Musa Shehu
Sashen Koyar Da Harsunan
Nijeriya
Jami’ar Usmanu Danfodiyo,
Sakkwato.
msyauri@yahoo.com
1.0 Gabatarwa
2.0 Ma’anar
Tarbiyya
1. a) Koyar
da ladabi da biyayya da ɗa’a da sanin ya kamata.
2. b) Faɗakarwa
game da abokan zaman tare.
3. c) Gargaɗi
ga riƙe halayen kirki da gaskiya da kunya da haƙuri da sauransu.
4. d) Koyar
da ladabin zance da kyautata sutura don ta kasance daidai da al’adar al’umma.
5. e) Tsara
rayuwar mutum ta yadda zai sami damar amfanuwar al’ummarsa.
6. f)
Kyautata kyawawan al’adun al’umma da inganta su tare kuma da bayyana munanan
al’adu domin a guje su.
7. g)
Kyautata hankalin mutum don samun rayuwa tagari.
8. h) Kawar
da kai ga abin mutane da kare ɗiyauci da riƙon amana.
3.0 Dabarun
Tarbiyyar Hausawa
Kunya : A magana, kunya wata kalma ce ko kalmomi da ake furtawa masu nauyi ga al’adar rayuwa da zamantakewa da mutuncin ɗan Adam, kasancewarsa mutum irin mutane. Ta fuskar aiki kuwa, kunya wani aiki ne da ake aikatawa da gaɓoɓi wanda al’ada ke hange da cikas da munin da zai ƙarasar ga ma’abota hankali ga mai aikata aikin domin tsira da mutuncinsu. (Bunza 2006:249-250). Idan an ce ana jin nauyin mutum ko ana jin kunyarsa, to ana girmama shi kenan. Wato idan mutum zai aikata wani abu ya duba abin da zai je ya dawo ta ɓangaren kansa da tsakaninsa da jama’a. Kunya na hana aikata ayyuka munana domin kare mutunci. Tun fil azal Bahaushe mutum ne mai ɗabi’ar kunya a rayuwarsa, saboda haka yake ƙoƙarin cusa wannan al’ada ga ‘ya’yansa. Saboda kunya, Bahaushe bai iya kiran sunan ɗansa na fari musamman a ɓangaren mata. Mace ba ta kiran sunan mijinta kai tsaye sai dai da wani sunan na daban. Haka ma budurwa tana kunyar a ji saurayinta balle ta faɗi sunansa a gidansu, ko ta kai wa iyayensa ziyara. Haka dai wannan kyakkyawar al’ada take tafiya a rayuwar Hausawa.
Kare ‘Diyauci : Bahaushe bai san karuwanci ba balle masu yin sa.’Ya’yan Hausawa mata tun suna ƙanana akan yi ƙoƙarin cusa musu al’adar nisantar maza da kuma illar da ke tattare da kusantar su. Don haka ne ko a wasannin dandali ƙungiyar mata daban na maza ma daban. Wannan tarbiyyar ba ta tsaya a nan kawai ba, hatta idan aka yi wa mace aure akan kai ta da wani farin ƙyalle da ake kira bante wanda za ta fara kwanciya da shi. Ta wannan ƙyalle ne za a gane ta kare ɗiyaucinta ko akasin haka. Idan aka yi nasara ta kai bante wato ba ta taɓa sanin ɗa namiji ba sai ga mijinta na aure, iyayenta kan yi murna da kasancewa masu alfahari da ita. Idan kuwa aka sami akasin haka, to yarinyar ta bar abin faɗe da zubar da mutuncin iyayenta. Wannan al’ada ya yi tasiri ainun ga ‘yan mata wajen ganin ba su zubar da mutuncin gidansu ba, da kuma barin abin faɗe a baya.
Gaskiya Da Riƙon Amana : Hausawa mutane ne da suke da kyakkyawar tarbiyya da himmatuwa zuwa ga ɗaukar halaye nagari irin su gaskiya da riƙon amana. Babu yaudara ko cin amana a rayuwar Hausawa. Wato mutane ne masu karimci da shimfiɗar fuska wadda aka ce ta fi shimfiɗar tabarma. Duk wanda ya haɗa hulɗa ta kasuwanci ko na zamantakewa da Hausawa zai tabbatar da cewa Hausawa mutane ne masu gaskiya. Wannan ne ya samar wa Hausawa kyakkyawar dangantaka ta kasuwanci tsakaninsu da al’ummomi daban-daban na cikin gida da ma sauran ƙasashen duniya.
