Ticker

6/recent/ticker-posts

Gudunmawar Sassaka Ga Bunkasa Tattalin Arzikin Kasar Kabi

Takarar da aka gabatar a taron kara wa juna sani na kasa na biyu da Tsangayar Fasaha da Nazarin Addinin Musulunci ta Jami’ar Usmanu Danfodiyo ta shirya daga ranakun 10-12 ga watan juli, 2017.

Rabi’u Aliyu Rambo

Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato
dirindaji12aa@gmail.com
phone: 08125507991

ABSRACT


The wood carving industry has been practice in many parts of West African communities particularly in Hausa land. The industry has passed through many stages of development from purely primitive structure to a near-modern business. Woodcarving is an important and well established traditional artifact industry in Kabbi kingdom. The industry has a very rich cultural based that has influence in many ways, its organization, product and survival to date. In view of the above, the paper intends to discuss the role of woodcarving occupation for enhancing economic activities in Kabbi kingdom particularly present day Argungu Emirate.

TSAKURE


Sana’ar sassaka wata tsohuwar sana’a ce da aka dade ana aiwatarwa a sassan al’ummomin kasashen Afrika ta yamma musamman a k’asar Hausa. Wannan sana’ar ta samu wanzuwa cikin matakai daban-daban na bunk’asa tun daga tsohon tsari na gargajiya ya zuwa sabon tsari na kasuwanci. Sana’ar sassak’a damfare take da muhimmanci a k’asar Kabbi. Sana’ar ta tattaro ababe da dama da suka shafi al’adu ta fuskoki mabanbanta, Wad’annan kuwa sun had’a da tsarin sana’ar da kayayyakin da takan samar da kuma wanzuwarta zuwa yau. Bisa ga wannan, takardar ta k’udurci tattaunawa a kan gudummawar sana’ar sassak’a wajen bunk’asa tattalin arzikin k’asar Kabbi musamman masarautar Argungu a yau.        

Gabatarwa

Sha’anin sana’a musamman ga al’ummar Hausawa abu ne mai dad’ad’d’en tarihi da muhimmanci ga rayuwarsu. Wannan shi ya sa sana’o’insu suka yi tasiri a cikin al’amurransu na yau da kullum. Domin ita sana’a, ita ce ginshik’in raya tattalin arzikin al’umma. A k’asar Argungu kuwa akwai sana’o’i daban-daban da al’ummar ta kan aiwatar domin bunk’asa tattalin arzikinsu daga cikin su kuwa har da sana’ar sassak’a. Don haka, wannan takardar ta mayar da hankali ne a kan  gudummawar  da sana’ar sassak’a kan bayar wajen bunk’asa tattalin arzikin k’asar Argungu domin kawo ci gaban k’asa baki d’aya.

Sana’ar sassak’a wata tsohuwar sana’a ce a k’asar Kabbin Argungu, Al’umar k’asar Argungu sun dad’e suna aiwatar da ita tun kaka da kakanni. Galibi masu aiwatar da wannan sana’ar suna yin ta ne domin samar wa kansu abinci da kud’ad’en kashewa musamman wajen biya wa kansu wasu buk’atoci na yau da kullum. Sana’ar tana taimakawa wajen bunk’asar wasu muhimman sana’o’in Hausawa, domin ba tare da sana’ar sassak’a ba, da wasu sana’o’in ba su kammalu ba. Irin wannan gudummawar da sana’ar sassak’a kan samar a cikin al’ummar k’asar Argungu ya taimaka wajen bunk’asa tattalin arzikin wad’annan al’ummomi.

Manufar wannan takardar ita ce k’ok’arin gano tare da bayanin gudummawar sana’ar sassak’a ta fuskar kayan aikinta ko wasu kayakin da take samarwa ko wasu ‘bangarorin rayuwa na musamman wajen bunk’asa sassa daban-daban na tattalin arzikin al’ummar masarautar Argungu.

2.0 Waiwayen A Kan Ma’anar Tubalin Wasu Kalmomin Taken Bincike


A wannan sashe, nazarin ya yi k’ok’arin bayanin wasu muhimman kalmomin da aka yi amfani da su wajen gina taken wannan bincike. A nan an kawo ra’ayoyin masana daban-daban dangane da ma’anar wad’annan kalmomi. Kalmomin da aka yi bitar ma’anar su a nan sune “sassak’a” da “tattalin arziki”.

