Koronar Ƙasata

    Duk da cewa cutar korona gaskiya ce, a ƙasata al'amarinta ya zo da wani sabon salo da za a iya fasaltawa da maganar Bahaushe cewa: "Akwai lauje cikin naɗi!" Baitukan waƙar sun kare wannan ikirari.

    1. Salamun alaikum ga ku ‘yan’uwana,
    Na gaishe da kowanku barka da rana,
    Musamman Musulmi na yankin Arewa. 

    2. A farkon zuwan wagga cuta Korona,
    Ƙasata ta ɗauke ta ɗaukar sakaina,
    Ana dariya har da mai ƙyalƙyalewa. 

    3. Kawai sai Korona ta ɓullo da aiki,
    Ta jefa mu tarkon hanun masu mulki,
    Suna zare saƙar a bakin abawa. 

    4. A da 'yan watanni kaɗan baya-baya,
    A kan wagga cuta Koronar maraya,
    Fasihanmu sun gargaɗin faɗɗakarwa. 

    6. Sukan ce mutane ku dawo mu tuba,
    Balai yakan cinye yaro da babba,
    Idan ya taho taliki bai hanawa.

    7. Ƙasar China can anka faro Korona,
    Ta ratsa ta jirgi ta zo har gidana,
    Ta hannunsu manya ta hau zagayawa.

     

    8. Talakkanmu bai san hawa koko sauka,

    Yana zaune ɗakinsa yumɓu da bukka,

    Ta shafai ta fiska dubu sai daɗawa.

     

    9. Wajen yin ibada a ce wai Korona,

    Da hulɗa da juna a ce wai mu daina,

    Mutum ya zamo shi ake wai gujewa.

     

    10. Ku duba a kan wanga cuta Korona,

    Ake kora kowa gida dan ya zauna,

    Da dai ba a lura da yunwa kashewa.

     

    11. Ku gane fa yunwa da tsoro biyun nan,

    Idan sunka kama ka sai an ga wannan,

    Kamar dai tufafi a fili sakawa.

     

    12. A yau ga shi dukkansu sun mamaye mu,

    Musamman Korona tana razana mu,

    Mu tsere gida ba guda mai fitowa.

     

    13. Ɗayar ko tana can a lungun kusurwa,

    Ta damƙe ka dolen ka sai kai fitowa,

    Da yunwa da tsoro mutum bai iyawa.

     

    14. Kawai ga shi kowa a yau sai da jambu,
    Muna wanke hannu kamar an yi kambu,

    Korona ƙazama kina takurawa.

     

    15. Talakkanmu ya sha wuya wanga zango,

    Macuta a nan sunka bubbuɗe shago,

    Na cutarmu kaitonku yayan zubarwa.

     

    16. A kan wai a nemo abin ci a ba da,

    A ce malamai koina ai ibada,

    Kawai sai a kulle mu wai an tarewa.

     

    17. Muna ji muna yi gani dan ku gane,

    Cikin asbitocinmu kowa a zaune,

    Kawai babu kaya na aiki riƙewa.

     

    18. Idan ka yi tari a ce wai Korona,

    Kana zazzaɓi ba batun ma a auna,

    Abin ma da gangan ake maƙƙalawa.

     

    19. Dukan wanga giɓi ta gun shugabanni,

    Ya ɓullo gaba dai cikin yan awanni,

    Kuɗaɗen Korona suke wawashewa.

     

    20. Ya sa dole sai mun yi kishin ƙasarmu,

    Musamman jihohin Arewarga tamu,

    A mulki mu zaɓo aminai sakawa.

     

    21. Bayanin a da can fa mun ji shi baya,

    Wajen kakani kar mu zazzauna baya,

    Kasar tamu ce kar da dai mui sakewa.

     

    22. Sukan ce wa mu kun ga daular Arewa,

    Wajen shugabanci idan kun sakewa,

    Watan wattaran za ta zam durƙushewa.

     

    23. Ƙabilu su cuce ku arnan maƙota,

    Da ƙarya da cuta su nannarka sata,

    Su danne ku dukkanku ba mai ɗagawa.

     

    24. Su maishe ku bayi ku zauna da yunwa,

    A kulle ku ba mai fita noma dawa,

    Tufafinku tsumma abin daddagewa.

     

    25. Kawai zuciya ta mace ba tunani,

    A tsari kamar babu ma shugabanni,

    Da cuta da yunwarka ba mai kulawa.

     

    26. Ƙasa taku amma a ƙyale ku boda,

    A ƙwace muƙaman da ku kun ka gada,

    Iyaye da kaka ya zam yai gushewa.

     

    27. Ku zauna a bukka gidajen karare,

    Wuta babu kullum idanu a zare,

    Kuna ji a zage ku ba mai hanawa.

     

    28. Haba ‘yan uwana ku leka ƙasata,

    Ina ne talauci ya nuna a fata?

    Da ci baya wannan batu sai Arewa.