Zumunta : Ƙoƙarin kusantar ‘yan uwa da abokan arziki da ziyartar su a kai a kai, ita ce zumunta. (Alhassan da wasu 1982) Tarbiyyar Hausawa tana jaddada ziyarce-zuyarce tsakanin ‘yan uwa da abokan arziki. A tsarin rayuwar Bahaushe, maƙwabci tamkar ɗan‘uwa ne, domin idan aka wayi gari sai an gaisa kafin kowa ya fita tasa harka. Don haka, idan wani abin farin ciki ko akasinsa ya samu maƙwabcin mutum, za a zauna a taya shi murna ko juyayi idan mara kyau ne. Haka ma duk wani abu da ya samu ‘yan uwa na murna kamar haihuwa ko aure akan taru domin a sada zumunci kuma a ƙarfafa shi. Har ta kai ga Bahaushe kan ɗauki ɗansa ya ba ɗan‘uwansa riƙo domin ƙarfafa zumuntar da ke tsakaninsu.
Mallakar Sana’a : Al’ummar Hausawa tun asali al’umma ce wadda ta dogara da kanta wajen samar da hanyoyin tattalin arzikinta. Ta haka ne ya zama a kowane gidan Bahaushe za ka tarar yana da sana’o’in da yake aiwatarwa. Don haka, yakan yi ƙoƙarin gina yaransa bisa wannan sana’a domin su girma da ita, su kuma kauce wa zaman kashe wando da sa ido da yawon gararanba a cikin unguwa.
4.0 Illolin
Zamani A Kan Tarbiyyar Hausawa
Kallace-kallacen finafinan Turawa da Indiya abu ne da ya zama ruwan dare a ƙasar Hausa. Finafinan sun sami karɓuwa sosai a ƙasar Hausa, inda ake kallonsu a wurare daban-daban da suka haɗa da gidajen kwana da na silma da gidan kulab da manyan makarantun boko da ire-irensu da dama. Abin ban haushi ga kallace-kallacen irin waɗannan finafinai shi ne, babu wani koyarwa ko tarbiyya da ake samu a ciki wadda ta dace da al’adar Hausawa, face fajirci da lalaci. Alal misali, idan ka dubi finafinan Indiya za ka tarar babu wani abu mai kama da tarbiyyar Hausawa sai faɗace-faɗace na gaira ba dalili da soyayya irin wadda ta saɓa wa koyarwar Bahaushe. Za ka tarar da saurayi da budurwa suna rawa da waƙa suna rungume-rungume da sumbuitan junansu. A ɓangaren finafinan Turawa kuwa abin ba a cewa komai, domin lalacin bai tsaya ga runguma da sumbuita ba, har tsiraici akan nuna zahiran ana lalata tsakanin mace da namiji. An wayi gari al’ummar Hausawa sun raja’a wajen kallon ire-iren waɗannan finafinai na batsa musamman matasa maza da mata. Babu abin da matasa ke yi yanzu sai ƙoƙarin kwaikwayon irin waɗannan miyagun ɗabi’u. Budurwa za ta iya sheƙowa ta rungume saurayinta ta sumbace shi a gaban jama’a tamkar dai yadda Taurawa da Indiya ke yi. Wasu matasan ma har kwaikwayon nau’in lalatan da suka kalla suke yi ga ‘yan matansu domin su sami abin ƙararwa ga sauran abokai.