2.1 Sassak’a

Masana da dama sun tofa albarkacin bakinsu tare da kawo ra’ayoyi makusanta juna dangane ma’anar sassak’a. A misali, Zaruk da wasu, (1987:54) sun bayyana cewa:

“Aikin masassak’i dai shine sarar itace da sarrafa itacen ta hure shi domin aikatar da shi zuwa dukkanin irin abubuwan da ake buk’ata. Misali ta irin wannan ne ake samar da kayan aikin gida kamar turmi da ta’barya. Masassak’a ne ke samar da turmi da akushi da ta’barya da kuyafa. Sannan sukan sassak’a kujerar zama ta mata zuwa su k’otar fartanya da dai sauransu”.

Bisa ga wannan ma’anar a iya cewa, Sassak’a ita ce aikin da ake yi domin samar da kayan amfani musamman kayan aikin noma da suka had’a da k’otar gatari da kalme da kuma kayan aikin gida da suka had’a da kujerar zama ta mata da akushi da sauransu, kuma ana sarrafa su ne da itace. A k’amusun Hausa kuwa na CNHN, (2006:393) an bayyana ma’anar sassak’a da “Abin da aka sarrafa daga itace kamar allo da turmi da mutum-mutumi, sana’ar sassak’a sana’a ce ta sarrafa itace don samar da surori”.

A ra’ayin  Wushishi, (2011:24) cewa ya yi: “Sana’ar sassak’a aiki ne na hure ice da aiwatar da shi don a mayar da shi wani abin amfani kamar jirgin ruwa da kujera da kyaure da turmi da ta’barya da akushi da suransu”. Wannan ra’ayin yana nuni da cewa, sassak’a sana’a ce ta sarrafa itace. Haka Alhassan da wasu, (1982:54) a cikin nasu littafin suna da ra’ayin cewa: “Sassak’a na nufin sarar itace da sarrafa itacen ta hure shi domin aikatar da shi zuwa dukkan abubuwan da ake buk’ata”. A nan wannan ma’anar tana k’ok’arin bayanin cewa, sassak’a sana’a ce da ake sarrafa itace domin samar da wani abin buk’ata na yau da kullum ga al’umma. Har wa yau a cikin wani rubutun Alhassan da wasu, (1980:41) sun k’ara bayyana ma’anar sassak’a da cewa: “Sana’ar sassak’a sana’a ce da ake hure ice a mayar da shi abin amfani, kamar jirgin ruwa ko kujera ko kwacciyar sirdi ko takalmin d’angarafai ko allo ko mutum- mutumi da makamantansu”. Duba daga wannan ma’anar za a ga duk dai maganar sarrafa itace zuwa wasu abubuwan amfani ma’anar ta k’unsa.

Bisa ga wad’annan ra’ayoyi na masana dangane da ma’anak’a, ana iya cewa sana’ar sassak’a wata sana’a ce da ake aiwatarwa ta amfani da sarrafa itace zuwa wasu abubuwan buk’atocin al’umma na yau da gobe musamman abin da ya shafi kayan aikin gida da sufuri da yak’i da kid’a da aikin gona da dai wasu buk’atoci na musamman.

2.2 Tattalin Arziki

Kafin a tsunduma cikin gundarin bincike a wannan haujin, ya kamata a fahinci cewa tattalin arziki kalmomi ne guda biyu wad’anda ke tafiya da manufa guda. A ra’ayin Auta, (2006:194)   ya bayyana kalmar “tattali” da cewa, kalma ce mai nuni da renon wani abu har ya kai ga girmansa. Ita kuwa kalmar “arziki” a wannan muhallin tana nufin samun ‘dukiya’ ko wani abin da mutum zai mallaka wanda za a iya sarrafawa zuwa biyan wasu buk’atoci na rayuwar yau da kullum. Haka a CNHN, (2006:432 da 19) an bayyana ma’anar wad’annan kalmomi (tattali da arziki) da cewa, ‘tattali’ na nufin tanadi ko kula ko adana wani abu ko ajiye wani abu don yin amfani da shi nan gaba. A hannu d’aya kalmar ‘arziki’ na nufin tajirci ko dukiya ko samu ko hali ko kud’i ko wadata ko sukuni ko daula ko abin hannu ko hannu-da-shuni. Duba daga wad’annan ma’anonin kalmomin guda biyu, idan aka gwama su wuri d’aya watau “tattalin arziki”, wad’annan kalmomin na iya d’aukar ma’anar abin da mutum ya mallaka tare da ririta shi da kuma amfani da shi ta hanyar da ta dace cikin basira. Don haka, masana da dama sun bayyana ra’ayoyinsu dangane da ma’anar tattalin arziki. Binciken ya yi waiwaye ne a kan wasu daga cikin ra’ayoyin. Ga misali, Ibrahim, (1982:7) ya bayyana cewa: “Tattalin arziki tsari ne na sarrafa albarkatun k’asa da sauran ni’imomin da Allah Ya yi wa ‘Dan adam domin samar da muhimman abubuwan buk’ata da rarraba su ga jama’a masu buk’ata”. A ra’ayin Umar,(1983:5) cewa ya yi “Tattalin arziki tsari ne na inganta da bunk’asa hanyoyin shigar kud’i da sauran abubuwan buk’atun ‘Dan adam musamman abinci da sutura da muhalli”. Wannan ma’anar nuni take da cewa, duk wata hanya ta samun kud’in shiga da samar da abubuwan more rayuwa ita ce hanyar tattalin arziki. A ra’ayin Auta, (1986:107) ya bayyana shi da cewa: “Tattalin arziki tsari ne na sarrafa wasu abubuwa domin samun abubuwan buk’atun rayuwa.” Har wa yau, Shinkafi, (2016:5) ya rawaito Simith, (1976) da Mill (1844) da Marshal (1890) da J.B (1803) da Robbins (1932) da Umar (1983) duk sun aminta a kan cewa:

