallaka a kudancin ƙasar nan, sun kawo dokar dole
kowa ya
riƙa tafiya da fitilar a-ci-bal-bal cikin dare. Duk wanda aka kama babu fitila
tana ci a hannunsa da dare za a hukunta shi. Wai! Don su gane makasan su.
Laccar Aji II a Tarihi tare da S.U. Lawal, Sashen Tarihi Jami’ar Sakkwato,
1984.
[xxvii] . Wannan ita ta
ba Turawan Mishon damar kiristintar da wasu ƙananan ƙabilu a Arewacin ƙasar
nan da Arawan jamhuriyyar Nijar da gundumar Argungu.
[xxviii] . Don ƙarin bayani a
dubi, Walter, R. How Europe Underdeveloped Africa, Ibadan.
[xxix] .
Rahotannin Mr. Hamper ɗan leƙen asirin Ingila a Iran ya tabbatar da haka.
Fasarar Hausa ta
Sa’idu Muhammadu Gusau.
[xxx] .
Idan haka ne, me ya sa ba a tilasta kowane ɗan ƙasa ya aje harshensa na gado ba
ko a cikin
gidansa ya yi Turanci? Duk abin da bai sa aka yi wannan dokar ba, shi zai ba da
damar karantar da Hausa cikin Hausa.
[xxxi] . Wayyo!
Sun manta babu harshen da ya tarar da nahawunsa a rubuce. Kowane harshe a doron
ƙasa
shi ya zauna ya tsara nahawunsa a rubuce. Ai Turanci bai tarar da ko littafi É—aya
na nahawun Turanci saukakke ba! Yaya aka yi? Yadda duk aka yi, haka za mu yi.
[xxxii] . Haka Turanci ya
sha wahalar, har yanzu ya kasa ciwo kan matsalolin amma ya ci gaba da aiki.
Hausa ma ta shirya haka.
[xxxiii] . K’asashen da ke koyar
da ilmi da harshensu fa? Me ya fi daɗi da irin yadda ƙasashen Asiya da
Larabawa da Rasha ke koyar da ilmi da harshensu?
[xxxiv] . K’arya suke yi, a
tambayi Rev. G.P. Bargery a shekarar 1933 ya tara fiye da kalmomi miliyan
É—aya ya tace ya yi babban K’amus. Shi ne gawurtaccen Æ™amusun Hausa na farko.
[xxxv] . Ina! Wace ƙasa
ta fi China da Rasha da Indiya da Masar da sauran ƙasashen duniya masu amfani
da harshensu ci gaba yau. Kai! Wawa hatta da wayar hannu yanzu China ke yi wa
duniya Limanci ita da Japan.
[xxxvi] . To, ai kai Bahaushe
ne. digirin Hausa aka ba ka. Malaminka harshensa yake yi wa yaƙi. Kai! Me
zai hana ka yi wa naka? Shi ke nan, in Malaminka ya ga Annabi ka gan shi, in
bai gani ba, kai ka ci bone?
[xxxvii] . To! Wannan ita ce babbar
hujja. Babu wata bayan ta.
[xxxviii] . Ai ba Aljannu da tsuntsaye za su
yi aiki ba. In kowa ya yi kamar yadda kuka yi, Hausa ba za ta
kawo yau da rai ba.
[xxxix] . Wannan ra’ayin
Turawan mulkin mallaka ne aka ara musu. A gai da Mishon.
[xl] .
Mun ga haka a bayyane. Allah Ya taya shanu cirri.
[xli] .
Don ƙarin bayani a dubi, Yakasai, S.A. 2011, Jagoran Ilmin Walwalar
Harshe Garkuwa Media,
Kaduna.
[xlii] . Ta
haka Turawa suka ‘bata muna sunayen garuruwanmu: Dubi wai, Zaria, Kankia,
Zagga,
Chafe/Tsafe d.s.
[xliii] . Haka ake
yi wa karin harshen Sakkwato da Arabci da Gimbananci da Gobarci da sauransu.
[xliv] . Me
ke aukuwa a yau ba haka ba?
[xlv] .
A dubi rayuwar É—aliban Hausa da aka yi wa wannan cutar. Ba su iya Hausa ba, ba
su iya Turanci
ba.
[xlvi] .
Barka da samun nasarar tabbatar da gushewar sa a karatun Hausa a Nijeriya.
[xlvii] . Abin da
ake so ke nan ga harshen Hausa. Allah Ya tsare ta.
[xlviii] . Irin Prof.
Bello Bada, Prof Asabe Kabir, Prof Malami Buba, Prof. Tsiga sun taka rawar
gani.
Allah Ya taimake su.
[xlix] .
Irin su Prof. Junaidu, Prof. Mukoshy, Prof. Mukhtar Prof. Adeyanju da sauransu.
[l] .
Irin su Prof. Dalhatu, Prof. Galadanci, Prof. Bagari, Prof. Hambali, Prof.
Danladi Yalwa, Prof.
Audu Yahaya Bichi, Prof. MaikuÉ—i K’araye da sauransu.
[li] .
An yi PhD a kan adashin Bahaushe a UDUS, a fannin tarihi aikin Bala Usman,
Mahdi Adamu,
Bello Alƙali, Abdullahi Rafi Augi, S.U. Lawal da Baƙo duk kan Hausawa ne.
[lii] .
An yi PhD a fannin Mathematics kan hisabin Hausawa a ABU, Zariya. An yi PhD a
University of
London kan gine-ginen gidan Bahaushe.
[liii] .
Mun ga haka, mun tabbatar da haka a yau (2014).
[liv] .
A fannonin Al’ada da Adabi da Harshe.
[lv] .
Aikin da aka yi a kansa shi ne taken: Champion of Hausa cikin Hausa, A
festschritt in Honour of
Dalhatu Muhammad, ABU, at 50.
[lvi] .
Su ne É—aliban farko na Hausa cikin Hausa.
[lvii] . Har
Allah Ya karɓi Hambali ba a taɓa jin ya yi laccar Hausa cikin Ingilishi ba.
Allah Ya gafarta
masa.
[lviii] . Na ambaci na Yakasai a lamba ta (41) na Ahmadu Bello Zariya shin e: Nahawun Hausa, NNPC, Zaria.
[…] Hausa Cikin Hausa Martabar Hausawa Da Mai Karatun Hausa […]
ReplyDelete