4.2 Finafinan Hausa
Finafinan Hausa waɗanda aka fi sani da finafinan kanawa sun fara samuwa ne a wajajen shekarar 1980. Finafinan sun ci gaba da bunƙasa da samun karɓuwa ga jama’a har zuwa yau. Da farko mutanen da ke cikin harkar suna da tunanin yaɗa al’adar Hausa da kuma tunanin gobe. Saboda haka, a finafinansu na wannan lokaci sukan yi ƙoƙarin kwatanta al’ada da tarbiyyar Bahaushe. Alal misali, idan aka ɗauki fim ɗin “Ki Yarda Da Ni” za a ga cewa an yi ƙoƙarin kauce wa wasu abubuwa da suka saɓa wa al’ada, hasali ma an nuna faɗakarwa ta zamantakewar aure tsakanin kishiyoyi. Hatta waƙar da aka yi babu rawa a cikinta ballantana a sanya matsattsun kaya irin na Turawa. Da tafiya ta yi tafiya sai finafinan suka fara ɗaukar sabon salo na amfani da wasu ababe da suka yi hannun riga da al’adar Hausawa. Domin tun daga suturar da ake ba ‘yan mata suna sawa, da irin rawar da ake yi, babu maganar tarbiyya a ciki balle a tarbiyyantar. Idan aka dubi finafinai irin su Guɗa da Gabas da ‘Yan Hutu da sauransu da dama, babu komai a ciki sai raye-raye irin na fitsaranci da rashin kunya. An wayi gari yara ƙanana ba su da aiki sai waƙe-waƙen da suka kalla a finafinai.’Yan mata kuwa sai ƙoƙarin sanya matsattsun kaya suke yi domin su burge samarinsu, kamar dai yadda ake yi a cikin finafinan. Haka ma sau da yawa a finafinan za ka tarar an yi ƙungiyoyin ‘yan daba waɗanda ba su da mafari a fim ɗin sai kawai don a nuna yadda ake shaye-shaye da ta’addanci.
4.3 Sufurin Miyagun Ƙwayoyi
Sufurin miyagun ƙwayoyi da tabar wuiwui ya zama ruwan dare a kusan kowane saƙo na ƙasar Hausa, ba birni ba ƙauye. A wasu wurare na ƙasar Hausa ma har shuka irin wannan taba ake yi ana sayarwa a wurare daban-daban na ƙasar Hausa. A sakamakon haka, an wayi gari matasa sun tsunduma a rijiyar shaye-shayen ƙwayoyi da barasa da nau’o’in ganyayen taba kamar wui-wui da maganin tarin yara (Tutolin), har ma da hodar Iblis. Matasa har ƙungiyoyi suke haɗawa na shaye-shayen taba da ƙwayoyi wanda kan kai su ga fita cikin hayyacinsu su riƙa aikata ayyuka na assha da ta’addanci a cikin al’umma. A wani lokaci har ƙwayoyin da ake ba dabbobi suke sha don kawai a ƙara lalacewa. Irin ɓarnar da ƙwaya da taba suka yi wa matasa a ƙasar Hausa Allah kawai ya san iyakarta. Da yawa matasa sun sami taɓuwar ƙwaƙwalwa, wasu sun zama ‘yan ta’adda a cikin gari, wasu sun gagari iyaye, ƙarewar ƙarau, wasu ma sun faɗa harkar fashi da makami da sufurin miyagun ƙwayoyi. A ɓangaren mata kuwa, nan ma ba baya ba, domin a maimakon tsoratarwa da tarbiyar Hausawa ke yi na mata su riƙa nisantar maza domin kare ɗiyaucinsu. Sai ga shi yanzu an wayi gari an samar da ƙwayoyi da allurai na hana mata ɗaukar ciki, wato dai an ba su tiketin zuwa iskanci domin sun san ba za su ɗauki ciki ba balle a yi abin kunya. Abin bai tsaya ga ‘yan mata kawai ba, hatta matan aure a yanzu suna shan waɗannan ƙwayoyi da allurai domin kada su haihu da wuri ko domin taƙaita haihuwa wai don kada iyali su yi yawa a sha wahalar rayuwa.