“Tattalin arziki gaba d’ayansa abu ne da ya tattaru ga k’ok’arin kula da albarkatun k’asa da sauran ni’imomin da Allah Ya yi wa mutum ta yadda za su bunk’asa su, sarrafa su da samar da abubuwan da mutum ke buk’ata domin rayuwar  jama’a ta gudana cikin sauk’i”.

A ra’ayin Yakasai, (2012:35) ya nuna cewa: “Sana’o’i sune mafi girman tafarkin da Hausawa suke bi domin samun abubuwan buk’atu. Ta hanyar sana’a suke sarrafa albarkatun k’asa da sauran ni’imomi domin biyan buk’atunsu…”

Duba daga wad’annan zantuka da masana da d’aliban ilimi suka yi, a tawa fahinta kusan duk bori guda suke wa tsafi, domin zantukan duk sun tafi a kan hanyoyin samun kud’i ko wasu abubuwa da rayuwa ta dogara a kansu domin inganta ta. Idan kuwa haka abin yake, ko shakka babu, sha’anin sana’ar sassak’a ta yi ruwa da tsaki wajen inganta tattalin arzikin al’umma musamman al’ummar k’asar Argungu da ake nazarin a kansu ta fuskoki daban-daban. Dalijan, (2012:41) ya rawaito Ibrahim, (1992:25) inda ya bayyana cewa, sana’o’in Hausawa sune k’ashin bayan ginuwar tattalin arzikinsu.

Baya ga wad’annan ra’ayoyi, akwai sauran zantuka da dama da tuni masana da manazarta suka yi a wannan haujin , domin k’arin bayani ana iya duban ayyukan Ayagi (1976:11) da Koko, (2004:5) da Sallau, (2010:14)

Duba daga irin wad’annan ra’ayoyi da ya shafi tattalin arzikin Hausawa, sana’ar sassak’a ba kanwar lasa ba ce a wannan haujin, domin za a ga cewar, sana’a ce da ta taimaka sosai wajen samar da ci gaban k’asar Hausa baki d’aya ba ma k’asar Argungu ba kawai  ta fannoni daban-daban kamar yadda bayani ke biye a k’asa.

3.0 Gudummawar Sana’ar Sassak’a Ga Bunk’asar Tattalin Arzikin  K’asar Argungu

Sana’ar sassak’a kamar sauran sana’o’in gargajiya na Hausawa ta taka muhimmiyar rawa wajen bunk’asa tattalin arzikin al’ummar Kabawa ta fuskoki daban –daban. Daga cikin muhimman hanyoyin da sana’ar ta bayar da gudummawarta a wannan haujin sun had’a da: Bunk’asa tattalin   arziki, samar da aikin yi ga al’umma, samar da kud’in shiga ga hukuma, samar da kayan aiki ga al’umma, samar da wasu kayayyaki ga wasu sana’o’i, samar da kiwon lafiya, k’ara inganta zumunci da zaman lafiya, inganta tsaro, inganta sufuri da sauransu.

 3.1 Samar Da Ingantaccen Tsaro


Lamarin tsaro wani abu ne mai matuk’ar muhimmanci ba ma ga al’ummar Hausawa ba kawai, har da sauran al’ummomin duniya baki d’aya. Don haka, babu al’ummar da rayuwarta za ta inganta ba tare da samar da muhimman hanyoyin tsaro ba. A nan za a ga cewar masassak’a sun taka mihimmiyar rawa a wannan haujin. Alal misali, idan aka dubi kayan yak’in da masassak’a kan taimaka wajen samar da su kamar k’otocin mashi da bindiga da itacen baka da k’otocin adda da wuk’ak’e da sauransu, dukkan wad’annan sun taimaka wajen inganta sha’anin tsaro a k’asar Argungu.  Bunza, (2016:14) ya bayyana cewa:

“Ba a yin yak’i sai da makami kamar yadda wani makami ba ya kammala sai da taimakon masassak’a ta hanyar samar da ‘bota/k’ota da icen baka, wasu makaman yak’i ba su kamala kuma ba za a ji dad’in amfani da su yadda ake so ba. Wannan ke nuna muhimmancin masassak’a a  ‘bangaren tsaron gargajiya ta hanyar sarautar da suke kanta”.