     

    29. Muradinmu shi ne miya ta ji magi,

    Yawan namu ya zam yawan ‘yan agwagi,

    Rago na gaba jarumi na kusurwa.

     

    30. Ƙwarewarmu na nan wajen karya doka,

    Misalinmu shi ne ruwan marka-marka,

    Ya rushe gidaje tsiro yai kashewa.

     

    31. Wajen ci da bacci a nan mun fi himma,

    Gaba ɗanmu kowa yana doka hamma,

    Abin tausayi mun fi son shaƙatawa.

     

    32. Arewarmu mata gwanaye na guɗa,

    Mazan ko a layi tufafinmu dauɗa,

    A nan za mu zauna muna shantakewa.

     

    33. Iyalenmu kullun ciki ne da goyo,

    Haba kai Bahaushe gwanin nuna wayo,

    Ka gane fa wautar kana ɗan taɓawa.

     

    35. Idan tajiri ne gwanin aure-aure,

    Ya auro baƙaƙe ya auro farare,

    Ɗiya barkatai dukka ba mai kulawa.

     

    36. Su taso da sata suna shaye shaye,

    Da 'yancinsu 'yanmata sun saba gaye,

    Suna karuwanci halin tamfatsewa.

     

    37. Idan ko faƙiri Bahaushe ya taso,

    Yana ƙi a mulkeshi ko da yana so,

    Gida nai iyalinsa ce mai ginawa.

     

    38. Ta koya wa ‘ya’yanshi tallan gurasa,

    Da yawo na banza a bangar siyasa,

    Kuɗi son shi ta sa wa su ba hanawa.

     

    39. Abin tausayi dubi Mallam Bahaushe,

    Da yunwa jiki nai maƙoshi a bushe,

    Mutuncinshi ‘yar fan biyar kan sayarwa.

     

    40. Cikin rayuwa nashi sam babu tsari,

    Yana kwance sai son jiki ga ko buri,

    Kawai shi a yau za a yo ay gamawa.

     

    41. A wannan ƙasa tamu in har ka duba,

    Ta fiskar siyasa da bauta wa Rabba,

    Mutanen kudun ba su son ‘yan Arewa.

     

    42. Zama tare amma a rai an yi ɗai-ɗai,

    Dalilin ko shi ne uwar ce guda ɗai,

    Ta haife mu sannan ta hau jarrabawa.

     

    43. Cikin ƙaddara sai a kai matta fyaɗe,

    Ta ɗauko ciki duniya na ta zunɗe,

    Ta haife su shegu magaftan Arewa.

     

    44. Arewar ta cishe su dan bassu kowa,

    A yau ga shi su ne su ke yin ɗagawa,

    Tufafi a da kun ga ba sa sakawa.

     

    45. Da gero da dawa kuɗin auduga ne,

    Gyaɗa har da shanu a bar tone-tone,

    Da su anka yo rijiyar mai cirewa.

     

     

    46. Kawai sai a zo yau batu kan Korona,

    A kwashe kuɗaɗe a je can a ƙona,

    Arewarmu ba ma mutum mai kulawa.

     

    47. Ana kakkashe yan uwa can a yamma,

    Gabas dubi Kanuri an ɓad da dama,

    Kisa ya zamo kwalliya nan Arewa.

     

    48. A rana a ɗau ran mutane tamanin,

    Ɗari, koko maitan a yanka tsakanin,

    Gurubi na rana gabanin fitowa.

     

    49. Musibar ga ta afku ta mamaye mu,

    Kisan rai Arewarmu ya takura mu,

    Kiyashi da yancinsa mu an hanawa.

     

    50. Baƙar gamnatin nan a kan wai ta dawo,

    Batu kan ta'adda tsaron nan a kawo,

    Kawai sai Korona ake tallatawa.

     

    51. Kashedi muke shugabannin Arewa,

    Su o'onmu gwamna ku duba shi wawa,

    Muradinsa naira da hutu habawa!

     

    52. Mu zabe ka domin wakilcin Arewa,

    A tsere wa yunwa tsaro ai tsarewa,

    Kawai sai ka ƙyale mu ba ka kulawa.

     

    53. Musulmi a yau ba dabarar siyasa,

    A duka wa arne a ce mar “dear sir,

    Kawai dan a mulki ana son daɗewa.

     

    54. Ƙwaƙwalensu tamkar ƙwaƙwale na birrai,

    Kuɗaɗe su sace su miƙa su Turai,

    Tsurut ɗan kaɗan za su zo sui rabawa.

     

    55. Bayanin ga mai hankali za ya gane,

    Misali a haƙƙi a ce naka sa ne,

    Sukan ba ka ƙwai sai su ce kai afawa.

     

    56. Ku gane fa ƙwai bai zamowa abinci,

    Mugunta ina za a ce mai azanci?

    Bayanai da Hausa abin karrarawa.

     

    57. Abin kaito wai sai mu karɓa mu gode,

    Muna jam sago ɗon ɓuri hanko hande,

    A Facebook da Youtube muna sassakawa.