4.4 Littattafan Soyayya
Littafan adabin kasuwar Kano waɗanda aka fi sani da littafan soyayya, sun fara samuwa ne a wajajen shekarar 1984 a lokacin da kamfanonin wallafa irin su NNPC da NORLA da sauransu, suka daina ayyukan wallafe-wallafen littattafan da suka saba samarwa. Wannan ne ya ba da kafar hudowar littattafan soyayya da kuma samun karɓuwa ga jama’a. Waɗannan littattafai sun taka rawar gani wajen yin tasiri a rayuwar Hausawa musamman matasa maza da mata. Matasa sun zurfafa wajen karance-karancen waɗannan littattafai ba dare ba rana. Iyaye sun kasa more wa ‘ya’yansu, kunyar iyaye da magabata ta kawu ga idon matasa, sun daina tunanin komai sai soyayya irin ta littafi. Sau da yawa za ka cimma saurayi da budurwa sun kasa samun sukuni ko ma su kwanta rashin lafiya wai saboda soyayya. Babi komai na inganta tarbiyyar Hausawa a cikin littafan sai soyayya irin wadda ta saɓa wa al’adar Hausawa. Haka ma karatun littafan ya taimaka wajen hinjirewar ‘ya’yan Hausawa na dole a bari su zaɓar wa kansu wanda za su aura ko kuma su bi duniya.
4.5 Karatun Boko
Karatun boko na daga cikin abubuwan da suka taka rawa wajen taɓarɓarewar tarbiyyar Hausawa. Kamar yadda aka sani cewa, makarantun boko wuri ne da ke haɗa ɗalibai iri daban-daban da ma ƙabilu mabambanta, don haka ana iya samun ɗalibai nagari da akasinsu su haɗu wuri ɗaya suna cuɗanya tare a koyaushe. Sau da yawa akan tura yara makaranta da kyakkyawar tarbiyya sai a wayi gari labarin ya sauya a sakamakon haɗuwarsu da ɓata-gari. Daman Hausawa na cewa, “zama da maɗaukin kanwa....”. Shaye-shaye da haɗa ƙungiyoyin asirai sun zama ruwan dare a makarantunmu na boko musamman makarantun gaba da sakandare. Haka ma sau da yawa akan koyo mummunar ɗabi’ar nan ta namiji ya sadu da namiji wato “luwaɗi”. A ɓangaren mata kuwa, abin sai dai a shafa fatiha. Domin kuwa har soyayya akan ƙulla tsakanin mace da mace tare da mummunar ɗabi’ar nan ta saduwa da junansu wato “maɗigo”. Ko kuma a iske mace tana amfani da kyandir a gabanta tamkar namiji ne ke tarawa da ita.
Bayan wannan, sau da yawa wasu ‘yan maata idan sun kammala karatun sakandare ko Jami’a, za a cimma tarbiyyarsu ta ƙaranta, ba sauran kunya, ba ladabi da biyayya ga iyaye, wai kan mage ya waye. Hasali ma wata za ta fara kallon iyayenta a matsayin gidadawa musamman idan ba su yi karatun bokon ba. Don haka ba a sa ta dole sai abin da ta ga dama. Sau da yawa akan sami matar aure ta ƙulla alaƙa mai ƙarfi da wani saurayi wai shi ke koya mata darasi da sauran ayyukan da suka shafi karatu. Su kuwa yara maza har wasu sunaye suke yi wa iyayensu musamman uba. Ba su iya faɗar Baba ko Abba sai dai a ce, “old man ko boss”. A wani lokaci ma idan mahaifi na da kuɗi bai bari a hole, akan riƙa kiransa mai gadi, wato mai gadin dukiya, wai an yi karatun boko an waye.