Wannan bayani ya k’ara fid da tasirin masassak’a musamman ta yadda sassak’an kan taimaka wajen kammaluwar kayan tsaro a k’asar Argungu.

Baya ga wannan, a shekarun baya idan aka samu bak’o a gari, a kan tambaye shi irin sana’arsa, idan masassak’i ne sai a kai shi gidan shugabansu. Shi kuwa shugaban zai sa masa ido yana kallon hankalinsa, idan an aminta da shi sai a saukar da shi, idan kuwa ba a aminta ba sai a sallame shi ya k’ara gaba. Yin wannan kuwa ba k’aramin taimakawa yake ba ta fuskar samar da tsaro a k’asar A rgungu.

Baya ga wannan a d’akin adana kayan tarihi na Kanta da ke Argungu, an nuna mani wata kujera wadda aka sassak’a, ita wannan kujerar bincike ya gano cewar a lokacin yak’i idan mai ita ya hau ta, duk abin da ya umurci abokan gaba su aikata shi za su aikata. A nan za a ga ire-iren wad’annan kayayyaki na sassak’a sun taimaka wajen samar da tsaro a k’asar Argungu. Haka masassak’an sun samar da sirdin rak’umi da dawaki wad’anda aka yi amfani da su a lokuttatn yak’i. Haka sun taimaka wajen samar da kayan kid’a na yak’i daban daban da ake amfani da su wajen k’ara wa mayak’a k’aimi da zuguguta su kamar tambari da sauransu. Samuwar ingantaccen tsaro kuwa shi zai taimaka wajen samun walwalar neman abinci da bunk’asa tattalin arziki.

3.2 Samar Da Aikin Yi Ga Al’umma

A yau a bayyyane yake cewar wannan sana’ar ta samar wa mutane masu d’imbin yawa aikin yi a cikin al’umma. Duk da yake cewa, sana’ar sassak’a sana’a ce da aka gada tun kaka da kakanni, wannan bai hana wasu wad’anda ba su gaje ta ba shiga cikin harakar. Wannan kuwa ya haifar da k’aruwan jama’a masu aiwatar da wannan sana’a. Daga cikin d’an abin da suke samu ne suke sarrafawa wajen hidimominsu na yau da kullum. Fa’idar wannan kuwa a fili take idan aka dubi yadda matasa a yau suke zaune ba tare da wani abin yi ba sai dai zaman kashe wando. Don haka, akwai buk’atar matasa su rungumi wannan sana’ar domin kauce wa zaman banza wanda ba abin da zai haifar illa k’arin fatara a cikin al’umma. Yin rik’o ga wannan sana’ar zai taimaka wa matasanmu wajen dogaro da kai.

Bisa ga wannan jama’a da dama na cikin k’asar Argungu a yau sun himmatu wurin aiwatar da wannan sana’ar wanda ta taimaka wajen inganta tattalin arzikinsu da fuskoki daban-daban.

3.3 Samar Da Kud’in Shiga Ga Hukuma

A nan a bayyane yake cewa, masu aiwatar da wannan sana’ar ta sassak’a suna samar wa hukumomi kud’in shiga, domin masassak’a kamar sauran masu sana’o’in hannu suna kai kayan sassak’ansu a kasuwanni daban-daban domin sayarwa. A lokacin da wad’annan kayayyaki suka kai kasuwa kuwa, masu amsar haraji sukan aza masu kud’in da za su biya wanda za a sanya a asusun hukuma domin ciyar da k’asa gaba. Irin wad’annan kud’ad’e ne ake gudanar da ayyukan da suka shafi gina asibitoci da makarantu da hanyoyi da samar da ruwan sha da sauransu a cikin lungu da sak’o na k’asar Argungu. Samuwar irin wad’annan ababe kuwa ya haifar da bunk’asar tattalin arzikin masarautar Argungu cikin sauri.