     

    58. Fa haƙƙinmu titi na jirgi da mota,

    A samar da hasken, tsaro babu mita,

    Kawai jar kasa za a zo ai zubawa.

     

    59. Fa haƙƙinmu dukkan gari ai drainage,

    Kawai sai a ɗora mu tsari na mannage,

    Da an yo ruwa sai gini yai zubewa.

     

    60. A samar da tafki ƙasa tai yabanya,

    Cikin damina ai ta noma kiyaya,

    A rani a sake tsiro yai tsirowa.

     

    61. Kawai sai a zo lambatu za a tona,

    Siminti kaɗan sai ƙasa dubi ɓarna,

    A can unguwar gefe lungun kusurwa.

     

    62. Abin ma da kunya iyalensu na can,

    Ƙasashe na Turai abincinsu na can,

    Ku duba mutanen ga ba tausayawa.

     

    63. Batun ilmu yau babu mai so ya furta,

    Na allo da boko abin ya ƙazanta,

    A yau jami’o’inmu duk an rufewa.

     

    64. Da dama akwai malamai yan private,

    Ta nan ne abincinsu sun seta target,

    Ɗiyan malami babu mai tallafawa.

     

    65. Korona bala'inki ya illata mu,

    Dalilinki an kori almajiranmu,

    Karatun na Qur'ani zai durƙushewa.

     

    66. Abin tausayi dubi almajirin nan,

    Bakauyen da mota ta mar toliyan nan,

    A ce shi ya kawo Korona habawa!

     

    67. Kawai an ga dai bai da galihu ne ma,

    Iyayenshi aikinsu kiwo da noma,

    Ya sa alhakin kansa an kai sakawa.

     

    68. Idan har ka duba cikin zamanin nan,

    Batun shugabancin baƙi ɗan kasar nan,

    Kaɗan ne kwarai masu aikin yabawa.

     

    69. Yawancinsu daula da naira su ke so,

    Siyasarmu kullun muradin su kwaso,

    Kuɗaɗenmu, komai abin ba a cewa.

     

    70. Haba shugabanni na yankin Arewa,

    Muradanku sun mai da kowanku wawa,

    A yau duk cikin naku ba mai ta cewa.

     

    71. Idan har kuna so mu bar yin kashedi,

    Mu bar kama suna a waƙe na kundi,

    Ku mulke mu tamkar Tafawan Balewa.

     

    72. Ku zam jarumai sai mu ce kun yi daidai,

    Muhimman mutane mutunci kamar dai,

    Uba gun mu Sardauna sai mui yabawa.

     

    73. Kamar Murtala soji Allah jiƙai nai,

    Ku ɗauke mu 'ya'yanku dan mun fi ƙannai,

    Idan kun ƙi Mamuda ba ya ragawa.

     

    74. Idan har da biro da sauran takarda,

    A hannunmu to kar ku yo inda-inda,

    Fa Mamuda waƙa ku san bai ajewa.

     

    75. Makaminmu sulkenmu kaya na yaƙi,

    Idan har da yawu a bakin mawaƙi,

    Ƙwarai za ya tofar shi dan bai haɗewa.

     

    76. Gwani Rabbi yau gamu roƙo muke yi,

    Nufi duk na sharri ga mu kai kiyayi,

    Ka fisshe mu wayonmu mu yai gazawa.

     

    77. Magafta na bayinka mun ba ka zaɓi,

    Ka jefa su rami su tattaka caɓi,

    Ka maishe su birrai gidan zoo sakawa.

     

    78. Idan shugaba gunmu cuta yake yi,

    Ya ɗau wanga cuta Korona a yayi,

    Cikin teku Allah ka sa yai nutsewa.

     

    79. Idan ko ka so sai ka maishe shi jaki,

    A lallafta kaya a kai nai kucaki,

    Ka mai da shi mashin mu hau mui burawa.

     

    80. Halittarsa Allah ka sa yai ƙusumbi,

    Ya zamto gajere baƙi ga fa tumbi,

    Da sanƙo, gatsori ka sa sui fitowa.

     

    81. Ku ce kun ji amin abokai da dangi,

    Mu dage da roƙo cikin wanga ƙangi,

    Du’a’inmu Allah Gwani bai hanawa.

     

    82. Batun nawa sam ba ba’a ba habaici,

    Kashedi na ɗan yo mu farka a bacci,

    Mu gane Korona da ƙarya haɗawa.

     

    83. Ina yin salati wajen Ɗan Amina,

    Muhamman masoyi abin nuna ƙauna,

    Iyalai, abokansa ba na cirewa.

     

    84. Cikin baituka na tamanin a jere,

    Da ƙarin biyar nai batu na na more,

    Na fiddo bayani ina bayyanawa.

     

    85. Fa'ulun Fa'ulun Fa'ulun rufinta,

    Salamun Salamun Salamun rufe ta,

    Korona bayaninki ni nai rufewa


    Daga
    Mahmud Ahmad Musa

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.