4.6 Kafofin Sadarwa na Zamani
Hanyoyin sadarwa na zamani musamman irin su yanar gizo (internet) da wayar salula (handset) sun taimaka matuƙa wajen samar da ci gaba a rayuwar Hausawa. A maimakon hanyar sadarwa ta wasiƙa da sauran hanyoyi na gargajiya da ake amfani da su a da domin sadarwa tsakanin al’umma wanda kan ɗauki lokaci kafin saƙo ya kammala, a yanzu an samar da sauƙaƙan hanyoyi na waɗanda ke gudana cikin lokaci ƙanƙane a duk faɗin duniya, wato ta amfani da yanar gizo da wayar salula da sauransu. Sai dai kuma ba a nan gizo ke saƙa ba, domin Bature yana cewa, duk wani abu mai amfani yana da rashin amfani. Haka lamarin yake a ɓangaren waɗannan hanyoyi na sadarwa na zamani, domin kuwa suna ɗauke da munanan abubuwa da suka yi tasiri ainun zuwa ga lalacewar tarbiyyar Hausawa. Alal misali, sau da yawa za a iske ba komai a wayar wasu sai hotuna da finafinan batsa da waƙe-waƙe marasa ma’ana. A ɓangaren yanar gizo kuwa, nan ma sai dai a shafa fatiha a watse. Domin akwai wasu tashoshi da mutum zai kamo waɗanda babu komai face finafinan batsa. Sai a iske namiji ko mace sun shiga yanar gizo, a maimakon su binciko abin da zai amfani rayuwarsu ko karatunsu ko abin da duniya take ciki, sai kawai su shiga shafin da za su kamo finafinan batsa su yi ta kallo sai sun raba dare ko ma sai zuwa wayewar gari. Haka ma akwai wani shafi da mutum zai shiga a yanar gizo kamar irin su “Tuiter da Facebook” waɗanda mutum zai iya ƙulla dangantaka da wasu matattakin banza da ke a faɗin duniya ba tare da sanin matsayinsu ba, inda a wani lokaci ma har ƙulla abotaka ake yi tsakanin mace da namiji ba tare da an san juna ko an taɓa haɗuwa ba. Da irin wannan kallace-kallacen banza ne har wasu ɗalibai kan manta da abin da aka turo su yi makaranta har a kai ga korarsu daga makarantar domin kwalliya ta kasa biyan kuɗin sabulu.
4.7 Siyasar Zamani
Siyasa tsarin mulki ne da Turawa suka ɓullo da shi domin ci gaban al’umma da ma ƙasarsu baki ɗaya. Amma sai aka wayi gari abin ba haka yake a ƙasar Hausa ba. A maimakon kyautata wa al’umma da samar da ci gaban ƙasa, sai abin ya sauya ya koma cin amanar ƙasa da danne haƙƙoƙin jama’ar cikinta. Siyasa a ƙasar Hausa ta haddasa mummunar adawa tsakanin jama’a. Sau da yawa za a iske babu ga-maciji tsakanin ɗan’uwa da ɗan’uwa, zumunci ya yanke saboda adawar siyasa. An wayi gari manyan ‘yan siyasa sun yi ƙoƙrin jawo hankalin matasa suna amfani da su wajen bangar siyasa. Suna sawo miyagun ƙwayoyi da tabar wuiwui tare da haɗawa da kuɗin da ba su taka kara sun karya ba suna ba matasa suna sha domin hankalinsu ya gushe su ji daɗin yin ta’asa ga abokan hamayya da sauran jama’ar gari. Matasa kan kafa ƙungiyoyi masu zaman kansu a ƙarƙashin wani babban ɗan siyasa, ba saye ba sayarwa, babu karatun boko balle na Arabiyya, sai zaman shaye-shaye da sa ido ga kayan mutane. Iyaye sun kasa sa ‘ya’yansu ido balle su more musu, duk dai da sunan siyasa. Su kuwa ‘yan siyasar, saboda son mulki da kwaɗayin abin duniya sun tsunduma dumu-dumu cikin harkar tsafi. Sau da yawa akan kama su da wasu sassan jikin mutane waɗanda za a yi musu tsafi da shi domin kawai buƙatarsu ta neman mulki ta biya.
4.8 Kallon Ƙwallo
Kallace-kallacen ƙwallayen Turawa abu ne da ya yi ƙamari a duk faɗin ƙasar Hausa birni da ƙauye. Kusan kowane saƙo na ƙasar Hausa ka shiga ba ka rasa gidan kallon ƙwallo. Abin ba manya ba yara, kowa na da nasa kulab. Sau da yawa za ka iske mutum ya bar sana’arsa ya wuce zuwa kallon ƙwallo. Sai iske gardama ya kaure tsakanin ɗa da mahaifi domin kowa da nasa jarumi. Ƙarin abin haushi ga wannan lamari shi ne, matasa sun ɗauki mummunar ɗabi’ar sanya wa kansu sunayen ‘yan ƙwallo. Sau da yawa za ka iske sunan mutum na yanka ko na laƙabi ya ɓace sai dai sunan wani ɗan ƙwallo. Sunayen ‘yan ƙwallon Turawa irin su Messi da Ronaldo da Henry da Baggio da Kaka da sauransu, sun zama ruwan dare ga matasa. Yara ƙanana ma ba a bar su a baya ba, sai ka iske yaro ɗan ƙasa da shekara goma sha biyu ba ya da aiki sai zuwa gidan ƙwallo. Iyayensa ba su ganinsa balle su more masa. Gardamar ƙwallo da faɗace-faɗace sun zama ruwan sha ga matasa.