Bugu da k’ari, kayayyakin sassak’an da suke sassak’awa sukan jawo ‘yan yawon bud’e ido daga wasu k’asashe domin cire kwarkwatar ido da nuna sha’awarsu ga wad’annan kayayyaki. Ta wannan fuska, ita kuwa hukuma da sauran al’umma suna samun taro-sisi daga wad’annan masu yawon bude ido ta hanyar jirga-jirgansu da wurin kwanansu da abincin da za su ci, duk al’ummar k’asar Argungu na amfana da su ta wannan haujin a sanadiyyar kayayyakin da masassak’a kan samar. Ita kuwa hukuma tana samun kud’in shiga daga wad’annan masu yawon bud’e ido. Misali irin kayayyakin da masassak’a kan samar a lokacin wasannin bikin kamun kifi na Argungu kamar jiragen ruwa da ake amfani da su butum-bumin kifi  domin kamun kifi duk sun taimaka wajen inganta tattalin arzikin k’asar Argungu.

3.4 Samar Da Muhimman Kayan Aiki Ga Al’umma

Masassak’a sun taimaka kwarai da gaske wajen samar wa al’ummar k’asar Argungu muhimman kayayyakin aiki da suke buk’ata wajen hidimominsu na yau da kullum. Wannan kuwa a bayyane yake idan aka yi duba daga nau’ukan kayayyakin da suke samarwa wad’anda suka had’a da turame da ta’barya da muciya da akushi da dangarafai da k’otoci da kujerun zama na maza da mata da sauransu. Dalijan, (2012:107) ya bayyana cewa:

“Masassak’a suna da amfani ga al’ummar Hausawa saboda sune ke samar musu jirgin ruwa da turmi da ta’barya da akushi da kuyafa da ludduna. Sa’annan masassak’a ke samar da kujerar zama ta mata da kwacciyar sirdi ko dangarafai da k’otocin garma da kalme da hauya da  gatari da sungumi da alluna da mutum-mutumi da sauransu”.

Dukkan wad’annan ababe, kad’an ne daga cikin nau’ukan kayayyakin da masassak’a kan samar domin amfanin al’umma na yau dakullum a k’asar Argungu. Ko shakka babu, amfani da wad’annan nau’ukan kayayyaki ga al’ummar k’asar Argungu sun taimaka wajen bunk’asar tattalin arzikinsu ta fuskoki da dama. Misali masu sana’ar dakau suna amfani da turmi da ta’barya da masassak’a suka samar domin inganta sana’arsu wanda a k’arshe zai haifar da bunk’asar tattalin arzikinsu.

3.5 Samar Da Kayayyakin Aiki Ga Wasu Sana’o’i

Baya ga d’imbin kayayyakin amfani da masassak’a kan samar wad’anda suka shafi na aikin gida da na sufuri da aikin gona da sauransu. Har wa yau, sana’ar sassak’a ta taimaka wajen samar wa wasu sana’o’i kayan aiki. A nan babu ko tambaba, manomi ba zai iya noma ba sai da fartanya, duk da yake mak’era ke k’era ta, amma ba za a iya aiki da ita ba sai da k’ota, ita kuwa k’ota masassak’a ne ke samar da ita. Haka abin yake ga sana’o’i da dama da ake aiwatarwa a k’asar Argungu inda za a tarar akwai nau’in gudummawar da masassak’a kan bayar domin gudanar sana’o’in. Misali masassak’a na samar wa masak’a itacen kwafa da cakarkara, marina kuwa masassak’a sun samar masu da itacen bugu da mabuga da mucciyar motsa rini cikin gwagwa da dai sauransu. Duk wad’annan sana’o’i kuwa sun taimaka wajen bunk’asa tattalin arzikin Kabawa.

3.6 Samar Da Kiwon Lafiya

A k’asar Argungu, daga cikin rukunin jama’a masu bayar da magungunan gargajiya akwai masu aiwatar da sana’o’in gargajiya wanda ya had’a da masassak’a. Shi kuwa sha’anin kiwon lafiya abu ne mai matuk’ar muhimmanci ga kowace al’umma, domin rayuwa ba ta inganta sai da lafiwa. Saboda haka ne ma wani mawak’i ‘Dangiwa Zuru yake cewa: “Lafiya uwar jiki babu mai fushi da ke” .  A wannan fuskar ta samar da ingantaccen kiwon lafiya, masassak’a sun taimaka kwarai wajen bayar da wasu magunguna na gargajiya da za su taimaka wajen kawar da wata cuta ko rage rad’ad’inta a cikin al’umma. Wannan kuwa ba zai rasa nasaba da ganin cewa masassak’a suna tu’ammali da nau’ukan itatuwa daban-daban a cikin daji ba domin aiwatar da sana’arsu. Daga cikin magungunan da masassak’a kan bayar domin inganta kiwon lafiya sun had’a da maganin basur (d’ankanoma) da maganin daji da maganin ciwon ciki ko zafin ciki da sauransu. Haka sukan bayar da magungunan riga-kafin wasu cututtuka da na kariyar kai da nuna waibuwa. Samar da irin wad’annan magunguna suna taimakawa wajen samar da al’umma masu ingantaccen kiwon lafiya, wanda a k’arshe zai ba su damar fafatukar neman abinci da sauran fad’i-tashi domin inganta rayuwa baki d’aya.

Har wa yau, a cikin sana’ar sassak’a ana samun motsa jiki ta hanyar zuwa daji saran ice da aikatar da shi zuwa abin da ake buk’ata. Wad’annan aikace-aikace suna taimakawa wajen motsawar jini a jikin ‘Dan adam, wannan kuwa ba k’aramin taimakawa yake ba wajen inganta lafiyar al’umma wanda a k’arshe zai ba su damar hada-hada domin bunk’asa tattalin arziki.

3.7 Inganta Zumunci  Da Zaman Lafiya A Tsakanin Al’umma

Kalmar zumunci tana nufin wata dangantaka ce ta jinni (haihuwa), ko ta aure ko ta zamantakewa ( makwabtaka ko mu’amula). Haka zumunci na iya d’aukar wata dangantaka, ko dangi, ko ‘ya uwa. A tak’aice ana iya cewa, zumunci wata alak’a ce ta jini ko mu’amula da ya shafi jituwa a tsakamin al’umma domin gudanar da harakokin rayuwarsu ta yau da kullum. Don haka, inganta zumunci wani abu ne mai muhimmanci a cikin al’umma. A nan masu wannan sana’ar ta sassak’a sun taimaka wajen inganta wannan zumunci ta fuskoki da dama. Da farko dai za a ga cewa, ta hanyar bukukuwan da sukan yi na k’arshen shekara; ana tara ‘yan uwa da abokan arziki wuri d’aya a ci, a sha a yi raha a tsakanin juna. Haka idan aka tashi bikin nad’in sarautar sarkin masassak’a a kan gayyaci jama’a daga wurare daban-daban domin taya juna murna, yin wannan kuwa ba abin da ya ke haifarwa in ban da k’ara dank’on zumunci a tsakanin al’umma. Haka idan lalurar aure ko haihuwa ko dai wani biki na musamman ya samu masassak’i, ‘yan uwansa sukan tara masa taro-sisi domin ya share wa kansa hawaye. Baya ga wannan, a lokacin bukukuwa da wasaanin masassak’a sukan tattauna matsalolin da suka addabe su tare da fid da hanyoyin magance matsalolin cikin hikima da basira ba tare da tada jijiyar wuya ba. Haka sana’ar ta taimaka wajen samun kyakkyawan huld’a da zaman tare tsakanin masassak’a da sauran al’ummomi a sassa daban-daban, wannan kuwa a bayyane yake idan aka dubi yadda masassak’a kan fita da kayan sassak’arsu a k’asashe daban-daban na duniya. Had’uwarsu da sauran wad’annan al’ummomi ya haifar da k’arin dank’on zumunci na cikin gida da na waje. Saboda irin wannan zumunci ne ya haifar da wasan barkwanci a tsakanin masassak’a da mak’era a k’asar Argungu.

Wannan kyakkyawan zumunci da zama lafiya da masassak’a suka wanzar ya taimaka wajen bunk’asa tattalin arziki a k’asar Argungu. Hausawa na cewa, “Sai da zama lafiya ake iya komai” don haka in babu zama lafiya da k’aunar juna tilas tattalin arziki ya samu cikas a cikin al’umma.

3.8 Wata Kafa Mai Nuna K’ima Da Martabar Kabawa

Ganin cewa al’ummar Kabawa sun d’auki lamarin sana’a da muhimmanci, wannan shi ya haifar idan mutum ba ya da sana’a a k’asar Argungu ba a yi masa d’aukar cikakken mutum wanda ya san ciwon kansa. Wani lokaci ma har hana masa mata akan yi domin ana ganin ba shi da abin ciyar da ita. Don haka, sassak’a kamar sauran masu sana’o’in gargajiya na Hausawa suna jawo wa kansu k’ima da daraja a gaban al’umma, kuma sana’ar tasu ta zama abin alfahari da tink’aho a gare su, saboda ta wannan sana’ar ce suke ci su sha da sauran wasu buk’atoci na rayuwa baki d’aya. Hassan, (2013:212) ta bayyana cewa:

“Sana’o’in kan sa darajarsu (Hausawa) ta d’aukaka  yadda ake gane basirarsu da fasaharsu domin ko da Turawa suka zo k’asar Hausa sun tarar da Hausawa da sana’o’insu na gargajiya, wannan ya sa Turawa suke jinjinawa Hausawa, anan ne Hausawa suke yi wa    kansu kirari da wai “tun kafin a haifi uwar mai sabulu Balbela take da farinta”.