5.0 Mafita
- Dole iyaye su
sake ɗaura ɗamara wajen ci gaba da yi wa ‘ya’yansu tarbiyya ta gari, da ɗora
su bisa sahihiyar hanya komai ɗacinta a gare su, matuƙar dai za ta kasance
mai alfanu ga rayuwarsu da ma jama’a baki ɗaya.
- Haka ma dole
malaman addini su ƙara zage dantse su miƙe wajen ci gaba da wa’azi da faɗakarwa
musamman ga matasa waɗanda su ne abin ya fi shafuwa. Addinin musulunci da
koyarwarsa hanya ce da ta ƙunshi cikakkiyar koyar da tarbiyya. Duk mutumin
da ya rabauta da addini zai kasance mai ɗa’a da biyayya ga haƙƙoƙin Allah
da na jama’arsa. Don haka yana da kyau a cusa wa mutane son addininsu da ƙoƙarin
tsare iyakokinsa domin samun sakamako nagari a rayuwar yau da kuma gobe.
- Gwamnati kuwa
tana da babbar rawar da za ta iya takawa dangane da wannan matsala. Kamata
ya yi ta yi amfani da kafafen yaɗa labarai domin a riƙa watsa wa’azoji da
faɗakarwar da malamai ke yi domin su isa a kowane sashe da ake tunanin zai
sadu da jama’a. Haka kuma ta yi ƙoƙarin magance shigowa da miyagun ƙwayoyi
da allurorin da ‘yan mata ke amfani da su domin kauce wa ɗaukar cikin
banza, da hana shuka ganyayen tabar wuiwui da shigowa da nau’o’in barasa.
Har wa yau, samar da aikin yi ga jama’a da kuma ɗaukar nauyin wasu zuwa
makaranta domin samun ilimi. Yin haka zai rage wasu miyagun halaye da zaman
kashe wando da yawon gararanba a cikin gari. Har ila yau, gwamnati ta sa
baki ga finafinan da ake yi a gida da kuma waɗanda ake shigowa da su daga
waje domin tabbatar da sahihancinsu na dacewarsu da al’adar Hausawa da
koyarwar addini.
- A ɓangaren siyasa kuwa, nan ma dole gwamnati ta sa ido na ganin an daina amfani da matasa wajen bangar siyasa, da ɗaure musu gindi wajen yin ta’addanci da cin mutuncin jama’a na ba gaira ba dalili.
Kammalawa
Videos: Technology, Economy, and Society, Jami’ar Bayero Kano.
Bunza, A.M. (2006) Gadon feɗe al’ada. Tiwal Nigeria limited, Surulere Lagos.
Chamo, I.Y. (2004) “Tasirin al’adun Turawa a cikin finafinan Hausa” a cikin Hausa Home
Videos: Technology, Economy, and Society, Jami’ar Bayero, Kano.
C.N.H.N.(1981) Rayuwar Hausawa. Littafin da Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar
Bayero Kano ta wallafa.
Dogondaji, U.M. (2004)“Tasirin tatsuniya ga yaran Hausawa” Kundin digirin farko Jami’ar
Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato.
Fagge, A.M. (2004) Economy and society in Hausa cultural productions: Implication of
Hausa Home Videos of Social Change, a cikin Hausa Home Videos Jami’ar Bayero, Kano.
Gusau, S.M. (1999) “Tarbiyya a Idon Bahaushe”, a cikin Journal of Hausa Studies, Jami’ar
Bayero, Kano.
Ka’oje, U.I. (2006) “Tarbiyya a Ƙagaggun Labaran Hausa : Nazari kan ‘Ya’yan Hutu na
Malama Bilkisu Funtuwa” Kundin digirin farko, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo Sakkwato.
Malumfashi I.A (2004) Currents Trends in Hausa Fiction:The Emergence of the Kano Market
Litereture. A cikin ‘Dunɗaye Journal of Hausa Studies, Volume 1 No 1 UDUS.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.