Don haka, rik’o ga sana’ar sassak’a yana k’ara daukaka martabar masu aiwatar da sana’ar a idanun al’umma na ciki da wajen k’asar Hausa.  Yin wannan kuwa kan iya haifar da sha’awa ga wasu na waje su shigo a dama da su a wannan sana’ar, wanda a karshe zai haifar da ci gaban sana’ar ta bunk’asa.

3.9 Wata Kafa ta Rayawa Da Adana Al’adu

Sana’ar sassak’a ta zama tamkar wata kafa da al’ummar Hausawa ke amfani da ita wajen rayawa da kuma adana wasu muhimman al’adunsu. Wannan a bayyane yake idan aka yi duba da yadda masassak’a kan samar da wasu muhimman kayayyakin aiki da suka shafi wasu al’adu daban-daban a k’asar Argungu. Misali idan aka dubi turmi da ta’barya da kujerun zama na maza da mata da sauran nau’ukan kayayyaki da dama da sukan samar, wad’anda ake amfani da su wajen aiwatar da wasu aikace-aikace da suka shafi al’adun Hausawa musamman na masarautar Argungu. Wad’annan kayayyaki na sassak’a da aka adana, wani lokaci ana iya samun masu buk’atar su kuma su saye su da tsada domin tarihi. Samuwar irin wad’annan kud’ad’e kan taimaka wajen inganta tattalin arzikin k’asar Argungu.

A hannu d’aya, sassak’an wad’annan kayayyaki na al’ada zai bayar da damar a samu adana su musamman a d’akunan adana kayan tarihi  na k’asar Argungu. Wannan zai bada damar na baya su iya ganinsu a zahiri, musamman da yake a yanzu akwai hasashen nan gaba sana’ar za ta gushe saboda barazanar tsarin game duniya (globalization).

 

 

3.10 Samar Da Nishad’i Da Ciniki A Tsakanin Al’umma

Samar da nishad’i a tsakanin al’ummar Hausawa yana daga cikin muhimmacin sana’ar sassak’a a k’asar Hausa. Za a iya fahintar wannan idan aka dubi yadda masassak’a suke gudanar da wasu bukukuwa na musamman wad’anda suka k’unshi kad’e-kad’e da raye-raye a cikin al’umma. Daga cikin bukukuwan da sukan gudanar sun had’a da bikin nad’in sarautar sarkin masassak’a na gari ko yanki ko unguwa. Haka suna aiwatar da wasu bukukuwa a lokacin sallah ko aure ko haihuwa. Dukkan wad’annan bukukuwa sun taimaka wajen samar da nishad’i a tsakanin al’umma.

Haka a lokacin aiwatar da wad’annan bukukuwa ana samun had’uwar jama’a daga sassa daban-daban na k’asar Argungu da kewaye. A irin wannan had’uwa ana samun saye da sayarwa a tsakanin al’ummomin da suka halarci bikin, wannan kuwa na taimakawa wajen bunk’asa tattalin arzikin mahalarta bikin.

4.0 Kammalawa

Bisa ga bayanan da suka gabata an gano cewa,  sana’ar sassak’a  a k’asar Argungu wata tsohuwar sana’a ce da aka dad’e ana aiwatarwa a k’asar. Don haka, sana’ar ta bayar da gagarumar gudummwa wajen bunk’asa tattalin arzikin al’ummar masarautar Argungu ta fuskoki da dama. Daga cikin abin da takardar ta gano a wannan haujin sun had’a da: Samar da ingantaccen tsaro da samar da aikin yi da samar da wasu kayan aiki ga wasu sana’o’i da samar da kiwon lafiya da inganta zumunci da zama lafiya da kafar inganta zumunci da ciniki a tsakanin al’umma da sauransu. Ko shakka babu, samuwar irin wad’annan guummawar sun taimaka sosai wurin inganta tattalin arzikin al’ummar k’asar Argungu ta fuskoki da dama. Don haka, sana’ar sassak’a a k’asar Argungu ba abin wofintarwa ba ce.

 

 

Manazarta


 

Alhassan, H. da wasu (1980) Zaman Hausawa Na ‘Daya, Don Makarantun Gaba da Firamare. Zaria: Institute of Education, Ahmadu Bello University.

Auta, A. L. (2006) Tattalin Arzikin Al’umma: Nazarin Sana’o’i da Kasuwancin Hausa. In Algaita Journal of Current Reseach in Hausa Studies, No 4 vol 1 pp 194-204.

Auta, A.L. (1986) Jima Sana’ar Sarrafa Fata da Muhimmancinta a K’asar Hausa. Kundin Digiri Na Farko, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

Bunza, D.M. (2016) Tsaro A K’asar Hausa: Gudummawar Sarautun Tsaro A Arewacin Nijeria. Takardar da aka gabatar a taron k’ara wa juna sani na k’asa da Tsangayar Fasaha da Nazarin Addinin Musulunci ta shirya daga ranar 1-3, Maris,2016 . A harabar jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

CNHN, (2006) K’amussun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press.

Dalijan, B.M. (2012) Noma Da Ginuwar Tattalin Arzikin Hausawa Na Gargajiya. Kundin Digiri Na Biyu, Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

Hassan,  F.M.(2013) Saki Reshe…Tsokaci Dangane Da Sana’o’in Hausawa Na Gargajiya A Jiya Da Yau. In Excerpts of International Seminar on The Deterioration of Hausa Culture. Organised by Katsina State History and Cukture Bureau in Colabaration with Umaru Musa Yar adua University, Katsina. pp 217-226.

Ibrahim, M.S. (1982) Dangantakar Al’ada da Addini: Tasirin Musulunci Kan Rayuwar Hausawa Ta Gargajiya. Kundin Digiri Na Biyu, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

Rimmer, E.M da Ingawa, A. da Musawa, A. da Auna, Y.I. (1984) Zaman Mutum Da Sana’arsa. Zaria: Northern Nigerian Publishing Company.

Sallau, B.A.S. (2010) Wanzanci da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Kaduna: M.A Najiu Professional Printers.

Sanyinna, A. B. & Sanyinnawal, S. I. (2015) Uwa Ma Ba ‘Ya Mama: Dangantakar Sana’ar K’ira da Wasu Sana’o’in Gargajiya Na Hausawa. A Cikin Shagari Journal of Languages. 1st Edition, School of Languages, Shehu Shagari College of Education, Sokoto.

Sanyinnawal, S. I. (2015) Cud’ed’eniyar Sana’o’in Gargajiya a Adabin Bakan Bahaushe. Kundin Digiri Na Biyu. Sashen Harsunan Nigeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

Sarkin Gulbi, A. (2014) Magani a Ma’aunin Karin Magana. Kundin Digiri Na Uku. Sashen Harsunan Nigeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

Shinkafi, R.H. (2016) Tattalin Arziki da Had’in kan Nijeria a Idon Muhammadu Sarkin Taushin Katsina. Mak’alar da aka gabatar a taron k’ara wa juna sani kan Matsayin Harshe da Tarihi da Addini Wajen Bunk’asa ci gaba da Had’in kai da Tsaro a Nijeriya. Wadda aka gabatar a Tsangayar Fasaha da Nazarin Addinin Musulunci, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato. Daga ranar 1-3 maris, 2016.

Umar, M. B. (1983) Tasirin Tattalin Arzikin Hausawa na Gargajiya. Takardar da aka gabatar a taron k’ara wa juna sani, Sashen Koyar da Harsunan Nigeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

Wamba, S.A. (2015) An Bar Jaki Ana Bugun Taiki: Gudummawar Sana’o’in Gargajiya Ga Tattakin Arzikin K’asar Hausa. Mak’alar da aka gabatar a taron k’asa da k’asa na farko wanda K’ungiyar Manazarta Harshen Hausa ta shiya kan Hausawa da Harshensu. A Sashen Nazarin Harsunan Nigeriya Da Kimiyar Harsuna, Jami’ar Jahar Kaduna a ranakun 23-25 ga watan Maris, 2015.

Wushishi, S.S. (2011) Dangantakar Magani Da Wasu Sana’o’in Gargajiya Na Hausawa. Kundin Digiri Na Biyu, Sashen Harsunan Nigeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

Yakasai, S.A. (2012) Taskar Al’ada Da Tarihi Da Nishad’i: Kammalallen Sharhin Littafin Tatsuniyoyi Na Dokta Bukar Usman. Kano: Gidan Dabino Publishers.

Yola, M. M. (2014) Sana’o’in Hausawa Na Gargajiya Da Tasirinsu A Zamanance. A cikin Garkuwan Adabin Hausa.  A Festschrift in Tribute to Abdulkadir Dangambo.  Zaria: Ahmadu Bello University Press. pp 507-514

Zaruk, R.M da wasu, (1987) Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Manyan Makarantun Sakondare Littafi na ‘Daya. Ibadan: University Press Limited.

 

Post a Comment

1 Comments

Post your comment or ask a question.